Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 26

Bakin ruhi complete - Chapter 26

Bakin ruhi complete Chapter 26: Bakin ruhi complete Chapter 26. Hanci da baki na saki ina kallonsa jin wani zance,ƙila ya fahimci haka sai ya ce "je ki…

3,358 words

Hanci da baki na saki ina kallonsa jin wani zance,ƙila ya fahimci haka sai ya ce "je ki zauna kan kujera don Allah " saboda yanayin yadda yayi magana yasa na ja ƙafafuna na je na yi zaune. Bokitin ruwan ya kawo a gabana kafin ya zube kan gwiwansa, hannuwana ya kamo ya jimƙe su sosai kafin ya tsunduma su cikin ruwan."Tofa yawunki" ya faɗa ,na dube shi cikin ido ya ce "eh tofa" kamar ba zan yi ba sai kuma na tofa shi ma ya zuba nasa a gaban idona na kowanne suka ware kansu tare da soma tafasa,nawa suka fitar da color ɗin baƙi yayin da nasa kuma suka fitar da wani irin fari suna ƙyalli kamar farar azurfa.

"A shekarun baya irin haka ta taɓa kasancewa a tsakanin wasu aminai biyu maza.Dukkansu ƴan ƙauye ne,in na ce miki ƙauye ina nufin irin hatsabibin ƙauyen nan mai ɗauke da abubuwan almara,ban tsoro da kuma firgici.Abubuwan da suka yi wannan ƙauye ado da ƙawa su ne baƙin tsafi,Maita da kuma alƙawari a tsakaninsu da duniyar ruhani.A cikin aminnan nan biyu ɗaya shi ne kakanki Nalado,ɗayan kuma shi ne Kakana Maitama.Su biyun ba iya abokaina ba ne, a'a ƴan uwa ne na jinin maƙwabtaka iyayensu ma suna yin wannan zumuncin kafin ra'ayoyi biyu mabanbanta su raba su .Kamar yadda na faɗa miki cewa ƙauyen sun ƙware a harakar baƙin tsafi to haka Nalado da kuma Maitama suka laƙance shi.A wani bincike nasu ne nasu na matsafa suka gano akwai wata keɓaɓiyar duniya wacce ta kasance ta hatsabibai,fatale da kuma aljanu.Yarda da ƙarfin tsafinsu ne yasa suka ratsa dajin AOKIGAHARA,wanda shi kuma a cikinsa tsagi biyu ne .Yankin duhu da kuma yankin haske,da zuwansu sai suka rasa ta ina za su bi Nalado ne ya fara cewa abokinsa "mu shiga inda ke da hatsabin duhun can mu gano mene ne ya harzuƙa wurin har yayi baƙi haka kamar zunubi" amma sai shi abokin nasa Maitama ya ce "a'a Nalado me zai hana mu shiga dai inda ke da hasken ka sani ko can ɗin aljanna ce can kuma hanyar wuta ce?"

"Kana nufin nan ne lahirar da muka ji Musulmin cikinmu na faɗa?"

"Eh to kusan hakan ne nake gani,in ba haka ba a ina ne ke da hanyoyi biyu mabanbanta?" cewar Maitama. Sai Nalado ya ce "in kuwa haka na zaɓi na shiga ɓangaren da ke da duhun ko ba komai na san zan tarar da tsofaffin bokaye da matsafa da aljanun da suka bijire suka saukar da fasadi a cikin doron duniya,ka ga sai na roƙi su bani ƙarfin ikonsu ta yadda in mun koma duniyarmu zan baza mulki na kuma mulki kowa "

Maitama ya ce "ni kuma na zaɓi bangaren haske ta yadda zan hana ka cika baƙin nufinka na mulkar duniya,zan tabbatar kuma duk inda ka ɗiga ɗigon baƙin kalarka ni kuma zan bi ko ina ina jefa ƙwayar haske a ciki" bayan kowa ya faɗi furicin bakinsa kamar da wasa sai kowa ya kama hanyar da ya zaɓa tare da kutsa kai a ciki" Maheer na kawowa nan da zancensa na yi saurin ƙwace hannuna ina zarar ido yayin da zuciyata ke matsananci bugawa kamar za ta faso allon ƙirjina ta faɗo. Dakyar na iya haɗa yawu murya na ɗan rawa ina kuma nuna shi da yatsa,"kenan...kenan ka san Kakana Nalado? Kenan ni..ni.Ni da kai.." sai kuma na yi shiru.

Maheer ya lumshe ido tare kuma da buɗe su kafin ya ce "yes mu ƴan uwan juna ne,Innarku ƙanwar mahaifina ce shi ya aurar da ita kuma ga mahaifinki Ibrahim saboda ya cika burin mahaifinsa Maitama wanda ya kasance Kakana"

Hawaye ne suka soma yi min zuba,yayin da Maheer ya ci gaba da cewa "na soma baki labarin nan ne saboda babu wata sauran mafita,tun da kika yi tozali da ƴan uwan Daddy masu kama da Innarki na san dole ki bi didigi ta ya haka za ta kasance"

Na ce "amma a can garinmu Innarmu nada wasu iyayen har da ma ƴan uwa"

"Na bogi ne,amma na asalin sun rasu ko kuma na ce miki suna can a ɓoye in ba ki manta ba kuma kin ganni a tsaye tare da wani mutum mai shafafar fuska to wannan shi ne Kakana Maitama mahaifin Daddyna da kuma Innarki ya zo gare ni ne don sanar da ni an ɗaura mana aure ni da ke"

Zumbur na tashi tsaye kamar wacce aka tsikara,shi ma Maheer ya tashi tsaye yana mai ci gaba da cewa "wallahi tallahi a gaske nake Haulat an ɗaura aurenmu in kuma ba ki yarda ba za mu je ni da ke can wurin Papy ya faɗa miki da bakinsa ke ɗin matata ce"

Ba wai ban yarda da furucinsa ba,a'a yadda ya ce wai shi mijina ne ya saka ni cikin tsananin shock da na kasa controling kaina.Wani irin jiri nake ji na yi luuu zan faɗi yayi saurin taro ni na faɗa kan ƙirjinsa.Ƙanƙame shi na yi gam ina mai lumshe ido haɗi da soma sauke numfashi da sauri-sauri ko Allah zai sa na ji sassaucin abin da nake ji.Ina jin lokacin da Maheer ya zagaye ƙuguna da hannunsa ya gyra mini tsayuwata a ƙirjinsa kafin ya ɓalle maɓallan rigar sanyin jikina wacce dama can shi ne ya saka mini ita.Hullar ya ture ta yi baya,sai a lokacin na ɗaga kai na dube shi muna kallon juna cikin ido.So nake na furta masa kalmar so ko zan samu sukunin abin da nake ji,amma kuma ba zan iya ba na ci alwashin shi ne zai fara faɗa mini ita sannan kuma sai na gwara kansa sannan ya ji kalmar a bakina.A hankali ya zare mini rigar ta faɗi ƙasa,sai yanzu ne kuma na ga ashe riga da wando ne a jikina na Adidas waɗanda suke mallakinsa.Da sauri na lumshe idona ban shirya ba ganin ya soma matso fuskarsa kusan tawa,murya can ƙasan maƙoshi ya ce "ina son mu haɗe tunaninmu wuri guda Please Queen" sai ya sauke lips ɗin nasa kan nawa,yayin da ni kuma na aiwatar da abin da ya ce ɗin.Sosai nake jin daɗin yadda yake min sumba,na shagala sosai a cikin shauƙin kafin na ji wata muryar na cewa "to ni dai ya isa haka ka sakar mini jika haka" da wani mugun sauri na fizge bakina daga cikin na Maheer sai na ga sam ba a ɗakinsa muke ba muna cikin wani ɗan ɗaki ne na kara,gefe kuwa wannan mutumin ne a zaune kan gadon itace. Maheer ya saki murmushi kafin ya ƙara jawo ni ya manna a ƙirji sannan ya ce "Papy na cika alƙwarin da na ɗaukar maka,na furtawa fitinaniyar jikarka komai ka ganta da rawar kai take ƙila kuma tun yau ita ce za ta fara ƙoƙarin cika burinka"

Wanda ya kira da Papy ya ɗauki wani abu ya wanke fuskarsa da shi sai ga shi ya dawo normal mutum ana ganin dukkan gaɓoɓin fuskarsa,sannan kamanninsa da Innarmu ne na gani jere ras a tattare da shi.

Wani ƙyalle ya miƙo min na karɓa,ya ce "idanun Hassana ne,Kakarki ce ta kawo min su ajiya ta ce duk ranar da kika zo na baki su domin mayarwa da ƴar uwarki kayanta" Yana gama furta hakan sai na buɗe ƙyallen,ƙwayar ido biyu ce a ciki sai motsi suke kai kace yanzu ne aka cire su har da kumfan jini.Murya na ɗan rawa na ce "wacce ta je gidanmu? Mai ganin nan ita ɗin Kakata ce?" ya jinjina kai yana murmushi kafin ya ce "ku zauna ,ni nan zan baki dukkan tarihinki da kuma abin da ya shafi ahalinmu.Labarin da King Maheer ya baki wannan shimfiɗa ce,zan sanar da ke komai kafin na roƙi alfarma a wurinki ki yarda ki amince da da King a yau a matsayin mijinki"......

*Intermission/tsakiya*🌚

Sai kuma ranar asabar in sha Allah za mu ɗora daga inda muka tsaya,nan ne labarin ya zo a tsakiya zan je hutun kwana biyu .

Ga waɗanda ke karanta mini book ba tare da sun biya kuɗin karatu ba ku sani ban yafe muku ba,duk wacce ta ji haushi kuma ta biya ni😝

My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

31

"Kamar yadda Maheer ya faɗa miki sunana Maitama,banda babban aboki kamar Nalado.Tun ƙurciyarmu mun taso muna ganin kakanni da iyaye ana tsafi da kuma maita,sai dai ba mu taɓa ɗaukar haka wata illa ba sai ma bazama da muka yi wurin koyo.Da farko dai kamar ba za mu iya ba sai ga shi mun koyi siddabaru,duk ranakun kasuwa haka muke bin gari-gari muna wasar tsibo ta rufa ido.Na san za ki so sanin ta ya muke yin haka? To hanya mai sauƙi ce,muna aiki ne da aljanu saboda in ka kafircewa Allah ka yi kuma duk abin da aljani ya sharanɗa maka to shi kuma zai zamo yaronka.Da wannan muka soma cin abinci,yin siddabaru za mu rufe kwano babu komai amma da zarar mun buɗe shi sai lafiyayyen abinci ya bayyana a ciki wanda ba kowa ya kawo shi ba sai aljanin da ke yi mana aiki.A cikin irin wannan ikon ne muka haɗu da wata bafulatana,a kallon farko da Nalado yayi mata ya ji yana son ta maimakon ya je ya sanar da ita sai yayi amfani da tsafinsa ta zo gare shi ta ce tana sonsa.Wannan abu da ya faru sai na ji ni ma da buƙatar na samo tawa bafulatanar,sai dai abin da ban sani ashe Nalado da yake abokina yayi min sihiri ta yadda ba zan taɓa yin aure ba.Dalilinsa na yin haka ba komai ba ne saboda yayi bincike ya gano cewa duk ranar da na samu macen aure to za ta yi silar raba mu .Da haka na gaji da neman aure har na haƙura,kafin Allah ya haɗa ni da matar mafarkina wacce ta kasance Siren .Ba zan manta ba,a wani yammacin Laraba ne mun je kamo kifi ni da Nalado sai dare yayi mana a can ga shi kuma ba mu kama sosai ba.

"Maitama ya kamata mu koma gida ka sani sarai muna da matsala da esprit ɗin ruwa a matsayinmu na matsafan baƙin tsafi " Nalado ya faɗa yana mai ɗaukar kifinsa da ya kama.

Sai na ce masa "a'a sai dai ka tafi ni kam sai na kamo mai ɗan yawa kafin na koma gida,ko ka manta gobe ne ranar gasa?"

"Hahaha! Dama akwai wani tsafi da ake yi da kifi wanda ban sani ba? Ka ga sam ba zan shiga wannan gasar ba saboda na san ba zan ci ba.Ko ka san da cewa manyan matsafa daga ɓangarorin duniya ne za su halarci wannan gagarumar gasar?"

Na ce "ni kam zan shiga kuma ina nan da kai sai na shigo layin zakaru uku" Nalado yana yi mini dariyar shaƙiyanci ya tafi,yayin da ni kuma na ci gaba da jefa ragata a cikin kogin da hasken faɗuwar rana ya haska shi. Kamar da wasa na soma jin ragata ta ɗau nauyi,da sauri na soma jawo ta ina murna cewa na kamo babban kifi kafin kuma murnar ta koma ciki a daidai lokacin na yi tozali da wata halitta rabi mutum rabi kifi sai juya idonta take suna kawo haske.Ko babu tsafi dama can ni ba ma'abocin tsoro ne ba hakan yasa na mazge duk da kuwa na yi mamakin ganin irin halittarta.

"Ke kuma wace ce ke?" na samu na jefo mata tambayar .Da idonta masu ƙyallin haske ta dube ni kafin ta ce "ni ce matarka wacce ƙaddararka ta haɗa ma da ita,ka sani samuna a matsayin matarka shi ne mafita a gare ka"

Baki da hanci na saki ina kallonta,ina jin maganarta tamkar gatanar gizo da ƙoki.To ta ina ma bil'adama zai auri aljana? Don kuwa marabarta da aljana ƴar kaɗance.

Ba tare da na tanka ta ba na ɗauki tarkacena zan yi tafiyata amma ta tsayar da ni ta hanyar cewa,"gasar da za a yi gobe kai ne za ka zamo Zakara,muddin za ka ɗaura wannan abin a ƙugunka" sai ta miƙo min wata aba kamar laya.Saƙo na yi ina kallonta kafin na karɓa ina mai ci gaba da kallonta can na ce "in zancenki ya zama gaskiya mene ne farashin abin da zan baki?"

"Aurena za ka yi shi ne farashin"ta bani amsa,ba tare da wani tunani ba na ce "na yarda" sai ta yi suka ta koma cikin ruwa yayin da ni kuma na tafi gida na kaiwa Innarmu ɗan kifin da na kamo don ta sarrafa shi mu ci da dare.

Bayan ta zuba shi tukunya sai kuwa ya ƙara auki,"Maitama zo ka ga yadda kifin nan ya cika tukunya" shine abin da ta faɗa ,na je na leƙa na gansa mai yawa a nan take na ji a raina aikin Siren ɗin nan ce wacce ban ma san sunanta ba.

Bayan an gama girki muna ci sai mahaifina yake cewa "Maitama ban san a cikin me ka tsoma hannunka ba,amma ina ji a jikina tamkar za a canza maka alƙibila daga tsafin da muka gada zuwa wani tsafin na zamani"

Murmushi kawai na yi,don ko na ce na yi magana ba zan faɗi gaskiya ba in kuma na yi ƙarya mahaifina babban matsafi ne zai gano hakan.Bayan mun gama sharɓar romon kifi sai na kimtsa na je gidan Nalado domin basa labarin abin da ya faru da ni bayan ya tafi. Na nemi izini har babu iyaka amma bai fito ba,cikin rashin jin daɗi na koma gida ina ji a raina ƙila matarsa ce ta hana shi fitowa tun da na fahimci ta tsane ni kawai haka don ina abota da mijinta.

Da na koma gida haka na yi ta juya wannan igiya da kifin ruwa ta bani,kafin kuma na mayar da ita ma'ajiyarta. Washegari tun safe bayan mun yi sallah na yi wanka da ruwan magunguna na asirai da tsafi,ban ɗaura laya ko ɗaya ba illa igiyar nan kawai sannan kuma na saka yaƙinina a kanta.

Gidan Maigari na yi tsinke inda gangunan tsafi ke ta kaɗa kansu yayin da kuma dakaru waɗanda za su yi gasar tsafi kowanne ya samu wuri ya zauna.Ni ma sai na bi ayari ina ta duba inda zan ga Nalado amma ban gansa ba har sai da aka soma gudanar da gasa wacce ba gasar komai ce ba sai ta ɗaukar wani rawani wanda ya kasance na wani tsohon matsafi da yayi mulki kusan ƙarni uku baya.Haka mutane suke ta gwada sa'arsu sai dai wasu da zarar sun taɓa rawanin suke faɗuwa a mace,wasu tunkararsa ma kawai suke yi sai su faɗi a some ganin haka yasa duk sauran da muka yi saura suka ji tsoro suka janye suka fasa shiga sai yayi saura ni ɗaya tal.

Na soma takawa kenan don ɗauko rawanin sai ji na yi an jawo ni baya,Nalado ne har ƙasa ya zube yana roƙona "a'a Maitama kar ka yi wannan kuskuren,wallahi in ka tafi mutuwa za ka yi .Dubi gabanka gawarwakin mutane ne a zube kamar ƴan tsaki, waɗanda a harakar tsafi sun dame ka sun shanye amma ka ga duk sun mutu masu damar ne suka some dubi wasu ga su can sun haukace" na saki murmushi tare da miƙar da shi tsaye,akwai wani kallo da nake yi wa Nalado don basa tabbacin zan kai labari akan abin da na sa gaba.Yanzu ma shi na yi masa,sai ya ɗan waro ido kafin yayi ƙasa da murya "ka tabbata?" na jinjina masa kai kafin na sake shi na je na hau kan dandamalin da aka ajiye rawanin wanda ashe manyan sheɗanu ne ke a tsaye kansa suna gadinsa.Ba tare da tsoro ko ɗarrr ba na kai hannu na ɗauki rawanin tare da ɗora shi a kai sannan na juyo na fuskanci al'umma waɗanda suke cike da mamakin ta yadda aka yi na haye.

Kiɗa aka soma yi ana yin duk wani abu da ya shafi tsafi,yayin da ni kuma a inda nake tsaye nake iya hango Mayu daga cikinmu ,sannan da waɗanda aka haramtawa yin tsafin zamani.Daga inda nake ina hango wuraren da ke ɗauke da wasu tsoffin asirai ,wasu abubuwan ma ban san da su ba.

Bayan kyaututtukan da na samu sai duk aka soma wa watsewa,sai a lokacin dangina na kusa suka fara zuwar min yi mini barka a haka har na samu keɓewa da Nalado.

"Aboki mene ne sirri?"ita ce tambayar da ya fara yi min . Na ce "za ka gani,amma ka bari sai dab da magarib " duk yadda Nalado ya so na faɗa masa sirrin a lokacin sai na ƙi,a haka muka rabu maraice na yi kuma ya zo har nan gida ya same ni sai muka kama hanyar tabki.Kan hanyar ma sai da ya sha min kai da tambayoyi amma ban basa amsa ba,har muka isa muka yi tsaye muna kallon ruwan.Ba a ɗauki lokaci ba kusa ruwan suka soma yin motsi kafin ta fito tana kaɗan bindin,Nalado ya ja da baya da sauri yayin da ni kuma na ƙure ta da ido ina kallo ina jin wani sonta na fizgata saboda silarta ne martabata ta yi sama.

"Barka da zuwa Sarkin matsafa " shi ne abin da ta furta,na amsa da "yawwa" sai na ga tana kallon Nalado,sai ka gabatar mata da shi na ce "wannan shi ne abokina Nalado"

Ta ɗan yamutsa fuska kafin ta ce "na sani,amma ai shi ma sarki ne na wani yanki" Nalado na jin haka sai ya matso ya ce "sarki kuma?" Ta ce "eh na ga tambarin sarauta a saman goshinka sai dai babu tabbacin cewa za ka iya ɗaukar wannan kambun duba da baƙar zuciyarka mai cike da ha'inci da kuma zalunci ,saboda mene ka yi haka? Me yasa za ka cutar da wanda ya yarda da kai?"

Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da Nalado kafin ya ce "ki yi min afuwa ba zan sake ba" "Mene ne sunanki?" na tambaye ta don kawar da zancensu,ta maido dubanta gare ni kafin ta ce "Zinaru! Ya zancen maganarmu ka shirya auren nawa a yau ko kuwa?"

Muka kalli juna da Nalado sannan na basa labarin yadda muka yi da Zinaru,a cikin ƙwayar idonsa na hango tsantsar hassada saboda ya fahimci auren Zinaru da zan yi tamkar taka wani matsayi ne a duniyar tsafinmu.

"Na amince" na faɗa ba tare da wata shawara ba hakan kuma sai ya ƙara fusata Nalado saboda shi ɗin tamkar wani ubana ban taɓa ɗaukar wani mataki ba sai na basa shawara,kuma abin da ya zartar shi nake amfani da shi.

Zinaru na gama jin amsar da na bayar sai ta koma cikin ruwa ba tare da ta yi min bayanin yadda za a yi auren ya kasance ba.A ɗan hassale Nalado ya ce mini "ka yi hauka ne Maitama? Ka kuwa san yadda ruhikan ruwa ke da ƙarfin tsafi? In fa ba ka yi hankali ba wallahi za ta canza ka ne ta mayar da tsafinka wani iri"

Na ce "kar ka damu ,duk wani muƙami da wani matsafi zai buƙata ni na gama samunsa.Ko ka san girman tsafin da ke cikin rawanin nan kuwa? To bari ka ji in faɗa maka,ɗazu kafin ka zo har matattu na dinga gani suna yawo cikin gari sannan wai bayan wannan duniyar da akwai wata duniyar"

"Wata duniya kamar ya?"

"Ɓoyayyar duniya ce wacce aka killace domin matsafa,amma ilimin tsafinmu bai yi ƙamarin da yasa muka san da ita ba.Kai duk ba wannan ba,ashe akwai wuri na musamman da aka keɓe domin zuwa neman taimako ko kuma kiran wani dodo ko aljani,sai dai fa har yanzu ban san ta ina ake bi a je ba kuma ba a sanar da ni ba"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull