Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 5

Bakin ruhi complete - Chapter 5

Bakin ruhi complete Chapter 5: Bakin ruhi complete Chapter 5. Cike da mamaki na duba lokaci,ƙarfe biyun dare ne.Amma haka na fita na same ta cikin mota,ina…

3,327 words

Cike da mamaki na duba lokaci,ƙarfe biyun dare ne.Amma haka na fita na same ta cikin mota,ina shiga ta fizge ta kuwa ta soma yin gudu kamar za ta tashi sama tambayar duniya kuma ta ƙi bani amsar abin da ke faruwa . Gidanta muka wuce,tana yin parking duk muka fito hankali tashe take jan hannuna zuwa ciki.Wannan dai ɗakin muka shiga wanda na yi laƙabi da ɗakin sirrinta,ko da muka shiga sai ta buɗe madubinta ta tsaga yatsanta jini ya soma zuba ta kamo nawa da niyyar tsaga shi kenan mijinta Alhaji ya shigo ɗakin yana salati tare da jefo mata tambaya "Zulaihat tsafi cikin gidana? Dama ke MATSAFIYA (Mrs SADAUKI) ce ban sani ba? Ai kuwa yau..." bai ƙarasa kai ƙarshen maganarsa ba Zuly ta jefa wuƙar hannunta tare da furta furucin tsafi nan take wuƙar ta sauka daidai tsakiyar ƙirjin Alhaji a nan take ya faɗi jini na yi masa malala......

My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [02/04 12:10] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.

*FCWA*☀️

________________________

07

Ban taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba,kisan kai ne aka yi a gabana ga gawa kwance cikin jini.Tsabar ruɗewa da na yi yasa na soma zagayen ɗakin ina ihu,yayin da ita kuma Zuly ta soma tsafe gawar tana barbaɗa mata wata hodar tsafi kafin ƙyaftawar ido gawar ta ɓata ko kumfan jini babu,a wannan lokacin ne na ƙara ganin bala'in da na tsoma kaina a cikinsa.Zuly ta nufo ni da niyyar kama ni amma na yi tsalle na koma can gefe ,idonta ta juye tamkar wata zakanya kafin ta soma yi min magana cikin wata irin murya "Luby ki zo mu wuce ba mu da sauran lokaci,in kuma kika jinkirta duk abin da ya biyo baya babu ruwana"

Ina kuka ina ƙari na ce "amma Zuly kisan kai fa kika yi,mutum ne fa kika kashe kuma mijinki"

"Babu ruwanki da wannan matsalar ki zo mu wuce" ta yi furucin tare da yin tsalle ta zo ta cabko ni muka tashi cikin iska kafin mu ratsa ƙofar da ke cikin mirror.

A wani ɗaki muka bayyana,da na duba da kyau sai na ga wancan dai ne na ƙasar waje.Duk yadda na so na bijiro da zancen kisan kan da ta yi ta hana,a gaggauce ta tirsasa ni na shirya cikin kayan arna kafin mu fito.Yanzu ma buɗe mana mota aka yi muka shiga ,muna tafe ina duban hanya sai na ga wata ce aka ɗauka ba waccan ba.Mun yi tafiya mai ɗan nisa kafin mu isa, wannan karon a tare muka shiga ɗakin taron mai ɗauke da ɗumbin jama'a daga ƙasashe daban-daban.Ciki kuwa har da oga shi ma ya haɗe cikin wasu baƙaƙen suit kamar sauran mazan,wuri muka samu muka zauna oga ya dubo inda muke zaune fuskarsa ta nuna alamun damuwa.

Can kamar minti biyu wani zabaya ya fito sanye cikin jajayen kaya kansa ya ɗora wata hulla kamar ta sheɗan,gashin kansa da idonsa duk wasu iri ne kamar wani makaho haka ya ƙanƙance su yana ƙarewa kowa kallo ,da ya zo kaina sai ya tsayar da dubansa gare ni.Gabana ne yayi wani irin mugun faɗuwa ,so nake na kauce idona amma tamkar wacce aka yi wa dabaibaye na kasa.

"Mansoor fatan ka yi wa ɗalibarka bayani?" shi ne abin da ya faɗa .

Muryar oga na ɗan rawa ya ce "a'a tukuna dai Boss "

Bai ce komai ba sai ya zauna kan kujerar ya soma yin wasu maganganu da ban gane su ba saboda kogin tunani da na abka,ban farga ba sai da na ji Zuly ta zungure ni sai na dawo hayyacina nan kuma na ƙara jin wani zancen banza wanda kuwa hankalina ya kasa ɗauka.

Oga ne ke bayani kamar haka "Luby a family muna da wata ƙa'ida,babu virgine a tsarin tafiyarmu in ma ta shigo to dole a yi amfani da ita don kawar da budurcinta.In irin wannan damar ta samu to Boss ne yake yin wannan aiki ,kamar yadda tsarin yake zai yi amfani da ke a gaban dukkan family bayan nan kuma sai ki karɓi zoben ƙarfin iko da kuma madubinki wanda zai sauƙaƙa miki yin balaguro zuwa ƙasashen duniya da kuma in an tsara meeting"

Wata irin bazawarar dariya na yi,don abin jin shi na yi kamar wasar kwaikwayo sai na miƙe tsaye kamar mahaukaciya ina mai ci gaba da yin dariya kafin na ce "wato na basa budurcina? Akan wane dalili kenan? To ba zan yi ba,sai dai ku cire ni daga cikin family ɗin amma ba zan taɓa aikata zina ba"

Da wani mugun sauri oga ya zagayo ya zo inda nake ya kama kafaɗuna ya ce " Luby wannan dolenki ne! Kin ga ki ajiye hankalinki babu fa wata matsala sau ɗaya tak ne zai yi shi kenan "

Hawaye suka zubo min masu ɗumi,ji nake kamar na shaƙe wuyan oga har sai ya mutu na sake shi .

"Na bata nan da sati ɗaya,ta je ta yi shawara don ina da ayyuka masu muhimmanci a gabana kowa zai iya tafiya" Boss ya faɗa tare da miƙewa ya koma hanyar da ya fito. Nan kowa duk ya watse,Zuly ta kama hannuna muka fito muka bar oga can.Har muka isa gida tana yi min nasiha haɗi da shawarwarin banza wanda in sun shiga kunnena sai su fita ta ɗayan kunnen,sam ban ji zan iya yin abin da suka ce ba.

Na yi tunanin da zarar mun je za mu koma can Kamaru ne,amma sai na ji wata sabuwa wai zan sake yin wani zama da mutanen da na tallata musu hajarmu.

Cikin bahon wanka na shiga na lumshe ido,tunanin iyayena da kuma abubuwan da suka faru suke ta min yawo a kwanya.Har sai da ruwan suka huce na zuba wasu sannan na yi wanka na fito,cikin kayan bacci na shirya sannan na kwanta sai dai fa na kasa yin baccin haka na yi ta yin juyi bisa gado.Can sai ga Zuly ta shigo hannunta riƙe da ƙaramin tray ,tashi na yi zaune ita ma ta zauna bakin gado tare da miƙo min kofi ɗaya na madara ita ma ta fara shan guda.

"Wacce shawara kika yanke ?" ta jefo min tambayar.

"Game da me fa?" ni ma na tambaye ta.

Da ɗan mamaki ta dube ni kafin ta ce,"maganar Boss ɗin ce kika manta?"

"Shi wane ne?" ban ida rufe bakina ba kofin da ke riƙe da hannuna ya tarwatse har sai da kwalba ta shige min hannu nan take jini ya soma zuba. Jikin Zuly ya ɗauki rawa,sai ta dubi madubin da ke a ɗakin kafin kuma ta taimaka min ta tsayar da jinin ta naɗe min shi da bandeji.

Sosai na tsorata ban taɓa tunanin Boss nada power har haka ba,don babu tantama shi ne ya tarwatsa kofin.A tsorace nake kallon Zuly kafin na ce "don Allah ki mayar da ni gida"

Muryar Boss ta fito ɓaro-ɓaro ta cika ɗakin "duk inda za ki je ba za ki taɓa boyewa ganina ba,na soma bibiyarki kenan"

Da sauri na rungume Zuly ,sai aka ƙwanƙwasa ƙofa ita ce ta bada damar shigowa.Ƴar aiki ce,cikin Yaren turanci ta ce "oga na falo yana jiran ku " tana gama faɗa ta fice.

After dress na ɗauko na ɗora a sama kafin mu fita falon,Oga na zaune ya hakimce fuskar nan kicin-cikin kamar za ta tsage. Na sunne kai tare da samun wuri na ja na tsaya ganin irin mugun kallon da yake jefo min.

"Zuly kin ga saboda ke ina shirin samun matsala da Boss ? Ta ya za ki kawo wacce kika san za ta kawo mana cikas? Faɗa min wace shawara kuka yanke yanzu?"

