Bakin ruhi complete - Chapter 37
Bakin ruhi complete Chapter 37: Bakin ruhi complete Chapter 37. "Kenan kashe shi za a yi?" na yi tambayar sai dai kafin ta bani amsar ƙofar makarantar ta…
3,328 words
"Kenan kashe shi za a yi?" na yi tambayar sai dai kafin ta bani amsar ƙofar makarantar ta buɗe,idona bai sauka ko ina ba sai cikin na MAHEER wanda shi ne a gaba tawagarsa na bayansa. Wani irin burki karnukan suka ja a daidai lokacin da suka kwasa a guje suka tunkari Maheer ɗin .Mentor da sauran malaman makaranta su ne kuma suka dinga kwantar wa da ɗalibai hankali suna cewa kowa ya koma ɗakinsa baƙi ne na gida matsalar dai ba su sanar za su zo ba. Nadia ta kama hannuna ta ce "mu je" ban musa ba na take mata baya ina waiwayen Maheer wanda tuni ya soma shigowa maƙarabansa na take masa baya,har zan tsaya sai kuma idona ya sauka kan aminiyata.Da ido kuma Aliyar ta yi mini alama da kar na nuna na san su kawai na bi Nadia mu tafi ɗin,ba don na so ba haka na bi bayanta muka muka koma can ɗakinmu yayin da kuma zuciya da ruhina ke tsumayen abin ƙauna....
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
43
A yayin da kowa ya samu damar shigowa cikin makarantar shi Dr Umar kasa shiga yayi saboda babu ɗigon komai a cikin jininsa kamar yadda Aliya ya faɗa tun farko . Mentor ya dube su ya ce "shi kuma wannan?"
"Abokinmu ne,yana son zama kamar mu amma ba mu da lokaci isasshe ballantana mu ƙaddamar da shi amma please ka basa izinin shigowa na san da sannu za ka yi alfahari da shi" Maheer ne yayi maganar wanda idonsa suka soma sauya kala zuwa na Siren sakamakon tururin son Haule da ya yo masa sama ita ma ta dinga jefo masa kallon so.
Shi Mentor bai san taƙamaimai abin da ke faruwa ga MAHEER ba,yayi tunanin ma aiki ne yake yi da ruhikan ruwa wannan yasa bai wani damu da bincike ba ya kwance matakan tsaron da suka hana Dr Umar shigowa ɗin.
Shi ne yayi musu jagora zuwa wani ɓangare na cikin makarantar kafin ya sa a kawo musu cofee sai ƙamshi yake ,babu wanda ya damu da shi don hankalinsu ba kwance yake ba. Aliya ce wannan karon ta ɗau magana tana mai cewa "sunana Evaliya ina ɗaya daga cikin waɗanda suka rayu a tsawon ƙarni uku da suka wuce,na yi zamani da manya kuma shararrun matsana na duniya.Na san sirrikan ruhaniya da kuma yadda lamurran can ke gudana,amma har zuwa yanzu kana da ilimin da ni ban da shi ya mai girman Mentor da son samu ne ina son a koyar da ni yadda ake yin baƙin tsafi da kuma wargaza shi " yadda ta yi magana cikin taushin murya haɗi da sadda kai ƙasa yasa ta saye zuciyar Mentor,sai dai duk da haka bai sa shi yayi saurin bada kai bori ya hau ba sai da yayi mata tambayoyi ita kuma ta dinga basa amsa sannan ya yarda da zancenta.
Can kuma ya dubi Dr Muhamud ya ce "da alamu kuma wannan ɗin jinsinku ɗaya kuma kamar kuna son junanku ba?"
Duk shiru suka yi , Mentor ya ce "me zai hana a ɗaura muku aure ne kamar tafiyar taku za ta fi tafiya daidai" ya ida maganar cikin salon barkwanci yayin da kuma su Maheer suka soma ƴar kallon-kallon.
Mentor ya saki wani murmushi kafin ya je ya buɗe wani wuri ya ciro wata ƙatuwar kalanda ya buɗe ta tare da ɗora ta kan wani table.Zanen doddani ne iri-iri tun na ƙarnin farko zuwa yanzu,ba tare da sun tambaye shi ba ya ci gaba da cewa "tun kafin ku zo nan na san da akwai ranar da za ku zo,na yi karatu mai zurfi da bincike akan abin da kuka sa gaba sai dai har zuwa yanzu ban dace ba ban cika burina na yin gamdakatar da BAƘIN RUHI ba.Ban damu ya kashe ni ba,burina dai na gansa a fili ba wai iya hoto ba"
"Meke haɗinmu da baƙin ruhi kuma Mentor?" Lubna ta faɗa don a tunaninta rame ne yake son yi musu . Ya dube ta kafin ya ce "wannan ɗakin da muke ciki ya kasance keɓaɓen wuri mai bayyanar mini da gaskiyar duk wani baƙo da za mu yi don haka bari wani zancen ɓoye gaskiya"
Kusan lokaci guda suka ja numfashi kafin MAHEER ya ce " a binciken da ka yi me ka samu matsayin result dangane da fafatawar da tawagar bil'adama da kuma baƙin ruhi ta kasance?"
