Bakin ruhi complete - Chapter 35
Bakin ruhi complete Chapter 35: Bakin ruhi complete Chapter 35. "Abokina ni ma ban sani ba,amma yadda kasan akwai aljana doguwa mai tsotse jinina haka nake…
3,259 words
"Abokina ni ma ban sani ba,amma yadda kasan akwai aljana doguwa mai tsotse jinina haka nake ji,sam ban iya yin bacci" David ya faɗa kamar a ɗan tsorace,hakan yasa MAHEER yin shiru da bakinsa sai ya yanke shawarar kwana a nan.
Da dare yayi sosai sai David ya kwanta a waje yayin da MAHEER shi kuma ya shiga ɗaki yana mai yin addu'ar Allah nuna masa abin da yake damun abokinsa.Yana kwantawa ya ji tamkar an shaƙe masa wuya an hana numfashinsa tafiya normal,yayin da kuma yanayin ɗakin ya canza ya dinga jin saukar hucin mutane da yawa amma bai ganin kowa.Ƙoƙarin cutar da shi ake son yi amma tamkar akwai wani ɓoyayyen ruhi mai kula da shi MAHEER ɗin sai suka kasa cin galaba kansa.Wani irin shuuu ya ji irin kamar an ƙetara mutum in yana kwance,sai a lokacin Maheer ya samu damar ganin wata inuwa za ta gudu sai yayi saurin cabko ta a wani irin fitinanen zafi ne ya ratsa masa hannu a dole ya saki inuwar, washegari ko da ya farka sarai ya tuna komai sai kuma hannunsa da ya gani ya ɗauki ja kamar alamun jini ya kwanta.
Dakyar MAHEER ya yin sallah,bayan ya gama ko sallama bai yi wa David ba ya kama hanyar gida amma yadda zafi ya rufe shi ya ji yana buƙatar yin wanka da ruwan sanyi ko kuma ya samu inuwa mai kyau ya kwanta ya huta.Hanyar da yake jin ƙamshin ruwa ya nufa,bai kuwa kuskure ba wani tabki ya gani wanda ya kasance magudanar ruwa sai zillo suke farare tasss da su.Daga nesa sai Maheer yake jin tamkar ana zuƙo ruhinsa ana son nitsa shi ciki,amma da ya so dab da ruwan sai ya ji wata irin nutsuwa ta saukar masa.Sam bai wani damu da jawabin Maigari ba tun can farko,hakan ya sa ya zauna ya dinga wanke jikinsa.Yadda ya ji ruwan ƙarau masu mugun sanyi kawai sai ya shige ciki yayi wanka yana jin wani irin daɗin sanyi na ratsa shi.Ya ɗauki sama da minti talatin kafin ya fito ya kama hanyar gida,da ya isa ne Umar ya tambaye shi lafiya yake ta nishaɗi haka sannan kuma yayi kyau sosai hasken fatarsa ya fito sosai.
Maheer ya ce "wanka na yi da ruwan tabki yanzu da na fito daga wurin David"
Da ɗan mamaki Umar ya dube shi kafin ya ce "amma kuma ya aka yi kayan jikinka ba su nuna ka shiga ruwa ba?" yayi tambayar ne yana taɓa rigar Maheer wacce take a bushe ƙamas.Shi ma sai a lokacin ya lura da hakan sai ya shiga mamaki yayin da shi kuma Umar ya shiga yi masa dariya har ya kira Mahmud ya labarta masa abin da ke faruwa. Ganin kamar suna son ƙaryata shi sai ya ce "wallahi gaske na yi wanka,in kuma ba ku yarda ba ku zo na kai ku tabkin"
"Eh mun yarda amma dai ba da wannan kayan ka shiga ba"
"Da su na shiga mana,in kun yi gardama ku zo mu je" ya faɗa tare da yin gaba su kuma suka take masa baya har suka isa bakin tabkin.
Wannan karon shi da Mahmud suka shiga sannan kuma suka fito a tare,sai dai abin mamaki iya kayan Mahmud kawai suka jiƙe banda na MAHEER.A wannan gaɓar wani abu ne mai kamar tsoro ya ratsa zuciyoyinsu musamman ma shi uban gayyar.A haka suka dawo gida bayan duk sun faɗi abin da suke tunani game da al'amarin,sam sai Maheer ya kasa sukuni da suka yi girki ma kasa ci yayi.Da maraice kuma yayi wanka ya nufi asibiti don a can zai kwana wurin gadi,aiki ya fara kafin ƙafa ta tsananta duk sai suka je suka kwanta.Yau ɗin ma kamar jiya haka aka kashe ƙwayaƙwayin fitilun lantarki aka kunna na fitilar ƙwai mai yi da kalanzir.Kasa haƙuri MAHEER yayi ya tambayi abokin aikinsa,"ni kam me yasa ake kashe ƙwan lantarki duk dare?"
Sai da yayi ɗan jimmm kafin ya ce "saboda hasken lantarki yana jawo hankalin fatalwa da kuma baƙin ruhi"
"Ka yarda da fatalwa?" MAHEER ya tambaya. Abokin ya ce "eh sosai saboda a nan aka haife ni,kuma na sha ji da ganin abubuwan ban mamaki amma in ka yi garma kana iya kunna hasken lantarkin sai ka ga abin da zai faru da kai"
Maheer yayi wata irin dariya don sam bai yarda ɗin ba,sai dai bai ce komai ba.Abokin aikin nasa na yin bacci Maheer ya kai hannu ya danna makunin wuta,ɗakin ya gawaye da haske sama da minti goma shiru babu wata alamar abin tsoro har sai da MAHEER ya ja tsuki ya ce "dama na san ƙarya ce" martanin tsukin aka maido masa,kafin yayi wani yunƙuri kuma ɗakin ya cika da ruwa maƙil tamkar kuma mai cutar shanyewar jiki haka MAHEER ya kasa yin motsi yana ji yana gani har ruwan suka luluɓe shi duka kansa ya nitse a ciki sai dai abin mamaki sam bai ji wannan alamar ba ta dantsewar numfashi normal yake jinsa kai kace dama shi halittar ruwa ne.
A sannu a hankali kuma ya soma jin ana jan fatun idonsa ana rufe su,daga nan ya fita hayyacinsa sai tashi yayi ya tsinci kansa gaɓar kogi...... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
41
Maheer ya tashi zaune yana duba ko ina na wurin,tsit kake ji sai kukan jemagu da kuma ƙarar gudun ruwa.A saninsa dai a asibiti yake kwance amma me ya kawo shi nan bakin tabki sam bai sani ba. Yana zaune ya ji murya mai sanyi ta ce "sannu!"
Da sauri ya juyo,nan yayi arba da wata tsaleliyar budurwa fara tasss da ita,mai dogon gashin kai da yalwar girar ido da ta goshi.Murmushi ta sakar masa kafin ta zauna gefensa tana mai cewa "kana zaune kai ɗaya me kake yi?"
"Babu komai" ya bata amsa. Ta ce "amma yanayinka ya nuna kana cikin damuwa" ta yi furicin tare da ɗora hannunta kan wuyansa,nan take wani lantarki ya ja Maheer ya soma jin wani mugun sonta da ƙaunarta.Ba tare da ya tambaye ta ba kuma ta ce "sunana Bairama"
Ya ce "ni kuma Maheer"
Ta ce "ai na sani" sai ta dinga juya idonta suna kawo wani haske,ya ce "kina da kyau sosai,wace ƙabila ce ke?"
Bairama ta kalle shi tsakiyar ido tana mamakin wane irin ruhi ne haka gare shi mai ƙarfi da ta kasa cin galabar mallake shi duka ya fita hayyacinsa?
"Ko balarabiya ce?" yayi tambayar yana kallon dogon gashinta da ke kaɗawa cikin iska .
"Za ka sani a sannu yanzu dai zan tafi gida"ta yi furicin tare da tashi ta yi suka cikin ruwa tsumbul,ruwan suka faltsa a fuska Maheer ya lumshe ido da sauri tare da jan doguwar ajiyar zuciya.Yana buɗe ido ya gansa a kwance kan gado a cikin asibiti.
Ya tashi da sauri yayi zaune ƙafafunsa na lilo,ɗakin babu duhu hakan ya basa damar ganin tattakar ƙwan lantarki da ya faɗo ya fashe yayin da kuma fitila a ci balbal ke ta yin aiki.
Idonsa ya ga kamar suna yi masa gizau,ruwa ne ke shigewa ƙarƙashin tile har suka ƙwafe.Ya ja numfashi yana tunanin shin mafarki ne duk abin da ya faru ko gaskiya ne? Ruhinsa ya fi aminta kan cewa kawai mafarkin ne yayi sai dai ƙamshin turaren nan da ya ji a jikin budurwar da ta ce masa sunanta Bairama ya kasa fita a ƙofofin hancinsa.
Yana zaune a haka shugaban asibitin ya turo ƙofa ya shigo, Maheer ya ɗago kai suka haɗa ido sai ya ga yana watso masa wani kallo kafin ya ce"ka zo" sai kuma ya fice.Maheer na sauko ƙafafunsa ƙasa ya ji wani sanyi ya ratsa shi kamar irin dai ka shiga ruwan ƙorama ko makamancin haka.Yana fita sai ya nufi ofis ɗin shugaban,a zaune ya tarar da shi ofishin babu ƙwan lantarki sai wata fitila wacce ba normal ba,an ƙerata ne da ƙwarangwal kan wata dabba,ta bakinta ne wutar ke fitar da haskenta.
"Ga ni shugaba" ya faɗa a ladabce.
"Ranar da kuka zo ba a faɗa muku dokokin garin nan ba?" yayi tambayar cikin wata murya mai nuni da fushi.
Maheer ya ce "an sanar" "Shi ne kuma ka taka doka?" "Wace doka?" ya tambaya don shi har ga Allah bai kawo a kansa cewa kunna ƙwan lantarki shugaban ke magana ba.
Da jajayen idonsa waɗanda kana gani ka ga na mugu ya ɗago ya dubi Maheer,gabansa ya faɗi yana tuno idanun nan fa irinsu ne ya gani a tsuntsuwar nan. "Fita!" ya faɗa cikin fushi,Maheer yana fitowa direct hanyar komawa gida ya kama saboda yadda zuciyarsa ke azalzala yana jin wani ɓacin rai da bai san yana da shi ba sai yanzu.
Garin da sauran duhu don safiya ba ta yi ba,yana fitowa daga harabar asibitin ya ji tamkar ana take masa baya can kuma ya ji wata murya cikin wani salo tana kiran sunansa "Maaaheerrr!" wani irin zuuu ya dinga jin dodon kunnensa na yi yayin da muryar ke ratsa ƙashi da ɓargonsa tana game ruhinsa kan ya farga ya fita daga controling ƙwaƙwalwarsa kawai sai ya soma tsoma ƙafafunsa duk inda ya samu a haka har ya isa inda amon muryar nan ke kiransa yana dab da ɗora ƙafarsa kan wani ƙaton dutse sai ya ji an jawo shi ta baya yana juyowa yayi tozali da Bairama wacce ta ci ado kamar za ta je gasar kyawu,sai a lokacin kuma Maheer ya ɗan nutsu ya soma duba wurin da yake a tsaye,ba ko ina ba ne makwantar matattu.
Kafin ya yi magana ta ce "ba a fitowa tsakiyar dare fa,ka ga saura ƙiris ka faɗa tarkonsu zo mu je" A yayin da take magana bakinta kawai ya tsure da ido yana kallo yana jin wani shauƙin sonta na fizgarsa,wanda kuma ba komai ya haifar da haka ba sai yadda Bairama ta baje kolin basirarta wurin asirce shi.Sam Maheer bai cikin hayyacinsa,burinsa guda ne tal shi ne su kasance tare shi da ita kamar yadda wannan ne babban burinta auren jinsin bil'adama.
Duk yadda ruhinsa ke da ƙarfi amma kasa jure kaidin Bairama yayi,a dole ya saduda ya nemi izinin aurenta a daidai wannan lokaci.Ita kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta aminta a nan take tana mai ce masa,"sai dai fa ni Kirista ce,don haka aurenmu zai kasance ne a cikin Coci kuma ban so ka faɗawa kowa kawai ka zo a ɗaura mana auren"
"Babu damuwa yadda kike so haka za a yi" Maheer ya faɗa.
Ta ce"gobe da ƙarfe ɗaya na dare ka zo akwai wata Coci da ke nan bayan gidan Maigari" ta ida furucin tana furzo masa ɗalasiman tsafi wanda ya ida gigita shi ya zauce.
Kamar wasu masoyan gaske haka suka kamo hanya ta yi masa rakiya har ƙofar gidansu,a nan suka tsaya suna hira wacce Maheer yake ji kamar ya mutu tsabar daɗinta.
"Maheer lafiya kake tsaye kai ɗaya kana dariya?" Mahmud ya tambaya wanda ya fito sallar asubah. Maheer ya juyo tare da cewa "ni da amaryata ta gobe ce,ka ganta sunanta Bairama .Sweety wannan abokin karatuna ne,Mahmud"
"Hahaha! Wai hauka ne ka soma ko me? Wace ce kuma Bairama?"
Cike da mamaki Maheer ya dubi Bairama da ke tsaye a gabansa kafin ya ce "ga ta mana,ko dai ba ka yarda cewa gobe ne aurenmu ba? Ko ita ɗin ce ba ta yi maka ba?"
Mahmud wanda a haƙiƙanin gaskiya idonsa bai ganin Bairama sai yake ganin kamar zaucewa ne Maheer yayi,ita kuma a ɓangarenta duk da tana ji tana kuma ganinsa sam ba za ta iya yin wani kataɓus ba ne a kansa saboda yana da alwala da kuma niyya mai kyau ta zuwa masjid.
Maheer zai sake cewa wani abu sai Mahmud yayi atishawa tare da ambaton sunan Allah, kamar ɓacewa wata haka Bairama ta ɓata ɓat daga gabansa a daidai nan kuma MAHEER ya soma controling kansa.
"Mahmud masjid za ka je? Ka jira please na shiga na ɗauro alwala sai mu wuce"
"Ita Bairamar har ta yi sallah kenan?Allahu Akbar!" Mahmud yayi tambayar cike da shaƙiyanci yana wata dariya.
"Kin ga wai..." sauran maganar ce ta maƙalewar Maheer ganin ya juyo a karo na biyu zai yi magana amma babu Bairama a gabansa wacce ita kuma kunnuwanta ne sam ba za su jiri ambaton Allah ba.
"Dariyar me kake yi?" Maheer ya tambaya wanda ya dawo cikin ganiyar hankalinsa. "A'a babu komai ku ci gaba da hirarku "
"Hira kuma?" Ya tambaya. Mahmud bai sake cewa komai ba yayi gaba,yayin da shi ma Maheer ya shiga daga ciki sai da yayi wanka sannan yayi alwala ya wuce masallaci shi ma.Bayan sun gama sallar suka kamo hanyar gida,cikin wani yanayi yake cewa "wai don Allah ko ka lura da wani canji a tattare da ni? Wani zubin sai na ji tamkar ana yi mini magana cikin kwanyata fa"
"Ai na ga alamu don yanzu ma a tsaye na gan ka kana dariya kai ɗaya da na tambaye ka shine ka ce mini ai tare kuke da Bairama kuma aurenta za ka yi"
'Bairama?' ya nanata sunan a zuci kafin a zahiri ya ce "sai kuma na ji kamar na san sunan" sai ya ci gaba da maimaita sunan ko Allah yasa ya tuna sai dai duk yadda yake tunanin mamallakiyar sunan to ta wuce nan. Bayan sun shiga ciki haka ya samu shimfiɗa ya kwanta tare da lumshe ido,kamar a mafarki kuwa ta bayyana a gare shi hoton siffarta tana yi masa murmushi kafin ta matso ta yi masa wata muguwar sumba wacce ta saka shi yin bacci bai shirya ba,nan ɗin ma ba ta sauya zane ba mafarkinta ne ya soma yi ta kai shi can ƙasan ruwa tana ciyar da shi abinci.Wanda kuma duk da yana duniyar mafarki,to kuma ya faru a gaske ya ci abincin mai ɗauke da sihiri wanda dama tana ɗaya daga cikin hanyoyin da miyagu,malaman tsibo ko aljanu suke bi don ƙarfafa sihirin da suka yi wa wani ko kuma don yi masa wani sabon salon tsafin.Sun fi zaɓar sihirin cikin abinci ne saboda ya fi jimawa kafin ya karye,da wannan malamai suke yi mana nuni yana da kyau ka dinga dafa sana-makki ka zuba zuma haɗi da yi masa karatun Alkur'ani duk ma kowacce aya ce ka iya,don magance sihirin cikin ciki.
Haka Bairama ta ciyar da Maheer,bayan ya farka ma sai ya ji sam bai jin yunwa yayin da dai kuma ya sake aukawa cikin kogon mantuwar wane ne shi.Abu guda ya sani Bairama wacce ita kuma ta kasance aljanar ruwa kuma matsafiya.
Ko ido bai wanke ba ya tashi ya nufi Cocin da ta sanar da shi,haka yayi zaman jiranta har dare yayi sannan ta zo cikin wata shigar mai fizgar ruhi. Babu wani alƙali da ya ɗaura musu aure kawai dai ita ce da kanta ta tsara komai ta kuma ƙaddamar cewa sun zama ma'aurata.Kamar raƙumi da akala haka ta ja Maheer zuwa gidan da ta ware domin su rayu cikin bil'adama kafin ta tsafa shi ta yadda za ta iya kai shi ƙarƙashin ruwa . Gidan yayi datti sosai,ga yana ga gara amma idon Maheer sun magance bai ganin kowa sai ita.Duk yadda Bairama ta so ta kusanci Maheer lamari ya cuttura don tamkar yadda ƙirjin soja ke ɗauke da garkuwar tare alburushi to shi ma haka Maheer yake ɗauke da matakan tsaron masu kula da mutumcinsa. Tsawon sati guda tana ciyar da shi gubar tsafi,saura guda kacal da take sa ran da zarar ya ci shi to fa shikenan gangar jikinsa ma ta zama tata.
Ido lumshe ta dinga basa wani lemu da ta haɗa ,bayan ta gama sai ta shiga toilet.Shi kuwa Maheer kamar wanda ya haɗi kunama haka ya shiga fitar da zufa,ga yawun bakinsa sun ƙi tsayawa wajen neman abin da zai tsayar da yawunsa ne ya tuna da goron da tsoho ya basa,cikin ikon Allah ya gansa tare da jefa shi a baki ya dinga taunawa.Kamar ana yi masa ƙarin ruwa haka jijiyoyinsa da suka takure wuri guda suka dinga warwarewa,a daidai lokacin da Bairama ta fito cikin siffarta ta Siren a daidai kuma wannan gaɓar ce Maheer ya tuna da komai da ya faru da shi .
Ko kaɗan bai ji tsoron ganinta a haka ba, sannan bai nuna mata wata alamar tsoro ba ko kuma ya nuna mata ya dawo hayyacinsa ya san duk makircin da take shiryawa.
Kan gadon ta hauro,sai dai hucin saukewar numfashin Maheer ta haifar mata da wani rikitacen zafi har ta so guduwa amma ya damƙo ta yana cewa "please ki zauna kusa da ni sweety"
Wani kallo ta bi sa da shi tana jin tamkar ta ƙurma ihu, Maheer ya lumshe ido a wannan karon wata tsohuwa ce ta ziyarci tunaninsa tana zaune bakin rijiya tana gasa kifi.
"Wane ne ya buɗe makullin da ya rufe ɗayar idonka?" shi ne abin da ta tambaye shi,kafin kuma ta ci gaba da cewa "haƙiƙa kai ɗin gwarzo ne ko a duniyar bil'adama,yin gardama da neman abin da ya fi ƙarfinka yana ɗaya daga cikin alamomin waliyantaka.Ungo wannan" ta yi furicin tana mai miƙo masa da wani ƙwai Maheer ya dai ga ya buɗe hannu ya karɓa amma bai san ko a gaske ne ba. Yana buɗe ido sai ya ga Bairama ba ta kan gado,a hankali ya miƙe ya je ya leƙa toilet can da yake jin motsin ruwa.A kwance ya tarar da ita tana ta faman wasa da ruwa,sai wani juya bindinta na kifi take.
"Sweety!" ya furta cikin wani salon jan hankali don ya ɗauki alƙawarin ba zai taɓa nuna mata wani canji ba shi ma sai ya gasa mata aya a hannu.Idonta ta ɗago ta dube shi a galabaice kafin ta ce "ina wanka fita ina zuwa " ba tare da ya ce komai ba ya fita ya tsaya bakin ƙofa,yana lumshe ido sai kuma ya ci gaba da ganin abin da ke wakana a can cikin toilet ɗin.Bairama ta cire gangar jikinta na Siren ta ɓoye cikin WC kafin ta saka na bil'adama,sai a lokacin ta fito da ta zo kusa da Maheer kuma sam ba ta ji wannan azababen zafin ba.Hira suka yi sosai kafin ta ce za ta je kasuwa ta siyo musu abubuwan buƙata.Ya barta ta tafi bayan fitarta sai ya ɗauko wannan gangar jiki ya sayo petur ya ƙone ta ƙurmus.Ko minti goma ba a yi ba sai ga Bairama ta dawo fuskarta ta yi baƙi ƙirin,gashin kanta duk ya ƙone.Ido cikin ido suke kallo ita da Maheer kafin ta ce "wane ne kai? Me yasa za ka yi mini haka?"
Kai tsaye ya bata amsa da "dalilin da yasa ke ma kika yi mini abin da kika yi shi yasa ni ma na yi.Wane ne ni kuma ke ce nan kika nuna mini ainahin ni ɗin wane ne"
Cikin zafin rai ta ce "yadda ka tarwatsa ni kai ma haka za ka ƙarashe rayuwarka ba tare da ka san daɗin rayuwa ba,har abada ba zan bari ka zauna da mace ba ko ka aure ta sai na kashe ka kuma ka sani ruhina zai ci gaba da gudana a taka gangar jikin ne,kai da yin wata mu'amala da wata mace sai a lahira" tana gama faɗar haka ta wangale baki bakinta wani baƙin abu ya fito ya shiga jikin Maheer yayin da kuma gangar jikinta ta bi iska.