"So take mu koma Kamaru,kuma ni ma na ga kamar hakan zai fi.In mun je can za ta fi samun damar yin tunani in tana ganin Abbanta " Zuly ta faɗa ,ban san dalilin da yasa ta kawo Abbana a cikin wannan lamari ba.

Oga ya ce "babu matsala za ku iya komawa,amma ki bari har zuwa gobe don yanzu haka an tsinci gawar mijinki ƴan sanda sun soma yin bincike.Kin ga in suka biyo ta kanki za su samu ba ki ma ƙasar,kuma in kin je ki nuna cewa labarin mutuwar ne ya maido da ke"

"Kenan in haka ne sai dai mu bi jirgi ba ta madubi ba?" Zulyn ta faɗa sam babu wata damuwa a tattare da ita.

Oga ya miƙe tsaye ya ce "eh hakan za a yi,na riga da na tsara komai" yana gama faɗa ya murza zobensa nan take ya ɓace ɓat.

A ɗakin Zuly na kwana, washegari kuma tun da safe muka shirya tsaf zuwa aeroport,jirgi ne na musamman wanda bai da buƙatar sai mun nuna wasu takardu.Tamkar zan fita daga wuta haka nake ji,don na lashi takobin da zarar mun sauka Kamaru ko ƙasa da sama za su haɗe ba zan ƙara shiga sabgar Zuly ba na fita daga family kenan.

Jirginmu na sauka ƴan sanda suka tarbe mu,nan na ga ikon Allah yadda Zuly ke kuka idonta duk sun yi ja sai wani rangaji take kamar za ta faɗi sai na taro ta .Daga nan police station muka wuce aka yi mata tambayoyi kafin ta nemi tana son ganin gawar mijinta.

Duk yadda ta so mu je tare zillewa na yi na tafi can asibiti,a zaune na tarar da Ummah tana kuka.Tana ganina ta taso ta ce "ina kika shiga tun jiya muna nemanki a waya ba mu samu ba? Auta kuma ta ce min kuna kwance tsakar dare kika fita kika bar gidan,ina ne kika je?"

"Wurin aiki mana Ummah,amma ai gani na zo.Ya jikin Abba?"

Hawaye ta goge da mayafinta kafin ta ce "ɗazun nan aka kawo masa kwara-kwara wacce zai dinga yin tafiya kawai sai kwacaaa na ji ya faɗi.Likitoci sun ce aikin da aka yi masa a ƙafa ya lalace sannan ya samu shanyewar ɓarin jikiii " ta fashe da wani kuka mai tsuma rai ,nan take jikina ya ɗau rawa.Ban ida rikicewa ba sai da na je na ga yadda Abba ya koma ,kukan ni ma na dinga taya Ummah ga likitoci sai rubuta sabbin magani suke.

Cikin wuni guda suka rikita mana lissafi don kuwa an kai gaɓar da kuɗin hannun Ummah sun ida dama oga ne ya bata su. Wuraren sallar magarib kuma babban likitan ya fito da wani zance,"kuɗin gadonku sun ida ku je ku zuba wasu kafin nan da ƙarfe goma na dare "

Ummah ta dube ni ta ce " Lubna ki je ki biya,ko har yanzu ba a baki ko dala ba sai aikin?" a cikin kalamanta sai nake jin kamar har da ɓacin rai,wato gani take na ɓoye kuɗin ne musamman suturar da ke jikina da ke tsadadiya babu wanda zai yarda kan cewa banda kuɗi.

"Bari na je na dawo" shi ne kawai abin da na faɗa kafin na fito,tafiyar ƙasa na soma yi ina tafe ina tunani har na isa gidan Zuly .A falo na tarar da ita,muka gaisa sama-sama kafin na shiga ɗaki na ɗauko wayata iphone wacce zuciyata da ruhina suka yarda da na sayar da ita na yi wa Abbana magani.

Har na kai bakin ƙofar fita na ji muryar Zuly na cewa"kina tunanin kuɗin sayen magani su ne za su warkar da mahaifinki? To in dai haka ne kin makaro "

Da sauri na juya ina kallonta,ta sakar min wani murmushi tana mai kankare akaifarta. "Me kike nufi a nan?" na samu dakyar na tambaye ta zuciyata na ɗan dokawa.

