Bakin ruhi complete - Chapter 30
Bakin ruhi complete Chapter 30: Bakin ruhi complete Chapter 30. Bayan baƙar wuyar da Maheer ya shayar da ni ban wani jima ba bacci ya ɗauke ni sai kuma na…
3,308 words
Bayan baƙar wuyar da Maheer ya shayar da ni ban wani jima ba bacci ya ɗauke ni sai kuma na soma yin mafarkin rayuwata da ta gabata wacce na yi makarantar matsafa.A ranar da muka gama darasi haka suka yi mini sarƙa don cutar da ni ,hakan ya hassala ni duk suka zube ƙasa kamar matattu a wannan gaɓar ce headmaster ya ce zamana a nan ba zai taɓa yiyuwa ba amma kafin nan zai bani wani abu.Na yi tunanin abin arziki ashe mugunta ce ya shirya mini,haka ya kai ni wani ɗaki mai masifar duhu ina shirin yin magana ƙofa ta ja ta ƙage kanta.A bisa wani abu da ke ƙyalli tamkar gudun ruwa ne na hangi wasu idanuwa suna kallona,kafin na soma jin tamkar ana kusanto inda nake sai dai babu haske ballantana na gani.Ido na rumtse hakan sai ya ƙara mini ƙarfin jin sautin,a hankali na soma fafutukar damƙo shi har Allah ya bani sa'a kuwa na cabko shi .Wata irin narkakar azaba ce na ji tamkar irin mutum ya taɓa wayar lantarki,a daidai kuma wannan lokaci ne idona ya iya ganin mummunar halittar wacce ba zan taɓa manta ranar farko da na taɓa tozali da ita ba.Ban sani ba ko haɗuwar hannuna da jikinsa ne ya fesar da wani abu mai kamar iskar tiyagas ko me,amma ta silarsa ce na fito daga wannan makaranta aka halbo ni wata ƙasar wacce ta bani damar zuwa gidan Hajiya a matsayin ƴar aiki.
Fuska na yamutsa jin kamar ana shafar mini gira,a hankali kuma na ware idona a kansa.Sai ya sakar mini murmushi yana cewa "Queen kin tashi?" ban basa amsa ba sai idona da na ja na kulle,"ki tashi ki ci abinci" ya faɗa wannan karon yana mai ɗora hannunsa kan cikina,"ban so!" na faɗa a shagaɓe,ya saki wani ɗan murmushi mai sauti kafin ya ce "sai me kike so?"
"Bacci zan yi!"
"A'a ya isa a haka! Ki tashi ki yi sallah ma ko da daga zaune ne"
"Na ƙiya ni banda lafiya"
"Please Babyna!" ya faɗa ,da sauri na buɗe ido jin sunan da ya kira ni.Ƙuri muka yi wa juna kafin daga bisani ya soma yawo da yatsunsa kan fuskata har ya kawo ɗaya kusan bakina na yi rab da shi na cije .Ya shiga yin dariyar nan mai tafiya da imanina,"ka sauke ni ƙasa please kafin Hajiya su dawo"
Wani irin kallo ne ya jefo min kafin ya ce "ban gane na sauke ki ƙasa ba,to ƙasa wurin wa? Wa zai kula mini da ke?"
"Ni zan kula da kaina"
"Sai ka ce wata babba,ke da ba ki wuce a dinga feeding naki ba ke ce kika san wani kula da kai?"
"Ni da ban iya tsarki ba ko?" na faɗa ina haɗe rai,shi kuwa da sauri ya ce "ni dai ban ce haka ba"
"Ai ranar nan ka faɗa "
"Wasa nake miki ai"
"A'a na ƙi wayon a gaske kake " Bai kula ni ba saboda na soma yi masa rigima a gasken gaske,fita yayi ni kuma na ƙoƙarta dakyar na tashi na shiga toilet.Ina fitsari kamar na fasa ihu tsabar zafi,har da ƴar guntuwar ƙwalla.Bayan na yi alwala na shimfiɗa dadduma na zauna na fara yin sallah,ina shirin salamcewa ya shigo .Bayan na gama sai da na yi addu'o'i na shafa ,sannan ya zo ya ajiye trayn a gabana.Na turo baki ina gunguni amma don tsabar hali irin na Maheer sai da ya fassara ni.
"Shi ne aka ƙi kawo miki kazar amarci don an ga har an yi daren farko?"
Tsakiyar idonsa na kalla na shiga yi masa murmushi,kafin ya zuba mana abincin sai kuma ya hana na saka hannuna ya dinga bani da nasa ba ko da cokali ba. Yadda nake jin yatsunsa a bakina hakan ba ƙaramin shauƙi ya saka ni ba,sam ji na yi ma tamkar ana ƙara mini wata yunwar tsabar yadda na saki jiki na ci sosai .Ina shan ruwa ya bani magani sannan na shiga toilet na yi brush,ina fitowa na ce "sai an jima zan tafi ɓangarenmu"
"Ga Maheer mahaukaci sai ya bar ki haka nan ki fita?" ya faɗa yana tsure ni da ido . Na kangaɓar da kai na ce "ayyaaa zan je na kwanta na huta ne"
"Nan ɗakin kuma babu abin kwanciya?"
"A'a akwai amma a can zan fi samun nutsuwa hankali kwance na yi bacci,kuma ..kuma ni ban saba kwanciya kan gado ba"
Maheer ya ƙanƙance ido ya haɗe ya dawo sak yadda yake tun farko kafin ya ce "me yasa ba ki son zaman lafiya? Ko kin manta halin da kike ciki ne? Sai na bar ki kuma ki sauka ƙasa ki je ki ci gaba da yin aiki?"
Na yi ƙasa da idona ina jin wani irin tsoronsa fiye da na can farko.Mu je ki kwanta ya faɗa tare da soma cire mini rigar ta sama,na riƙe ta gam na ce "ni dai ka bar min ina son kayata"
"Zan canza miki wasu kayan ne ki sha iska"
"A'a don Allah!" na faɗa kamar zan yi kuka,ya kama hannuna ya ja muka je can kusan bed.Ya zaunar da nu kafin ya shiga wanka,da sauri na tashi don guduwa sai dai fa ƙofar ta ƙi buɗe wa .Babu shiri na koma can bedroom ɗinsa daidai nan shi kuma ya turo ƙofa sarai kuma ya ganni,ya girgiza kai ni kuma na turo baki gaba ina jin wani iri.
A gabana ya kimtsa sannan ya zo ya kama hannuna ya ce "taso mu je to na ga da dukkan alamu ba ki shirya sanar da Hajiya matsayinki a gidan nan ba,sai dai fa ba zan yarda ki ci gaba da sayar da abinci ba"
Miƙewa na yi sai ya ja ni zuwa bakin drowersa,ya buɗe dutsen ranar nan ya danno haske.Maheer ya ɗora yatsansa ɗaya ni ma haka can sai ga dutsen ya buɗe tamkar wani akwati.
Ba komai ne a ciki ba sai wata gajeriyar wuƙa mai ɗauke da wani rubutu,"wannan shi ne makamin da ke iya kashe baƙin ruhi kawai,na san ba sai na faɗa miki cewa ke ce za ki kashe shi ba ,ki kula sosai sannan ki nutsu yayin aiwatar da aikin" Maheer ya faɗa yana mai ɗauko wuƙar ya ɗora mini ita a tafin hannu.Wani irin shock na ji,da sauri na lumshe ido wasu irin sabbin abubuwa na ratsa duk wani ɓargon jikina.
Tsawon lokaci ina a haka kafin Maheer yayi mini rakiya zuwa ƙasa,har cikin ɗakinmu ya kai ni sai ya zauna tare da ni."Ina son tafiya gida" na faɗa dakyar kamar wacce aka yi wa dole,Maheer ya ce "na sani ! Amma ai tare za mu je" Na girgiza masa kai na ce "a'a ni ɗaya zan je kai ka zauna a nan ƙila za su buƙace ka" "To sai yaushe za mu sanar da Hajiya zancen aurenmu?"
"Ka jira lokaci kawai shi ne zai sanar"
Haka muka ta yin hira har lokacin sallar la'asar yayi, Maheer ya fita kenan su Hajiya suka dawo. A zaune suka tarar ina sallah ,babu wanda ya san dalilin zaman in banda Aliya da take danne dariyarta anty Bahijja kuwa wanka ta shige yayin da Yasmine ta kwanta bacci, Lubna kuwa kallona take da mamaki kafin ta ce "lafiyar yin sallah daga zaune?"
"Lafiya lau har kun dawo?"
"Eh! Amma ya na ganki duk wani iri?" Lubna ta sake tambaya,ban bata amsa ba na jawo jakar kayana na ɗauko furen floris na jimƙe da hannu ina mai lumshe ido nan take ya koma zobe na saki murmushi sannan na kamo hannun Yasmine na saka mata shi.
Da anty Bahijja ta shigo ita ce ta soma jansu da hira yayin da ni kuma na yi lamo ina tunanin abin da muka yi ni da Maheer.Ina sonsa wannan yasa duk uwar wuyar da na sha ban ji haushinsa ba.
Ana turo ƙofa na ɗago kai,shi ne sanye cikin shirin fita fuskar nan tamau.Duk gaishe shi suka shiga yi ,ya amsa musu idonsa na kaina Lubna uwar iya yi sai cewa ta yi "Haule ke ba za ki gaishe da Alhaji ba?" kanzil ban ce mata.
Shi kuwa inda nake ya matso ya ajiye ledar hannunsa ,can ƙasan maƙoshi kuma ya furta "ya jikin naki?" sai da na saci kallonsu na ga duk sun kawar da kai in banda Lubna da ta saki baki tana kallonmu.
Yadda ya sunkuyo ya kuma ƙi miƙewa yasa fuskokinmu suke dab da juna,da kyar na ce "na warke fa ka tafi"
Ya saki murmushi mai sauti tare da shammata ta ya ɗora hannunsa kan cinyata yana mai cewa "bari mu gani to" da sauri na jimƙe hannunsa ina kafe shi da na mujiya,ba zato na ji yayi min kiss kan leɓe kafin yayi tafiyarsa.Na ja wani dogon numfashi ina mai kallon Lubna,raina na ji ya ɓace irin sosai ɗin nan ban taɓa sanin kuma ƙarfin powerta ya hauhawa ba sai da na ji Lubna na ihun wayyo idonta ba ta gani....
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
35
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ihun Lubna shi ya fargar da ni kan aika-aikar da na yi mata ba tare da na sani ba,haka kuma ba ni ce na tsara yin haka ba.
Aliya ta ƙyalƙyace da dariya tana kallona kafin ta ce "da kyau Queen! Ke kuma gobe sai ki sake yin gulma a toh in ba gulma ba Sarki da basarakiya na lubayya shine za ki kafe su da shegun idonki masu kama da na fara"
"Aliya ya isa haka mana! Ni ma ba da son raina na yi ba" na faɗa tare da juya idona suka kawo haske tare da fita ya shiga cikin na Lubna nan take ta dawo normal,ba ta ƙara ko da minti ɗaya ba ne ta fita ta bar ɗakin daidai nan kuma Yasmine ta farka tana mai cewa "Mama yanzu na gama mafarki an tarwatsa duniyar BAƘIN RUHI,Dad ya zo ya neme ki gafara ya ce ya tuba ki zo mu koma can gidansa.Amma Please Mama ko a gaske hakan ta faru don Allah kar ki je ni ban sonsa na tsane shi"
Na saki murmushi kafin na ce "dama ba za ku koma ba,in sha Allah za ku je can gun danginku"
Yasmine wacce na gani ta ƙara kyau a yanzu duk wata sauran damuwarta ta kau sai ta zo ta rungume ni. Haka muka dinga tattaunawa akan abubuwan da suka shuɗe har dare yayi muka ci abinci muka kwanta Lubna ba ta dawo ba.Washegari ma haka sai jibi ta zo a ranar da ake ta hada-hadar zuwa ɗaurin auren Maheer da kuma Ikilima,tun a daren jiya nake fushi da shi akan na ce ya je ya samu Hajiya ya ce a fasa auren amma ya ƙi ya ce ba zai iya watsa mata ƙasa a ido ba.
Tun da na yi sallar asubah nake a kwance kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa,Aliya da anty Bahijja waɗanda su biyu kawai suka san da igiyoyin aure a kaina sun yi rarrashi har sun gaji .Hatta ciwona ya warke,zare kawai za a cire amma na ƙi aje hankali ballantana har ya samu damar fidda mini shi.
"Ki daure ko madara ki sha" cewar anty Bahijja tana mai miƙo min kofi cike da madara,cike da takaici na kalli kofin nan take ya tarwatse a hannunta har sai da ta ji tsoro.Aliya ta zo da sauri ta ja hannun anty Bahijja suka fice,kafin ta dawo ita ɗaya ta zo ta gyara wurin da ya ɓace.
Cikin jin haushi na ce "Aliya wato ku ba ku damu ba ,za a yi mini kishiya shine kuka samu damar cin abinci har da shan madara?" ina gama faɗar haka sai ga hawaye. Ta girgiza kai kafin ta ce "Haule ƙin cin abinci ai ba shine mafita ba,ki sani wannan salon kishin raggon salo ne.Ki jira kawai har dare yayi lokacin da aka kawo amarya zan faɗa miki yadda za ki yi,ta yadda Oga Maheer ba zai iya kusantar kowacce mace ba sai ke"
"To amma ai ta aure shi dai" na faɗa ina shafar ƙwalla.
Aliya ta ja tsuki ta ce "ke fa matsalata da ke wani sa'in kanki sai yayi ta rawa ta yadda ba ki tsayawa ki fahimci abin da ke gabanki,to mene ne auren? Ina ce dai ga banza don ka auri mutum amma ba ku kusanci juna ba.Ni fa yadda kika tayar da hankalinki ya fi ban takaici kan maganar auren ,tun da ta ji ta gani mijin wata za ta aura ai sai a zuba mu gani mu da ita shege ka fasa" a hassale ne Aliya ke maganar ,ranta kuma sosai ya ɓace ni kuma hakan da na gani yasa na ɗan ji sassauci.
Cacaniyar dangi da abokan arziki kuwa ta cika gidan,gefe guda kuma masu yi wa amarya jere ne a can sama aka buɗe ɗaya sashen da ke da kwai.
Toilet na shiga na sakarwa kaina shower,ruwan pampo da na idona suna ta zuba lokaci guda.Ina nan tsaye na ji an shigo ana guɗa wanda hakan ke nufi an ɗaura auren dai ,sautin kukana ne ya ƙaru ina ta tunanin yadda Maheer ya shayar da ni zumar soyayya. Sama da minti talatin ina ciki ban fito ba har sai da na ji Aliya na bubuga ƙofa,kasa kallonta na yi na je na canza kaya kafin na hau dadduma na fara sallah.
"An ɗaura! An ɗaura! Yau dai Oga Maheer Allah ya yi nufi zai angonce waiii irin wannan shekaru da ya ɗauka bai yi aure ba yau akwaita " Lubna ce ta shigo tana faɗar haka,duk da ina cikin yin sallah sai da na ji hantar cikina ta kaɗa a haka dai na daure na ci gaba da yi.
"Haba Lubna ya kike murna abun ko kara babu?" anty Bahijja ta faɗa .
"Kara ta me? Ai na haƙura da shi kin san an ce in son gaske kake yi wa mutum to dole ka so duk abin da ke saka shi farin ciki"
"To an gode kina iya tafiya" Aliya ta faɗa .
"In tafi in je ina? Hahaha! Ina ce dai kafin duk ku zo nan gidan ni ce farkon zuwa kuma k..." sauran maganarta ce ta maƙale mata a maƙoshi saboda kamun sandar makauniya da na yi wa maƙogoronta ba tare da kuma na motsa daga inda nake zaune ba.