"Babu gamsashiyar amsa,don wani binciken ya nuna baƙin ruhi zai ƙara wanzuwa a doron duniya a karo na biyu a kuma cikin gangar jikin wanda ya fara cakarsa da wuƙar sirri..." MAHEER yayi saurin katse da "kana nufin a jikin Queen ?"
Aliya ta ce "ka barsa mana yayi mana bayani"
Mentor ya ci gaba da cewa "wani binciken kuma ya nuna zai dawo a duniya amma zai dinga shawagi cikin iska saboda rashin wanda zai yi dakonsa,yayin da kuma wani binciken ya fitar cewa ba zai samu damar shigowa ba saboda hanyar da jaruman mutane za su toshe kwata-kwata " a daidai wannan gaɓar ma sai da suka sake kallon juna kowanne na fatan Allah sa result ɗin ƙarshen ita ce wacce za su samu ɗin.
A nan ya bar su ya kama gabansa bayan ya basu wasu littattafai masu magana akan doddani har da ma mutanen farko kafin zuwan canjin yanayi.
★HAULE
Da na je can ɗaki sam kasa nutsuwa na yi,burina bai wuce na ji ni a ƙirjin MAHEER ba.Kasa jura na yi ta yadda hatta Nadia sai da ta gane ina cikin damuwa.
"Ya dai? Ya na ga duk kin tashi hankalinki daga zuwan baƙin nan,ko dai akwai wanda kika sani?" ta tambaye ni.
Na girgiza kai na ce "a'a kawai ban jin daɗin jikina ne amma ban san kowa ba"
"Hahaha! Wai me kike ɓoye mini ne? Ko dai akwai mijinki a cikinsu?"
Ido na tsura mata na kasa bata amsar tambayarta,sai da ta sake cewa "ki faɗa mini mana kika sani da akwai taimakon da zan yi miki?"
Na ja numfashi kafin na ce "eh wannan na daga gaba shi ne mijina"
"Awooo! Handsome ɗin nan? Yana da kyau sosai gaskiya kin yi dacen miji.Amma me yasa ba ki je wurinsa ba?"
"Ina tsoron Mentor ne,kina ga ba zai iya yi masa illa ba in ya gano cewa ya zo ya tafi da ni ne?"
"A'a babu abin da zai yi masa ai na ga yana da ƙarfin iko da kuma izza "
"A'a bai da wata power a yanzu ni na sani"
Nadia ta ce "ki bari har dare yayi sosai zan kai ki har ɗakin da ake sauke baƙi sai ku gana da mijinki"
Na saki wani murmushin jin daɗi kafin na ce "na gode sosai Nadia bayan Aliya ke ce wacce kika nuna mini ƙauna da kulawa"
Ta mayar mini da martanin murmushin kafin ta ce "ina fatan ke ma za ki mayar mini da alkhairi " Na kamo hannunta kafin na ce "kar ki damu zan kasance mai kirki fiye da yadda kike tunani " haka muka yi ta zaman jiran dare har lokaci yayi da za mu tafi.
Kamar wasu ɓarayi haka muka fito,Nadia na gaba ina take mata baya.Da powerta ta yi amfani har ta gano wane ne ɗakin Maheer a cikin jerin ɗakunan baccin,tana shirin buɗe mini ƙofa muryar Aliya ta katse mana hanzari.
"Me kike shirin aikatawa? Wace ce ke da za ki yi mata jagora?" ta yi furicin tare da cire hannuna da ke cikin na Nadia. Cike da masifa ita kuma Nadiar ta ce "ke kuma a su wa ɗan wake a hotel? To ita ɗin ƙawata ce" ta ida furucin ita kuma tana mai kamo hannuna nan ɗin ma Aliya ƙara fizge shi ta yi tana kallona.
Ni kuma banda murmushi babu abin da nake yi,wato Aliya na kishin ƙawance ne ganin na samu wata bayan ita.Ban ce komai ba sai da na ga suna shirin yin faɗa,"Aliya don Allah ki yi haƙuri zan yi miki bayanin wace ce ita ke kuma Nadia ki yi shiru Please "
Cike da jin haushi ta ce "ni ban damu da sanin wace ce ita ba,kawai ta rabu da ke ta je ta kama gabanta ina ce dai ni ce ke baki shawara akan komai da ya dace to ban yarda ki je wurin Oga Maheer ba ko za ku haɗu ba yau ba"
Nadia ta yi wata irin dariya kafin ta ce "to Mama yadda kika ce ai haka za a yi? Kina tunanin har kina da wani ƙarfin iko da ban mallake shi ba?" sai kawai ta furzo da wata wuta don ƙona Aliya amma na yi saurin tarewa sai dai kafin ni ma ta sauka jikina Maheer ya fito yana dakatar da wutar ta hanyar furzo ruwa nasa ɓangaren.