Ta miƙe tare da zuwa dab da ni sannan ta ce "ina nufin ko duniya za ku yawace babu asibitin da za ta iya warkar da cutar mahaifinki,ke ce maganinsa in kina so ya warke dole ki bai wa Boss haɗin kai" tana gama faɗa ta bar ni nan tsaye.Na jima cikin shock kafin na fice,wajen wani mai sayar da wayoyi na je na karɓi kuɗi tare da bar masa wayata jingina. Ko da na isa asibiti na tarar ana yi wa Ummah tijara,haka dai na biya kuɗin gado da kuma na sauran maganin da ba a siya ba.

Na yi tunanin na kawo ƙarshen matsalar duk da kuwa furucin Zuly bai bar kwanyata ba,ashe nan duk shimfiɗa ce aka yi min mamakin na gaba. Ƙanwata auta ita ce ta kawo mana abincin dare mun ɗan taɓa hira kafin ta koma gida ni kuma na yanke shawara zan zauna tare da Ummah.

Dare ya tsala bayan duk kowa ya kwanta,na ji motsin buɗe ƙofa wanda yayi daidai da farkawata daga bacci sai dai tamkar gawa haka na sandare na kasa motsi.A gabana oga da Zuly suka shigo ɗakin suka yi tsaye kai ga Abba,can kuma Boss ya bayyana su biyu suka danne Abba yayin da shi kuma yayi masa wata allura wacce ta sa shi soma yin ihu da kururuwa yana kiran zai mutu su tausaya masa su bar cutar da shi,cikin ɗacin rai Boss ya ce "ƴarka ce duk ta ja maka masifa ba za mu taɓa barinka ƙalau ba sai ranar da ta amince da ƙudirina"

Ina jin lokacin da Abba ya soma magana cikin azaba,"Lubnata ba za ta taɓa aikata abin da kuke so ba,na gwammaci na dawwama cikin wannan masifar kan na ga ta gurɓata rayuwart..." Zuly ce ta ɗauke Abbana da wani mari wanda hakan yasa sauran maganar ta maƙale masa,suna gamawa suka fice sai kuma a lokacin kawai jijiyoyin jikina suka ci gaba da yin aiki.

Dakyar na iya tashi na je na yi tsaye gaban Abba ,idonsa ya zuba min yana kuka.Bakinsa ya juye ba zai iya yin magana ba,amma a haka ina fahimtar abin da yake son sanar da ni.Na faɗa jikinsa na saki wani irin kuka mai cin rai wanda yayi sanadiyar tashin Ummah ita ma sai ta soma yin kukan don ta yi tunanin mutuwa yayi.

Sai da likitoci ne suka shigo suka tabbatar mata da ransa,allura bacci suka yi masa saboda wani irin abu da ya soma yi kamar mai cutar hauka.

Jikin Ummah na je na ƙanƙame ta ina mai ci gaba da yin kuka yayin da ita kuma ta soma rarrashina tare da kwantar min da hankali Abba zai samu lafiya.

Da gari yayi haske suka sake shigowa suka duba Abba,suka ce jikinsa ya ƙara mutuwa da buƙatar a yi masa gashin ƙashi .Haka suka tura gadonsa aka shiga da shi wani ɗaki,ni da Ummah iya bakin ƙofa kawai muka tsaya.Daga nan muna jin yadda Abba ke ƙwallowa yana ihu da ransa.

Sosai kururuwarsa ke taɓa min zuciya ,sai nake ganin duk laifina ne.A haka dai na fita don zuwa mu yi cinikin wayata da na baro jiya,nan ɗin ma wata masifar na tarar shagon wayoyi ya ƙone ƙurmus sai gawawarkin wayoyin ga su nan jere ringis duk sun ƙone.Yana ganina ya ƙara ƙaimin kuka,ni ce na basa haƙuri don da ace ya san ta dalilina ne yayi asarar nan ƙila kotu ce za ta raba mu.

Idona sun rufe,babu komai cikinsu sai ɓacin rai.Gidan Zuly na nufa don so nake a yita ta ƙare,ko da na isa na tarar da ita a zaune tana karɓar ta'aziyar mijinta ga mutane duk sun cika falon.Ɗakin da aka ware domin ni na shiga bayan na yi mata alama da ido ina son ganinta,sai dai ina shiga na tarar da Boss a hakimce kan gado yana murmushi...

My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [04/04 11:00] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.

*FCWA*☀️

________________________

08

A lokacin da na ga Boss kwance kan bed sam babu sutura a jikinsa,wani irin bugawa zuciyata ta yi sai dai na kasa ɗaga ƙafata ballantana na koma baya na fita daga ɗakin.

Cike da shaƙiyanci yake cewa "ki gama gujegujenki ni ɗin nan ne zan raba ki da budurcinki,in kuma kin fi ƙaunarsa kan mahaifinki ai shi kenan" yana gama faɗar haka ya ɓata kamar walƙiya.Na ja ajiyar zuciya,abin da na fahimta a family su komai nasu ba su yinsa dole sai ta daɗin rai wannan dalilin yasa ko da wasa ba su saka ƙarfi ba wurin baiwa Boss ni ba.

Ina nan tsaye ina saka wasiƙar jaki Zuly ta turo ƙofa ta shigo,kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai tare da yin gaba.Ni kuma na take mata baya ina mai kiran sunanta,sai da ta cire zumbulen hijabinta sannan ta juyo ta fuskance ni ta ce "Luby ban san wace irin zuciya ce da ke ba marar tausayi,duk halin da Abbanki yake ciki kin kasa haƙura ki bada kai bori ya hau.Me za ki yi da shi budurcin? Ina ce duk don da dai ki kai shi ne gidan mijinki,to ki sani a family ba a auren bare.Duk wanda ko wacce ta shigo babu aure to dole ne ya zaɓi abokin rayuwa cikin ƴan ƙungiya,kuma ina ce ai a gabansu za a yi komai ba za ki samu matsala da mijinki ba tun da ya san komai"

Tamkar mai cutar dundumi haka na ji a lokacin,sai kuma na fahimci ba ƙaramar ƙungiyar asiri ce wannan ba wacce ta ɓoye sirrika masu yawa sai a sannu ne za ka dinga ganinsu suna fitowa. Ban kai ga cewa komai ba Zuly ta ƙara da "kawai ki amince ita ce shawara da zan baki" Idona wani irin raɗaɗi na ji suna yi min kamar an watsa barkono ciki,maƙoshina ya bushe ƙamas dakyar na iya tattaro yawu na haɗiye kafin na ce "ban gane ba zan iya auren wani ba? Zulaihat wai wannan ɗin duk mene ne? Wane irin dokoki ne wannan? To ki tsaya ki ji in faɗa miki daga yau a yanzu da nake faɗa miki na fita daga family har abada,ku je can ku yi tsafinku kuɗi ne dai to ban so ku riƙe abinku.Kuma wallahi kika yi ƙoƙarin ɓullo min da wani sharri to sai na je har ofishin ƴansanda na shaida musu ke ce kika kashe mijinki" ina gama faɗar haka ban tsaya ɓata wani lokacina ba na fita na bar ta cike da shock.

Duk a tunanina shikenan na huta na jefar da ɗan mangoro na huta da ƙuda sai dai ina isa asibiti na tarar da tashin hankalin da ban taɓa zato ba. Jikin Abba ya rikice sai aman jini yake dunƙule-dunƙule,likitoci sun duƙufa wajen bincike amma result bai nuna alamun wata cuta ba ga jinin Abba sai ƙasa yake yi ga shi banda kuɗi,jinin kuma sai an saya.

Duk da yana cikin firgici da gushewar hankali bai hana shi isar min saƙon kar na saki na bayar da mutumcina ba.Banda kuka babu abin da nake yi,ji nake kamar na je na cewa Zuly na amince sai dai fa duk shaƙiyancina na tsani zina ban ƙaunarta ko kaɗan.Ko da ace saurayina ne wanda nake so ban ji zan iya basa kaina ba ballantana sindiƙin ƙato mashuriki matsafi.

A lokacin da zuciyata ta yi rauni sosai,shine ganin yadda jini ya soma yi wa Abba zuba ta hanci da kuma ido daga ƙarshe yayi shaƙuwa shikenan ashe ta fitar rai ce.Wuaren ƙarfe bakwai ne na yamma likito suka tabbatar mana da hakan,tsabar tashin hankali yasa na suma aka bani gado.Ban san abubuwan da suka faru ba sai a washegari na farka tuni kuma an kawar da gawar Abba an kai shi mankwancinsa na gaskiya.Sai a lokacin na yi kukan mutuwarsa kamar raina zai fita,kafin a sallame ni daga asibiti Allah ya ƙulla alaƙa tsakanina da wani Dr David shine ma ya ɗauki nauyin biyan kuɗin maganina har na ji ɗan sauki.

Bayan na koma gida ma haka yake zuwa yana kula da ni,kusan ma in ce shi ya ɗauki nauyin gidanmu tun da babu wanda ya tallafa mana daga dangi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull