Bakin ruhi complete - Chapter 25
Bakin ruhi complete Chapter 25: Bakin ruhi complete Chapter 25. Bakin ƙofa ta yi tsaye tana kallon yadda Maheer ya mayar da dukkan hankalinsa kan ƴar…
3,358 words
Bakin ƙofa ta yi tsaye tana kallon yadda Maheer ya mayar da dukkan hankalinsa kan ƴar aikinsu.Idonta ne suka ciko da hawaye kafin ta taka a hankali ta ce "meke damunta?" bai juyo ba haka bai bata amsa ba saboda a duniya bai so ya ga mace na kuka saboda shi kuma ya ji alamun kukan cikin muryarta.
Aka sake turo ƙofa, wannan karon Aliya ce tare kuma da Dr Muhamud shi ma cikin zafin rai ya ƙarasa yana kallon yadda Haule ta riƙe hannun Maheer shi kuma ya wani ƙure ta da ido.
"Mene ne ke damunta? Yanzu na ga Aliya a waje ta ce Haulatu kuka kawo" Dr Muhamud ya danne abin da yake ji ya daure yayi maganar,cikin iya yi kuma ya kai hannu zai raba hannun su Haulen,Maheer ya ɗago manyan idonsa ya watsa masa tare da furta" kar ka saki ko cikin kuskure ka taɓa mini mata,babu ruwanka kuma da abin da ke damunta saboda ban kira ka a nan ba"
Dr Muhamud ya ce "ta ina ta zama matarka? Maheer me yasa kake yi min haka ne? Saboda kawai ka ji na ce ina sonta shi ne kake ƙoƙarin hana hakan ginuwa?"
Maheer ya juyo ya dubi Aliya kafin ya ce "ina son kowa ya fita ke kuma ki tsaya" nurse Fatee na jin haka ta fice,shi kuwa Dr Mahmud kamar ba zai fita ba sai kuma ya nufi ƙofa.Yana tafe yana jin jiri,sam kasa nutsuwa yayi kawai ya ɗauki motarsa ya wuce gida yana shiga ya tarar da Fa'iza a zaune ta hakimce kan kujera tana kallon tv.
"Kaiii!" ta kira shi gatsal kamar wani ƙanenta, Dr Muhamud da ke ƙoƙarin shiga ɗakinsa ya dawo da sauri yana cewa "na'am! Ban lura da ke ne ba"
Kallon tsaf ta yi masa tana kaɗa ƙafa kafin ta ce "me kake ɓoye mini Mahmud? Ka sanar da ni kafin na bincika da kaina"
Jikinsa ne ya ɗau kyarma,saboda ya fi kowa sanin shaƙiyanci irin na Fa'iza da kuma yadda ta ƙware wajen sarrafa tsafi kamar rainon aljanu. "Dama a wurin aiki ne na samu saɓani da Dr Maheer "
Ta ja tsuki kafin ta ce "ai laifinka ne,babu yadda ban yi da kai ba ka zo ka shiga group amma ka ƙi .Saboda kawai ya ga yana da power ne yake juyawa ku,amma kai ma inda ka yarda an ƙaddamar da kai ai da shikenan "
Shiru Dr Muhamud yayi yana tunani kafin ya ce "kin tabbata cewa ba a kashe mutum a cikin group? Kuma zan fi ƙarfin Dr Maheer?"
Fa'iza ta ce "wa ka taɓa gani na kashe? Na faɗa maka iya ƙarfin iko ne za su baka sannan su bunƙasa arzikinka,kuma kai dai ne ka jahilci lamarin amma hatta gwamnan garin nan har da shi a ciki"
"Ya ake shiga group ɗin?" Dr Muhamud ya tambaya yana jin cewa akan Haule babu abin da ba zai iya yi ba. Ta ce "zo mu je" ta yi maganar tare da jan hannunsa suka shiga ɗakinta,kayan aikinta ta fiddo ta yi rubuta a saman madubinta a nan take ƙofa ta buɗe wasu abubuwa suka fito waɗanda shi kuma Dr Muhamud ya kasa jurar haka ya faɗi ya suma.Hankali tashe Fa'iza ta soma ƙoƙarin tashe shi amma ina tuni zuciyarsa ta daina bugawa,kamar mahaukaciya haka ta fice ta je ta kira mai gadi bayan ta rufe madubin ya koma normal.Shi ya taimaka mata suka shiga mota ta kai shi can asibitin da yake aiki,sai a lokacin kuma kawai Dr Maheer ya iya fitowa ya bar Haule da Aliya.
Kallo guda ya yi wa Dr Muhamud ɗin ya fahimci abin da ke faruwa,ya haɗe rai kafin ya dubi Fa'iza ya ce "dole sai kin fallasa sirrin da kika binne kafin a iya ceto shi,kin yi ganganci jan ra'ayinsa zuwa ƙazamin group ɗinku wanda sam mutumin kirki irinsa bai dace a ce ya shiga cikinsa ba kamar yadda bai dai dace da auren mata irinki ba.Na san ba tun yau kike jin haushina ba sai dai ki sani duk abin da kika daɗe shekara da shekaru yau zai tarwatse da izinin Allah kuma sai iyayensa sun san tuggun da kika yi wa ɗansu" yana gama faɗar haka ya ɗauki waya ya kira alhajin su Dr Muhamud,Fa'iza kuwa sai fiƙi-fiƙi take yi da ido don tun ranar da ta shiga group ɗinsu na matsafa shugabansu ya sanar da ita Dr Muhamud na ɗauke da fararen taurari,muddin ta yi sake to shi ne zai yi ajalinta.
Dr Maheer zai fita amma ta yi saurin tare shi tana kuka tana cewa "please ka taimaka ka bar ni da raina kar ku kashe ni" banza yayi da ita ya nufi ɗakin Haule don da buƙatar dole ta tashi su haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin ceto Dr Muhamud.
Yana shiga sai Aliya ta yi saurin tashi daga kusanta ,shi kuma ya maye gurbinta yana kallon Haulen tare kuma da tsoron me zai faru in ta tashi ta tuna duk abin da ya faru tsakaninsu a haka yayi shahada ya ɗora bakinsa kan nata.....
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
30
Sosai na yi mamakin ta ya aka yi Hajiya da Innarmu suke da sarƙa iri ɗaya alhalin ban taɓa ganinta ko a wuyan wata ko kuma a kasuwa? Hasali ma ita wannan sarƙar ba bugun kamfani ba ce Kakana na wurin uwa shi ne ya ƙerata da hannunsa kamar yadda Innarmu ta sanar da ni. A hankali na ɗan ƙara matsawa ina mai kallon sarƙar, niyyata na karɓe ta daga hannun Hajiya don sake gaskatar wa amma sai ta katse mini hanzari ta mayar da ita cikin gidanta .
Sai a lokacin kuma muka haɗa ido da Hajiya ,ta ƙanƙance ido kafin ta ce "Haule ba ki ganin baƙi da ba za ki gaishe su ba?"
Murya na ɗan rawa na shiga gaishe su kafin kuma na tsayar da idona gun wata mata mai kama da Innarmu sosai,banbacinsu bai wuce wannan ta fi ƙananun shekaru ba sannan fatarta ta fi kyawu da haske.
Muryar Hajiya na tsinkayo tana mai cewa "autarsu Daddyn Maheer ce wannan,su ma sauran duk ƙannansa ne sai wannan da ke cousin nasa" Hajiya ta shiga gabatar mini da su kamar na tambaye ta.
Na saki murmushin ƙarfin hali ina mai cewa "ai ga kama nan a fuska" amma sai na kasa ɗauke idona kan matar wacce ke da yawan fara'a.
"Ango ka sha ƙamshi" ɗaya daga cikinsu ta faɗa tana dariya, wannan yasa na juya na kalle shi sai na hango shi yana murmushi kafin ya ƙaraso. Abu guda na lura yadda Maheer ya dubi aurarsu Daddyn kafin ya saci kallona,tabbas da a ce ya san Innarmu ko a hoto ne da zan iya cewa ƙila shi ma kamar tasu ce ya gani amma sai na watsar na nufi sashenmu saboda kunnuwana ba za su juri jin yadda ake ambaton sunansa ana gama shi da na Ikilima ba.
Ina shiga na tarar da su Lubna kai ga Yasmine wacce ke baccin wahala. Anty Bahijja ce ta soma yi mini bayanin abin da ya faru "jikin nata ya motsa sai da Lubna ta tsaga yatsanta ta shayar da ita jininta "
Na dubi Aliya kafin na ce "kina ganin ba ƙara maida mana aiki baya zai yi ba?"
"Wai me yasa ita ba za a yi mata allurar jinin naku ba ne ?" Aliyu ita ma ta jefo min tambaya. Na ce "saboda ba iya guba ba ce kawai ke jikinta,duk an tsafe ta da buƙatar kuma mu cire macijin cikinta"
"Ta ya kenan?"
Shiru na yi kafin na ce "ina ga daga yanzu kar a sake bata jinin Lubna in ya ji wuya ai dole zai fito" ina gama faɗar haka aka turo ƙofa,tun daga ƙamshinsa na fahimci shi ne sai kawai na miƙe na nufi toilet.
"Ki dawo ki zauna ko kuma wallahi...kin san sauran" ya furta cikin wata irin murya.Na san halinsa sarai zai iya biyo ni toilet ɗin babu ruwansa da idon mutane.Ina turo baki na dawo na zauna sai a lokacin ya sake cewa "Aliya ɗaure mana ita" "To" ta amsa kafin ta dabaibaye Yasmine da haskenta kawai sai ta farka tana kuka na yi tunanin nan ɗin ma karatun ɓoyayyar duniyar zai karanta ayoyin Alkur'ani inda ake zancen sihiri da kuma wasu Azkhar.
(*- قَالَ مُوسَى مَا جِئْتُم بِهِ السِّحْرُ إِنَّ اللّهَ سَيُبْطِلُهُ إِنَّ اللّهَ لاَ يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ* *- وَيُحِقُّ اللّهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ*
*- وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ* *- فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ* *- فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَانقَلَبُواْ صَاغِرِينَ* *- وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ* *- قَالُواْ آمَنَّا بِرِبِّ الْعَالَمِينَ* *- رَبِّ مُوسَى وَهَارُونَ*
*إِنَّمَا صَنَعُوا كَيْدُ سَاحِرٍ وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَى*
*وَقَدِمْنَا إِلَى مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاء مَّنثُورًا*
*●اللَّهُمَّ رَبَّ النَّاسِ، أذْهِب البَأسَ، اشْفِ أنْتَ الشَّافِي لاَ شِفَاءَ إِلاَّ شِفاؤكَ، شِفَاءً لاَ يُغَادِرُ سَقما.*
*Allahumma rabbi n-Nâs, adz-hibi-l-Ba's, wa-shfi anta-sh-shafi, lâ shifa'a illâ shifii'uk, shifa'an Lâ yughâdiru saqamâ*
*●بِسْمِ الله أرْقِيكَ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ، مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ، اللهُ يَشْفِيكَ، بِسمِ اللهِ أُرقِيكَ.*
*Bismi-l-Lâhi arqika wa-l-Lâhu yashfika min kulli dâ'in yu'zika, wa min kulli nafsin aw "aynin hâsidin Allâhu yashfik*
*●أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق*
*Aûdhu bi kalimâti-l-Lâhi-t-Tâmmâti min shari mâ khalaq*
*●بسم الذي لا يضر مع اسمه شيء في الأرض ولا في السماء وهو السميع العليم*
*Bismni-l-Lâhi-l-Lazî lâ yadur maa-s-mihî shay'un fi-l-'Ardi wa lâ fi-sSamâ', wa huwa-s-Samîu-l-"Alîm*)
Jikin Yasmine ne ya soma rikiɗa zuwa wata halitta marar kyawu sai wani irin juyi take tana mahaukacin ihu wanda iya nan ɗakin kawai ake ji saboda yadda Aliya ta baza basirarta ta yadda ba za a jiyo mu ba.
Maheer sai ƙara sautin karatun yake kafin can na ce "ina ga da buƙatar a tofa ayoyin cikin ruwa a bata ta sha kamar yadda Kaka ta sa malam ya yi wa Jafet" Maheer ya ɗan dube ni kafin ya ce "je ki ɗauko kunnuwan magarya a kitchen ki daka su ki kawo" ba tare da na ce komai ba na je na kawo kamar yadda ya ce ya karɓa ya zuba ruwa yayi karatun,bayan yayi sai na karɓi kofin na shiga cikin dunƙulen hasken Yasmine ta yunƙuro za ta kwaɓe kofin amma na yi saurin juya idona na daskarar da ita ,wajen bata ruwan sai da na sha wahala sosai kafin ba ɗura mata su nan take cikinta ya soma girma yayi tsini har sai da cibiyarta ta zazzalo .
Wata ƙara ta yi kafin ta soma yin amai ,a daidai nan kuma Aliya ta kwance ɗaurin da ta yi.Duk baya muka yi muna kallon yadda Yasmine ke aman wani abu mai kumfa kafin can wani ɗan jinjirin maciji baƙi siɗik ya faɗo yana wiƙi-wiƙi da ido.
Cikin sauri Maheer ya fiddo nasa ya haɗiye shi,a duk duniya babu abin da nake tsoro sama da maciji ƙila don ya taɓa sara ta ne wannan yasa na tsorata na ƙanƙame Lubna kasancewar ita ce kusa da ni. "Ga shi nan kusan ƙafafunki" Lubna ta faɗa cikin tsokana na yi ihu tare da soma dire-dire duk suka hau yi mini dariya in aka cire Oga Maheer da ya saki baki yana kallona.Muna haɗa ido na nutsu tare da kawar da kai na je gun Yasmine wacce ta koma so weak duk ta yi laushi.
"Ki biyo ni ki karɓi ruwan da za a yi mata wanka" Oga Maheer ya faɗa yana mai ficewa,na dubi Aliya ita kuwa ta ce "ai kin san dai ba da ni yake ba ko? Sai ki je ki karɓo" shiru na yi ban ce komai ba sai Lubna ta ce "bari na je na karɓo"
"Me yasa kike son matsa kanki ga gini? Yanzu kin ji ya ambaci sunanki?" cewar Aliya. Lubna ta ce "ai bai faɗi sunan kowa ba"
"Eh saboda HAULE kawai yake yi wa haka kuma ita ma ta sani bai taɓa kiran sunanta ba"
"To ai sai ta je ta karɓo" Lubna ta faɗa a ɗan hassale,sai kuma suka soma cacar baki ba su yi shiru ba sai da anty Bahijja ta yi musu magana.
Ni kuwa don su nutsu da kyau sai na ce "anty Bahijja ida bani labarinki mana"
Ta ce "tun daga wannan lokaci na soma karɓar izaya wurin Mr Sahil,yayin da ɓoyayyun halayensa suke ta ƙara bayyana a gare ni.Yana nemana mu yi normal sex,in buƙatar haka ta tashi a can ɗakina yake zuwa in kuma ta haramtacciyar hanya ce to a ɗakinsa za mu yi a gaban wannan halittar da ke cikin mirror.Na gwada tserewa ya fi cikon casbi amma ban ci nasara ba saboda yayi mini mugun kafi.Zancen fatalwar matarsa kuwa da farko sai na ɗauki hakan ba gaskiya ne ba,sai dai yadda nake yawan ganin giftawar mutum yasa na yarda sai kuma farashin tsorona ya sake hauhawa.Ba zan manta ba wata rana na shiga ɗakinsa na soma yin bincike nan na gamu da wata takarda mai ɗauke da hotunan mata kusan su biyar kowacce da sunanta da kuma ranar da ta mutu,tsoro ya kama ni saboda yadda na ga kuma dukkansu Mr Sahil yayi hoto da su da dukkan alamu kuma na ranakun aurensu ne.Nan ne fahimci cewa tushen arzikinsa matansa yake bayarwa matsayin sacrifice,ina nan zaune sai ya shigo na ɗaga kai fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ga kuma wani tsoro da ya kama ni.Ba tare da na ce komai ba ya bani amsar tambayar da ke mini yawo a kwanya,"eh abin da kike tunani haka nan ne,sai dai ke ba zan bayar da ke ba za ki zauna tare da ni ki haifa min yarinyar da zan baiwa shugaba domin ci gabana da kuma naki "
"A'a ni ba zan zauna a gidanka ba,za ka sawwaƙe min na koma gidan iyayena " na faɗa amma sai ya ƙyalƙyace da dariya kafin ya ce "wane iyayen ? Can lahira za ki tarar da su? To tsaya ki ji Bahijja na kashe iyayenki ,ba za ki sake ganinsu ba.Kwaɗayinsu ya ja musu suka aura mini ke ba tare da wani bincike ba yanzu ai sun ga ribar haka" tun daga wannan lokaci na riƙi kuka matsayin aboki,na rame sosai na rasa abin da ke yi mini daɗi.Ga azabar Mr Sahil ga kuma yadda fatalen matansa ke yi min yawo a cikin gida,sai ina zaune in ji suna magana cikin raha "ita wannan sai yaushe za ta buyo layinmu?" "hahha! Wa'adinta bai yi ba ita ma za ta mutu ta dawo tsagenmu " ire-iren waɗannan maganganu su suke sa na ƙumshe kaina a ɗaki na toshe kunnuwana.Ban samu kaina ba sai ranar da Mr Sahil ya bani wasu ruwa ya ce maganin da zai sa na bar jin maganarsu ne,eh na bar ji sai kuma na manta duk wata izaya da yake yi min a haka har na raini cikin Yasmine na haife ta.Tun daga ranar da ta zo duniya sai ya bar nemana kwata-kwata a cewarsa shi ne sharaɗin da aka yi masa sai dai fa yana neman matan banza,ga kuma Yasmine da ke yin abu duk dare kamar tana yin sex da na yi masa magana sai ya ce duk yara na yin haka ai da wannan ya ɗaure bakina har ta girma .A satin da ya gabata kafin na haɗu da ku ne yake shaida mini jagabansu zai zo gidanmu,wai za mu yi sex mu uku in kuma na ƙi sai ya yi da Yasmine in ta cika shekaru sha takwas" tana kawo wa nan ta yi shiru tana mai yin kuka mai taɓa rai.
Ina shirin soma rarrashinta Hajiya ta ƙwala kirana daga can falo,da sauri na miƙe na fita. "Hajiya ga ni " na furta . "Ki ɗauki bokiti ki cika da ruwa ki kaiwa Maheer " ta faɗa tana gyara kwanci,na so na tambaye ta ina baƙin suke ganin sai ita ɗaya amma na yi shiru na je na cika bokiti da ruwan na hau sama ina tsayuwa ƙofar ta buɗe da kanta na shiga ciki kafin kuma ta rufe kanta .Na ajiye bokitin da sauri ina kawar da kai ganin daga shi sai gajeren wando ya tsaya yana wani danna remote yana canza channel.
"Sai yanzu kika ga damar zuwa?" ya tambaye ni,sai na juya na ɗan saci kallonsa hankalinsa na kan tv amma da yake har a ƙeya ido ne da shi sai da ya ga na kalle shi.
"Ki ci gaba da satar kallon kyakkyawan jikin da ya saka kika suma ɗazu" "Ka buɗe mini ƙofa zan fita" na faɗa cikin dakiya. Sai a lokacin ya ajiye remote ɗin ya tako kusa da ni har da wani riƙe ƙugu kamar mace ya ce "ba ki shigo don ki fita ba,ina son jin labarinki ne zo mu je" ya faɗa tare da kamo hannuna na fizge na ce "mu je ina? Shi labarin ba a iya saurarensa a nan sai mun shiga bedroom?"
Ya ƙanƙance ido yana mai cewa " yaushe na faɗi cewa mu shiga bedroom? Oh! Abin ne bai ishe ki ba? Oyaaa zo mu je to na sake lugwigwita ki" hannunsa na buge ina harararsa kafin na turo baki gaba,yayi dariyar shaƙiyanci kafin ya ce "don Allah H.lat me kike so da ni ne? Ke ko tausayina ba ki ji sai wahalar da ni kike?"