Bakin ruhi complete - Chapter 32
Bakin ruhi complete Chapter 32: Bakin ruhi complete Chapter 32. Hajiya ko da take duba waya sai ta ga tuni ma MAHEER ya kashe kiransa.
3,365 words
Hajiya ko da take duba waya sai ta ga tuni ma MAHEER ya kashe kiransa.
★ASIBITI
Tun da na soma yin bacci aka ja ruhina zuwa wani wuri mai bala'in duhu ,haka na yi ta tafiya amma ban ganin komai a gabana can kuma na ji an riƙe ƙafafuwana,wani lantarki ne na ji ya ja ni da sauri na rumtse ido na sake buɗe su tare da sauke kaina ƙasa amma ban ganin kowa saboda matsanancin duhu.
Amon wata murya na soma ji mai cike da rauni da kuma neman agaji tana cewa"ina yi miki wannan furicin ne idona suna masu shatatar da hawaye,ni ɗin na kasance mace mafi shekaru a danginmu kaf don na kai shekara talatin har da bakwai amma ban taɓa samun tsayayyen saurayi ba ,ina son aure amma babu mijin.Gorin ahali,cin fuskar ƙawaye ba su taɓa tunzura ni zuwa wajen malami ba ballantana boka.Abin da na riƙe shi ne kawai addu'a,ana cikin haka ne mahaifina ya kawo mini wani a matsayin wanda zai aure ni.Sosai ji daɗi,duk da yanayin shi mutumin bai yi mini ba amma haka na yarda na amince ko ba komai dai ni ma zan yi aure kamar kowa.Cikin ƙanƙanen lokaci aka fara shirye-shiryen aurenmu,bayan biki bayan an kai ni ɗakina amma sai shi mijin nawa ya ce za mu je can gidan iyayensa mu yi sati ɗaya haka al'adarsu take.Bayan mun je can gidansu ina ta baza ido domin ganin a inda za mu kwanta sai dai babu,gidan iya ɗaki ɗaya ne da falo.Surukata ce ta matsa mini na je na yi wanka sai na canza kaya,bayan na yi wanka ina tsaka saka kaya sai ga mijina ya shigo yana mai shaida mini wai daren farkonmu mu huɗu za mu yi shi ,da na ce masa ban gane ba sai yake shaida mini za mu yi tarayya mu huɗu ni da shi da kuma iyayensa.Dukan furucinsa bai gama hucewa ba sai ga iyayensa sun shigo babu sutura a jikinsu,ban taɓa ganin bala'i ba irin wannnan kawai sai na fasa ihu na fito a guje sai ban kai bakin ƙofa ba na ji na zurma cikin wannan ramen da nake ciki,sama da kwana uku nake a nan ko ƙwaro ban taɓa gani ba in ba ke ba ki taimaka mini ki cece ni" ƙarshen labarin nata yayi daidai da farkawata daga bacci sai dai tamkar recoding haka amon muryarta ke yi mini suwa a cikin dodon kunne,na lumshe ido ina jin zuciyata na bugawa don kuwa na gane muryar wace ce,ita ɗin ƴar uwata ce Ƴa kuma ga Kawu Hamza babban Yayan kaf iyayenmu maza.Da na buɗe idona a karo na biyu sai na lura a inda nake,sai kuma na dinga jin motsi a cikin toilet duk da ban ga wane ne ba amma na fi kyautata zaton MAHEER ne.
Cike da tausayinsa saboda hukunci da zuciyata ta yanke mini a yanzu na yi saurin tashi ina mai furta wasu harufan da suka haifar da wani iska ya soma kaɗawa har gashin kaina na tashi sama,ƙofar ce ta buɗe da kanta na bi na wuce har na fito bakin ƙofar asibitin nan na yi arba da ainahin protector ɗina,wata jibgegiyar mage ce mai zanen tambarin tauraro da wata a goshinta,idonta sharrr suke sai haske suke fitarwa.A kan magen nan na hau ta soma yin wani juyi kamar ana kaɗa majaujawa kafin kuma ta cillo mu tushena,garinmu a kuma cikin gidanmu....... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
37
Kallon tsanake na yi wa gidan namu,duk an sauyawa komai an zuba uwar dukiya.Tsarin gidan tamkar aljanu ne suka ƙera shi tsabar yadda yayi kyau ya tsayu cikin tsari.Na ɗan saki murmushi jin kakari tamkar na fitar rai,ko da yake shi ɗin ma ne saboda mutuwar ce ke tunkaro mai kakarin saboda ina ɗauke da makami ƙwaya ɗaya tal da zai iya kashe shi ya koma inda ya fito.
A hankali na ci gaba da takawa ina dosar ƙofar da za ta sada ni da babban falon gidan.Tsit ko ina yake lokacin da ƙofar ta buɗe mini da kanta na shiga,yadda aka jera ɗakunan da kuma yadda aka tsara su bai hana ni na gane ɓangaren kowace direct sai na doshi ɓangaren Innarmu har na je bakin ƙofa na ji an dafa kafaɗata ta baya.
Da sauri na juyo,nan na yi tozali da Hassana a tsaye kan ƙafafunta gurbin idonta na kawo jini.Na rungume ta cikin farin cikin ganinta kafin na kira sunanta cikin sanyin murya,ta amsa mini da "na'am HAULE kin dawo?"
"Eh na dawo "
"Ina buƙatar mu keɓe a wani wurin da ba gidan nan ba domin sanar da ke komai da ya faru bayan ba ki nan"
Ba ta ida rufe bakinta ba na soma jujuya iskan bakina ,nan take wasu katangu huɗu suka yi mana iyaka da gidanmu ta yadda ko da wani ya shigo ba zai ji abin da za mu ce ba haka kuma bai ganinmu .
Ta ja wata ajiyar zuciya kafin ta ce "tun bayan tafiyarki abubuwan da aka saba yi suka ci gaba da tafiya har ma sai da aka samu ƙari.Kusan kullum sai iyayenmu maza sun yi meeting akan wannan ranar wacce za ki dawo,sun yi mata tanadi na musamman don sun sha alwashin naɗa ki sarautar kuma shugaba,sai dai al'amarin da ya faru yasa komai ya rogaje komai ya tsaya cak.A jiya na ji Kawu Hamza na cewa ke ce tushen wannan matsalar ,ko ma mene ne to ke ce sila don haka ko kin zo sai kin bar gidan nan don zamanki a ciki tamkar maido da zaren saƙa gadarsu baya ne, macce-maccen da ake yi sun ɗan tsagaita saboda dukiyar da BAƘIN RUHI ya musu sakayya da ita sai dai fa suna kawo mutanen da ba a cikin ahalinmu suke ba.Haule duk yaron da ya kuskura ya shigo gidan nan to fa ba zai fita ba,in kuma mace ce yadda kika san ana cire ciki daga mahaifar uwarsa haka suke cire budurcinta su miƙawa dodonsu.Gangar jikin kuma in ta yi rai za su haukata ta ko kuma su sa ta bar garin.
A kwanakin baya wani mutum ya zo nan gidan kwana ɗaya yayi kacal aka soma shirin bikin Mardiyya.Manufar auren nasu don ƙarfafa ginin matakin tsaron ɗakinsu na sirri da suka ɓoye dodonsu,kuma sarai iyayenmu maza sun san da cewa ahalin mijin an barranta su saboda yanayin tsafinsu da kuma uwar shirkar da suke yi.
Ita kuma baiwar Allah ta yarda ne tana ta murna saboda kawai ba ta taɓa aure ba,HAULE in da kin ga mijin Mardiyya bai brush haƙoransa yadda kika san masarar yin tuwo haka suke,ba shi ɗaya ba har da family ɗinsa amma a haka ta yarda ta yi auren da bai da amfani kawai don ta gaji da gori.Tun bayan auren hankalin iyayenmu maza ya tashi,saboda ƙofar da ta rage wacce ake iya kutse ta nan har zuwa lokacin ba ta haɗe da juna ba,hakan na nufin Mardiyya ba ta yi abin da ake so ba" shiru Hassana ta yi ,ni kuma na ce "ta ya aka yi kika ga duk abin da ya faru alhalin babu ido a tattare da ke?"
