Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 40

Bakin ruhi complete - Chapter 40

Bakin ruhi complete Chapter 40: Bakin ruhi complete Chapter 40. "Babu komai! Bari na tsane miki gashin da kyau sai ki yi wanka" ta faɗa tare da soma yi…

3,373 words

"Babu komai! Bari na tsane miki gashin da kyau sai ki yi wanka" ta faɗa tare da soma yi mini wasu manyan kitso guda biyu tana gamawa ta fice,ina kallonta yadda take sharar ƙwalla .

Shiru na yi ina tunanin wane ne tsohon ruhina? Ban sani ba,don in ba don Maitama ya shaida mini ba sam ban san ma ruhi biyu ne da ni ba.Sai da na yi wanka mai kyau kafin na fito,na tsane jikina na saka wata rigar bacci mai santsi sai na yi zaune kan kujera.Babu jimawa Aliya ta sake shigowa ta kawo mini Apple da madara ,ta tsiyayaini a kofi kafin kuma ta zuba wani magani fuskarta dai cike da takaicin nan da ban san na mine ne ba kamar dai na wacce aka sanarwa da ranar mutuwarta.

"Aliya wai meke damunki?" na tambaye ta. "Gobe ne ake yin gasar abinci zagayen ƙarshe,ki kwanta ki huta don ina so mu yi komai a tare" ta faɗa maimakon ta bani amsa. Ina shirin yin magana kuma sai MAHEER ya shigo,da sauri ta fice bayan sun gaisa shi kuma ya zo ya zauna kusa da ni.

"Mene ne nan?" ya faɗa yana kallon madarar da Aliya ta zuba mini ,na ce "madara ce mana" kawai sai ya ɗauka ya soma sha.

Ni kuma na yi shiru na tsura masa ido kawai ina tunanin da ace babu shi da ban san abin da zai faru da ni ba."Ba ki tambaye ni ta ya aka yi na zaɓi na mutu da BAƘIN RUHI ba" MAHEER ya faɗa. Ban ce komai ba sai hannuna da na sarkaye a nasa ina shafar sajensa da ya kwanta luf gwanin sha'awa,ya ci gaba da cewa "a yayin da kika kashe Kawu Hamza sai baƙin ruhi yayi tsalle ya diro nan gidan da niyyar ya shige ki kamar yadda alƙalamin ƙaddarar da suka yi rubu da shi ya bayyana cewa ke ce za ki gaji Kaka Nalado,amma sai na tari aradu ba gammo na ce ya shige ni zan yi masa hidima.A daidai lokacin da yake ratsa gangar jikina a wannan sa'ilin ne Aliya ta fito daga cikin ɗaki ta gani,ban san mene ne ta yi ba amma tabbas ta sarrafa wani magic nata sai ya zamana ni ne zan fi ƙarfin baƙin ruhi na sarrafa shi ba wai shi ne zai sarrafa ni ba .A cikin wannan dare mun yi lissafi iri-iri dangane da wanda zai haƙura ya tafi ɓoyayyar duniya domin kawar da baƙin ruhi .Tashin farko ta ce ita za ta ɗauki wannan kasadar don ba za ta iya jurar ta zauna a duniyar nan alhalin babu ke,gara ta yi tafiyar mai mafari ta mutu madadinki.Sai dai duk yadda muka ɗora tsaunin cimma nasara ya ƙi daidaita,sai kuma ta kawo shawarar mu jingina wa Aliyu shi tun da ba mutumin kirki ne ba.A nan mafita biyu muka samu muddin Yaya Aliyu yayi dakonsa to ke ce da hannunki za ki caka masa wuƙa a zuciya su mutu su duka biyun,mafita ta biyu mai rauni ce in mun yi nasara saka ruhin a gangar jikin yaya Aliyu zai iya yiyuwa ya boɗare ya fi ƙarfinmu kuma,kuma dai ba zai yiyu ma ya iya mutuwa ba.Dole na ɗauki kasadar dai ta na mutu tare da shi,kamar yadda ki ga komai ya faru"

"Amma lokacin da numfashinka ya fita gangar jikinka me ka ji?" na tambaye shi wannan karon ina mai ɗale cinyarsa.

Sama yayi da rigar jikina yana shafar fatata kamar mai yi mini susa,kafin ya ce "wata duniya ce na tsinci kaina mai abubuwan ban mamaki,a cikinta na hango duk wasu mutane waɗanda tun ina yaro ake zarginsu da maita,haka ma matsafa daga cikinsu.Sannan abin da zai baki mamaki bayan tawagar Kaka Maitama da Nalado akwai wasu keɓaɓun jarumai da suka zo tarbena suna murna tare kuma da bani labarinsu.Daga ciki dai akwai wani Mahadi ya ce shi ne jarumin nan wanda ake yi wa laƙabi da KABEWAR KAN KABARI,sai wata sarauniya wacce ta kasance shugabar masu MAITAR IDO ita muna da alaƙa da ita ta jini " na ɗan turo baki na ce "kenan kallon mata ka yi?"

Yayi dariya tare da kamo leɓena na ƙasa ya ɗan ciza kafin ya ce "dayawan jaruman fa mata sun fi yawa,a can ɗin ma sai da wasu ɗaliban MAKARANTAR MATSAFA suka so kawo mini caffa amma gimbiya Ayodele ta yi saurin taimakawa esprit ɗina ya koma can cikin MUTUWARE sai numfashina ya dawo"

Na ja ajiyar zuciya na ce "ko ka san da ina sonka sosai?"

Tamkar ya suma haka ya tsaya cak da numfashi,kafin ya lumshe ido yana wani ajiyar zuciya.Fuskarsa na tallabe da dukkan tafukan hannuwana na ci gaba da cewa "ina sonka sosai MAHEER! Tun ranar farko da na soma ɗora idona a kanka na ji a raina kaina makullin sirrina"

"H.lat kar fa ki haukata ni da daɗin kalamanki" MAHEER ya faɗa yana jan numfashi tare da ida cire mini rigar duka ya yar.Da sauri na manna ƙirjina da nasa don ko bra ban saka ba,karon farko da tun da muka zama abu ɗaya na ji mahaukaciyar kunyarsa.So yake ya ciro ni amma na ƙi yarda na laƙanƙame masa kamar cingam,murya na ɗan rawa ya ce "please H.lat!"

Kaina na soma jujuyawa a ƙirjinsa ,kafin cike da dubara na cire maɓallan rigarsa.Cike da tsokana na mayar da muryata ta yara na ce "a yi feeding ɗina" sai na ɗora bakina a ƙirjinsa ina wawura kamar yadda yara ke yi.

Kusan suma MAHEER yayi,ya zame mini kamar mahaukaci ya soma yi mini wasu salon da suka sa sai da muka zube kan capet. Sai da ya gajiyar da ni sosai kafin ya yi mana wanka,tsabar iya yi irin nasa kuma ya hana mu saka kaya wai a haka za mu kwanta luluɓa kawai muka yi.

Shiru kawai na yi ina tunanin abubuwa dayawa da suka shuɗe,ina son sanin halin da Hassana take ciki a yanzu da kuma ahalin gidan namu .Ina lumshe ido kuwa na hango ruhin Hussaina tana sakar mini murmushi kafin ta ɓace ,cike da nutsuwa na yi bacci.

Duk yadda na gaji ɗin kuma bai hana ni yin sallah kan lokaci ba har ma na shiga kitchen na yi abubuwan da zan yi,duk da dai yanayin Aliya duk yasa na ji wani iri. Sai da na koma sama na yi wanka sannan na sauko a karo na biyu,Hajiya na je na gaida ta amsa cikin sakin fuska kafin ta ce "ina Maheer?"