Aliya ta saki murmushi kafin ta ce "hakan shi ne daidai,Oga MAHEER ya zo gare ki ba wai ke ki je ba ga shi sannu a hankali zai kuma samun wani ƙarfin ikon ya kuma juya ruhin Bairama"
Haka-haka nake jin kalaman Aliya sakamakon jirgin so da ya zo ya sure ni,kallon juna muke ni da Maheer kamar yau ne muka saba ganin juna.Nadia ta ja tsuki ta yi tafiyarta,Aliya ta ce "a je dai can a ƙarata ba mu da buƙatar ƙawancenki"
Na saki murmushi mai sauti ina ɗan satar kallon Aliya ita kuma da sauri ta kawar da kai bayan ta yi mini alama da ido. Na sunne kai ina wasa da yatsun hannuna,ya zo dab da ni tare da jawo ni ya rungume ƙam a ƙirjinsa.A tare muka ja ajiyar zuciya yayin da Aliya kuma ta yi wani siddabaru wani abu mai kamar ginin ƙanƙara ya zagaye mu har da fitar da ɗaki .Kamar mai jira haka Maheer ya lalubo bakina ya soma yi mini wata irin sumba,bayansa na zagaye da dukkan hannuwana ina jan numfashi mun kwashi sama da minti goma yana abu ɗaya kafin ya janye bakinsa ya tsure ni da idonsa masu fallasa sirrin zuciyarsa.Duk yadda na so na tsere daga wannan kallon mai kashe jiki da saukar da kasala kasawa na yi,murya can ƙasan maƙoshi ya furta "shi ne kika tafi kika bar ni ?"
Ban ce komai ba sai ƙirjinsa da nake ɗan dannawa,ya ja ajiyar zuciya kafin ya ci gaba da cewa "saura ƙiris na mutu fa"
Na ce "ai tare za mu mutu"
"Zan fi kowa murnar haka"yayi furicin tare da sakar mayar da bakinsa kan nawa, wannan karon yana mai raba ni da kayan jikina.Duk yadda na yi zaton zan kasance da Maheer mu mori juna abin ya zarce nan,wata irin nutsuwa muka samu kai kace muna cikin ɗakin aurenmu ne sam ba mu yi la'akari da inda muke ba.Sai bayan komai ya lafa ne bangon ya baje,duk yadda na so na koma can ɗakinmu amma MAHEER ya hana ni ya ja ni zuwa ɗakinsa bayan mun tsabtace jikinmu muka kwanta ,bacci na yi wanda rabon da na ji daɗinsa har na manta.
Sai wuraren asubah muka farka,na ɗan ɗago kaina ina kallonsa ba tare da na tashi daga kan ƙirjinsa ba.Gashina ya soma shafawa kafin ya ce "good morning " ban amsa ba sai sake mayar da kaina na yi na lafe ina lumshe ido haɗi da sauke numfashi ina jin wani farin ciki.Kamar dai rayuwar mafarki haka nake jin lamarina da Alhaji Maheer .
A nan ɗaki muka yi sallah,na shagwaɓe masa ina yi masa kukan yunwa can cikin kunnena yayi mini raɗa na yi masa dukan wasa kafin na miƙe zan fita muka yi kiciɓis da Mentor shi kuma zai shigo .Da sauri na ja baya cike da tsoro,yayin da shi kuma MAHEER ya taso ya zo ya tsaya ba tare da wani jinkiri ba ya ce "ita ɗin matata ce kuma..." Mentor yayi saurin katse shi yan mai cewa "ni ba wannan ba ne a gabana,na zubar da duk wasu abubuwana zan fuskanci burina na son ganin baƙin ruhi ke ma daga yau kin zama free/libre za ki iya zuwa duk inda kike so"
Wani irin numfashi na ja,cike da mamaki na ce "amma Mentor ta ya aka yi ka canza ɓangare?"
