Bakin ruhi complete - Chapter 3
Bakin ruhi complete Chapter 3: Bakin ruhi complete Chapter 3. Yanayin fuskar Lubna ya canza kafin ta ce "ban ma san daga ina zan fara ba,farko dai zan iya…
3,350 words
Yanayin fuskar Lubna ya canza kafin ta ce "ban ma san daga ina zan fara ba,farko dai zan iya cewa na yarda da karin maganar nan da Hausawa ke yi ' ba duka ƙyalƙyali ne gwal ba' tabbas na yarda da hakan bayan shekaru biyu da suka gabata na rayuwata.Kamar dai kowacce ƴar talakawa haka na tashi da burin samun aiki mai tsoka , wannan yasa na kashe kaina wurin yin karatu tuƙuru.Na bi duk wani matakin ilimi da kika sani,na yi digiri har da digirgir sai dai fa samun aiki ne ya zama jan aiki.Tun ina ajiye takarduna har na gaji na bari,cikin haka ne Umma ta sama min gurbin aiki nan wurin Hajiya can farko iya zuwa can restaurant ne aikina ina kai wa costumer abinci .Kamar yadda kika sani iya wannan aikin kawai ba wani kuɗi ne masu yawa ba,amma haka nake yi don gujewa zaman banza.Sama da wata biyar ina wannan aikin ,daidai ɗaya rana ban taɓa cire burina na samu babbar kujera akan karatun da na yi ba.Sau tari ina jin haushi in na ga masu kuɗi suna shigowa nan su ci abinci na kuɗaɗe dayawa har su bar ragowa nan.Masu zuwa da ƴan mata kuwa haka zan zauna ina ta kallon yadda maza ke tattalinsu,duk abin da kika duba a jikin ƴan matan kuɗi kawai ke magana.Sai fa rayuwarsu ta soma burge ni ina sha'awar cewa ina ma ni ce,zan iya ce muku ma har hassadarsu ke tsarga min musamman in na ga mace wacce ba ta yi wani dogon karatu ba amma tana da kuɗi sosai nake jin haushi.Sai kuma ƙarfin imanina yayi ƙasa ina ganin Allah ya azurta kowa amma ni ya bar ni cikin ƙuncin talauci ni iyayena waɗanda kusan ma a lokacin ni ce ke kula da su saboda Abbana da ya samu karaya bai aikin komai.
Kusan da wannan burin yin kuɗi nake kwana nake kuma tashi da shi har Allah ya jefo min wata ƙawata da muka yi makaranta da ita.Ba zan manta ba wata baƙar rana ce wacce ta shiga lissafin ƙaddarata,ina kwashe plate ɗin da aka ci abinci na ji muryar wata da na sani ta kira suna "oh Lubna ? Ke ce?" ni ma cike irin zumuɗin nan irin ka jima ba ka ga mutum ba na nufe ta zan rungume ta amma don wulaƙanci ta yi saurin ja baya tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi kafin ta ce "wai ƴar aiki kika zama bayan duk uban karatun da kika yi? Ki rasa abin da za ki yi sai tarben customer ?"
Duk da na ji babu daɗi haka na danne zuciyata na ce "to ya zan yi tun da ban samu aikin gwamnati ba,faɗa min Zulaihat ina kike aiki?"
Ba ta bani amsa ba sai wuri da ta samu ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin,"me ke da kwai marar nauyi ? Don yunwa nake ji shi yasa ma na tsaya da motata cikin rana na ci abinci na wuce" ni kuwa gwiwaina ne suka yi sanyi jin Zulaihat ce wai da mota duk da ban yi mamaki ba duba da suturar jikinta iya jakarta ma tana iya ciyar da ƴan gidanmu na tsawon wata biyu,uwa uba kuma wayarta iphone wacce kusan duk masu zuwa restaurant ɗin nan ina ganinsu da ita. Jiki na yi min ɓari na ce "jira na je na kawo miki" sai na koma can ciki na haɗo mata abincin da na san ƴan gayu irinta na so har da lemun kwalba,da na kawo mata sai ta bani damar zama kan kujerar da ke kallon tata.A kunyace na zauna, Allah yayi min sa'a ma babu kowa.Cike da yanga take juya cokali cikin plate ɗin kafin ta soma ci tana latsa waya,message ne na WhatsApp ta soma kunna wa ina saurare kusan duk akan manyan kuɗi ne da kuma kayan da mutane suka yi oder ko kuma suka saya suka yaba,can kuma ta soma mayar wa na ji tana zancen za ta tura miliyoyin kuɗaɗe.Ni kuwa ina zaune sake da baki ina kallonta,kuma kar ku ji zancen wasa wallahi burge ni ta yi yadda take abu na ƴan gayu.Hummm! Faɗar mintinan da na share a zaune kafin Zulaihat ta dube ni ƙaramin misali an fi goma sha,can ta ɗago ta dube ni da idanunta da suka sha gashin zamani ta ce "Lubna gaskiya ba zan ɓoye miki ba na ji takaicin ganinki a wulaƙance kina boyi-boyi,da kyawunki da iliminki.Amma dai komai ya wuce tun da Allah yasa mun haɗu zan duba na gani"
Ba tare da na san wane aiki ne za ta samo min ba na shiga yi mata godiya,nan ta shiga nuna min hotunanta da ta yi ƙasashen duniya .Ni kuma sokuwa girman burina sai ƙara farashi yake ina jin cewa ni ma nan gaba kaɗan zan koma kamar Zulaihat,da za mu rabu sai ta bani lambata da ke jikin wani ɗan ƙaramin kati mai ɗauke da dukkan address ɗinta da kuma kantinta na business.Ba ta bar ni haka ba,sai da ta ware dubu goma ta bani shi ma wai don ba ta da canji ne kuɗinta duk daloli ne.
Da na isa gida kasa bacci na yi,haka na yi ta juyi kan shimfiɗa .Saƙo kuwa na rubuta shi ya fi cikon casbi kuma sai na goge a ganina sam ba ta cancanci in yi mata text ba.Can na daure na kira ta, lokacin ƙarfe goma saura kwata na dare,har zan yanke kiran sai kuma na ji ta ɗauka tana cewa "Lub baby ƴar halak kin ƙi ambato yanzu na gama maganarki wurin oga "
Na washe baki na ce "na zata ma kin yi bacci,na gode sosai da wannan ƙoƙari me ogan ya ce ?"
"Ki zo gobe nan babban kamfani yana son ganin ki,sannan ki haɗo da takardun karatunki sai takardar shaidar ɗan ƙasa da kuma hotonki kala biyu "
Tamkar na yi hauka haka na ji lokacin ba tare da na san ƙaddara ce da rabon a yi ke ja na ba.Tun a daren na jawo ambalof na shiga haɗa takarduna don dama kusan ina da komai da ake buƙata in aka fidda hoto.Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ni a wannan daren,shi ma rabi da rabi ne.Tun bayan sallar asubah na shaidawa Umma zancen aikin sosai ita ma ta yi murna.Zuwa ƙarfe takwas na je gidan hoto aka yi min guda biyu,a nan take kuma aka bani su.Daga nan na kira Zulaihat sai ta ce na jira za ta zo ta ɗauke ni,ina nan tsaye ina jiran zuwanta sai wata tsohuwa ta tsaya kusa da ni tana mai neman sadaka .Murnar na samu aiki yasa na zuge jaka na bata sadaka,tana karɓar kuɗin sai ta soma juya su haɗi da kallona tsakiyar ido ta ce "ƴata ki koma gida inda za ki je ɗin nan babu alkhairi " wani irin haushin ta bani kafin ma na kai ga yin magana Zulaihat ta parker motarta tana yi min horne,da sauri na zagaya na buɗe na shige ina jin tsohuwar nan na sake jaddada min maganarta amma na yi kunnen uwar shegu da ita .
Fuska a sake muka gaisa kafin ta ce "ke ma dai kin kusa ki faso gari ki huta da yawon raba abinci a restorant"
Na yi murmushi na ce "ai kuwa dai kin ga ban ma shaida wa Hajiyar na samu aiki ba"
"In an gama miki interview ai sai ki je ki sanar da ita"
Haka muka ta yin hira har muka isa wani katafaren kamfani,duk da ina cikin garin amma ni ban taɓa ganinsa ba da idona ina dai jin labarinsa.Tun da muka fito daga cikin mota ake gaishe da Zulaihat,sai na fahimci tana da babban matsayi a wurin . Jikina ne ya soma yin rawa lokacin da muka shiga ofis ɗin ogan,komai na wurin ja ne tun daga labulaye capet da kuma kujeru.Hatta kalandar da ke ɗauke da jerin sunayen watanni ita ma ja ce,haka ma book ɗin nan da mutane ke ɗauke abu mai muhimmanci shi ma ja ne.
Wuri ta nuna min na zauna kafin ta ce "jira yanzu zai fito" sai na sakar mata murmushi kawai ina mai ci gaba da sauraren bugun zuciyata.Kamar minti biyar haka wani babban mutum ya fito,baƙi ne wulul kuma gajere yana da ƙiba sosai ga kuma ƙaton tumbi kamar mai cikin wata tara .
Cike da girmamawa na sauka na gaishe shi har ƙasa,ya amsa cikin sakewar fuska kafin ya bani umarnin na koma inda nake.Zulaihat ce karɓi takarduna ta miƙa masa,a nutsu ya shiga duba su kafin ya soma yi min tambayoyi ina basa amsa daidai da abin da na sani.
Ya yi wani murmushi da ya ƙara bayyana muninsa kafin ya ce "Zuly ƙawarki nada kaifin basira kam,ina ga ita ya kamata mu baiwa kujerar mai kula da baƙinmu na waje ko ya kika ce?"
Ta yi wani murmushi tana mai cewa "ai kuwa ko a makaranta ita ce ta ɗaya,sannan ta saba jagorantar duk wani abu da ya shafi jagoranci ina ga babu matsala in dai ta yarda za ta yi"
Sai duk suka maido dubansu gare ni,wata irin rikicewar na yi da kuma mamakin ƙarshen furucin Zulaihat wai in na yarda.To me zai hana na yarda ? Abin da na jima ina nema ɗin shekara da shekaru.
"Ba ki ce komai Luby" Zulaihat ta faɗa . Muryata har rawa take na ce "na yarda mana ina so,in dai maganar turanci ce ai kin san nan na fi ƙwarewa babu wata matsala" ina gama faɗar haka sai ogan ya miƙo min wata takarda haɗi da jar biro ya ce na saka hannu a ƙasa wanda ke bada tabbacin na yarda da dukkan sharuɗan zan yi aiki a kamfanin . Hum! Haule kin san dayawa mutanenmu ƴan Afirka muna yin babban kuskure shi ne saka hannu a takardar da ba ka karanta jawaban da ta ƙumsa ba,to ni ma a lokacin haka na rabbata hannu na miƙa masa.A tare suka saki wata ajiyar zuciya mai bayyanar da tsantsar farin ciki.
Sai a lokacin kuma ogan ya buɗe ƴar takardar da ke ɗauke da hotunana biyu,ɗaya ya ɗauka sannan ya buɗe wani fayil mai ɗauke da hotunan mutane dayawa sannan ya maƙala nawa tare da yi masa wani rubutu can ƙasa. Bayan ya gama sai ya dubi Zulaihat ya ce "ki kai ta wurin shopping ki tabbatar kin zaɓa mata kayan da za su fi dacewa da aikinta,sannan inda buƙata har gyaran jiki a yi mata .Kin dai fi ni yadda ya kamata na bar miki komai a hannunki,sannan zuwa gobe za ta soma aikin kuna iya tafiya"
Ba mu ƙara cewa komai ba muka fito,cikin yanayin tsarguwa na ce "Zulaihat mene ne kuma na yin gyaran jiki? Halan datti gare ni irin sosai?"
Ta tuntsire da dariya ta ce "in ba abinki ba ke da za ki tarben turawa in ba ki kama kanki ba kina ganin za su yarda su zuba hannun jari a kamfaninmu?" Murmushi kawai na yi na basar,daga nan gidan gyaran jiki ta kai ni cikin wata ƙatuwar inji na shiga iya kaina kawai ke waje shi ma bayan an gama wannan ɗin sai da aka saka min relax aka sa ni a tukunyar busar da gashi.Bayan mun gama komai sai ta saya min wata doguwar abaya wajen matar mai gyaran jikin,na saka sai na dawo tamkar wata balarabiya na yi kyau sosai.Daga nan gidan cin abinci muka je bayan mun cika tumbinanmu sai muka wuce mall,yadda na ga Zulaihat na jido riga da wando yasa na yi mata magana don ba zan iya saka su ba amma sai na ta saurare ni.Bayan su kuma ta saya min har da after dress da kuma sari ,wasu kayan ma ban san da irinsu ba.
Na yi tunanin gida za ta kai ni amma sai ta wuce da ni gidanta,a falo muka zube ta sa masu aikinta suka kwaso tulin kayan da ta sayo min kowanne da takalminsa. Sai da aka kawo mana kayan maƙulashe muka taɓa tare da jus sannan na soma duba kayan,sai dai ban ɗauki lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni a nan take kuma na soma yin wani mafarki marar kan gado..... [02/04 11:31] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
05
Mafarki ne wanda sam rabon da na yi sa ina jin tun lokacin isar min da saƙon balaga.Sai da wannan ya sha banban da wancan,don wannan sarai ina ganin wanda ke tarayya da ni.Ba kowa ba ne ba sai oganmu wanda yanzu ya gama yi min interview,abin mamaki kuma a cikin mafarkin bai fi yadda yake yabona ba yana cewa "ashe Zuly ta yi gaskiya kina da taurari masu kyau masu haske,ke ɗin maƙurar ilimi ce" ban farka ba har sai bayan komai ya kammala.A hankali na buɗe idona da suka yi min nauyi,sam ni na manta ma a inda nake sai bayan na watsake ne na tuna gidan Zuly ne nake.
A hankali na tashi zaune ina jin duk jikina na yi min ciwo kamar wacce aka yi wa shegen duka.Ta zo da murmushinta ta ce "ashe kin tashi? Bari na sa a haɗa miki ruwan wanka in kin gama sai ki ci abinci"
Ɗan murmushin yaƙe na yi na ce "to" sai ta ƙwala kiran ƴar aikinta bayan ta zo ta faɗa mata aikin da za ta yi sai kuma ta dube ni kamar mai son tantance wani abu kafin ta ce "kayanki suna ɗakinki an jera a drower"
Abun mamaki kasa yi mata muso na yi ko kuma na tambaye ta yaya na samu ɗaki a nan gidan.Ita ce ta yi min jagora na isa can ɗakin wanda tuni an haɗa min ruwan wanka a baho,kar ku ji zancen wasa a ranar nan Zuly ce ta yi min wanka tamkar wata ƴarta ni kuma na kasa yin wani kataɓus.Duk da ina tune na yi mafarki amma sam tunanina bai bani na tsarkake jikina ba,saboda controling nasa ake yi.Bayan na fito ita ce ta bani kayan da na saka,sannan aka kawo min abinci kamar yadda ta shaida min tun farko.A cikin abincin nan Allah kaɗai ya san irin kalar maganin da aka saka min amma a haka na ci,kar ku tambaye ni maganar sallah don dama can farko ni ɗin na kasance mai wasa da ita ba kullum nake cika biyar ba sai in Umma ta yi min faɗa wannan yasa ko kaɗan ban samu ƙarfin zuciyar yunƙurin yinta ba. Ina cin abinci Zuly na yi min hirar yadda aikina zai kasance a gobe da kuma yadda tsarin yake,sai kuma ta soma nuna min yadda ake yin aiki da wata ƙatuwar waya bayan nan kuma ta kira ƴan aiki biyu suka yi min tausa da wani man da aka tanada don yin tausa sai dai shi sun garwaya shi da gubar tsafinsu. Har cikin ɓargon jikina nake jin yana ratsa min ,a sannu a hankali kuma bacci ya ɗauke ni nan ɗin ma mafarki na yi gani nan a wani ɗakin taro duk turawa ne ciki ni ɗaya ce baƙar fata.Masayar turanci kawai muke yi kowanne na yaba kamfanin da yake yin aiki,bayan mun gama meeting kuma sai muka je muka yi wanka cikin swimming pool maza da mata haka duk muka shiga ciki babu wata suturar kirki.Ina farkawa wannan karon babu kowa a ɗakin sai ni ɗaya,sannan babu wani haske sosai shuru na yi ina daidaita tafiyar numfashina.Daga nan kwance na ga lokacin da wata baƙar inuwa ta fita amma ban iya tantance ta mace ce ko ta namiji. Kamar minti biyu sai ga Zuly ta shigo tare da kunna ƙwan lantarki,na lumshe ido tare kuma da buɗe su. "Ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai saura "shine abin da ta ce min. Da mamakin jin wai har dare yayi gari ya waye na ce "kina nufin yanzu safiya ce?" wani irin kallo ta yi min kafin kuma ta fita,na sauke ajiyar zuciya na tashi na shiga toilet sai a lokacin kuma na lura da an canza min kayan jikina zuwa na bacci.
Cikin bahon wankan na shige,ina tunanin kaina a can ƙasan zuciyata sai dai fa na kasa tuna wace ce ni daga ina nake abu guda kawai ke cikin ƙwaƙwalwata shi ne aikina da kuma Zuly sai oganmu wanda nake jin mugun tsoronsa ya samu wuri a zuciyata ya zauna daram.
Bayan na gama wankan sai na fito,da taimakon wasu turawan masu aikinta na kimtsa cikin wasu arnan kaya riga da wando waɗanda suka ɗame ni sosai suka fitar da shap ɗina.Tamkar wata ƴar tsanar roba haka na koma na yi kyau sosai,gashin kaina kuwa an dunƙule min shi tsakiya sai aka ƙara min da ribbob na gashin doki ta yadda ya sauka har gadon bayana.
Zuly ta shigo ita ma cikin shiga mai kyau sai dai na fi ta haɗuwa kasancewar na fita kyawun fuska da na jiki.Jaka ta miƙa min da sabuwar waya irin ƙatuwar nan wacce ake aikin ofis,kafin ta ce "mu je" ta kamo hannuna,dakyar nake tafiya saboda yadda ban saba hawan takalmi masu tsini ba.
Da muka fito harabar gidan nan na ga ikon Allah don kuwa ba gidan da muka zo ba ne ni da Zuly,wannan tamkar aljannar duniya haka yake.Hatta motocin da ke wurin sun sha banban da waɗancan,cike da girmamawa aka buɗe mana gidan baya muka shiga abun mamaki har da masu take mana baya.Sai da muka hau babban titi ne sannan na gane nan ɗin fa Turai ce ba Afirka ba,wani kamfani ne muka je tun a bakin ƙofa Zuly ta tsaya kafin ta ce "ki nutsu ki aiwatar da aikinki kar ki wani damu jin cewa ke ce baƙar fata a cikinsu" kai na jinjina mata kafin Bodyguard biyu su take min baya har zuwa ɗakin da za a yi meeting ɗin.
Direct kujerar da ke ɗauke da sunana na je na zauna,suna ne wanda ba wanda uba mahaifina ya saka min ba a'a Oga ne ya canza min shi ba tare da na san ta ya aka yi kuma na gane nawa ne ba.Leena shine sunan da ke jikin ɗan ƙaramin allon gabana,sai da na yi gyaran murya sannan na danna wayar hannuna wacce ke ɗauke da dukkan bayanan da za mu tattauna a kai.
"Sunana Leena daga ƙasar Kamaru,wakiliyar kamfanin El Mansoor a yau mun kawo muku wata babbar haja wacce muke fatan za ku ji daɗinta sosai fiye da sauran business namu na baya" ina kawowa nan sai na yi shuru ina yi musu murmushi su kuma duk fuskokinsu sun nuna zaƙuwar jin abin da zan ce ɗin.
Na ci gaba da cewa "a ƙididdiga ta malamanmu na spirituality sun gano cewa dayawan mutane a yayin yin bahaya mutum na zubar da kaso hamsin cikin na abin da ya shafi taurarinsa marar kyawu,yayin da kuma zubar da yawu a lokacin da mutum ke tsugunne kan salanga yake ɗauke ɗigo biyu na sinadarin tauraronsa mai haske.In muka haɗa hamsin da biyu sun tashi ɗari cicif.Na san dayawanku za su tambaya ta ya aka yi aka samu ɗari? To amsar mai sauƙi ce duk tauraro mai haske ɗaya yana daidai da kaso hamsin na baƙin tauraro,da za a saka su a injin markaɗe a garwaya su to tasirin farin tauraro ne zai ƙwace kaso mafi rinjaye.Kun ga shi kenan mun samu tauro ɗari kenan" duk shiru suka yi suna nazari amma babu wanda ya iya cankar ainahin gamsashiyar amsar kawai sai suka fara yi min tambayoyin yadda za su yi su zuba hannun jarin wanda dama ni shi nake jira.Sai na soma yi musu bayani dalla-dalla "iya adadin kuɗin da mutum ya zuba iya adadin taurarin da zai samu,kenan kowa sai ya aiko min da saƙon abin da ya yanke ta adreshing email namu" Ina kawowa nan sai Zuly ta shigo ita da wasu masu aiki su biyu suna ɗauke da tray,amma ita Zulyn ce ta ajiyewa kowa kofin shayi a gabansa tana ajiye min na ɗauka na soma kurɓa ina kallon yadda suke shawara a tsakaninsu.