Ta saki wani murmushi kafin ta ce "saboda a baɗini ni ba makauniya ba ce,matar da ta yi mini aikin idon nan ta saka mini wani abu na musamman sannan ita ce ta toshe bakina don kar na yi magana.Kuma na ga amfanin haka don na ji sirrin iyayenmu maza wanda wanzuwata a wuri bai hana su yin hira"
Ban ƙara cewa komai ba ,sai formula da na karanto domin jawo ƙwayoyin idanun Hassana da Papy ya bani.Babu jimawa suka bayyana a tafin hannuna,na buɗe ƙyallen kafin na ɗauki ido ɗaya na saka mata shi ma na biyun haka.Jini ya soma zuba kafin kuma ya tsaya,sai ta dube ni tsakiyar ido ta saki murmushi tana mai cewa "Haule kin ƙara kyawu fa"
Na ce "Yanzu dai je ki kwanta,kuma gobe duk abin da zai faru kar ki fito daga cikin ɗaki ki zauna kawai zan zo gare ki" ta jinjina kai alamar ta ji ta ɗauka,na tarwatse katangun da na yi kafin ta kama gabanta ni kuma na shiga ɗakin Innarmu.
A kwance na tarar da ita kan sallaya tana bacci ,a hankali na taka na je na yi zaune kusa da ita ina mai ci gaba da kallonta kafin .Na kai hannu na shafi gefen fuskarta,cikin baccin ta furta "Haule?"
"Na'am Innarmu " na amsa,tarau ta buɗe idonta ƙila don jin muryata ne. "Haule ke ce ko kuwa mafarkin da na saba yi ne?"
"Ni ce da kaina Innarmu"
Da sauri ta tashi zaune tana kallona kafin ta kamo tafukan hannuna,hawaye ta soma yi suna ɗiga kafin ta soma magana cikin taushin murya "alhamdullah! Na gode ma Allah da ya nuna mini wannan rana,na jima ina tsamumaye sai yau Allah yayi nufi .Ina shi mijin naki?"
Na ɗan murmusa ina tunanin ko yaya MAHEER zai ji in ya duba bai ganni ba? Ko wane hali zai shiga a tsawon kwanakin da zai yi ba tare da ina kusa da shi ba? "Fatan dai yana lafiya ko?" Inna ta katse ni.
Na ce "eh lafiyarsa lau.Innarmu ashe shi ma Fahad ya rasu?" sai kuma hawaye suka ciko idona,Innarmu ta yi wani murmushi wanda ya fi kuka ciwo kafin ta ce "na ga rayuwa Haule amma yanzu ai komai ya zo ƙarshe tun da ga shi kin zo,shawarar da nake baki dai ki sa a ranki girman al'umma ya fi komai kar ji tsoro ko tausayin kashe wanda BAƘIN RUHI ke a cikin gangar jikinsa ko da kuwa Abbanki ne"
"Abba kuma Innarmu?"
"Eh yana ɗaya daga cikin makircin esprit sai su yi wasa da hankalin mutane su shiga a jikin wanda ba za ka iya ɗaukar mataki ba a kansa"
"Amma Innarmu..." da sauri ta katse ni tana mai cewa "zo ki kwanta HAULE " ban musa ba na tashi na kwanta kan shimfiɗarta,ido na lumshe ina jin wani daɗi na luluɓe ni yayin da kuma wani ɓangare nake cike da kewar mijina.Tunaninsa na yi ƙoƙarin lalubowa amma abin mamaki na kasa,ban san dalili ba kuma a haka dai na samu bacci ɓarawo ya ɗauke ni.
★A can ɓangaren MAHEER kuwa yana fitowa daga toilet ya ga babu HAULE ,tamkar wani mahaukaci haka ya soma duba ko ina na ɗakin amma babu ko da inuwarta ne.Cikin azama ya fito ya dinga dube-dube,sai dai kaf cikin asibitin ba ta nan.Ji yayi kansa na mugun sara masa,dakyar ya iya fita can harabar asibitin inda ya aje motarsa ya shiga yayi mata key sai gida.
A buɗe ya tarar da falon hakan yasa ya kutsa kai yana mai faman kiran sunanta amma shiru sai Hajiya ce ta fito take tambayarsa lafiya.
"Queen ce Mama ban gan ta ba,ba ta asibiti na duba ko ina fa"
Hankali ya yi wani mummunan tashi,murya na rawa ta ce " ban gane ba ta can asibiti,to ina za ta je? Bari na dubo ɗakinsu" Hajiya ta faɗa tare da shiga can amma iya su anty Bahijja kawai ta gani a kwance suna bacci har za ta fito sai ta ji motsi a toilet sai ta ce "Haule? Haule ke ce a toilet?"
Ambaton sunan HAULE shi ya tayar da Aliya daga bacci,yayin da kuma Lubna ta fito daga toilet daidai nan kuma MAHEER shi ma ya iso ɗakin duk da kuwa dare ne bai kamata a ce ya shigo ba.
Yadda duk kowa ya tayar da hankalinsa aka shiga duba Haule ta ko ina yasa Ikilima wacce ke can ƙumshe da baƙin ciki ita ma ta ji hayaniyarsu har ta fito,ba ta tambayi kowa meke faruwa ba amma yadda ta ga kaf ahalin su MAHEER waɗanda suka kwana a nan su ma sun tashi kuma hankalinsu duk a kansa yasa ta samo bakin zaren.
Ƙarin daɗa kuma fa da ta ji MAHEER na cewa "duk wanda ma ya san inda take gwara ya faɗa kafin na yi masa abin da bai yi zato ba" da sauri Ikilima ta bar wurin ta koma ɗakinta ta ɗauki waya ta kira Umma, ita kuwa sokuwa duk a tunaninta aikin da boka ne yayi mata ya ci sai kawai ta saki baki ta soma yin magana "to gobe tun da safe ki zo mu je mu yi masa godiya,ladar bayansa shine ki basa haɗin kai sannan ki tabbatar dai yau MAHEER ya kusance ki .Maganin da na baki ki ɗauke shi ki turara shi"
"Amma Umma ba shi ɗaya ba ne a falon ba"
"Babu ruwanki da sauran mutane ,ai iya shi ɗaya kawai maganin zai shafa"
Ita kuwa Ikilima jikinta na rawa ta ɗauko gawayin nan na zamani ta kunna ashana bayan ta tabbatar ya kama sai ta fita falo inda suke ta neman mafita.
Aliya na tsaka da cewa "Oga ni a tunanina mu je can asibitin mu duba Camera tsaro,in ma dai sace ta aka yi za mu gani in kuma Camera ba ta yi ba to...to ..to" tari ne ya hana ta ƙarasa abin da take son faɗa sakamakon hayaƙin da ya turniƙe wurin,duk kowa ya shiga yin tari banda MAHEER da ya kafe Ikilima da ido ita ma shi take kallo da idonta da suka yi ja kamar na tsohuwar mayya.Jikinta na ƴar kyarma ta ajiye mangal ɗin turaren,tana shirin yin kisisina don jawo hankalin MAHEER ta kai shi can ɗakinsu kawai ta ga yayi ball da mangal ɗin yayi sama tare da bugun fuskarta kafin ya faɗo ƙasa.
Ransa a mugun ɓace ya nufi ƙofar fita tare da cewa Aliya "zo mu je" da sauri ta bi bayansa ,suka shiga mota suka isa asibiti.
Camerorin tsaro ya shiga dubawa musamman na ɓangaren ɗakin da Haule ta kwanta,a hankali suka ga ƙofar ta buɗe amma babu kowa wanda ya fito haka suka dinga kallon yaɗa ƙofofi ke buɗe kansu da kuma rufe kansu amma kowa,da aka zo harabar asibiti ne suka hango idon magen da ta ɗauki Haule shi ma iya idonta ne kawai waɗanda suke ƙyalli.
Aliya ta ja ajiyar zuciya tana mai cewa "ta tafi gidansu"
MAHEER ya dube ta ya ce "ta ya aka yi kika gane?"
"Ga idon Roza nan na gani,magen maɗaukakiyar FARIN RUHI ce.Ka kwantar da hankalinka babu abin da zai same ta,yanzu tana da ƙarfin iko sosai wanda take iya tunkarar kasada kowacce iri" Sai a lokacin MAHEER kawai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanta.
★ HAULE
A cikin baccin da na soma ne na soma jin wani irin yanayi,yau shi ne farko da na ga ruhina ya bar gangar jikina zai yawo a cikin doron duniya.Balaguron ruhi ne,haka na fita daga gidanmu na bar gangar jikina a kwance a ɗakin Innarmu.
Gidaje na ƙetare har na isa can gidan Anty Mardiyya,tun a cikin soro na ci karo da ƙaton kai na Saniya an rataya masa layu sun fi kwano biyu sannan ga wasu rubuce-rubuce a bango da tambarin aljanu.A nan take duk na wargaza komai na ƙona su,hakan ya jawo hankulan ƴan gidan waɗanda kallo ɗaya za ka yi musu ka ga yadda tsafi da shirka ke yi musu ƙawa.
Duk iya shegensu ba su iya hango ruhina ba,haka na soma bincikar gidan har Allah yasa na ga baƙar rijiyar da suka jefa anty Mardiyya.A hankali na buɗe murfin sannan na shiga ciki,wurin baƙi ƙirin yake,amma shiga ta a ciki farin ruhina ya haskaka shi.Ban sha wahala ba na hango ta a zaune a ɗaure da wasu igiyoyi,tuni ta fice hayyacinta ni ce na cece ta na fito da ita daga cikin rijiyar.
Muna dab da fita na ji wata murya na tsayar da ni,na juyo muka haɗa ido ban san ma ta ya aka yi ba har ta iya ganina ba.
Ba tare da na tambaye ta ba ta soma bani labarin kanta wanda yasa na fahimci cewa ashe ba iya family ɗinmu ba ne kawai suka ƙware wurin tsafi ko kuma ɓoye wani sirrin,tabbas kowanne ahalin dai yana da wani sirri.
"Ina buƙatar taimakonki,ina tsakanin rai ko mutuwa nan ɗin gidan Uncle ɗina ne .Amma ni a yanzu ban san taƙamaimai ni wace ce ba,amma zan sanar da ke labarina duk da yana da tsayi amma zan sauƙaƙa shi ta hanyar gajarce shi .Tun lokacin da aka haife ni aka sayar da ruhina ga duniyar ɓoye,an yi ƙoƙarin kashe ni ta kowacce siga saboda a cikin family namu akwai wani mai ɓoyayyar fuska,ko kuma na ce mutum da rigar aljan wanda yake sayar da ƴaƴan ƴan uwansa domin samun ƙarfin iko da kuma arziki.Wannan mutumin ba kowa ba ne sai Kawuna,mugun mutumin nan yana ɗauke da wata baƙar takardar mai jerin sunayen rayukan da ya ɗauka,a samanta kuma ni ce ta gaba wacce zai kashe .Yadda nake mai riƙo da addini ne yasa har yanzu ya kasa kai ni ƙasa,amma duk da haka ya toshe hasken taurarina sannan yana yi mini izaya ta hanyar turo mini fatale suna firgita ni,duk inda zan je kuma sai sharrinsa ya bi ni wani sa'in sai ina tsaka da tafiya sai na koma mahaukaciya na cire duk suturar jikina,haka kuma duk dare na Allah haka ruhinsa ke zuwa yana amfani da ni da na gaji da yawo shi ne na zo na tare gidansa kamar yadda ya buƙata tun farko babu laifi ya bar yi mini izaya sai dai fa ban iya fita daga gidan"
"In kin fita daga nan za ki iya gane gidanku?" na tambaye ta,ta bani kuwa amsa da eh kawai sai na kamo hannunta muka fito.Sai a lokacin na rufe duk wata hanya sannan na cillawa gidan wuta ,na yi amfani da furicin Aliya ne a ranar da ta kashe matar nan da ta kashe ƴaƴan kishiyarta,tabbas akwai mutanen da in an samu dama kawai kashe su shi ne ya fi zama alkhairi.
Ita kuwa Anty Mardiyya sai da na zo tsakiyar gidanmu sannan na kwantar da ita na wuce ɗaki,na tarar da Innarmu a tsaye gaban gangar jikina tana tashe ni.Da sauri na mayar da ruhina a ciki kafin na buɗe ido na ce "na'am Inna"
"Tashi ki yi alwala " shi ne kawai abin da ta faɗa ,kamar yadda ta ce haka ɗin na yi na je na yi alwala na yi sallah bayan mun gama muka soma taɓa hira ina ta bata labarin su Lubna da Aliya .Can kuma na sauya zuwa na MAHEER ina jin zuciyata na yin sanyi,muna tsaka da nishaɗi aka turo ƙofa Abba ne fuskar nan tasa tamau babu annuri kafin na yi yunƙurin furta kalmar gaisuwa sai cewa yayi "ki zo ke da ƴarki a ɗakin hukunci" yana gama faɗa ya fice yayin da kuma na ga hankalin Innarmu ya tashi sosai,har ya kai na tambayi kaina a zuci 'yaushe kuma aka yi wani ɗakin hukunci ban sani ba? Me ake yi a can ɗin me kuma ya ƙunsa?????"
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*