Wani murmushi ya yi kafin ya ce "Haule tun ina ɗan yaro nake ɗauke da wata baiwa irin ta gane-gane,abin da ido bai gani to ni ras nake ganinsa.Duk wasu matsafa da Mayu na garinmu na san su,kuma na san lokacin da suke shirya makircinsu da kuma yadda suke yi,abin mamaki a ciki kuma ban taɓa jin tsoronsu ba.A lokacin ma wasu manyan mutane irin masu shekaru dayawa kallon yara nake yi musu duba da yadda su sam ba su san abin da na sani ba.Sannan tun ina ɗan ƙaramina na sha ganin ruhika da dama waɗanda aka ɗaure ta hanyar asiri ko tsafi haka nake zaɓar wasu daga ciki na warware musu wannan dabaibayi,haka kuma in Mayu suka yi farautar kurwa haka zan je na ƙwace kuma babu yadda suka iya da ni saboda suna jin tsorona.Duk wani mugu ya tsane ni saboda ina aikin alkhairi,daga ƙarshe kuma sai mutane suka canza mini aƙida ta hanyar yi mini ƙazafi cewa ai ni ma matsafi ne maye ne kuma da wannan ne na soma shiga lungu da saƙo wurin neman ilimin duniyar Ruhaniya .A cikin karatutukan da na samu ne na ji labarin BAƘIN RUHI da yadda kuma yake da ƙarfin iko fiye da kowa,burina guda na gansa na yi masa tambayoyi ko da kuwa shi ne zai yi silar ajalina"
Muka kalli juna ni da MAHEER,ya ci gaba da cewa "ku fito mu je ba mu da sauran lokaci " shi ne yayi mana jagora zuwa wani ɗakin cin abinci,kowa tuni ya fito har da Nadia wacce suke gasar hararen juna ita da Aliya.Wuri muka samu muka zauna,Nadia ce ta zubawa kowa gurasa bayan mun ci sai kuma aka raba mana gorar ruwa da wani abun guzuri.
Aliya kusan ita ce wacce ta fi kowa sanin abin da ya shafi duniyar Ruhaniya,duba da yadda ta kwashi tsawon shekaru a duniya wannan yasa ita ce ta yi mana plan da kuma tsara yadda tafiyar za ta kasance kafin kuma su haɗa ƙarfi da ƙarfe ita da Dr Muhamud su fitar mana da ƙofar da za mu dosa don isa can dajin sirri.
Hasken na bayyana a gare mu duk sai ya yi mana dabaibayi kafin kuma ya ɓalla mu can.Dirarmu ke da wuya Mentor ya dubi sawun takun takalmi kafin ya ce "da dukkan alamu ba mu ɗaya ne muka tsara plan ɗin zuwa nan ba,akwai masu son fiddo baƙin ruhi ko ma ta wace hanya ce kuma na fi zargin mahaifinki ne da yayyunsa Hamza"
Wani irin takaici ne ya rufe ni,ina shirin yin magana hancina ya shaƙo min ƙamshin turaren Yaya Aliyu.Tabbas duk yadda aka yi yana tare da iyayenmu maza,hankalina sai ya ƙara tashi don muddin suka ci nasarar dawo da baƙin sheɗanin ruhin nan to babu makawa cikin su biyu sai na rasa ɗaya,ko dai Abbana ko kuma shi Yaya Aliyun.
"Kowa ya nutsu ya dubi girman jihadin da zai yi,ku kore tsoro daga cikin zuciyoyinku don shi ne rauni na farko da zai sa mutum ya baƙunci lahira bai shirya ba.Sannan mu zama tsintsiya maɗaurinta guda,kar mu bari a raba kawunanmu don na san dole sai an samu waɗanda za su yi ƙoƙarin juya mana baya ko kuma ƙila ba da zuciya guda ma mutum ya zo nan ɗin ba " Aliya na gama rufe bakinta Nadia ta ɗau magana cikin zafin rai "eh ɗin ba da zuciya guda na zo nan ɗin ba,amma ai dai ban taɓa ɓoye sirrina ga wacce ta yarda da ni ba ke kuwa fa? Ina ce kin ɓoye mata abin da ya luluɓe mutuwar Dr David" nan fa rikici ya ɓarke a tsakaninsu duk yadda muka so mu raba su abu ya cuttura,sai wata hargowa ce mai kamar da ta dabbobin daji ta sa suka tsaya cak Aliya ta waro ido kafin ta yi magana can ƙasan maƙoshi "hucin baƙin ruhi ku yi shiru" ba ta ida rufe bakinta ba dajin ya ɗauki wani irin yanayi yana tayar da ƙura tamkar an koro awaki,ga wasu irin baƙaƙen gizazai da suka soma yin gudu suna haɗuwa daidai saitin inda muke a tsaye cirko-cirko kamar kajin da ke jiran a watsa musu gero,kafin ƙyaftawar ido dajin ya koma baƙi ƙirin ko tafin hannunka ba ka iya gani a cikin wannan tashin hankali ne na ji wani hannu ya janyo ni,na ja ajiyar zuciya don ko ido a rufe zan iya gane damshin tafukan Maheer.Cikin ƙirjinsa ya manna ni a daidai sa'ilin kuma aka soma gagaɓa wata dariya kafin wani haske mai ƙuna ya fasa sararin samaniya siffar BAƘIN RUHI ta bayyana....
[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
44