"Ya fita tun da safe" na bata amsa. "Ƙila yana can wurin Innarki kin san jiya can babban gida suka wuce da ita,ke ma ki shirya zuwa maraice sai mu je lokacin Aliya ta dawo "

"To Mama " na faɗa ,ina fitowa daga ɗakin Hajiya muka yi kiciɓis da Lubna.Ta wani zo da sauri ta rungume ni tana kuka kafin ta ce "Haule na gode sosai da yadda kike ƙaunata daidai da ɗaya rana ba ki taɓa guduna ba,kuma...kuma" sai ta yi shiru.

Na ɗan ja baya kafin na ce "Lubna daga ina kike? Me ya faru da ke ne?"

Ta ce "tun da muka rabu sai Jagaba ya kai ni wani gida ya tsare ni da wuƙa sai na sanar da shi duk wani sirri da na sani dangane da farin ruhi da tawagarsa,sannan kuma na faɗa masa yadda lamurran ƙungiyar family ke tafiya.Sai dai kafin ma na yi wani yunƙuri aka ƙara sanar da shi baƙin ruhi ya suɓuce daga hannunsu shi ne ya maido ni nan gida"

"Bai dai yi miki komai ba ko?"

Ta ce "Babu abin da yayi mini"

Ina jin haka sai na ja ajiyar zuciya kafin na ce "alhamdullah! Dama dai tsorona kar ya taɓa mutumcinki"

Idonta ya kawo ƙwalla ta ce "mutumci na nawa Haule? Ai babu sauransa,tun ranar da na biyewa son zuciya na bai wa Dr David shi a ranar kuma suka zuba mini ƙwayoyin cuta ta yadda wani namiji ba zai sake mora ta ba"

Cike da tausayinta na ce "duk wata matsala ta duniya tana da magani Lubna,kin ga ki nemi man lalle mai kyau tare da ƴaƴan magarya ki yi tafasa su sai karanta duk abin da kika sani daga cikin Alkur'ani mai girma ,in sun ɗan sha iska sai ki zauna a ciki ki kunna karatun Alkur'ani kina saurare har sai ruwan sun huce sai ki fita. Sannan kuma ki samu man zaitun da na Habbatu sauda da kuma jan muski da fari ki haɗe su wuri guda ki yi karanta surori uku na ƙarshen Alkur'ani,ki haɗa da ayarul ƙursiyu da amanar rasuluh.Sai ki karanta *Waƙadimna ila ma amilu min amalin faja'alnahu haba'an mansura* sau ba adadi ki dinga shafawa da izinin Allah duk wani tsafi ko sihiri ko wata cuta da jinnu suka sakar miki duk za ta fita,ke dai kawai ki yi yaƙini ki yarda da Allah sannan kuma kar ki yi gajen haƙuri ki maida hankali "

Lubna ta yi wani murmushin da ya fi kuka ciwo kafin ta ce "da a ce tun farko na sanar da ke gaskiyar labarina da ƙila tuni na warke"

Na ce "shi yasa babu kyau ɓoye cuta a wurin da mutum yake tsammanin samun maganin warakarsa,ba kuma ko ina ne zurfin ciki yake da rana ba" "Haka ne na gode sosai,bari na je gida na ga Ummah " har ta juya za ta tafi na tsayar da ita na ce "ki yi wa Ummah godiya don ba don ita ba da tuni kin faɗa tarkon sheɗan, addu'arta ce ta zama garkuwa a gare ki"

Ta saki murmushi kafin ta fice,ni kuma sama na haura na gyara ɗakin MAHEER tsaf ina dab da na shiga wanka ya shigo fuskar nan a murtuƙe yau ya koma sak Oga Maheer.Ganin yadda yake shan ƙamshi yasa na share shi na shige wanka,bayan na fito sai na ga yana haɗa kayana waɗanda shi ne ya saya mini.

"Za ki je babban gida,wai sai sun yi biki an kuma shafa miki lalle da duk wata al'ada da ake yi" ya faɗa kamar zai fashe .Ni kuma daɗi na ji ko ba komai zan ga Innarmu,na ɓoye murnata a ciki na ce"to mene ne na fushin? In ba ka so na tafi ai kawai sai ka sanar da su"

"Na sanar da su me? Hum! Ki shirya dai ku tafi ga Mama can ita ma yadda kika san ba ita ta haife ni ba haka ta goyi bayan hakan"

Kasa riƙe dariyata na yi kawai sai na shiga ƙyalƙyatawa,yayi tsaye yana kallona kafin ya fice.Sai kuma na ji babu daɗi,a haka na kimtsa na sauka ƙasa sai da na ci abinci kafin direba ya kai mu.

Babban gida,ya ci sunansa tabbas don yana da girma sosai sannan cike yake da ahali haka aka dinga gabatar mini da kowa har na saje da su.Sai yamma lis,sannan Aliya ta zo yau ɗin ma sai da ta bani madarar nan mai magani ina dab da na sha Innarmu ta aiko kirana a dole na ajiye kofin na fita.

Ina zuwa sai na tarar da anty Aliya ita da sauran cousin sun jibgo uwar sayayyar kaya,haka na zauna ina dubawa shaf na manta da zancen wata madara sai lokacin da Hajiya ne ta zo yin sallama za su koma ita da Aliya.

"A nan za ki zauna wai?" Aliya ta tambaye ni fuskarta cike da takaici. Na ce"eh sai an saka ni lalle wai"

Ta ɗan taɓe baki kafin ta ce "kar ki bari a yi miki wanka da ruwan lalle Haule "

"Don me?" "Saboda rayuwarki na cikin matsala" "Matsalar me kuma? Wai na tambaye ki yaushe ne aurenki da Dr Muhamud?"

"Ɗaya rana za a yi da na su Dr Umar da nurse Fatee " ta bani amsa. Na ce "shikenan sai ki tafi ki bar ni ko?" Ta dube ni tsakiyar ido kafin ta ce "sai ki nemo Nadia ku zauna tare" Na tuntsire da dariya na ce "wai tana wane wuri yanzu?" "Ɓoyayyar duniya mana ina ne za ta je in ba can ba? Suna can har da Mentor " "Ɗazu Lubna ta dawo" "Na sani! Ya kamata ki haɗa aurenta da Yaya Aliyu " "Don me?" na tambaya,ta ce "hakan shi ne daidai".Na ce "kin san da ta ɓoye mana labarinta ita ɗin ba budurwa ce ba" .Aliya ta ce "shi ma ai ba saurayi ba ne, Allah kaɗai ya san iyakar ƴaƴan mutane da ya ɓata" "Haka ne!" na faɗa ina jin kuma babu daɗi,haka dai muka rabu.

★ Cikin sati guda kacal wata irin nutsuwa ta saukar mini,ina zaune luntsum cikin ahalina ina samun kulawarsu babu takura sai rarrashi ta kowanne ɓangare.An tsayar da ranar bukukuwanmu duk a rana guda, kowanne ɓangare sai shirye-shirye ake yi musamman ma dai Lubna wacce ke ta fafutukar ganin ta samu lafiya.Ta ɓangarena kuma sam na kasa gane madarar mece ce Aliya ke bani kusan kullum,amma kamar abin tsafi ko ɗigo ɗaya ban taɓa sha ba don tamkar ana nisanta ni da shan madarar da zarar ta bani ita sai wani uzuri ya gifta kuma in na dawo ban ganin kofin.Wannan al'amari ya kwashi wurin wata guda currr,yanzu ma ta kawo mini ita amma zuwan Yaya Aliyu ya hana ni na sha duk ya bi ya tayawar wa da mutane hankali yadda yake kuka kamar ƙaramin yaro yana neman gafara.Da na ji alamun ni ma kukan zan yi sai na koma can ɗakina da aka ware mini,ina buɗo ƙofar daidai lokacin ne kuma wani hannu wanda ba a gani da kyau ya ɗauke kofin madarar da Aliya ta bani.Duk yadda na so na yarda da abin da idona suka gane mini sai aka juye mini kwanya haka a dole na watsar.Kwanciyata na yi da wuri,don gobe ne za a gudanar da shafin lallen amarya da kuma wanka.Sosai na yi bacci kamar matatta,sallar asubah ma dakyar na iya yin ta.Wuraren ƙarfe tara aka soma shagalin bikin,an shafa mini lalle wanda na ji tamkar an zuba mini wani sababi yayin wanka haka kawai na daure aka gama.Sam wunin kasa cin abinci na yi har dare yayi,ina shirin kwanciya anty Aliya ta shigo hannunta riƙe da kofin madara ko kafin ta kawo gare ni kofin ya faɗi ƙasa madarar ta zube.Na lumshe ido ina kallon ɗan jinjirin macijin da ke ɗauke da siffar madara yana kallona da idonsa ƙuru-ƙuru kafin ya narke kamar ƙanƙara.

Anty Aliya ta yi saurin ɗauko abin gogewa,sai dai kafin ta dawo komai ya ɓace kamar ma babu abin da ya zuba.Da wannan mamakin ta fita yayin da ni kuma na yi kwance lamo ina tunani,kiran waya ne ya katse ni.Maheer ne,hira muka yi sama-sama wacce take cike da kewa da kuma zaƙuwar ranar da za mu tare a karo na biyu. Muna cikin wayar ne wani iska ya soma shigowa ta window tare da soma kashe mini jiki,ban san lokacin da wayar ta fita daga hannuna ta faɗi ba.Wani irin yanayi nake ji kamar wacce aka tsoma cikin ruwan ƙanƙara,kafin a hankali na soma lumshe idona aka saka ni baccin dole.

Wata tsohuwa ce ta bayyana a gabana,hannunta riƙe da tasa da kuma almakashi.Muryarta a shaƙe take ba ta fita sosai,"lokaci yayi da za ki bayar da hadiyar da kika ɗauki alƙawari" shi ne abin da ta furta kafin ta ware cinyoyina,ina jin lokacin da take saka mini almakashi tana datse jinjirin da ke kwance cikin marata a haka har ta gama ta fiddo shi duka kafin ta haɗe shi wuri guda ya zama complete jariri,sai ya soma tsala kuka yana harba ƙafafuwa a haka ta bi ta window ta fita.

Daidai nan na ji wata irin muguwar azaba ta ziyarce ni,wacce ta yi silar tashina daga bacci.Kasa jura na yi kawai na fasa ihu,ƙuguna da marata sun ƙulle ga wani irin yajin azaba da nake jin yana tsirta mini kamar ƙasana zai buɗe.

Kusan duka ahalin suka kewaya kaina,suna tambayata amma babu wanda na iya ba amsa.Ina a haka aka kira MAHEER,ya zo ya kai ni asibiti can ɗin ma babu abin da ya sauya duk wasu allurai da ake tunanin za su yi mini magani an yi amma a banza.

Daga ƙarshe Aliya ta zo,idonta sun kaɗa sun yi ja ita ce ta sanar da su da su bar ɓata lokacinsu komai za su yi mini ba zan ji dama ba har sai in alƙawarin da na ɗauko ɓoyayyar duniya ya cika. A wannan wunin ranar mutuwa ce kawai ban yi ba,amma faɗar azabar da na sha ɓarnar baki ne.Sai da rana ta kawo tsakiya kawai na samu sauƙi wanda yake tafe da yin ɓarin cikin jikina,yana gama faɗowa wata zufa ta karye mini sai na ji kamar an gafarta mini.

Gado aka bani tare da saka mini ƙarin ruwa,idon MAHEER sun kaɗa sun yi ja kamar na Aliya su duka biyun kuma sun tsure ni da ido kamar ni ce na ce cikin ya fita.

Murya ba ta fita sosai ya ce "me yasa kika bayar da jinina ga tawagar duniyar ruhaniya?" wannan tambayar tasa ita ce ta sa na fahimci taƙamaimai abin da ke faruwa. Aliya ce ta basa amsa da "saboda ta ceto taka rayuwar! Oga Maheer ka sani ko kai aka baiwa zaɓi shi ne wanda za ka ɗauka,duk ita Haule ta yi zaɓin ne ba tare da ta san wane ne ta zaɓa ba.Maitama ya ce ruhi biyu ne da ita saboda tana ɗauke da ciki,da kuma aka tambaye ta wanne ta bayar sai ta miƙa rayuwarta su kuma a waccan duniyar kusan abin da ka fi so shi suke ɗauka.Duk a tunaninsu Haule ta fi son yaronka fiye da kanta shi yasa ta bayar da kanta,in kuma hakan ta faru dole kenan sai in ta haihu in kuma ta haihu tana iya canza shawara ta bayar da wani wanda ba lallai sai jininta ba kenan an samu hadiya mai rauni .Abin da na yi ta ƙoƙarin yi kenan,na kare jinjirin cikinta har sai ta haife shi in ya so ni na mutu madadinsa,sai dai kuma kash sun san duk wani plan ɗina hakan yasa duk lokacin da na bata madara sai an ɗauke mata hankali daga shan ta"

MAHEER ya ja dogon numfashi ya ce "Allah bamu wani wanda ya fi shi"

Aliya ta amsa da Amen yayin da ni kuma na soma hawaye ina jin kewa da soyayyar yarona, MAHEER ya matso ya janye hannuna da ke kan marata ya maye gurbi da nasa haka ya dinga shafa shi yana kwantar mini da hankali.

Ba mu wani jima ba aka sallame mu,bayan komawata gida sai aka soma yi mini gyara na musamman kwacokwam aka ɗauko Mamar Yusuf likitar mata tun daga Sokoto ta zo ta dinga yi mini mahaukacin gyara wanda na san ba don MAHEER ne ya ɓare ni a leda ba to da tabbas zai ce wata budurwa ce ni.

An yi bukukuwa cikin kwanciyar hankali,sai a ranar bikin ne muka haɗu da Abba wanda jiki duk yayi masa sanyi ya kuma tuba.A kallon farko da na yi masa kuma na fahimci dukiyar da BAƘIN RUHI ya mallaka musu ta bi iska komai ya ƙare ba su da komai in banda gidan da aka gina.

Su Hassana da Goggo Lami ma sun zo,tun daren biki su da sauran ahalinmu.Har ƙasa anty Mardiyya ta durƙusa ta nemi gafarar Innarmu da kuma bani haƙuri.

Sai da aka soma zancen zuwa ɗaukar amarya ne na ji wani labari da ya kusan sumar da ni don daɗi,wai an ɗaura auren Hassana da Yaya Aliyu sai na rasa da waɗanne kalamai zan yi wa Ubangiji godiya.

Amma a haka na daure na ci kwalliya don zuwa wurin ƙawata Aliya wacce Hajiyarsu Maheer ta yi ruwa da tsaki ta yi mata duk wani abu da ya kamata a ce uwa ta yi wa ƴarta.

Maheer ne ya zo da mota ya ɗauke ni iya ni ɗaya kawai,gidan Dr Muhamud muka yi tsinke tun a hanyar tafiya yake yi mini magiya da mu wuce kawai gidanmu in mun dawo. Ina shiga muka rungume juna ni da Aliya wacce ta yi kyau sosai,ba ta da wasu ƙawaye wannan yasa na zauna mata muka yi ta hira wacce za ta kasance ta ƙarshe a tsakaninmu don kuwa ita da Dr Muhamud duniyarmu da tasu ba ɗaya ba ya zama dole su koma can inda ke daidai da su.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull