Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 4

Bakin ruhi complete - Chapter 4

Bakin ruhi complete Chapter 4: Bakin ruhi complete Chapter 4. Ba a kuma ɗauki lokaci ba kowa ya soma faɗin abin da zai zuba na hannun jari,bayan nan duk…

3,313 words

Ba a kuma ɗauki lokaci ba kowa ya soma faɗin abin da zai zuba na hannun jari,bayan nan duk sai aka watse aka bar ni daga ni sai Zuly wacce ta danna wa oga video call tana murmushi tare da yi masa congratulations akan aikin da na yi nasara ba tare ni na san muhimmancin meeting ɗin ba ko kuma ina jawaban da na kawo suka dosa ba.

Yadda suke murna yasa ni ma na ji sanyi a raina,ina jin oga na cewa "ku tawo gida mu yi shagalin murnar a nan"

Yanayin fuskar Zuly ya ɗan canza ina ganin lokacin da ta saci kallona ta wutsiyar ido kafin ta ce "oga kana ganin lokaci yayi da Luby za ta ga zahiriya da idonta?"

"Eh mana! Ai ba zama za mu yi muna kashe kuɗi wurin controling memorynta ba kawai ku dawo yanzu,sai ku same ni a can filin hutawana "

Da ƴar damuwa a fuskarta ta ce "oga ko dai ka tarbe mu a can ɗin,don ina gudun Luby ta yi min tirjiya ko borin hauka"

"Ki yi yadda na ce" yana gama faɗa ya kashe,sai a lokacin ne ni kuma na jefo mata tambayar da ta ɗaure min kai "Zuly wace ƙasa ce nan? Ta ya aka yi muka zo nan?"

"Ki taso mu je,yanzu kin samu amsar tambayarki in mun koma Kamaru" ta faɗa tare da nufar ƙofa,sai na take mata baya ina mai ci gaba da yi mata wata tambayar "amma ina ne nan?" ba ta bani amsa ba har muka shiga mota muka isa gida. Da umarninta kuma na bi bayanta zuwa wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa sai wani madubi da aka rufe da jan ƙyalle.A gabana ta buɗe shi tare da ɗaukar wuƙa ta tsaga yatsanta jini ya soma ɗiga sai ta shafi madubin nan take yayi ƙara ƙiiiii tare da buɗewa ya fitar da hoton ƙofa amma fa ba ƙofar ba ce don ba ka ganin komai sai wani farin abu kamar gajimare.

Jikina ya ɗauki rawa na ce "ina ne nan kuma Zulaihat?" na yi tambayar ne jin tamkar tunanina ya dawo normal,iya ni ɗaya kawai ke sarrafa shi. "Ba mu da saurin lokaci Lubna ki zo mu tafi" ta faɗa tana kamo hannuna da niyyar shigar da mu cikin madubin,a tsorace na ce "mu je ina? Wai cikin madubin? Zulaihat wannan ai tsafi ne.Ina kika kawo ni? " ba ta bani amsa ba ta wani fizgo ni muka ratsa mirror ɗin sai gamu muna yawo cikin wani iska kafin kuma ƙyaftawar ido na gan ni a cikin ɗakin Zulaihat a cikin falo.Tuni zaren carbin tunanina ya tsinke,dukkan jikina rawa yake yi min ina son yi mata tambayoyi amma ina tsoron jin amsoshinsu don ban so a ce abin da nake zargi gaskiya ne.

Ita kuwa Zulaihat sai ta yi fuska tare da haɗe rai ta ce "ki tashi mu je Malama oga na jiranmu"

Cike da masifa na ce mata "babu inda zan je! Gidanmu zan tafi"

Nan ta yi wata dariya kafin ta ce "au haba? Kenan? To wuce ai ga ƙofa nan sai ki tafi"

Sam ban damu da gyatsen da ta yi min ba sai na fita daga ɗakin na fito harabar gidan,babu kowa a bakin get sai na je na buɗe ƙofa da zumar fita nan na yi arba da wata lukutar masifa don kuwa ruwa ne maƙil a wurin tamkar za su taɓo sararin samaniya,babu shiri na koma can cikin falon sai na tarar da ita tana shan ayaba cike da shaƙiyanci ta ce "har an dawo daga gidan ko kuwa an fasa zuwa?"

Idona ne suka kawo ruwa shaaa,ina kallon Zulaihat wacce da dukkan alamu babu ɗigon imani a ƙirjinta.Miƙewa ta yi tare da ɗaukar key ɗin mota ta ce "mu je" dole dangi na ƙi yasa na take mata baya muka shiga motar .Mai gadi ya buɗe mata gate yana wani murmushin da ya tabbatar min bakinsu ɗaya shi da Zuly duk munafukai ne,gudu sosai ta yi har muka isa gidan Ogan.Muna shiga ana kiran sallar magrib,a zaune muka tarar da shi kan kujeru na alfarma ya saka ɗan madaidaicin table a gaba mai ɗauke da cake wanda aka yi wa kwalliya kamar ba ci za a yi ba.

Tsoron Ogan ne ya ƙara ratsa ni,amma duk da haka ita ɗaya kawai ta gaishe shi.Ya amsa yana kallona kafin ya fara jawabinsa "Luby na san zuwa yanzu kin fara gane aikinki, sannan kin san cikin me kika shiga,da kuma su wa kike tare da su.Sai dai ki sani a tafiyarmu ba gudu ba ja da baya,kamar yadda kika saka hannu a yarjejeniyar tsarin aikinmu za ki yi komai da family suka buƙata wato ƙungiya,to ya zama dole ki yi shi.Sam family ba mu da matsala,ba kamar sauran ƙungiyoyin da kika sani ba ne,mu sam ba mu da buƙatar jini sai in dai mutum ne ya kawo taurin kai muke ɗaukar mataki mai tsauri a kansa.Abin da muke so ba komai ne ba sai abin da bai da amfani wurin al'umma,kamar dai abin da kika gabatar a yau wato kashi/bahaya sai kuma sperm ko yawu ko kuma audugar mata da suka riga suka yi amfani da ita shi kenan fa.Mene ne matsala a nan?" ya ƙarashe tambayar yana mai kafe ni da idonsa masu mugun dafi.

Wasu sabbin hawaye suka zubo min kafin na zube a gabansa na ce "don Allah ka yi haƙuri ka goge sunana daga ciki, wallahi na yi ma alƙawari babu wanda zan faɗa wa wannan labarin ko da kuwa iyayena ne"

Yayi wani murmushi ya ce "tuni ai iyayenki sun san da aikinki,don yanzu haka mahaifinki na asibiti an yi masa gyaran ƙafa sannan mun aika saƙon cewa yau ke ce za ki yi gadi a babbar pharmacie ɗinmu ta saida magunguna.Ko ba ki yarda ba?" yayi tambayar yana mai jawo wayarsa ya kunna min video duk abin da ya faru tun daga lokacin da aka ɗauko Abbana har izuwa lokacin da suke asibiti an yi masa aiki ga Ummah nan zaune kusa da shi fuskarta cike da farin ciki.

Wani irin tausayin kanmu ne ya kama ni,tabbas sun yi min dabaibayin da ban isa na warware ta sauƙi ba.

"In kuma kika ce za ki bijire minti biyu yayi yawa zan aika mahaifinki barzahu" oga ya faɗa . Cikin razani na dube shi,sai ya gaskata maganar ta hanyar cewa "ƙwaran gaske ,kamar yadda kai ki ƙasar Turai bai yi min wahala ba haka zan katse igiyar numfashin mahaifinki don haka kar ki kawo min wasa ki zo ki yanka cake ɗin nan kafin ya sha iska"

Yana gama faɗar haka sai Zuly ta miƙa min wuƙa,ba don na so ba na yanka cake ɗin wanda yayi daidai da jin wani mashi ya caki zuciyata tamkar ma zuciyar tawa ce na yanka. Mu uku muka cinye cake ɗin duka,kafin Zuly ta ja ni mu koma can gidanta.....

Ga masu son fara yin payment 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [02/04 11:51] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.

*FCWA*☀️

________________________

06

Da muka isa gidanta dakyar na samu na yi sallar isha'i,ita kuwa magrib kamar yadda lokacinta ya wuce to haka ta wuce ni don ba zan ranka ta ba. Gida nake son tafiya,amma da dukkan alamu ba zan samu wannan alfarmar ba.Haka na yi shuru cikin ɗaki ina tunani iri-iri da kuma mamakin yadda Zulaihat ta koma muguwar sheɗaniyar marar imani.Na goge hawaye masu ɗumi da suka zubo min lokacin da tunanin yadda na ga iyayena suna farin ciki ya faɗo a kwanyata.

"Luby sai fa in kin so ne za ki damu,kamar yadda oga ya faɗa miki mu family sam ba mu da wata matsala.Kin ga fa babu wani abu da za a nema wurinki in kika cire lokacinki,ni ban ga abin damuwa ba a aikin da babu kashe mutane ciki sannan ko jinin ɗan tsako ba mu buƙata"

A lokacin da ta yi min wannan magana sai kuma na ga fa kusan tana da gaskiya,duk da cewa su ɗin matsafa ne amma dai fa ba su kashe mutane.Amma abin da ya fi bani mamaki bai fi ta yadda suke son abubuwan shirme ba,cikin son sanin dalilin haka na jefo mata tambayar "Amma Zulaihat me za ku yi da kashin mutane?"

"Don Allah ki bar ce min Zulaihat ɗin nan,ki kira ni da Zuly sannan maganar me za mu yi da kashin mutane ke ce a ba ki san amfaninsa ba shi yasa amma da shine ai ake yin takin zamani ana kaiwa gona don yin noma"

Na ja ajiyar zuciya da yake ni sokuwa ce sai na yarda da maganarta,kuma in faɗa muku gaskiya sosai kalamanta suka yi tasiri a raina don sai na ji na kuma yarda zan yi aiki da su.Ban taɓa sanin illa ne ba sai da na haɗu da ke Haule na ga irin abubuwan da kike yi na ban mamaki.

Jin na samu ƴar nutsuwar ruhi sai na je na yi wanka da ruwa masu ɗumi,da na fito na sha salade na fruit sai kuma a lokacin ne Zuly ta bani wayata wacce take sabuwa dal.Wani irin daɗi na ji ganin ta canza min waya amma layina ne a ciki,ta yi wani murmushi tare da zama kusa da ni ta ce "kwaɗayin na gan ki cikin daula yasa na kawo ki cikin family,dubi yadda jikinki yayi kyau cikin ƙanƙanen lokaci "

Na ɗan yi murmushin farin ciki kafin na ce "ni dai ki koya min yadda ake aiki da ita" ta yi ƴar dariya kafin ta soma nuna min,muna yi muna taɓa hirar makaranta da kuma ƙawayenmu wanda muka yi aji guda.Duk wani wanda nake da labarinsa sai na faɗawa Zuly aikin da ya samu ko kuma halin da yake ciki.Ban taɓa tunanin cewa rahoto ne take haɗawa ba don farmakarsu sai a ranar da ni ma tawa mission ɗin ta zo,zan faɗa muku yadda komai ya wakana sannu-sannu.

A daren nan sosai muka jima muna hira kafin duk mu kwanta, washegari Zuly ce ta tashe ni sai kuma ta hana ni na yi wanka sallah kawai na yi na saka kayana waɗanda na fito da su daga gida sai jakata.

Fita muka yi muka shiga mota ta kai ni asibiti da tambaya muka samu ɗakin da su Ummah suke. Ina ganinta na je na rungume ta ina tambayar jikin Abba wanda ke bacci. "Da sauƙi sosai yanzu likita ya shigo ya duba shi tare da yi masa allura,ya aikin Lubna? wannan fa?" Ummah ta faɗa tana nuna min Zuly .

"Ah na manta ban gabatar miki da ita ba,Zulahait abokiyar aikina ce" na bata amsa.

Umma ta ɗan yi murmushi kafin ta ce "ma sha Allah! Allah ya taimaka ya baku sa'a ya kuma baku cimma nasarar aikinku,ki ƙara yi wa oganku godiya don Allah Lubna .Mutum mai kirki jiya bai bar wurin nan ba har sai da ya ga an shiga an kuma fito da Abbanki"

Wani irin sanyi ya ratsa ni jin wani abin farin ciki,na so in zauna da iyayena amma Zuly ta ƙi bani damar yin haka ta hanyar cewa "ki dai tashi mu je gida ki yi wanka ki canza kaya sai ki dawo ko?"

Da wannan tasa ta ci galaba kaina muka fito,"Zuly mene ne haka? Na ga kamar ba ki son na zauna tare da iyayena" na faɗa ina kafe ta da ido.

Ta ce "ke ba fa komai ne ba,ina so dai ki yi wanka ki canza kaya ko kin ji sanyi"

"Amma daga nan fa?" "Za mu wuce kamfani" ta bani amsa.Kafin mu shiga mota mu koma can gidanta,da isarmu kuwa wankan na shiga bayan na fito na shirya cikin ɗaya daga cikin abayar da muka siyo jiya.Ina tsaka da fesa turare ta shigo sanye cikin kayan atamfa har da luluɓa uban mayafi kamar ta ƙwarai,ina shirin yi mata tambayar ya na ga ta yi shiga ta kamala daga can falo na ji muryar wani gardi yana kiran sunanta cikin tsawa "Zulaihat?" murya na rawa ta amsa kafin ta kama hannuna ta ce "in ya tambaye ki wace ce ke sai ki ce ƴar uwata ce ke kun zo nan ne domin jinyar mahaifinki" ba ta bani damar cewa komai ba kuma ta ja ni muka fita can falo.

Yadda duk ta nutsu cike da tsoro yasa ni ma na kama kaina tare da gaishe shi cike da ladabi,dakyar ya amsa kafin ya ce "wace ce ke?"

Sai da na saci kallon Zuly kafin na ce "ƴar uwarta ce,jiya muka zo nan garin domin jinyar mahaifina da ke asibiti"

"Ita kuma ta ce min yau ne kika zo"

"Eh nan gidan ba,amma ai tun jiya muka zo ni da iyayena suna can asibiti"

"Wace asibiti?"

"Private asibitin nan da ke kusa da babbar kasuwa" na basa amsa,bai ƙara cewa komai ba sai ya je ya zauna kan kujera yayin da ita kuma Zuly ta je jikinta na ɗan rawa ta fara zuba masa abinci tana gamawa ta zo ta kama hannuna tare da jana muka koma can ɗakina.Bayan ta rufe ƙofa sai ta ja ajiyar zuciya,ni kuma na ce "wane ne kuma wannan?"

Cikin ƙasa da murya ta ce "mijina ne,ki bari daga baya zan yi miki bayani" tana gama faɗar haka sai ta fice ta bar ni sake da baki ina mamakin kenan Zuly tana da aure amma ta rasa wanda za ta aura sai babban mutum kuma irin mai zafin kai.

Bakin bed na zauna ina tunanin ni ma ai lokaci yayi da zan bai wa maza dama ,saboda can baya gani nake in ba aiki na samu ba to fa ba zan taɓa kula namiji ba. Tsawon lokaci ina wasiƙar jaki kafin Zuly ta shigo ," taso mu ci abinci" ta faɗa .Tashin na yi na mara mata baya,ita ce ta zuba mana sai da muka fara ci sannan ta soma bani labarinta.

"Lubna kamar yadda kika sani ba duk abin da mutum yake so yake samu ba,to ni ma hakan ce ta faru da ni.Bayan mun kammala karatu na fara neman aiki ,duk inda na je babu nasara sai na samowa kaina mafita wato ita ce ta auren miji mai kuɗi shine fa na auri Alhaji " tana kawowa nan ta yi shuru ban matsa mata da sai ta ƙara cewa wani abu ba lura da yadda take bani labarin a takure.Bayan mun gama cin abinci daga nan kuma kamfani muka wuce,kafin nan bisa hanya sai da ta ƙara gutsura min labarin nata.

"Akwai wani group mai suna sugar Daddy ,a can muka haɗu da Alhaji ta hanyar wata ƙawata na samun link ɗin.Tun da na tura hotona na gabatar da kaina ya biyo ni pc ya ce na yi masa ban kuma ja aji ba muka fara soyayya kar ki so ki ga yadda yake yi min batal ɗin kuɗi.Ba a ɗauki lokaci ba kuma ya zo gidanmu suka yi magana da iyayena waɗanda kafin auren sai da suka tambaye ni ai dai ina sonsa ko ? Na kuwa ce eh.Amma a zahiri ba haka abin yake ba,kawai saboda in samu gidan hutu ne yasa na amince da aurensa.Muna yin aure hannunsa ya koma na jariri hahaha! Ya bar bani kuɗi sai dai fa duk abin buƙata yana zuba min su a store kuma bai damu ba don na ɗiba na yi kyauta da su,ana haka sai na fara haɗuwa da manyan mata .In an je biki su yi ta liƙen kuɗi,wata don ta ɓarar da 200k ba wani abu ba ne ,to abin sai ya fara damuna har na soma tunanin ko rabuwa zan yi da Alhaji .Da na kai wa waccan ƙawata da ta bani link kokena sai ta haɗa ni da oga" tana kawo wa nan da labarin ta yi parking duk muka fito,duk da a lokacin na so jin yadda ta kaya amma na yi shiru muka shiga ciki.

Cike da girmamawa aka dinga gaishe ta,direct kuma ofis ɗin oga muka wuce.Yana ganinmu yayi saurin tasowa ya shayar da ni giyar mamaki don kuwa rungume Zuly yayi ƙyam a ƙirjinsa tare da feso wasu kalamai waɗanda suka sa na zauna ban shirya ba.

"Ya haka Baby? Na ji an ce mijinki yau yayi saukar asubah,shine ba ki faɗa min ba.Me ya kawo haka ko yayi miki wani abu ne?"

Ita kuwa ƙoƙarin fizge wa take,tana satar kallona da sauri na kawar da kai. Ina jin lokacin da oga ke ci gaba da cewa "faɗa min kun yi wani abu da shi ne?"

"A'a ! Please ka sake ni mana " ta faɗa.

"Luby ki ɗan fita ina son yin magana da Oga" ko kallonsu ban ƙara yi ba na fita,direct kuma ofis ɗinta na shiga wanda ke kusan na oga.Kaina na ji yana sara min a fili nake tambayar kaina "wai da aurenta take kula wani? Da aurenta take zina? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Ya Rabb ka tsare ni daga sharrin zina Allah kar ka jarabce ni da ita,kar ka kuma nuna min ranar da zan yi ta Ya Rabb kafin ranar nan ta zo Allah ka aiko tirela ta markaɗe ni na huta" haka kawai na ji hankalina ya ƙi kwanciya da wannan aikin,sai nake jin kamar na je na shaida musu ban so.

Bayan wajen minti talatin ina zaune sai ga Zuly ta shigo ,kallo ɗaya na yi mata na ɗauke kai. Ta zauna tare da soma magana ba tare da na tambaye ta ba,"sai haƙuri Luby,ni ma na fara gajiya sai dai ba a komawa baya.Kin ga a ranar da ƙawata ta haɗa ni da oga da farko iya aikin yi masa lissafi kawai ne nawa,amma sannu-sannu sai ya fara bijiro min da ainahin zuwan nawa.Cike da tako yayi nasarar kai ni kan shimfiɗarsa har sai bayan komai ya kammala ne na fahimci kuskurena,don da soyayya ya ɓullo min .Amma yana bani kuɗaɗe masu mugun yawa sai ya girgiza tunanina,sai kawai na biye masa kusan kullum in na zo aiki muna keɓewa yayin da shi kuma yake cika min jakata da ƴaƴan banki"

"Ita kuma alaƙar tsafi?" na jefo mata tambayar. "Shi ne ya bani power ya kuma nuna min yadda ake yin komai" "To amma me yasa ba ki rabuwa da Alhaji ki auri oga ? Ai hakan ya fi nake gani tunda da dukkan alamu shi oga kina sonsa"

Wani kallo ta yi min kafin ta ce "ki shirya za mu fita zuwa yawon ƙauyukan da za a soma aiki"

"Aikin me fa?"

"Na gina banɗakunan kan titi mana" ta bani amsa.

Ko da muka fito tuni motar da za ta yi yawo da mu ta zo,haka muka shiga mu da wasu sauran ma'aikata.Yawo sosai muka yi muna duba wuraren da za a gina banɗakuna,wasu cikin kasuwa wasu kuma kan titi.Sai bayan sallar azahar muka dawo,Zuly ce ta yi wa oga bayanin komai kafin ta sauke ni asibiti. Ina shiga daidai nan Abba ya rufe idonsa ya soma bacci,bayan na gaishe da Ummah sai na zauna na tambaye ta jikinsa ta amsa ana ta samun ci gaba.

Nan na wuni,har dare amma Abba bai tashi ba har likitocin sai da suka yi mamakin irin baccin nan da yake alhalin ba a yi masa allura ko magani mai sa haka ba.Saƙon Zuly na samu kan ina iya tafiya gidanmu ba sai na je can gidanta ba,da wannan na yi wa su Ummah sallama na je can gidan.A daren ne kuma na yi wani mafarki mai matuƙar firgitarwa,ga Abba nan yana kuka yana kiran sunana yayin da kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya sun ɗora shi kan garwashin wuta suna gasa shi tamkar wani tsire.

A firgice na farka wanda yayi daidai da kiran Zuly,"ki fito ina ƙofar gidanku" shine abin da ta faɗa min ta kashe wayar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull