Bakin ruhi complete - Chapter 36
Bakin ruhi complete Chapter 36: Bakin ruhi complete Chapter 36. Maheer ya ji kansa wani iri,amma a haka ya daure ya fito ya kama hanyar gida.Da ya isa babu…
3,233 words
Maheer ya ji kansa wani iri,amma a haka ya daure ya fito ya kama hanyar gida.Da ya isa babu kowa ,wanka ya fara da shi kafin ya tsane jikinsa ya gyara shimfiɗa ya kwanta .Motsi ya soma ji daga ƙasa da sauri ya tashi sai ya ga wannan ƙwan ne dai da tsohuwar nan ta basa,jikinsa har rawa yake yi wajen ɗaukarsa daidai ne abin cikin ƙwan ya faso ya fito.Wani jaririn maciji ne mai kyau sai ƙyalli yake yana juya idonsa,a hankali ya soma fitowa yana hawa jikin Maheer wanda tun lokacin da suka haɗa ido da macijin ya samu wani irin ƙarfin iko wanda ya danne ruhin Bairama ya daina jin motsinta. Tun daga wannan lokaci ya soma jin wata irin izza da taurin kai sun hawa sun zaune a tattare da shi,yayin da wani buri ya ɗarsu a zuciyarsa shi ne na kawar da azzalumai.
Ji yayi sam ba zai iya yin kwancin ba kawai sai ya miƙe ya saka kaya ya fito,abu na farko da ya soma cin karo da shi shine wani mahaukaci yana zaune kan titi sai magana yake yi shi ɗaya yana cewa "ku ma kun samu? Ko dai a ƙara muku miya" da ya tsaya ya ƙare masa kallo sai ya fahimci cewa a idon duniya ne yake mahaukaci amma a baɗini hidima ce yake yi wa azzalumai yana kashe ƴaƴan mutane yana basu.
Maheer ya je ya tsaya a gabansa,mahaukacin ya ɗago yana kallonsa jikinsa na rawa.Cikin ɗaure fuska ya ce "wane ne kai? Kuma waɗannan ruhikan yaran da ke hannunka me za ka yi da su?"
"Da gaske kana ganin abin da idaniya ba ta isa ta gani ba?" cewar mahaukacin . Maheer bai ce komai ba sai "Sahut!" wanda shi kansa bai san ta ya aka yi ya furta hakan ba,macijinsa wanda ke manne a cikin hannunsa ya ziro kai ya sari mahaukacin nan take duk wani dabaibayi da aka yi masa na sihiri ya kwance masa.
Maheer ya ce "yanzu ina jin ka wane ne kai?"
Idonsa na zubar da ƙwalla ya ce "sunana Tareeq,na ɗauki tsawon lokaci ina aiki a matsayin mai yin girki a manyan hotel -hotel,amma shekaru uku da suka gabata na samu wani shararren mai kuɗi ya ɗauke ni aiki.Tun kafin na fara aiki sai da abokaina suka sanar da ni ire-iren gidajen masu kuɗin nan suna da wasu ƙa'idodi wasu sirrikansu,amma sam ni ban ɗauki abin da wani muhimmanci har sai lokacin da na rasa duk wata wata nutsuwa da farin cikin rayuwata.
A hankali lamurrukan ke tafiya,girkin da aka bani yana da wasu ƙa'idoji wasu kwanakin za a ce in girka shi babu gishiri ,wani kuma sai na saka wata hoda ce zan zuba a ciki ban taɓa tambayarsu dalili ba kawai dai aikina nake yi ana biyana.
