Bakin ruhi complete - Chapter 33
Bakin ruhi complete Chapter 33: Bakin ruhi complete Chapter 33. Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
3,346 words
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
38
Yadda na ga hankalin Innarmu ya tashi sosai yasa na tambaye ta "yaushe kuma aka yi wani ɗakin hukunci? " ba ta iya bani amsa ba ,sai miƙewa da ta yi a dole ni ma na tashi .Tana gaba ina bin ta a baya har muka isa wani ɗaki,duk iyayenmu maza suna a zaune kowanne ya ɗaure fuska kamar tsohon kashi.
Innarmu ta zube ƙasa kan jan capet ɗin da ke malaye a ɗakin tana mai furta,"ko ma dai wanda irin hukunci ne za ku yi mata ni na ɗauka ku yi mini madadinta " da sauri na je na kama kafaɗun Innarmu ina son miƙar da ita,amma Kawu Hamza ya daka mini wata irin tsawa yana mai cewa "nan ɗin ni ne mai magana da kuma bada izinin kowanne motsi don haka ki zube gwiwanki ƙasa" a yadda na fahimta yayi haka ne don ganin shin ina da ƙarfin ikon ko kuwa dai su ne suke hasashe .Rawar jikin ƙarya na ɗauka kafin na zube kamar yadda ya ce ɗin,sai na ga suna ƴar kallon-kallon tsakaninsu.
"Tsawon shekarun nan kina ina ? Muna saurarenki muna son jin inda kika je ba tare da kin waiwayi gida ba" Kawu Hamza ya sake faɗa .
Idona ya kawo ruwa na soma kyarma tare da soma basu haƙuri,ganin haka yasa ya ce mu tashi mu fita.Innarmu ta fara miƙewa sannan ni,haka muka baro ɗakin muka dawo nata.Muna shiga ta tsure ni da ido kafin ta ce "ya aka yi kika iya sarrafa su? "
"Babu komai Innarmu kawai dai gaskiya ce ke son yin aikinta "
"Ya kamata ki gaggauta aiwatar da abin da ya kawo ki kafin su gano gaskiyar "
"Zan yi Innarmu amma sai zuwa dare" haka muka dinga yin hira har hantsi yayi muka yi wanka muka fito,sai a lokacin ƴan gidan suka san da na dawo yayin da kuma lokaci zuwa lokaci suke taɓo zancen gidan surukan anty Mardiyya ya ƙone ƙurmus Allah yayi mata awon arziki ita ba ta ciki.
Kan dianing masu aiki suka jera abincin breakfast,sai na ga abin banbarakwai don saman tabarma muka saba ci.Tashi na yi na ɗauki plate na zuba kafin na nufi ɗakinsu Hassana,tana kwance tana kallon sama na yi mata sallama ta amsa kafin ta tashi zaune.
Kusa da ita na zauna muna kallon juna muna murmushi kafin mu soma cin abincin,na ce "Hassana a cikin moments ɗinmu na baya wanne ne ya fi burge ki wanda yanzu kuma gidan nan ba a yinsa?"
Ta ce "cin abinci a faranti guda bayan mun gama kuma a yi gatana"
"Ni kuma ɗebo ruwa a rijiya,saboda a can ne tushen samo bakin zaren da muka yi a yanzu ya fara."
"Ba ki bani labarinki ba ,ya kika ji lokacin da kika bar gida har ta ya kika iya zama a wurin da babu Innarki?"
Na ɗan murmusa kafin na bata labarina a taƙaice,ta waro ido bayan ta gama ji ta ce "yanzu nan kina da aure Haule? Kam! Na so in ga mijinki kuwa"
"Kyakkyawa ne kuwa irin sosai ɗin nan, kuma inda kin ga yadda yake mugun sona "
Hassana ta ja numfashi kafin ta ce "ke ma ai kina sonsa sosai ,a yadda kike zuba wannan fara'a"
"Eh yanzu ma ji nake kamar na gansa a gabana "
"Da zarar kin yi aikin da kika zo ai shikenan "
"Wane aiki?". Goggo Lami ta faɗa wacce shigowarta kenan. Duk shiru muka yi muna kallonta,ba zan taɓa mantawa ba shekarun baya ma ta taɓa rutsa mu muna hira.Ban ɗauki tsawon lokaci ba na yi amfani da power na juye mata tunani akan abin da ta ji,sai kuma ta saki murmushi kafin ta ce "ah Haule ashe nan kika shigo?"
"Eh abinci muke ci " na bata amsa,ita kuwa fita ta yi ta bar mu nan.
Hassana ta ce "Haule mene ne kika yi a yanzu? Na ga idonki sun koma sak na mage"
Na ce "ina tsoron ta je ta sake faɗawa wani hirarmu shi yasa,amma ban yi don cutar da ita ba"
"Haka ne,yanzu yaushe kike tunanin shiga can?"
"Tare za mu je ai" na bata amsa nan kuma muka ci gaba da tattaunawa.
A can ɓangaren su Kawu Hamza kuwa sun gwada Haule ne kamar yadda ta yi tunani,sai dai fa ba wai sun bar ta ne ta tafi ba wai don sun gamsu ba a'a idonsu na kanta.
Kawu Laminu ya ce "hum! Kana ganin idon Haule ka san ba ita ce ta farko ba"
Kawu Hamza ya ce "tsorona dai guda kar a je wajen guje-gujen barin gida a ce sai da ta yi yawon ta zubar don kamar a cikakkiyar mace nake hango idonta,in kuwa haka ne kun san halin Maitama ba zai yarda ya zubar da makaman yaƙin ba kamar yadda ya faɗa lokacin da ya nemi a aura musu Haule "
"Ni kam Ibrahim ya na ji ka yi shiru? Fatan dai ba za ka bamu matsala ba in muka tabbatar Haule ce matsalarmu"
Ibrahim wanda ya kasance mahaifin Haule ya ce "kar ka manta na fi ka sadaukar da ƴaƴana duk don na ga Baba na ci gaba da rayuwa da runhin BAƘIN RUHI, sannan in maganar tsoro ce ka san ba na cikin sawun maza masu faɗuwar gaba.Ko yau aka tabbatar da Haule ce tushen matsalarmu ku yanke mata hukunci kai tsaye"
Kawu Hamza yayi wani murmushin jin daɗi jin abin da ɗan uwansa ya ce,ba banza ba yake ganin mahaifinsu ya zaɓi Aliyu matsayin Jagaba ba komai ya kawo hakan ba sai don sanin Aliyu daga tsatson Ibrahim ya fito sannan ita kanta Haulen abin da yasa suka fi zurfafa zatonsu kanta don sun ga ita ce taƙadiriya wacce ba ta da tsoro a kaf ƴaƴan shi Ibrahim ɗin, sannan tana da taurin kai da kafiya akan abin da ta sa gaba.
"Muna tsumayen ganin gaskiyar abin da kake faɗa" Kawu Laminu ya faɗa saboda a duniya yana jin takaicin Haule a tunaninsa ta dalilinta ne Hassana ta rasa idonta, sannan muƙamin da ke hannunta ya so a ce ƴarsa ce ke da shi.
Haka suka ta yin hira wacce babu abin kirki a cikinta kafin kuma su miƙe don yi wa sabon ginin tsafinsu ban ruwa.Yatsunsu suka tsaka dukkansu kafin su je gaban wata ƴar randar ruwa su dinga ɗiga shi,nan take ɗakin hukunci ya ɗauki wani hatsabibin duhu .Duk yadda suka so su sada da mahaifinsu abu ya cuttura saboda yana can a takure yana zaman jiran farmaki sai kakarin mutuwa yake . Ganin haƙarsu ba ta cimma ruwa ba suka haƙura ,ɗakin ya dawo normal .
★ Da dare bayan duk an ci abinci an kwanta ni da Hassana muka fito ta yi mini jagora zuwa ɗakin sirri ta ƙofar baya.Kamar yadda ta faɗa luluɓe yake da matakan tsaro ta ko ina illa ƴar siririyar hanyar da ba a toshe ba wacce dama alƙaluma sun nuna ta nan ne zan bi.
Na dube ta kafin na yi mata alama da ta tafi,ba ta musa ba ta juya yayin da ni kuma na bi na ratsa na shiga ciki dakyar.Tamkar wutar murhu haka ɗakin ya ɗau wani irin ja sosai yayin da kuma muke ƴar kallon-kallon ni da Kakana Nalado wanda yake cikin siffar mutane sai gumi ke yi masa tsiyaya kamar wanda aka bai wa gashin nama.
A halin yanzu in ban fi shi ƙarfi ba to za mu zo daidai,don kuwa ƙarfin ikonsa bai fi nawa ba.Da a ce kamar can baya ne da MAHEER bai tura mini nasa ƙarfin ikon ba,da tabbas Nalado ya soma azabtar da ni.
"Maitama ban san dalilinka na son kai ni ƙasa ba,kar ka manta tsawon shekarun da muka ɗauka ni da kai muna fafatawa a tsakaninmu amma ba ka taɓa yin nasara a kaina ba" shi ne abin da Nalado ya faɗa.
Yana dire furicin sai na ji tamkar har da esprit da ruhin Maitama suna cikin gangar jikina haka kuma duk rayuwar da yayi a baya ta dawo cikin kwanyata ta zauna daram.Wata irin dariya na yi kafin na ce " a'a Nalado kar ka yi ƙarya,ka tuna ni ɗin mai yin nasara ne kullum a kanka,in ba ka manta ba duk inda ka yada zango don yin mugunta ni ne nan ke haskaka wurin don mutane su farga"
"Duk da haka dai ga shi zaman doron duniya yayi maka wuyar zama ta sila ta,ka ga ka kama gabanka ka bar ni na yi rayuwata yadda nake so"
"Ba zan taɓa barinka cikin doron duniyar nan ba Nalado sai ka koma inda ka fito,zan mayar da kai duniyar matattu don can ne ya fi dacewa da kai " na furta ina mai yin tsalle na kai masa farmaki,na kumburtsi fuskarsa yayin da shi kuma yayi cilli da ni na faɗi gefe amma na yi saurin miƙewa muka ci gaba da gwabzawa.
Sai da na jigata shi sosai sannan ya fara rikiɗa cikin siffar da dama ita nake jira ya ɗauka.Da farƙo ƙashin bayansa ne ya fara kumbura ya faso fatarsa ya fito ya bayyanar da wani doro,kafin kuma wasu ƙahonni biyu su fito masa a kai zuwa can kuma harshensa ya zazzalo yana ɗigar da wasu yawu masu ɗohi da harshen yayi amfani wurin ɗaure ƙafata kafin ya ida rikiɗa ya dawo sak BAƘIN RUHI .
"Hahaha! Ka ha'inci abokinka ka haɗa jininka da jininsa a wuri guda don kawar da ni sai dai ka sani wannan shi ne babban kuskurenka zan fara cire ɗan jinjirin cikin mutumin da ta fi so a duniya kafin na kashe ta" ya faɗa cikin wata irin murya,daidai nan tunanina ya dawo jikina sai hankalina ya tashi jin wai ina ɗauke da cikin MAHEER amma zai cire shi.
Azabar da na ji ta huda cikina ce yasa na farga na tuna tashin hankalin da nake fuskanta,idona suka fara rufewa tsabar azaba ina jin yana ɗalasiman tsafi da niyyar cire cikin jikina.Dakyar na iya motsa bakina na furta harufan da nake amfani da su,nan wuƙar da muka fitar cikin dutsen nan ta bayyana a hannuna ban ɗauki lokaci ba kuma na daɓa masa ita tsakiyar baya.
Yayi wata irin kururuwa wacce ta girgiza kaf illahirin gidan,yayin da duk wani abu da ke na kwalba ya tarwatse ,bangon ɗakin ma wanda muke ciki haka ya tsage.
Da jajayen idonsa yake kallona kafin ya soma bajewa kamar wani hayaƙi yana bin iska,a daidai lokacin da BAƘIN RUHI ya mutu a daidai wannan lokacin ne kuma iyayenmu maza suka shigo ɗakin suna furta "Babaaa???" dakyar na ware idona na ga Kakana Nalado cikin jini yana kakarin mutuwa.
Muryarsa ba ta fita sosai yake cewa "Ibrahim na cire ka a cikin jerin ƴaƴana tun da har ka haifi annoba wacce ta yi silar mutuwata ta gaske sannan ta fitar da ruhin da ke bani duk abin da nake daga cikin gangar jikina.Ka sani ba zan taɓa yafe maka ba sai ka yi abu ɗaya tal ka maido da *BAƘIN RUHI* duniyar nan ka tarwatsa kaf zuri'ar Maitama,cikin jikin Haule kuma a cire shi ban ƙaunar haɗa jini da shi"shine furucinsa na ƙarshe wanda yayi daidai da soma fitar duk wani ƙarfin iko daga jikina yana koma can tushensa kamar yadda baƙin ruhin shi ma ya tafi can.
Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti, Innarmu na gefena yayin da nurse ke saka mini ƙarin ruwa. Innarmu ta saki murmushi ta ce "Haule kin tashi?"
Kai na jinjina mata alamar eh,sai ta furta "alhamdullah" haka na tsaya a kwance har sai da ƙarin ruwan ya ida sannan aka sallame mu muka nufi gida.
Tun da muka karyo layinmu na ga mutane sun cika wurin,haka muka ratsa muna ƙoƙarin shiga gida aka fito da gawar Kaka Nalado wanda tsofin garin ne suka ɗauko makarar suna tafe suna yin waƙoƙin tsafi.
Har zan kawar da kai sai kuma na ji Kawu Hamza na cewa "kar ki saki ki ƙara tako ɗaya don ba za ki shigar mana gida ba da cikin muguwar zuri'a ba"
Na tsaya cak ina kallonsa,nan kuma sauran ƴan uwansa suka taso su ma duk suka tsayu kan ra'ayinsa ina ji ina gani suka hana ni shiga har sai da Abbana ya zo ya ce "ina bada shawara a matsayina wanda Baba ya bar ma wasiyya cikar burinsa da ku bar surukar Maitama ta shiga gidan nan,ko ba komai ita ce makamin da za mu riƙe don cimma burin mahaifinmu " da kallo mamaki na bi Abba wanda yake jefo mini kallon tsana mai cike da son ɗaukar fansa, Innarmu ta ja ni zuwa ciki yayin da zuciyata ta kasa daina rawa fahimtar da sauran rina a kaba,zaune ba ta same ni ba....
[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
39
Muna shiga ciki direct ɗakin Innarmu muka shiga,har bakinta ke rawa wurin tambaya ta "Haule me ya faru a ɗakin sirri?"
"Babu komai Inna kawai dai na mayar da BAƘIN RUHI duniyarsa wanda yayi dai da mutuwar Kaka Nalado kuma iyayenmu maza sun shigo sun gani shi ne Kaka ya ce wai Abba ya san yadda zai yi ya tarwatsa ahalin MAHEER"
"Da kika soke shi da wuƙa a ina ne kika daɓa masa ita?"
"Ga bayansa"
"Da matsala Haule,kin ga da ace a ciki ne ko a saitin zuciya to da ba zai taɓa yarda ya dawo duniya ba.Amma bari na duba na gani ko da kwai abin da ya kamata mu yi kafin lokaci ya ƙure " ta faɗa tare da fiddo wani ƙaton littafi shi ma mai hoton dodanni.
"Lissafa mini siffofin shi dodon wanda Kakanki Nalado ke dakon ruhinsa" Inna ta umarce ni nan na shiga yi mata bayani dalla-dalla har na gama sai ga shi kuwa ta binciko hotonsa.
Bayaninsa ta soma karantawa har ni ma ina ji,yadda tsarin yake ko da dodon zai sake dawowa a duniya a karo na biyu to ba zai zauna a jikin wanda ya taɓa haifar ɗa ba,sannan mutum ne zai je can dajin sirri ya jawo shi izuwa gare shi.
Bayan mun gama karantawa sai na ja ajiyar zuciya na ce " kenan in haka ne Abba ba zai taɓa yin nasara ba,kuma kin ga iyayenmu maza ma duk suna da ƴaƴa"
Innarmu ta ce " ai suna iya nemo wani Haule,ni dai burina shi ne mu kamata yayi mu je nemansa kafin su rige mu zuwa sannan da buƙatar mu jira zuwan Aliyu mu kwatanta masa yadda abubuwan nan suke da illa"
Ambaton sunan Yaya Aliyu yasa gabana faɗuwa don kuwa a yadda na gansa tare da su Boss tsaf zai iya yarda ya ɗaukar wa kansa jidali. "Innarmu yaushe Yaya Aliyu ya canza daga mutumin kirki zuwa irinsu iyayenmu maza? Shi ne fa Jagaba na ƙungiyar baƙin ruhi,kuma wai ni ce excelency hum"
Shiru Innarmu ta yi tana nazari kafin ta nisa ta ce "Allah ya bamu nasara ,bari na kawo miki abinci"
"Innarmu me zai hana mu haɗa kayanmu mu tafi?"
"Babu inda za ku je,in kin ga kin sake fitar da ƙafarki waje to ki tabbata banda rai ne Haule.Ke da komawa cikin zuri'ar Maitama sai kuma a lahira in kun haɗu,ke kuma ina mai gargaɗarki da kar ki saki ki yi kuskuren saka hannunki akan lamarin da bai shafe ki ba" ya nuna Innarmu yana wani irin watsa mata harara,sai na ga ta sunne kai ban san dalilin da yasa har yanzu tsoronsa take ji.Bayan ya fita ne ta ce "ki fara shirin karɓo dukkan power ɗinki a karo na biyu don zaune ba ta ganmu ba,sannan ina so ki san yadda za ki yi ki raba ta gida biyu ki bai wa mijinki wani kaso don da buƙatar ya tsaya kusa da ke sannan hatta ciwon da ke cikinki a yanzu jininsa dai ne zai warkar miki da shi"
Shiru na yi ina shirin magana Abba ya shigo ashe laɓe yake yi mana,wani makirin murmushi yayi kafin ya ce "da kyau! To ki sani yau Haule za ta bar wannan ƙasar yanzun nan ba sai gobe ba zan tura ta makaranta ta ci gaba da yin karatunta,dakon BAƘIN RUHI kuwa ita ce nan za ta ɗauke shi a yayin da ya ratsa gangar jikinta ya shiga na sadaukar masa da jinjirin cikinta matsayin hadiya" yana gama faɗar haka ya wani cakumo ni ya fito da ni waje,can ɗakinsa na baraya ya kai ni wani turare ya shaƙa mini wanda yasa na fita daga hayyacina ko da na farka a wani wajen na tsinci kaina.
Dakyar na iya tashi zaune na ƙarewa wurin kallo,ya fi kama da asibitin gargajiya don ga kwalaban magunguna,da kuma ganyayyaki nan birjit.Ina a haka wani dattijo ya shigo fari tasss da shi,kana ganinsa ka ga Bature .Cikin wani Yare tun na ƙarnin baya yayi mini magana amma ban gane me yake faɗa ba,can ya canza harshe zuwa French ya ce "ki aje esprit ɗinki wuri guda a yayin da nake yi miki Yaren duniyarki,za ki ga sarai za ki tuno da kin taɓa iya shi" yana gama faɗar haka ya canza harshe,sai da na nutsun ɗin kamar yadda ya ce sannan na fahimci abin da yake cewa ɗin.
"Mahaifinki ya kawo ki wannan makarantar ne,za ki ci gaba da karatunki na boko da kuma na duniyar Ruhaniya.Ya bada amanar ki ne a hannuna,shawarar da zan baki kar ki ma gwada tserewa don an zuba matakan tsaro ta yadda ba ki tunani, muddin na same ki da wannan laifin zan yi miki hukunci fiye da yadda kike tunani kin fahimta?" ya jefo mini tambayar daga ƙarshe,na jinjina masa kai alamun eh duk da cewa a ƙasan zuciyata ƙarya ne ina da burin tserewar.
Wasu magunguna ya bani na sha sannan ya buɗe ciwona ya zuba mini magani ya kuma rufe shi.Bayan nan sai ya ja ni muka fito harabar makarantar wacce take maƙil da students maza da mata har da ma waɗanda suka manyanta.