Bakin ruhi complete - Chapter 29
Bakin ruhi complete Chapter 29: Bakin ruhi complete Chapter 29. "Haule duk wani ƙarfin iko da kike gani ana so mamallakinsa ne zai dinga controling nasa ba…
3,231 words
"Haule duk wani ƙarfin iko da kike gani ana so mamallakinsa ne zai dinga controling nasa ba wai ya bari power ta dinga juya shi ba.Kin ga ki guji duk abin da zai ɓata miki rai ko kuma hirar da za ta sa abokin hirar taki ya fusata ki,in kuma hakan ta faru da buƙatar ki basa yawunki don dole muddin ana so a fitar da kambun maitar da kika jefa masa"
"Ni ba mayya ce ba" na faɗa . Ya ce "na sani! Amma kina da power kashe mutum ta hanyar fushinki a kansa in hakan ya ɗauki lokaci ba ki gusar da ƙwayar cutar ba za ta iya yin sanadinsa "
"Na ji zan kiyaye" na faɗa ina tunanin to tun yaushe kuma hakan ta fara faruwa da ni? Tabbas hakan nada nasaba da ziyarar da na kai sannan Kakana Nalado yayi amfani da wannan damar don saka min wannan bala'in.
Cike da jin daɗi headmaster ya ce " yawwa ungo wannan littafin zai taimaka miki wurin gane wace ce ke" na karɓi littafin wanda har zuwa yanzu ban taɓa karanta ko sunansa ba ne ballantana kuma abin da ya ƙumsa.Bayan nan sai na wuce can ɗakin darasi kamar yadda ya ce,Aliya a nan ne na ga ikon Allah wai mutum da ƙafafun kaza,wasu kuma mutanen da gangar jiki normal amma kawunansu na karnuka ne in takaice miki dai magana iya ni ɗaya ce kaf ajin wacce take da cikakkiyar halittar ɗan Adam.A cikin darasin da aka gabatar mana ne na samu dalilinsu na sauya kawuna,na farko akwai ɓada kama wanda ko da a ce ka haɗu da wani mai ido ukun ne ba zai gane ka ba,na biyu kuma yana daga cikin ɗaukakar ƙarfin iko.
Darasi aka fara yi mana ana zuzuta ƙarfin ikon kowa sai abin ya bani dariya kuwa ƙyarƙyata bayan an tashi ina ƙoƙarin komawa makwancina kawai sai ji na an zagaye ni amma babu kowa a gabana iya ruhika ne" ina kawowa nan na yi shiru,saboda tsayuwar motar Oga Maheer.Na ɗan haɗe fuska na ƙi buɗewa na shiga ,Aliya ma sai ta yi tsaye tana kallona ƙila jira take har ni na fara shiga.Shi kuwa a zuciye ya fito ya zo ya tsaya a gabana,wani irin kallo ne yake yi mini mai ma'anoni dayawa na ɗan kawar da kai ina jin zuciyata na dokawa da ƙarfi,idon Maheer su ne raunina in ina kallonsu wani irin shauƙin sonsa nake ji yana fizga ta.Sam ban lura da lokacin da Aliya ta shiga ba sai ƙarar rufewar motar kawai na ji .Na lumshe ido da sauri jin hannunsa ya kamo nawa,"ke?" ya kira ni cikin wani yanayi,na buɗe idona tare da ɗago kai na dube shi."Me kike so da ni uhum? "
Ban ce komai ba sai baki da na turo gaba,"mu je" ya faɗa ,na maƙe kafaɗa na ce "ni akwai inda zan je" "Gidan Oga Mansur ko? Ke me yasa ba ki jin magana ba ki kuma auna yadda abubuwa za su tafiyar miki? Kina tunanin ita matar Oga Mansur kamar sauran mutanen da kike zuwar musu ne kai tsaye? Tana da ƙarfin iko sosai,don ita nata kalar tsafin tsantsar shirka ce ga Allah in kika ce ki tunkare ta kina iya faɗawa cikin tarkonta ko an faɗa miki ita sokuwa ce ba ta san za a iya kawo mata farmaki ba musamman da gasar nan ta gwamna ta tunkaro za ta yi tsafe-tsafe da bugun ƙasa da komai"
Jin ya gane inda zan je sai na saduda na ce "to amma ya za a yi mu tunkare ta kuma mu yi nasara ba tare da wata matsala ta auku ba?"
Murya ya rage can ƙasa ya ce "kin fa ji abin da Papy ya faɗa Queen dole ki yarda da King ki basa kanki " a yadda yake maganar kawai za ka iya jin yadda yake cike da tsantsar buƙatar hakan amma yadda ya jingini ko kuma na ce ya nuna shi bai so sai kawai na mazge na ce masa "a'a mu sake wata dubarar dai" kanzil bai ce ba ya buɗe mini murfin mota tare da wani cilla ni ciki irin ya ji haushina kafin ya zagaya ya shigo,a tsiyace ya ja muka bar asibitin.
Muna isa gida muka yi wanka tare da shirin zuwa restaurant,Hajiya ba ta gane komai ba.Da muka je can haka muka zauna muna ta hirar gasa da kuma yadda za a kawo ƙarshen BAƘIN RUHI.
Aliya uwar surutu ta ce "Haule kawai ki yarda ku angonce ke da Oga Maheer wannan ita ce babbar mafita akan dukkan matsalolin da suka addabi duniyar nan dangane da gubarsa da ya saki"
Na ɗan dube ta kafin na ce "Aliya ko dai ke kike zuwa wurin Oga Maheer ɗin?"
"Wa ni in ji ɗan daudu? Wannan lamari sai ke kaɗai ce za ki iya"
"Saboda ita kaɗai ce mace ko?" cewar Lubna.
Aliya ta bata amsa da "eh to kusan haka ne,saboda ko matan duniya sun haɗu sun yi sintiri ba za su yi wani tasiri a gun Oga Maheer ba sai ita iya Haulen kawai ce za ta iya ji da shi"
Lubna ta taɓe baki kafin ta ce "a faɗawa kaji zabi hira suke "
"Ke ma ai kazar ce" Aliya ba ta rufe bakinta ba Lubna ta kai hannu ta buge shi,nan suka hau dambe ina ta ƙoƙarin raba su amma sun ƙi.
"Waranceee!" muryar wata matashiya ta furta duk sai suka tsaya suka yi cirko-cirko amma da alamu kamar ita Aliya ta san ta .
"Kun tsaya yin faɗa kun bar costumers a can waje suna jira" ta faɗa tana mai kallonsu,a tare duk suka fita yayin da ita kuma ta matso kusa da ni tana mai ciro wata ƴar ganɗama ta miƙo mini.Kamar wacce ta asirce haka na karɓa tare da buɗewa na shanye abin da ke ciki tas kafin na jawo kujera na zauna ina kallonta,ta juya mini baya kafin ta soma yin magana "Papy ya baki layar da za ta baki damar yin abubuwa da dama ciki kuwa har da jin ƙarashin labarinsa da abokinsa Maitama amma tamkar ba ki san aikinki ba kin wani tsaya shirme.Ruwan da kika gama sha saƙo ne daga Innarki,magani ne da ya ƙumshi sirrika dayawa,tun daga gyaran jikin amarya zuwa tsimin amare sai dai wannan ya sha banban saboda tun ranar da kika zo duniya aka soma aiki a kansa.Na san ba ki san ni ba,to bari na gabatar miki da kaina sunana Ayush Yayar Innarki ce ni wacce Nalado ya bayar da jinina matsayin hadiya ga dodonsa.Ya nemi ya aure ni amma shi mahaifina Maitama ya ƙi yarda shi ne shi kuma ya kashe ni tun ina ƴar budurwata,amma ko dayake daga yau zuwa kwana uku za ki san komai" tana gama faɗa sai ta juyo muna facing juna .
Murya na ɗan rawa na ce "mene ne kika bani na sha?"
Ta yi wani murmushi kafin ta ce "maganin da zai yi miki jagora ne har zuwa turakar mijinki"
Idona suka ciko da ƙwalla kafin na ce "me yasa za ki bani abin da zai zubar min da ƙimata ? Saboda me ba ki shawarce ni ba?"
Ta tako ta iso inda nake ta dafa kafaɗata ta ce "saboda lokaci yayi da za ki cika burin FARIN RUHI"
Hawayen sai a lokacin suka samu damar zubo mini,na girgiza kai na ce "ni ban so kuma ni ban shirya ganin Maheer matsayin mijina ba wallahi ba zan je turakarsa ba"
"Aikin gama ya riga da ya gama,kin ga maganin da na baki iya kwana uku kawai za ki iya jurarsa in kuma kika zarta to tabbas ina mai shaida miki cikin biyu sai ɗaya ya faru ko dai ki rasa rayuwarki ko kuma dai BAƘIN RUHI yayi galaba a kanki ya mallaki gangar jikinki don kuwa saura ƙiris ya sabunta gangar jiki daga ta Nalado zuwa taki tun da ke ce magajiyarsa "
Ban iya ce mata komai ba sakamakon irin abin da nake ji yana game mini jiki tun yanzu,na miƙe dakyar na ɗauki kuɗin da zan shiga adaidaita na fice.
A cikin napep ma ji nake kamar na ƙurma ihu,muna isa na yi saurin shiga gida amma tamkar wani mayen ƙarfe haka benen Oga Maheer ke zuƙo ruhina,idona har wani rufewa suke lokacin da na nufi can na soma taka matakalar.
Ina tsayuwa a gaban ɗakin sai ƙofar ta buɗe kanta,wani zafi ne nake jin yana dukar mini fata.Kamar wata mahaukaciya haka na shiga toilet,sam ban yi lura da shi ba.Kayan jikina na tuɓe duka kafin na tsoma ƙafata cikin bahon wanka da na gani a cike da ruwa.
Ji na yi kamar na taka mutum,na ɗago idona masu kamar na mai jin bacci kowacce ta yi maye.Ido huɗu muka da shi ya kafe ni ko ƙyaftawa bai yi hakan sai tsunduma ni cikin wani mugun hali har ban san lokacin da na ida shiga ba.
Maheer yayi mini masauki kan ƙirjinsa,yadda jikinmu ya mannu da na juna yasa muka sauke numfashi a tare kafin Maheer ya soma yi mini sumba gefen wuya yana sauke mini numfashi mai ɗumi.Ƙanƙame shi na yi ina jin tamkar na fasa ihu,jikinsa na rawa ya ɗago fuskata yana mai kamo leɓena na ƙasa haɗi da soma yawo da hannunsa a sassan jikina.
Tuni casbin hankali da nutsuwarmu sun tsinke,dakyar ya iya fiddo mu daga toilet ɗin ya zube mu kan gado .Muryarsa can ƙasa a shaƙe ya ce "don Allah ki ci gaba da romance ɗina"
Ban iya ce masa komai ba,saboda abu biyu da suka saukar mini tsoronsa da kuma buƙatar zama abu ɗaya da shi.Oga Maheer namijin duniya ne cike da salon jan hankalin mace ya fara tafiyar da ni yana mai karanto addu'a,na rumtse ido da ƙarfi saboda azabar da na soma ji tana ratsa ni yayin da kuma kwanyata ke hasko mini ƙauyen Papy lokacin da ya shiga uƙubar Nalado.
Maitama na gani shi ma riƙe da wani littafi yana kirari wa fararen ruhika,har izuwa lokacin da suka wanzu a doron duniya suka shiga jikinsa.Nan take kuma garin ya dawo normal,yayin da kuma abotarsu da Nalado ta ci gaba da wakana ba tare da kowa ya bai wa ɗan uwansa labarin kiran dodon da yayi.A cikin sharuɗan da baƙin ruhi ya zartarwa da Nalado shine babu haihuwar mata a ahalinsa,duk macen da aka haifa shi ke shanye jininta,yayi da kuma ƴaƴansa maza suka taso cikin mugun sonsa da yin biyayya a gare shi.Tun yarinta suka fahimci wane ne mahaifinsu har izuwa ranar da Nalado aka wayi gari ya mutu,shi ne ya sanar da ƴanƴansa ko da an kai shi maƙabarta an rufe in dare yayi su je su tono shi su maido su ajiye a wannan ɗakin don ci gaba da rayuwa a cikinsu.Suna sonsa shi yasa bayan an gama komai suka je suka haƙo shi suka dawo da shi a cikin keɓaɓen ɗaki,tun a ranar ya tashi zaune kamar ba shi ya mutu ba.
"Zan ci gaba da rayuwa da ku har lokacin da zan ga kowa daga cikinku yayi arziki gobenku da ta ƴaƴanku kuma ta yi abin ƙwarai,sai dai fa akwai farashi dole ku bayar da ƴaƴanku domin wasu su cigaba" wannan shi ne furicin da Nalado ya hau ya zauna kuma duk suka yarda, wannan ne yasa ake ɗaukar member ɗaya a cikin family duk kowacce shekara.
"Queen? Queen ki buɗe idonki Please " na ji muryar Maheer tana faɗa,amma na yi banza da shi ne ƙi cewa komai.A daidai lokacin da Maheer ke janye jikinsa daga gare a daidai kuma wannan lokacin na soma jin wani ƙarfin iko na sake hawa kaina. Cikin ƙwaƙwalwata nake jin wata murya na yi mini raɗa "lokacin komawarki gida yayi".....
[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
34
Oga Maheer ne yayi mini wanka da ruwan ɗumi,tamkar wata mai jego haka ya gasa mini jikina da towel yana aikin jero mini sannu.Ido kawai na rufe saboda yanzu na dawo hayyacina na tuna kuma duk abin da muka yi,da irin yanayin da na gansa.Cikin wata siririyar murya ya shiga jero mini wasu addu'o'i masu tsayawa a rai tare kuma da godiyar abin da na mallaka masa mai daraja .A yadda yake da girman kai da izza sam ban tsammaci haka daga gare shi ba,idona a rufe na saki sanyayyen murmushi ina jin sonsa na ƙara samun gurbi ya kafa kujerar sarautarsa.
Wata jallabiyarsa H color ya saka mini,ya busar da gashin kaina ya fesa mini turare marar ƙarfi kafin ya ɗauko wata rigar sarauta mai hulla ya saka mini.
"Za mu je asibiti a duba ki" na ji muryarsa a slow,sai a lokacin na ware idona a kansa sai kuma na yi saurin sunne kai saboda muguwar kunyarsa.Na maƙe kafaɗa alamun ba zan je ba,"please ki yi haƙuri mu je sai nurse Fatee ta duba ki kin ga kin ji ciwo fa"
Hawaye suka zubo mini na ƙara maƙe masa kafaɗa ba tare da na ce komai ba,gusawa yayi daga kusan gadon da ya canzawa sabon zane.Ƙaramin akwati ya ɗauko tare da buɗe shi,ina ganin ya fara gyara zare da allura na fashe da kuka irin sosai ɗin nan.Cak ya tsaya yana kallona kafin ya ce "haka kike son ki zauna?"
Na kuwa gyaɗa masa kai ,yayi murmushi mai sauti kafin ya ce "a'a na ƙi ,a bari na gyara abina" na ɗauki pilow na jefa masa,yana murmushi ya fita bai wani jima sosai ba ya dawo hannunsa riƙe da leda.
Sai da yayi mini allurai kafin yayi mini ɗinki,daga nan bacci ya ɗauke ni ban ƙara sanin abin da ya faru ba.
Maheer ya ƙurawa fuskar HAULE ido,sai ya yanzu ma ne ya lura suna kama shi da ita sai dai fa ya fi ta kyawu.Laɓanta ya shafa waɗanda suke mugun burge shi,wani irin tausayinta ne ke ɗawainiya da shi ya fi kowa sanin in ba don ya nemi taimakon Yabobo ba an aika Ayush ta bata maganin nan ba da ƙila ba zai same ta cikin sauƙi ba.
Allurar shi ma ya haɗa ya yi wa kansa kafin ya raɓa gefenta ya kwanta,tunani ne birjit suka fara yi masa yawo ciki kuwa har da na labarinsa wanda yake jin ya kamata a ce in HAULE ta farka ya feso mata shi ko da kuwa ba ta tambaye shi ba.
Yana shirin rufe ido ya ji ana motsi a cikin drower,da sauri ya sauko sai ya tarar da shi yana wani irin girgiza haɗi da bado haske.A hankali ya buɗe shi sai ya ga dutsen sirrin nan ne ke motsi,ya juya ya dubi HAULE sai kuma ya ji tausayinta don ya san yanzu kuma ita ce za ta gudanar da duk wani aiki saboda ƙarfin ikonta ya fi nasa ƙarfi,wanda ke jikinsa ne ya fice ya shige ta.Wani irin ɗaci yake ji in ya tuna ita ce za ta shige gaba wurin fafutukar abin da ke tunkaro su.
★ A can duniyar BAƘIN RUHI kuwa komai ya tsaya cak,duk wata power da ƙarfin iko sun bar aiki saboda uwar gijiya da ta ɗauki muƙami mafi girman daraja a rayuwata wato daren farkonta da mahaɗin rayuwarta wanda cikar burika dayawa ya samu.Ƙungiyarsu El Mansoor da duk wata wacce BAƘIN RUHI ne ya samar da reshenta suna cikin wani hali.Ciki kuwa har da Jagaba wato Yaya Aliyu wanda yake tsaka da meeting da wasu sabbin members da ya ɗauka.
Cikin firgici ya fita daga ɗakin taron ya shiga na sirrinsa,duk wani abu da ya shafi magic bai yi.Yana cikin haka ne kiran Boss Sahil ya shigo wayarsa,yana ɗagawa ko kafin yayi magana shi ma na Oga El Mansoor ya shigo sai kawai ya haɗe kiran wuri guda ya mayar da shi na group.
"Jagaba meke faruwa? Muna tsaka da ƙaddamar da aiki komai ya tsaya cak babu magic babu amo" cewar Boss,yayin da shi kuma Oga ya ɗora da "hatta zoben muƙamin ƙarfin iko ya yi ɓatan dabo daga hannayenmu, sannan na lura duk wani tsafi da ke jikin nurse Fatee ya fita ya koma a jikin matata ya sakar mata cuta me hakan ke nufi?"
Jagaba Yaya Aliyu ya ce "ni ma a nan wurina haka take,amma bari na kira daga can sama na ji"
"Ina jin tsoro Jagaba,kar a je baƙin ruhi ya koma duniyarsa a daidai lokacin da muke shatike muke cin duniyarmu da tsinke " Boss ya faɗa.
Yaya Aliyu ya ce "hakan ba zai taɓa faruwa ba" ya faɗa tare da kashe kiran nasu sai ya kira can gida,sai kaf iyayensu maza babu wanda ya ɗauka da ya kira Innarsu kuma ita wayarta ma a kashe take .Jikin Aliyu sai yayi wani mugun sanyi yana jin alamomin faɗuwa na bayyana a cikin gurɓatacen ruhinsa wanda ya gina shi da mugunta.Babu shiri ya fita ya sallami baƙinsa kafin ya soma haɗa kayansa na barin ƙasar gaba ɗaya.
★
Shekarun da suka gabata abubuwa da dama sun faru a cikin babban gidan wanda ya rayu cikin zalunci da cutar da kai.Duniya ta yi musu murmushi sun fara cin amfani baƙar shukar da suka shuka ta shayar da jinin ƴaƴansu ga baƙin dodo wanda ya kasance RUHIN ALJAN(MRS SADAUKI) a cikin gangar jikin mahaifinsu.A kaf shekarun da suka gabata babu wata shekara ƙwaya ɗaya da ta zo wacce ba su bayar da ɗaya daga cikin ƴaƴansu ba,a irin haka ne suka ɗauki Fahad wanda silar hakan ya haifar wa da Innarsu Haule da ciwon zuciya saboda rayuwar ƙunci da take.
Canjin zanen da gidansu ya samu bai ƙare ta da komai ba,a kullum burinta shi ne ta ga ranar da za ta durƙusar da Nalado da kuma ƴaƴansa a ƙasa.
A yau gidan ya tashi da wani irin rikitacen al'amari,tun bayan da aka canza fasalinsa aka mayar da shi gini mai doron zabo a ka kuma zuba ƴan aiki da kayan kallo dukkan matan gidan sun saki jiki suna cin dukiya in aka cire ita Innarsu Haulen.
Safiyar yau wani rikitacen al'amari ne ya faru a gidan,ɗakin sirri wanda ya kasance iya shi ɗaya ne tal ba a rushe aka gina sabo ba shine yau da kansa yake wata irin tsuwa tamkar an sakawa memory sai abubuwa yake yi daban-daban ga wani irin guje-guje da ake yi haɗi da kukan dabbobi iri-iri,hakan kuma ta faruwa ne saboda dawowar wani ƙarfin iko da ya watsu a duniya yana rabu daga can tare da dawowa ga mai tushensa.
Kaf a halin gidan sun yi cirko-cirko,iya iyayen kawai suka san meke faruwa sai Hassana wacce gurbin idonta shi ma ke ta yi mata zugi tana jin tamkar wani abu na fita. Duk wayar da Yaya Aliyu ke yi musu suna gani sai dai in sun ɗauka ba su san me za su ce masa ba kasancewar babu wani da ya san da zuwan wannan ranar,abin da suka sani shi ne kawai akwai magajin wannan muƙami na dakon BAƘIN RUHI a cikin gangar jiki kuma tun da Aliyu ya zama zakaran gwaji a kaf cikin danginsa sai suke tunanin shi ɗin ne dai Jagaba sam ba su taɓa kawowa cewa HAULE ce ta gaba wacce za ta ɗauki dakon BAƘIN RUHI a gangar jikinta ba.
★HAULE