Bakin ruhi complete - Chapter 41
Bakin ruhi complete Chapter 41: Bakin ruhi complete Chapter 41. Sai da dare yayi sosai sannan MAHEER ya shigo shi da Dr Muhamud,muka yi musu sallama ya kai…
1,397 words
Sai da dare yayi sosai sannan MAHEER ya shigo shi da Dr Muhamud,muka yi musu sallama ya kai ni can babban gida saboda ƙin yarda da na yi na bi bayansa haka muka rabu yana fushi da ni.
Da na shiga cikin gida sosai aka yi ta mini faɗan dalilin da yasa na fita ba a sani ba,shiru kawai na yi na shige ɗaki.Wanka na yi na canza kaya kafin na zauna gefen Hassana wacce ta yi uban tagumi,na yi ƴar dariya don na san abin da take zullumi. Na ce "dalla Malama ki saki ranki zo mu yi hirarmu da muka saba yi lokacin da muna gida" Ta yi ɗan murmushi kafin ta ce "jan ruwa a rijiya yana ɗaya daga cikin abin da ke janyo hirarmu Haule ko kin tuna?" Na ce "ƙwaran gaske ta ya zan manta da abin da shi ne mabuɗin da ya bankaɗe duk wani sirrin gidanmu " ta ja ajiyar zuciya ta ce "Allah dai ya jiƙan ƴan uwanmu" "Amen! Gobe za a fara yi miki gyaran jiki,ƙila rana ɗaya za mu tare ni da ke" Ta ce "na ji an ce ƙawarki ce ita uwar gidan,kina ga ba ta da matsala?" "Babu ruwanta ai,kar ki wani damu" haka muka ci gaba da yin hira har bacci ya ɗauke mu.
A ɓangaren amare kuwa cikin nutsuwa Aliyu da Lubna suka gudanar da abin da suka ta ƙoƙarin aikatawa ta hanyar haramun sai ga shi yanzu za su yi shi cikin lada.Duk da babu wata soyayya a tsakaninsu amma akwai fahimtar juna,sannan kowa ya san halin kowa.Ɓangaren Dr Umar kuwa duk da ya san nurse Fatee ta yi yayin son abokinsa hakan bai sa ya rage abu ɗaya da ya yi mata tanadi ba na dangane da rayuwar aurensu, Sosai ya taka rawar gani ya goge mata harda.Su kuwa a ɓangaren su Aliya tamkar wasu romio da julliet haka suka sha romon soyayyarsu,suna gama zama abu ɗaya sai suka narke suka zama wani haske tare da tashi sama suka koma duniyarsu.
★BAYAN WATA ƊAYA
Motoci ne birjit suka zo ɗaukata,tamkar yau ne farkon zuwana wurin mijina haka na sha kuka ina riƙe Innarmu amma haka aka cire ni aka fitar da ni,kusan a tare aka ɗauke mu ni da Hassana wacce ita ma take nata kukan. Na yi tunanin gidan Hajiya ne za a kai ni,sai bayan kowa ya watse ne na lura sabon gida ne danƙarere,babu jimawa MAHEER ya shigo cak yayi tsaye muna ƴar kallon-kallon kafin yayi wani murmushi da yasa gabana bada wani irin rasss na kuma haɗiye yawun tsoronsa.
"Ƴammatana!" ya furta can ƙasan maƙoshi lokacin da ya iso gare ni ya rungume ni,ban iya cewa komai ba sai numfashi da na ja."Mu je mu yi sallah" ya furta tare da ja na muka shiga toilet muka ɗauro alwala,bayan mun gabatar da sallah muka ci muka sha muka yi wanka tare da nufar turakarsa,inda a can ne muka buɗe wani sabon shafin sabuwar rayuwa wacce ke ɗauke da sanyin kwanciyar hankali,babu motsin BAƘIN RUHI babu wata damuwa in aka cire ta kewar Aliya da nake ji kowacce safiya a kuma kowanne lokaci.Ina ji kuma har abada ba zan taɓa cire wannan kewar a raina ba saboda Aliya ta taka rawar gani wurin kai motar nasarata ga ci,so nake yi mata na jini sam ba ta da banbanci ita da anty Aliya.
Wannan kewa tata ta ci gaba da yin gini a cikin birnin zuciyata har na tsawon shekaru biyu da shuɗewarta,sai a yau na samu sauƙin mikin da rashinta ya haifar mini da na samu na haifo mata takwara.Sai bayan shekaru biyu da tarewata a gidan MAHEER kawai Allah ya bani kyautar haihuwa alhalin kaf sa'inin aurena sun haihu dukkansu,Hassana, Lubna da kuma nurse Fatee kowacce da yaronta watanni ne kawai a tsakaninsu .A kullum in na tuna ni kaɗai ce ban haihu ba sai na shiga damuwa,amma da na mayar da al'amarina wurin Allah na yarda shi ne mai yi sai ga shi a safiyar yau na sauka.
"Congratulation an samu little Aliya" shi ne abin da MAHEER ya faɗa yana ɗora mini kyakkyawar babyn mai kama da ni a kan ƙirjina,na lumshe ido ina jin sanyi a raina. Na sumbaci goshinta kafin a ɗauke ta,aka kimtsa ni tare da kai ni ɗakin hutu inda dangina ke zaman jiran fitowata don tuni an kai musu Baby.
Lubna da Hassana an sha ɗinki atamfa iri ɗaya kai kace wasu ƴan biyu,sam ba su yin wannan mugun kishi.Gefe guda kuma nurse Fatee ce ke ta ƙoƙarin ganin ta nuna mini yadda zan shayar da baby.Duk barka aka shiga yi mini ina ta yin murmushi dai,na karɓi baby kenan zan soma shayar da ita na ji wani irin yanayi ya ratsa ɗakin.A hankali na ɗaga kaina na dubi jikin window,inuwar Aliya na gani a tsaye tana sakar mini murmushi kafin ta matso ta kama hannun babyn ta saka mata wani awarwaro mai masifar kyau.Da sauri na lumshe ido jin amon muryata can cikin dodon kunnena "congratulation Ummu Aliya ! Ƙanwar Aliya ! Aminiyar Aliya ! " ko da nake buɗe idona kuma komai ya dawo normal,amma awarwaron na nan dai a hannun baby. Abin da na lura dai shi ne har aka sallame mu daga asibiti babu wanda ya lura da shi,muna tafe cikin mota mun kawo wurin bada hannu wata almajira ta zo tana yin bara.Da sauri na zunguri Lubna wacce ke kusana na ce "wannan ba ƙawarki ba ce Zuly?"
Ba ta iya bani amsa ba sai hawaye da suka zubo kan kumatunta,haka motarmu ta wuce Lubna na waiwayen Zuly.Can ta ce "alhakin mutanen da ta cutar ne yake bibiyarta kamar yadda yake gasawa Momyn nurse Fatee aya a hannu,kowa yayi tagari don kansa"
Ko da muka isa gida na tarar da anty Bahijja ta zage dantse tana yi mini gyaran gida ita da masu yi mini aiki.Sosai na ji daɗin ganinta saboda a kaf cikin waɗanda BAƘIN RUHI ya fesawa gubar azaba ita ɗaya ce har yanzu muke zumunci da ita wasu kuwa tun ranar da na yi musu magani ba mu sake haɗuwa ba.Ba a yi girki ba,daga sabuwar restaurant ɗin gwamna ya mallakawa Hajiya matsayin goron nasara aka kawo mana abinci mai rai da lafiya,wanda aka rage kuma aka yi kyauta da shi.
A ranar sunan little Aliya taro ne aka yi na ban mamaki,wuraren ƙarfe biyun rana duk dangi da abokan arziki sun haɗu a wannan lokacin ne kuma wasu bushe-bushen algaita suka karaɗe gidan ba tare da an san daga ina suke fitowa ba kowa sai mamaki yake yi yayin da ni kuma na ƙurawa fuskar baby ido wacce take rikiɗe mini kamar ta aminiyata ga kuma awarwaronta sai haske yake fitarwa ,ban san me hakan ke nufi ba amma ina fatan Allah sa awarwaron hannun nan shi ne zai haɗe ruhin babyn da na Aliya ba a gaba kuma su haifar da wani sabon al'amari.
Ina ƙoƙarin cire mata shi MAHEER ya shigo ɗakin wanda babu kowa a ciki sai ni,fuskarsa cike da tsantsar farin ciki ya ɗauki babyn tare da kamo hannuna ya ja ni can bakin window ya shiga nuna mini taurari abin da ba a taɓa gani ba wai tauraro da rana tsaka.
"Babynmu ƴar baiwa ce ki yi murna da hakan,ki godewa Allah da ya baki aminiya irin Aliya don wannan gatan duk ita ce ta yi wa ƴarmu shi " shi ne abin da MAHEER ya furta,jin furucinsa yasa na ji na samu nutsuwar ruhi sai na kama hannun baby na kuma jingina ga kafaɗarsa muka ci gaba da kallon taurarin zukatanmu cike da annushuwa......
ALHAMDULLAH !!!
A nan labarin BAƘIN RUHI ya zo ƙarshe,in da akwai abin da wani yake ganin ya dace ace an rubuta sai ya yi wa kansa hasashe kamar yadda in kun lura buɗaɗen ƙarshe ne labarin ya zo da shi. Waɗanda suka biya kuɗi don bibiyar labarin nan ina matuƙar godiya da nuna soyayyarku,ƴan bati kuma masu niyya su sauke haƙi in kuma kun ƙi sai ku yi ta dakon haƙin nawa matsalarku ce.
My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ Chamsiya Laouali Rabo