Bayan wata shidda sai lamurra suka fara canzawa.Wata rana Alhaji sai ya ce na zauna nan na kwana a gidan,aka ware mini wani ɗaki na kwanta.Wuraren ƙarfe biyu na dare sai na soma jin wasu muryoyi ,abin da tunanina ya bani a farko kawai wani shagali ne ake yi kawai sai na fito na ɗan leƙo,wasu mutane na gani sun fi su goma sanye da baƙaƙen kaya su duka sun kewaya akan farantin abincin da ni ne nan na girka shi.Wasu irin ɗalasimai suke karantawa,kafin su dinga zuba abinci kan wata gawar budurwa.Cikin azama na koma inda aka ajiye ni,tun daga wannan rana na zama na musamman wurin Alhaji , sannan umarni kawai yake bani ina bi.Ya kan saka ni girka shinkafa da jinin mutane maimakon na zuba ruwa a tukunya,in zan yi miya haka za a bani haƙoran mutane na zuba a ciki,wani sa'in ma har farfesun kan jarirai nake yi musu.A ranar da na so yin ƙorafi Alhaji sai yayi mini tsawa yana mai cewa "manyan mutane masu power ne kake yi wa girki,in ka yi magana ina mai tabbatar maka farfesunka ne abu na gaba da za a girka su ci a gidan nan" Kalamansa sun tsoratar da ni,amma ba su hana ni sake gwada wata sa'ar ba sai dai kafin na yi wani yunƙuri suka daɗe mini baki ta hanyar cire ciwon da ke addabar yarona shekara da shekaru ya warke garas,sannan suka nemowa da matata aikin yi.Kawai sai na ja bakina na yi shiru na ci gaba da yi musu duk girkin da suke so har aka zo ranar da Alhaji ya sanar da ni cewa ina da zaɓi biyu ko dai na mallaka musu yarona,ko kuma na ɗauki rigar mahaukaci na dinga zuwa gari-gari ina yi musu farautar ruhikan yara ƙanana waɗanda ba su balaga ba.Zaɓi na biyu na ɗauka,haka na dinga jan ra'ayin yaran mutane in za su je makaranta sai na dinga basu kuɗi,wasu kuma chocolat da sauransu,amma da haukana ya bayyana ƙarara sai kawai na dinga amfani da idona wurin cabko ruhikan yara har da manya mutane waɗanda yin addu'ar neman tsarin Allah ba ta dame su ba sai dai su yi sallah su miƙe ba tare da sun roƙi Allah ya kare su daga sharrin duk wani abin cutarwa ba" mahaukaci na kawowa nan yayi shiru,yayin da ran Maheer ya ɓace kawai ya saka macijin ya sare sa wuya nan take mahaukacin ya mutu.
Daidai nan ne kuma tsohuwar nan ta bayyana a gare shi,fuskarta a ɗan haɗe.Ba tare da ta ce wani abu ba ta caka masa wata ƙaya a gefen wuya ta zare wani ƙarfin iko sannan ta ce "kana da zafin rai don haka ba zan bari ka ci gaba da riƙon power hukunci ba zan ajiye ta ne ga matar aurenka.Sunana Yabobo,uwa kuma shugabar duniyar Ruhaniya ta fararen ruhika" tana gama faɗar haka ta ɓace,Maheer ya ja ajiyar zuciya yana kallon yadda ruhikan yaran nan da mahaukaci ya damƙe yadda suke guduwa za su koma ga masu su.
A duniya tun can ya tsani wanda zai salwantar da rayuwar wasu domin shi ya gyara tasa rayuwar,tabbas gwara da Yabobo ta karɓe muƙamin nan don muddin yayi bincike mutum ya basa labarinsa in ya ga yayi mugunta sosai kawai kashe shi zai yi,amma yanzu da bai da wannan ikon na tambaya dole ya ja bakinsa yayi shiru .Direct daga nan asibiti ya nufa ,yana ƙoƙarin bin wata hanya sai ya ga an jawo gadon gawa za a wuce da ita MUTUWARE(MRS SADAUKI) amma abin mamaki gawar magana ce take yi masa..... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
42
"Ka ga ƴan baiwa masu muƙami bibbiyu,ga na ifiritan ruwa ga kuma na cikin iska,zo ka taimaka mini na sake dawo da ruhina a duniyar bil'adama ko da na daƙiƙa biyar ne burina na sha sigari da giya" shi ne abin da gawar ta cewa Maheer,cike da mamaki yayi tsaye yana kallon gadon da ake ɗauke da gawar har aka shige da ita cikin mutuware.
Direct ciki Maheer ya wuce,shugabansu shi ne mutum na farko da ya soma yin tozali da shi.Wannan karon suna haɗa ido ya gaishe da Maheer cikin girmamawa kafin ya ce "ina neman yafiyarka ashe kai ma cikinmu kake kuma kana ma gaba da ni,na yi tunanin cewa kawai ka taka dokar ne don ganin ƙwaƙwaf" Maheer bai ce masa komai ba,sai dai ya fahimci cewa a tsakanin miyagu akwai wani haɗin kai mai girma,da wannan ne yayi amfani ya shiga gari ya dinga binciken duk wani abu da ya shafi ɓoyayyar duniya a haka ne kuma ya samu tasirin furen floris har yake nunawa abokansa su Dr Muhamud da kuma yadda yake juya siddabaru,sai dai bai taɓa sanin ruhin Bairama na cikin gangar jikinsa ba sai a yanzu da ya rikiɗe ya zama maciji.
Shi ke ɗauke da zuciyarsa amma Bairama ce ke juyata,wani irin tunani take saka masa na tsanar mata ciki kuwa har ita Haulen ji yake da a ce zai ganta a yanzu da tabbas zai kashe ta ne. Tsawon lokaci Maheer na cikin siffar maciji kafin ya rikiɗe ya dawo mutum,sai a lokacin ya farga irin muguntar da ya yi wa Ikilima.Shi ne ya ciciɓe ta zuwa asibiti,an ci nasarar ceto ta sai dai fa bakinta ya samu matsala ya jirkice kuma ba zai dawo daidai ba.Tana dawowa hayyacinta ta dinga ƙara da ihun ba za ta zauna da Maheer ba,tuni danginta sun zo su ne masu rarrashinta.
A ɓangaren MAHEER kuwa bayan ya kai Ikilima asibiti sai ya wuce can wajen rijiyar nan,sai dai sama da minti talatin Yabobo ba ta fito ba nan ne ya ida yarda cewa yanzu fa bai da wani ƙarfin iko.Wani takaici ya luluɓe shi har sai da ya ji idonsa sun cika da ƙwalla,babu jimawa kuwa suka ɗiga cikin rijiyar nan take wani haske ya cika wurin kafin kuma fuskar Bairama ta bayyana,ta yi kicin-kicin da rai tana kallonsa shi ma ɗin ita yake kallo kafin ƙyaftawar ido kuma ta ɓace,ya ja tsuki tare da komawa a cikin motarsa yayi mata key sai gida.
Hajiya ta tarbe shi don jin lafiya,ya katse ta da "a kawo mini tea mai zafi" yana gama faɗar haka ya haye sama,ita kuwa Hajiya Lubna ta kira ta ce ta haɗa ta kai masa.Wannan lamari ba ƙaramin daɗi ya yi wa Lubna ba kawai ta shiga kitchen ta haɗa masa,sai da ta kai bakin ƙofarsa kafin ta jefa wani magani a ciki ruwan flask ɗin.Bayan ta nemi izini sai ta shiga sannan ta ajiye trayn tare da cika masa kofi ta basa,Maheer wanda ransa ke ɓace kawai karɓa yayi ya soma sha har sai da ya sha kofi biyu a na uku ne ya soma jin wani yanayi na buƙatar mace. Hannunsa na ɗan rawa ya ajiye kofin tare da lumshe ido yana tunanin Haule,bai taɓa jin kewarta ba irin na yanzu.
Lubna wacce ta fahimci cewa tarkonta ya yi nasara kawai sai ta miƙe ta shige bedroom ɗinsa,don samun wuri har da shiga toilet ta kunna pampo ta cire kayanta ta soma yin wanka tana wani irin murmushi tana jin yau dai burinta zai cika za ta ɗanɗana zumar Maheer sai ta ji abin da Haule ta ji.
Murya ta maƙe tana kwaikwayon irin ta Haulen,an kuwa yi katari Maheer ya shigo bedroom ɗin.Yadda ya ji tana kiran nasa duk sai ragowar hankalinsa ya watse bai san lokacin da ya cire kayansa ba ya shiga toilet ɗin.A tattare da Lubna Haule yake gani wannan yasa ya isa gare ta tare da rungume ta suka ci gaba da yin wankan tare yana romance ɗinta .
Hankalin Lubna yayi ƙololuwar tashi,burinta guda shi ne kawai ya kusance ta .Ido ta lumshe tana tuna ranar da ta soma yin sex ita da Dr David wanda guguwar sonsa ce ta ɗaga ta sama ta kai ta har wurin da yake ta yarda suka mu'amulanci juna.Yanzu kuma ga Maheer namijin da take jarabarsa tun ranar da ta ƙyallara ido ta gansa.
Wani irin abu ne ya ziyarce ta jin abin da rabon da ta ji shi tun shekarun baya da suka wuce,wani irin daɗi ne yake ratsa ta cikin shauƙin da ke fizgarga ne ta kai hannunta a ƙirjin MAHEER da niyyar mayar masa da martani,amma abin da hannuwanta suka taɓo mata ne ya watsar da duk shauƙin da take ciki.
Idonta ne ta soma buɗewa,da zaton ko ƙila hannuwanta ne suka jiye mata ba daidai ba don in ba kuskure ta yi ba ƙirjin mace ne ta ji ta dafa har sun fi nata girma.Tana ware idonta ta yi tozali da fuskar Maheer kuma,ƙirjin nasa ta ƙara taɓawa har yanzun dai ba ta canza zane ba.Tana shirin maida dubanta a can sai kuma idonta ya sauka cikin madubin da ke manne da bango,wata tsaleliyar buduwar ta hango rungume da ita tana yin sex da ita daidai nan igiyar numfashin Lubna ta soma katsewa tana shirin yin ihu Bairama ta danna ta ƙasa tare da rikiɗa ta koma maciji tana shirin shiga bakinta ta ji wani abu mai ƙarfi ya riƙe ta wanda ba komai ba ne sai addu'ar Ummah wacce ke can a gidan tana yi wa ƴarta Lubna addu'ar neman tsari.
Ba don rai ya so ba Bairama ta dawo da ruhinta a nan bedroom inda ta shemar da Maheer kan bed yana bacci.Babu jimawa kuma ya dawo hayyacinsa,sai ya tuna kuma duk abin da ya faru da shi.Daga inda yake yana jin kukan Lubna wacce ke can tana kukan nadamar da ba ta da amfani don kuwa tuni Bairama ta sakar mata ƙwayoyin cuta a al'aurarta.
Ransa ne yayi mugun ɓaci,cikin tsawa ya ce "wallahi ko ki fito ko kuma ni na shiga ɓalla ki" Babu shiri ta mayar da kayanta tare da fitowa a kunyace ta fita,ya bi bayanta da harara kafin ya soma tunanin ta ina zai ga Haule?
Wanka yayi ya kimtsa cikin wasu kayan Adidas masu dogon wando, kasancewar kayan baƙaƙe sai suka fitar da haskensa.Ƙasa ya sauko wanda yayi daidai da soma zubar ruwan sama,Aliya ya gani tana yi wa Hajiya bayanin yadda gasar girkin da suka yi a ranar farko ta kasance yayin da ita kuma take ta jimamin yadda Haule ba ta nan aka soma ita kuma tana kwantar mata da hankali.
A tare duk suka ɗaga kai suka dube shi,kana ganinsa ka san yana cikin damuwa.Aliya kuwa yau dai ta cire shakkarsa da take yi ta kafe shi da ido tana kallonsa tsakiyar idonsa,wanda shi kansa Maheer yayi mamaki sannan kuma ya soma jin kallon nata har tsakiyar ruhinsa.
Ta ɗan taɓe baki kafin ta juya ta kalli Hajiya ta ce "zan tafi can restaurant na gani"
Maheer ya ce "mu je na sauke ki" ta saki wani murmushi daga ɓoye don dama keɓewa take so su yi don tattauna matsalar da ta gani kuma ta tunkaro su.
Lema ta ɗauko suka fito har zuwa motarsa,yau dai a gaba ta zauna bayan yayi nisa sosai a tuƙi sai Aliya ta ce "me ya haɗa ka da Bairama?"
Ya ɗan juyo ya dube ta kafin ya ce "ke komai kin sani"
"Eh ko ka manta cewa ni ba jinsin mutum ce ba?"
"Ta ya zan manta alhalin ƙabilarku ɗaya da abokina Dr Muhamud "
"Duk dai ba wannan ba ka bani amsar tambayata"
"Tun shekarun baya ne lokacin ina tsakiyar karatu"
"Amma me yasa ka kira ta alhalin ba ka shirya son ta ba?"
"Ni ban kira ta ba"
"A'a fa! Kai ne ka kira ta don ruhikan cikin ruwa ba su cika fitowa ba sai in an kira su" nan ne fa MAHEER ya ba Aliya labarin abin da ya faru ita kuma ta jinjina kai kafin ta ce "da buƙatar ka koma can garin ka mayar da ita cikin ahalinta sannan ka bata haƙuri"
"Ni dai duk ba wannan ba,ta wace hanya zan haɗu da H.lat?"
"Hanya ce mai sauƙin bi amma mai cike da ƙalubale,don a dole sai in ta haɗe tunaninku wuri guda kamar yadda ka yi mata a farko to a yanzu ita ce ke da wannan ƙarfin ikon"
"Bayan haka fa?"
"Za mu je farautar BAƘIN RUHI da kanmu ba tare da mun bari ya sake dawowa cikin doron duniyar bil'adama ba,don maganar da nake yi maka tuni masu niyyar maido shi suna kan hanyar zuwa Japan inda a can ne dajin sirri yake"
"Ke yanzu ba za ki iya duba mana inda Queen take ba?"
"Ba ta cikin gidansu dai,sannan tun da ta rogaza baƙin ruhi wasu ƙarfin ikona suka gudu kamar sauran masu riƙe da shi,amma a ƙiyasina Dr Muhamud ne kawai za mu iya samu da nasa tun da bai taɓa yin aiki da shi ba"
"Na fahimta! Ita kuma wannan da ruhinta ke cikin gangar jikina?"
Aliya ta ce "ita tana bayyana ne a duk lokacin da wata mace ke ƙoƙarin zuwa gare ka da niyyar soyayya kenan ka ga yana da kyau ka sanar da ƴan matanka su nisance ka in ba so suke su rasa rayuwarsu ba,yau saura ƙiris ta sake sace gangar jiki ta dawo cikin wannan duniyar,don da a ce ta yi nasarar shiga bakin Lubna da tabbas ita ce BAƘIN RUHI ta biyu don za ta yi ɓarna sosai fiye da ma shi"
A cikin wannan ruwan saman da ke zuba kamar da bakin ƙwarya Maheer ya tattara abokansa waɗanda suka taɓa fuskantar barazanar da kuma shiga komar BAƘIN RUHI.
Aliya ce ta yi musu bayanin komai,Lubna wacce ita shaida ce ta fi nurse Fatee fahimtar gargaɗin da Aliyar ke yi na su cire MAHEER daga ransu sannan za su yi aiki ne domin ceton al'umma. Bayan sun gama tsara yadda komai zai tafi ne Aliya ta matsa kusa da Dr Muhamud ta shafi tafin hannunsa nan take wani haske ya bayyana duk sai suka matso suna kallon dunƙulallen hasken wanda ya fitar da shap ɗin lula.
Hankalin kowa na kan hasken in aka cire shi mamallakin ƙarfin ikon da ya tsurawa Aliya ido yana kallo.A hankali ta ɗaga kai ta dube shi,sai ya sakar mata murmushi yayin da shi kuma MAHEER yayi gyaran murya sai duk suka nutsu suka mayar da hankalinsu sai a lokacin kuma Aliya ta soma yin wani abu tana bincike har ta samu wata alama mai nuni da inda Haule take.
"Tana cikin wata makaranta mai bayar da horo na musamman akan matsafi da tsafi,an shimfiɗa matakan tsaro sosai sai dai duk da haka shigarta ba zai yi mana wuya ba duba da duk muna da tabo ƙarfin iko,wanda zai kasa shiga a cikinmu shi ne Dr Umar don bai da komai a ruhinsa "
Dr Umar wanda ya kafe kan cewa sai ya yi wa nurse Fatee rakiya kallon Aliya ya yi kafin ya ce"ki yi wata dubarar dai don ba zan bar wacce nake so ta yi tafiyar nan ita ɗaya ba"
Shiru ta yi na ɗan wani lokaci kafin ta ce "ok babu damuwa! Oga MAHEER ka fitar da rana da kuma lokacin da za mu tafi"
Maheer wanda yake a matse ya ga sanyin idaniyarsa sai cewa yayi "wannan lokaci shi ne daidai da mu tafi kin ga zubar ruwan sama alama ce ta nasara"
Aliya ta jinjina kai kafin ta ce "yanzu yadda za mu yi kowanne daga cikinmu zai ɗora yatsansa manuniya kan hasken nan sai ya lumshe ido yayin da Dr Muhamud zai yi mana jagora" ta ƙarashe faɗa tana ɗaga kai ta kalle shi,wani irin kallo suke jefowa junansu kafin kuma dukkansu su yi yadda ta ce Dr Muhamud yayi wani furuci sai ga su a zube bakin wata mahaukaciyar makaranta wacce aka gina da ƙasusuwan namun daji.
★HAULE Mentor na kiranmu sai yayi mana jagora can ajin darasi,a can ne na samu wani ƙarin haske dangane da baƙin ruhi da kuma duk abin da ya shafi duniyar Ruhaniya. Muna cikin yin darasin ne danjoji masu kula da matakan tsaro suka fara fitar da alamar jini,kusan duk a tare muka fita zuwa waje ina jin ana cewa shirya karnukan farauta a isa bakin ƙofa.
Babu jimawa kuwa aka fito da karnukan baƙaƙe ne ƙirin waɗanda kana gani ka san jinnu ne a siffar kare. Nadia ta yi tsaye kusa da ni tana mai cewa "ko wane mai ganganci ne ya hauro makarantar nan ba tare da neman izini ba?"