Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 24

Bakin ruhi complete - Chapter 24

Bakin ruhi complete Chapter 24: Bakin ruhi complete Chapter 24. "Me kike buƙata baiwar Allah?" Da sauri na ɗago na kalle shi tare da ce masa aiki nake nema…

3,330 words

"Me kike buƙata baiwar Allah?" Da sauri na ɗago na kalle shi tare da ce masa aiki nake nema yalaɓai,ban san me ya gani a tattare da ni ba da har yayi saurin bani aiki a kamfanin.Ciki muka shiga sai ya fara gabatar da ni ga sauran ma'aikata kafin ya kai ni wani wajen,"aikinki shi ne kula da Camera tsaro ki lura ki ajiye hankali ki dinga duba masu zirga-zirga a duk wani sashe"

Godiya na yi masa,tun a lokacin kuma na soma yin aikin nawa wanda kuma ba ni ɗaya ba ce har da wani matashi .Bayan fitar shugaba,sai ya dube ni da kyau ya wani taɓe baki kafin yayi mini wata magana mai kamar hannunka mai sanda ya ce "ki kiyaye aikinki kar ki yi abin da ba a saka ki ba,komai yana da ƙa'ida ki karanta wannan kundin domin sanin lokutan da ake kashe wasu camerori,sannan duk ƙarshen mako za ki fitar da report "

Duk da na ga kamar bai da kirki haka na karɓi kundin na soma karantawa, jefi-jefi kuma ina tambayarsa ya na bani amsa a haka muka yi aikin .Da lokacin tashi yayi sai na fita kamar kowa sai dai banda wurin zuwa ,sai kawai na yi kwanciyata nan bakin ƙofa cikin rumfa.Tsabar yadda na gaji sosai yasa na yi bacci sosai amma duk da haka sai na dinga jin motsi daga can cikin alhalin babu kowa hatta mai gadi iya waje ne kawai yake zagayawa.Washegari tun kiran sallar asuba na yi wanka a banɗakin da ke nan kusan kamfanin,haka na yi sallah sannan na zauna har lokacin aiki yayi na shiga daga ciki .

A cikin Camera sai na lura an kashe ɗaya,ban yi nauyin baki ba na tambayi abokin aikina "me yasa ita wannan take a kashe?"

"Sanoda haka mai kamfanin ya ce,a dinga kashe ta kullum in an sauka daga aiki " ya bani amsa,haka kawai na ji hankalina bai kwanta ba amma dole na yi shiru ya bani ƙosai na ci na sha ruwa.Muna dab da sauka aka kira shi an kai matarsa asibiti,da zai fita sai da ya jadadda min na kashe camerar nan kafin na fita na kuwa amsa da toh duk da cewa a ƙasan zuciyata ƙarya nake yi.

Yau ma da muka tashi bakin kamfani na kwanta,wuraren ƙarfe ukun dare kuma na tashi na yi wanka na wanke kayan jikina.Tsaye na yi don su bushe,sai dai irin yadda na ji ana motsi daga ciki yasa na je bakin ƙofar na kara kunnena.Sautin kiɗa na ji alhalin babu kowa ciki,gari na yin haske mai gadi ya buɗe ko ina lokacin fara aikin ma bai yi ba iya masu shara da guga ne suka soma amma don san sani abin da ake ɓoyo a kamfanin na yi sauri na shige.

Ɓangaren da nake aiki na shiga na yi tsaye gaban Camera wacce ake cewa a kashe,haka na yi ta kallon abubuwan da ke gudana har dare yayi sai komai yayi tsit har zan gusa sai kuma na soma ganin mutane na shigowa ta wata ƙofa da ban san da ita ba.A cikin mutanen wasu na san su ma'aikatan nan ne,shugaban kamfanin shi da kansa ya shigo ya zauna yana kallon wasu ƴan mata biyu da suke a ɗaure.A gabana yasa wuƙa ya yanka su jininsu kuma ya tara wani ƙaton kofi na zinare ya shiga ciki sai kuma suka fara yin shagali shi da sauran mutane suna shan jinin mutane.Hannuna na rawa na soma ƙoƙarin kashe Camera amma ta ƙi mutuwa haka ta ci gaba da nuno min abubuwan tashin hankali yadda ,daga bayana na ji motsi kafin na juya na ga an ziro hannu an kashe Camera sai a lokacin kuma ta mutu.Jikina ne ya ɗau rawa nan take kuma na soma bai wa shugaba haƙuri,bai ce komai ba ya fice.Ganin haka sai ni ma na fito domin guduwa,sai dai da na fito sai rasa wacce ƙofa ce zan bi na fice saboda ƙofofin da ke gabana sun fi ɗari a jere ras.

Kukan doki na soma ji tare da ƙarar takun sawunsa,can kuma na ji saniya da jaki su ma sun ɗauki nasu kafin na farga na tsinci kaina a wannan ɗakin dai da na ga Camera ta naɗo bayanansa sai yanzu kuma na lura ashe gidan ƙasa ne.

Kamar yadda na ga ƴan matan nan biyu a ɗaure,to ni ma haka na tsinci kaina.Ina nan cikin zullumi sai ga gangar jikin shugaba ta fara shigowa amma babu kai a samanta,ina shirin rumtse ido sai na ga ƙaton kan nasa a tsaye a gabana jini na ta zuba na buɗe baki da niyyar ƙurma ihu sai na ji wani abu mai kamar ƙodago ya cika bakina sai kuma na koma zarar ido.

"Kallo ɗaya na yi miki na san da aiko ki aka yi ki leƙi asirina,sai dai ki sani kamar yadda sauran ke zuwa amma ba za su koma ba ke ma haka" shugaban ya faɗa yana mai haɗe kansa da gangar jikinsa wuri guda kafin ya kama rigata da niyyar cire ta sai kuma ya ja da mugun sauri yana zaro ido,"tambarin BAƘIN RUHI? wace ce ke?" yayi min tambayar tare da cire min abin da yasa a bakina.

Ganin yadda ya firgita kawai sai na basa amsa kai tsaye da "jikar Nalado ce" ina furta haka ya soma bani haƙuri,amma ban san inda ƙarfin halin cewa "dole sai an hukunta ka a bisa azabtar da ni da ka yi" ya zo min ba.

Ina gama furta haka sai na ga hoton Kakana wato mahaifin iyayenmu maza ya bayyana a bangon ɗakin yana mai yin wani murmushi ya ce "wannan shi ne ainahin jinina Haule madala da kika amince za ki yi wa baƙin ruhi hidima,barin gida ba zai canza komai ba sai ma sake ɗaga martabarmu da za ki yi .Ki je ina alfahari da ke Hahaha !" yayi wata dariya bakinsa na fitar da wani feshin wutar da ya dabaibaye ni haɗi da cillo ni kuma a wata MAKARANTAR MATSAFA (MRS SADAUKI) .Hum ! A wannan makarantar ne na ga mutane iri-iri,kuma abin mamaki sun san da zuwana kamar yadda suka san wace ce ni.

Tarba ta musamman na samu,yayin da kuma suka dinga bani tarihin yadda Kakana Nalado ke da matuƙar jajircewa akan duk abin da yasa a gaba,da kuma faɗi tashin da yayi wurin ganin BAƘIN RUHI ya bazama a ko ina na duniya.

Cike da mamaki na ce "kenan Kakana ne baƙin ruhi?" na yi tambayar ne ga headmaster amma sai bai ban amsa ba sai cewa yayi "zo na nuna miki ɗakin baccinki,ki kwanta da wuri saboda zuwa ƙarfe biyun dare akwai darasi" Ban ce masa komai ba ya kai ni bakin ƙofar ɗakina sannan yayi tafiyarsa,na bi bayansa da kallo kafin na tura ƙofar na shiga sai na tarar da wata budurwa a zaune ta huda maƙoshin ɓera tana matse masa ciki yayin da jininsa kuma ke zuba cikin wani ɗan ƙaramin madubi mai kamar plate.

"Me kike yi haka?" na tambaye ta,ba ta ɗago ba ballantana ta bani amsa har sai da ta gama tatse dukkan jininsa sannan ta ɗauka ta shanye tare da lashe madubin sai a lokacin kuma ta ɗago ta dube ni.Ta washe bakinta wanda yake kamar na zombie kafin ta ce "ina son kai wa Kakana ziyara ne a can duniyar Ruhaniya ko za ki yi min rakiya?"

"Haule? Haule?" muryar Hajiya ta katse labarin da nake bai wa su Aliya ,na amsa da sauri tare da fita.A falo na tarar da ita a zaune tana duba wasu tsadadun kaya,ta ɗan washe baki ta ce "zo ki duba min a cikin waɗannan less ɗin wanne ya fi kyau"

Na matsa tare da soma dubawa can na ɗauki wani launin ja na ce "hajiya wannan zai fi yi miki kyau"

Ta ɗan ɓata rai kafin ta ce "ba fa ni zan saka ba,Ikilima ce nake son ɗinka ma shi saboda hotunan nan da ake yi na ango da amarya tun da na ga alamu shi Maheer ɗin bai ma fara shiri ba sai ka ce bai san wannan juma'ar za a ɗaura auren ba"

Ji na yi tamkar ta buga min guduma a kai,murya na ɗan rawa na ce "wai Alhaji ne zai yi aure amma ba mu sani ba?"

"To auren ne ya zo ta wata siga ,in ba haka aka yi ba ina ganin haka Maheer zai zauna a tuzurunsa bai aura ba,amma dai yanzu alhamdullah in sha Allah wannan juma'ar za a ɗaura masa aure shi da Ikilima"

Ban san lokacin da na saki less ɗin hannuna ba,na juya da niyyar tafiya na ji jiri ya ɗibe ni na yi baya zan faɗi amma na ji an tallabo ni tare kuma da cewa "Mama aure kuma?" muryarsa tasa na fahimci shi ne,sannan ƙamshinsa duk ya rufe min hanci. "Ita kuma wannan meke damunta ko cutar jinnun ita ma gare ta?" Hajiya ta tambaya,Maheer ya bata amsa yana mai cewa "ban sani ba dai sai na duba ta yanzu" yayi furicin ne yana mai riƙe kafaɗata da kuma ƙafafuna ya tallabe tare da soma tafiya da ni ya fara taka step ɗin sashensa,ina jin muryar Hajiya na cewa "mene ne kuma abin sai ka kai ta can sashenka ba za ka duba ta ba a nan?" bai kula ta ba,haka ni kuma ban buɗe idona ba don har yanzu maganar Hajiya ta ƙi barin jaririya ƙwaƙwalwata sukuni ga zuciyata sai lugude take yi da ƙunci.

Ban san lokacin da ya shigar da mu ɗakinsa ba sai da na ji taushin katifarsa,na ware ido sai na ga yayi min rumfa yana kallona kamar zai cinye ni.'Aurensa da Ikilima wannan juma'ar' zuciyata ta raya min nan take na ƙara jin haushinsa ban san lokacin da na fashe da kuka ba tare da sa dukkan hannuwana na ture ƙirjinsa amma ko gezau bai yi ba,kawai sai na soma dukansa.

"Keee!" ya daka min tsawa,na tsaya cak da abin da nake ina mai ƙanƙame jikina."Ki nutsu na duba ki in kuma kukan za ki yi ai sai ki je ki yi" yayi maganar yana mai jan rigata sama da sauri na mayar da kayata yadda take ina hararensa tare da yunƙurin tashi .

"Sahut!" ya furta da wani mugun sauri na koma na lafe tare da rumtse ido don ban ƙaunar ganin shegen macijin nan nasa,ina jin lokacin da ya ɗage rigata sama ya fara shafar marata yana wani furici cikin sauti ƙasa-ƙasa,nan take na soma jin wani feeling na bijiro min ban shirya ba na kai hannuna na ɗora kan nasa ina mai kuma buɗe idona sai kuma suka sauka cikin nasa,a hankali ya soma yin sama har ya iso daidai fuskata "kishina kike?" yayi mini tambayar ba tare da kuma ya bani damar amsawa ba ya dire bakinsa cikin nawa yana sumbatata yana kuma shafar cikina da sauri na ƙanƙame shi ina jin wani yanayi.....

🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟

*_GYARA SHINE MACE_*

*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻

*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*

Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje

Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir

Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi

Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare

Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,

Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi

*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

*Wannan page naki ne Maman Ayman uwar ɗakin Masheer 😂* 28

Tamkar yadda ake shayar da yaro haka Maheer ke shayar da ni yawunsa,ya sa tsinin hancinsa ya toshe nawa numfashi ma dakyar nake jansa ina sauke shi cikin bakinsa.Wasu irin abubuwa ne nake ji da ko kaɗan ban taɓa tunanin akwai wanzuwarsu a wannan duniyar ba.Banda hawaye babu abin da nake iya yi da kaina,sosai duk illahirin jikina ya saki sai shafar cikina yake yi wanda ban san dalilinsa na yin haka ba da na ji ya wuce a inda bai kamata ba sai a lokacin na dawo hayyacina na tuna a inda nake,da kuma wane ne nake tare da shi.

Sosai hankalina ya tashi,duk wata sauran nutsuwata kuma ta tarwatse.Kaina soma jujuyawa ina son cire bakina daga nasa ga kuma hannuna da ke rawa yana son janye nasa sai dai ko ɗaya babu wanda na ci nasarar yi saboda a wannan matakin Maheer ya saka ƙarfinsa yana yin wasa da sassan jikina yadda ya so,duk abin da yake yi kuma cikin ficewar hayyaci ne yake yinsa don ya rasa controling kwanyarsa.

Daga can ƙofa kuwa muryar Hajiya ce ke tashi haɗi da jijiga ƙofar tana ikirarin ya buɗe ƙofar uwar mece ce yake yi min,wane irin bada magani ne da har yanzu bai bani na fito ba.

Furicin Hajiya shi ke ƙara ƙaimin farashin tsorona da tashin hankali da ke cikin tunkarata. Cikin son nemawa kaina mafita na kafa haƙorana a kan ƙirjinsa na kantsara masa cizo da haƙorana masu kaifi,sai a lokacin Maheer yayi baya ya koma gefe yana mai dafe wurin,na yunƙura zan tashi ya wani fizgo ni na faɗo ƙirjinsa .Ƙafafuwansa yasa yayi min zobe da su tare da yin wani furucin da ya saɓule duk suturun jikinmu ina ganin haka casbin hankalina da kuma na numfashina ya katse .

Maheer kuwa duk da ya lura Haule ta bar wannan duniyar na wuccin gadi bai hana shi sarrafa gangar jikinta ba.Haɗuwar jikinsu a haka shi ya ƙara dagula masa lissafi,ba don ya san cewa dole sai in Haule na cikin ganiyar hankalinta zai yi sex da ita ba to da babu shakka babu abin da zai hana shi ya kusance ta duk da abubuwan da yayi mata a yanzun ma kusan kamar sun yi mu'amalar ne.

Surutun Hajiya da hargowarta sam ba su dame shi ba,don ya san ko Sarkin matsafa ya zo nan babu wanda zai iya buɗe ƙofar in ba shi ba.Wata irin wawuyar runguma ya yi wa Haule kamar zai mayar da ita ciki,yayin da yake jin hadarin sonta na ƙara gangamuwa a birnin zuciyarsa suna yi masa yayyafin ƙaunarta.

Wani irin tausayinta ne ya ji bayan ya gama bidirinsa,duk ya ɓata mata jiki da kuma shimfiɗar da suke a kai.Kamar wata baby haka ya ɗauke ta ya kai su toilet ya tsarkake musu jikinsu sannan ya canza zanen gado.Maimakon ya mayar mata da kayanta kawai sai ya zaɓo wasu kayansa Adidas ya saka mata,hatta bra ɗinta bai mayar mata ba,sai da ya busar da gashin kanta sannan ya soma ƙoƙarin dawo da ita a duniya sai da ya ci wuya sannan ya fizgo ruhinta sai dai kuma saboda shock ɗin da ta shiga ya taɓa lafiyarta a likitance.

Sosai hankalinsa ya tashi,sai ya kimtsa cikin wasu suit ya ɗora farar rigarsa sannan ya ɗauko wata rigar sanyi mai kamar jikin Zaki ya saka mata ya ɓalla maɓallanta sannan ya gyara mata zaman hullar a kanta.

Ɗaukarta yayi ya ɗora a kafaɗa sannan ya je ya buɗe ƙofa,a hankali ya soma saukowa daga kan step fuskar nan kicin-cikin yake kallon su Lubna da suka yi cirko-cirko suna yi wa Hajiya fifita duk da kuwa akwai ac a ɗakin.

Hajiya na ganinsa ta tashi tana kiran sunansa,ya ce "zan kai ta asibitinmu can sai su ƙara dubata" yana maganar ne yana juya idonsa tuni kuwa yayi nasarar canza tunanin Hajiya wacce ta ma manta da ainahin abin da ya faru.

"To ka tabbatar an kula da ita sosai ka ga ina son mu fara shirin gasar da za mu shiga tuni na sayo duk abubuwan da za mu buƙata.Ku kuma tsayuwar me kuke yi a nan?" ta ƙarashe tana tambayar su Lubna waɗanda suka cika da mamaki,ita kuwa Aliya cewa ta yi" Alhaji zan bi bayanku don na kula da ita"

Bai ce komai ba yayi gaba ita kuma ganin haka ta take masa baya har ta kai ƙofa Hajiya ta ce "in kika tafi wa zai kula da baturiya? Kin san fa nan duk taron kofi da faranti ne babu wanda zai tsinana komai in aljanun yarinyar can sun motsa"

"Ga Lubna nan Hajiya sai ta kula da ita" cewar Aliyar tana mai ɗan fita a guje don tuni Maheer ya shiga mota.A gidan gaba ya ɗora Haule kan kujera ya saka mata belt sai kuma yayi ɗan baya kaɗan da kujerar sannan ya zagaya ya zauna mazaunin direba,yayin da Aliya kuma ta shiga baya yana driving yana kallonta har suka isa asibitin.Yanzu ma kan kafaɗa ya ɗora ta ya shiga ciki,can VIP room ya kaita ya saita ac bayan ya kwantar da ita kafin ya jawo kayan aiki ya soma jona mata.

Ya ɗauki sama da minti goma kafin ya samu komai ya daidaita,gefe ya zauna yana shafar goshinta da ke fitar da gumi.Ya saki ɗan murmushi yana tuna baiwar surar da Allah ya yi mata sai kuma ya turɓune fuska tuna cewa har da laifin Hajiya da ta sanar da ita banzan auren da za ta yi masa.

Da kuma ya tuna halin kishin Haule sai ya ji wani sanyi,kamar wanda ke tsoro haka ya matsa fuskarsa ya kamo haɓarta da ke da ɗan tudu ya tsotsa haɗi dantsa haƙoransa sai ya ga ta ɗan zabura haɗi da yamutsa fuska.Yana shirin janye wa sai ya ji hannunta kan ƙeyarsa ta tallabe amma idonta a rufe suke tana bacci,haka ya ƙura mata ido yana kallo tsawon lokaci suna a haka kafin nurse Fatee ta shigo wacce tun ɗazu a gaban idonta Maheer ɗin suka shigo tana son shigowa tana tsoron yayi mata irin bala'in da yayi mata kwana bayan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull