Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 39

Bakin ruhi complete - Chapter 39

Bakin ruhi complete Chapter 39: Bakin ruhi complete Chapter 39. Maheer ya yi kamar yadda ta ce kafin ya soma magana "yana gun Mr Sahil mijin Bahijja yanzu…

3,350 words

Maheer ya yi kamar yadda ta ce kafin ya soma magana "yana gun Mr Sahil mijin Bahijja yanzu haka suna can gidansa har da su Yasmine ɗin wacce yake ƙoƙarin kaddamar da ita a cikin sabuwar ƙungiyar da suke shirye-shiryen kafawa a karo na biyu"

Na yi wani murmushi kafin na ce " har abada hakan ba zai kasance ba,don duk wata hanya da zan bi sai na binciko ta na hana kafuwar wannan ƙungiyar.Ruhinsa kuma yanzu za a maido masa shi ku dai nutsu ku riƙe mini shi" ina gama faɗar abin da ni kaina ban san ya ake ina furta hakan ba sai na kai hannuna na kama wuyan Dr Muhamud na soma yin magana cikin wani yare na mutanen farko,ɗakin ne ya yi ɗif duka hasken ya ɗauke babu jimawa kuma wata baƙar inuwa ta faso bango ta shigo.

"Lafiya kika aika kirana?'" ruhin Boss ya furta.

"Abin da ke hannunka nake son ka bani ta lafiya kafin na saka ƙarfi" na basa amsa ina juya idona suna fitar da wani irin haske. Yayi wata dariya yana shirin yin magana amma na riƙe masa maƙogoro ta hanyar juya idon nawa masu cike da ƙarfin iko,ya soma kakarin mutuwa amma don taurin kai ya ƙi miƙo mini sai da ya ga ina shirin kawo ruhin Yasmine yana damƙa mini ruhin Dr Muhamud ni kuma ina tsinka nasa tare da jefa shi ɓoyayyar duniya inda su ma can ne suke da niyyar kai Dr Muhamud don ba mutuwar gaske ce yayi ba.

Aliya da MAHEER suna tsaye duk suna kallona,sai a lokacin kuma na ƙara basu wani umarnin na su riƙe ƙafafuwan Dr Muhamud ɗin.

Ido na rufe ina mai yin ɗalasiman da suka kamata,nan take gangar jikinsa ta soma yin rawa kafin kuma bakinsa ya buɗe ruhinsa ya shige.Kamar ƙyaftawar ido haka ya miƙe yana jan numfashi,Aliya ta rungume shi cike da murna yayin da mu kuma muka shiga yin murmushin nasara.Haka muka fito muka wuce gida har da shi Dr Muhamud ɗin,can ɓangaren MAHEER ya tafi yayin da ni kuma na dawo ɗakinmu ni da Aliya,sai a lokacin ne ta bani tarihinta wanda na ji kamar almara don ban ma san iya adadin ɗaruruwan shekarun da da ta kwashe ba a duniya.

"Kina son Dr Muhamud ?" na tambaye ta ina mai kafe ta da ido .Ta saki ɗan murmushi kafin ta jinjina kai,na ce "ya kamata ki musulunta,ki yi addinin Musulunci da niyyar kanki a kuma hukunce kamar yadda ya zo"

"Na sani! Yanzu me kika yanke game da BAƘIN RUHI?"

"Zai koma inda ya fito,zan yaƙe shi" na bata amsa.

Yanayin fuskarta wani iri kafin ta ce "yaƙarsa abu ne da ba zai kawar da shi ba na har abada,ko ya koma wani zai iya ƙara kawo shi amma kashe shi shine daidai"

"Ta ya kenan?" na tambaye ta.

Ta yi ɗan jim kafin ta ce "dole wani rai ya salwanta" "Ni ban gane abin da kike son cewa ba" "Za ki gane in lokaci yayi,yanzu dai sai da safe ni zan kwanta" tana gama faɗar haka sai ta juya mini baya ta yi kwanciyarta,babu jimawa kuma bacci ya ɗauke ta.Ni ma wuri na samu na kwanta sai dai fa ba baccin na yi ba,a'a balaguron ruhi ne na lula a can garinmu.

Dare yayi duk kowa bacci yake,gidan ba baƙona ba ne wannan yasa na soma ratsa ko ina har na isa ɗakin anty Mardiyya tana kwance tana sharara bacci,idonta sun yi suntum da alamun na kukan mahaifinta ne da ta yi wanda na aika barzahu. Fitilun idona ne suka hasko mini yadda ta bangaji Innarmu,cike da zafin rai na soma kallon duk wani bango na ɗakin ina jefa wata ƙwayar cuta nan take shaƙar iskan ɗakin ta canza hayaƙi ya turniƙe wurin ga wani irin yanayi na shi ba duhu ba kuma ba haske ba,sai kuma uban zafi kamar tukunyar sabuwar burodi .

Zufa ce ta soma yi mata tsiyaya,amma ba ta farka ba ƙila ta gaji ne sosai.Wuyanta na shaƙe da furicin bakina,nan ta buɗe ido tana shure-shure amma ba ta ganina sai da na ga tana shirin mutuwa sannan na ƙyale ta.Zaune ta yi tsakiyar shimfiɗa tana maida numfashi kafin ta jawo butalin ruwa ta buɗe tare da kafa bakinta,sai dai na hana ruwan motsi ballantana mu su fita su shiga maƙoshinta.A ɗan tsorace take jijiga gorar ga dai ruwan amma ta rasa dalilin da yasa ba su fita,a dole ta ajiye shi amma na cira shi sama ya tsaya cikin iska tare kuma da buɗe murfinsa ruwan suka soma tsiyaya a gaban idon anty Mardiyya.A guje ta nufi ƙofa sai dai kafin ma ta ƙarasa na murza key wanda tana ji tana ganin kuma yadda ake murza shi amma ba ta ganina.

Cak ta tsaya tana kuka tare da soma waige-waige,so take ta yi magana amma ta kasa.Daidai nan na saka bulala na soma tsula mata tana ta ihu da kururuwa amma a banza tun da babu mai jin ta ballantana ya kawo mata agaji,sai da na yi mata lilis kafin na bar ta a nan kwance cikin fitar hayyaci.

Ina fitowa sai na yi tsinke ɗakin Kawu Laminu wanda tun da jimawa na fahimci ya tsane ni wanda kuma ƙiyayyar mahaifina ce ta shafe ni. Yana zaune yana ƙirga kuɗi,wuri na samu na zaunar da ruhina ina kallonsa.Shi ɗin ya kasance mugu wannan yasa ya ji a jikinsa ba shi ɗaya ba ne a ɗakin duk da kuwa bai ganina,na saki murmushin mugunta ina juya ido a nan take kuɗin ba suka dinga yaga kansu irin ƙanana sosai.

Kawu Laminu ya soma ɗan ƙaramin hauka don duka kuɗinsa ne da ya mallaka har da ma na cuta wanda ya kwashe na Kawu Hamza.

Almakashi na ɗauko daga ɓoyayyar duniya na soma aiki da shi kamar mai yanka atamfa na soma yawo da shi kaf cikin ɗakin hakan ya hana duban Kawu Laminu saƙar don duk inda almakashi ya gifta shi ma sai ya duba har ta kai na matsa shi kusan fuskarsa tuni ya soma fitsari cikin wando amma a haka na soma aske masa kai ina yi masa askin ɓarayi kafin kuma na mayar da almakashin mai siffar ƴar tsanar roba na fitar masa da kai da hanci da baki,ya shiga yi wa Kawu Laminu dariya daidai nan ya faɗi a some.Raina fari ƙal na baro gidan, binciken Yaya Aliyu na soma yi amma ban gansa ba a haka na wuce inda na bar gangar jikina na koma cikinsa.

Washegari kiran sallah ne ya tashe ni daga bacci,dakyar na tashi na yi wanka na gabatar da sallah.Aliya ba ta cikin ɗaki hakan yasa ina gamawa na wuce kitchen,a can na tarar da ita kuwa tana aiki sai na kama mata muna yi muna hira har ta kawo mini zancen Lubna.

"A tunaninki mene ne yasa ita ɗaya kawai suka ci galaba a kanta?" Aliya ta tambaye ni.

"Saboda ita ce mai rauni" na bata amsa.

Ta taɓe baki kafin ta ce "ko kuma ita ce munafuka ba,ita kuma Nadia fa wane wuri kika ajiye ta a yanzu?"

Na saki ɗan murmushi don na fahimci cewa har zuwa yanzu Aliya na kishinta ne.Na ce "ni yanzu wani tunani ne yake ratsa kwanyata,me zai hana mu nemo tsohuwa Yabobo ta bamu wata hanyar da ba sai wani rai ya salwanta ba?"

Ta ce "ba za ta iya zuwa duniyar nan ba,don tana can tana kula da su Anty don dab suke da dawowa gida"

Na sauke numfashi kafin na ce "ni dai ban so rayuwar kowa ta salwanta"

Cikin ɗacin rai Aliya ta ce "abin da ya zama kuma dole ne,don tuni ma an fitar da mutane biyu waɗanda ake sa ran ɗaya daga ciki ne zai mutu tare da BAƘIN RUHI "

Gabana ya faɗi daram! Murya na ɗan rawa na ce "su wane ne kenan?"

Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba kafin can ta ce "ɗayan dai Yaya Aliyu ne"

"Na biyu kuma fa?"

Tsakiyar ido ta dube ni kafin ta kawar da kai,"don Allah faɗa mini wane ne na biyun ?"

Ƙin bani amsa ta yi kawai sai ta ɗauki flask ta zuba dafafen kayan tea ta miƙo mini tana mai cewa "ki kai wa mijinki" Na ƙi karɓa ina mai cewa "Aliya ki faɗa mini"

"Ba yanzu ba,ungo ki je ki dawo"

Na karɓa na ɗora kan tray ɗin da ta shirya komai nasa,kafin na fita sai dai ina daf da hawa matakalar benen trayn ya faɗi komai ya zube daidai nan Hajiya ta fito tana jan salati.A yadda na ga tsoro ƙarara kan fuskarta na fahimci ba wai na asarar kofunan da suka fashe ba ne,Aliya ma fitowa ta yi jikinta na kyarma .

"Ina sauri ne sai suka zube" na faɗa cikin sanyin murya,Aliya ta haɗiye wasu yawu kafin ta ce "Haule mu je ɗaki ki kwanta ki huta" sai ta ja hannuna muka wuce can ɗaki,gefena ta zauna cike da damuwa lokaci zuwa lokaci kuma tana satar kallona yayin da ni kuma nake jin zuciyata na yi mini wata irin rawa.

"Ban san mene ne kuke ɓoye mini ba ke da Hajiya ,amma fuskokinku sun nuna" na faɗa kamar zan yi kuka.

Cikin sanyi Aliya ta ce " Haule in dai zan sake dawowa a duniyar nan a wani zamani,to ke ce za ki sake haifata"

Sam ban fahimci abin da take nufi ba,sai na ɗauki maganar ta shirme.Na ce "na haife ki kuma?"

"Eh ina nufin ki yi mini takwara" ta faɗi haka tare da shafa cikina tana wani irin murmushi,wani irin sanyi ne ya ratsa ni sai na ji kuma tamkar an ɗaure jijiyoyina.A hankali kuma idona suka soma lumshewa,babu jimawa bacci ya ɗauke ni wanda sam babu wani abun alkhairi a ciki sai mutuwar waɗanda nake ji a cikin ɓargon ruhina da aka nuna mini.

Ina farkawa na ga MAHEER gefena,yana shafar fuskata sai na fahimci hawaye ne yake share mini. "Kina kuka Queen me yasa?" ya tambaye ni.

"Ina Aliya ?" ita ce tambayar da na yi masa. "Sun tafi restaurant " ya bani amsa.

"Mu je ka kai ni" na faɗa cikin sauri tare da yunƙurin tashi amma ya hana ni ta hanyar riƙe ni gam,ido cikin ido muke kallon juna kafin ya ce "ina so ki ƙaryata abin da aka nuna miki cikin mafarki wannan shi ne maslahar ruhinki" na girgiza masa kai na ce "tun da ka ga haka to tabbas zai faru ɗin"

"Haule?" ya kira ni wanda kuma yau shi ne karon farko da ya taɓa kirana da wannan sunan,na dube shi cikin ido sannan ya ci gaba da cewa "a jiya na yi balaguron ruhi,na je gidansu nurse Fatee kuma na yi nasarar rogaza sauran sihirin da ya rage a yanzu ta san wace ce mahaifiyarta,ita ma Hajiya Bintar ta dawo hayyacinta yayin da ita kuma Momy ta zauce ta fara yin rashin lafiya mai kamar hauka.Oga kuma na tsinka igiyar da ke saita maganarsa don ya fi kowa sanin dabarun kafa ƙungiya a halin yanzu kuma ba zai iya yi musu komai ba.Boss kuma ya mutu,a yau aka rufe shi tun bakwai na safe duk fatar jikinsa ta yi duhu ta rine,Bahijja kuma ta tafi can wurin danginta ita da ƴarta.Mutum ɗaya ne kawai ya rage a ahalin family shi ne Yaya Aliyu,shi kuma bai da gogewa da yadda ake gudanar da komai duk wanda za su taimaka masa babu su sai mahaifinki kawai wanda shi kuma rashin Inna a kusa da shi ya raunata ruhinsa.Faɗa mini ina BAƘIN RUHI yake a yanzu?"

Shiru na yi ba tare da na basa amsa ba,don a iya bincikena na daren jiya ko sawunsa ban gani ba. "Ban sani ba" na basa amsa. Maheer ya miƙe tsaye tare da juya mini baya,a hankali kuma ya shiga cire rigarsa har ya fitar da ita duka.A mugun razane na tashi tsaye ina waro ido saboda ganin ƙaton tambarin baƙin ruhi a allon ƙashin bayansa na hagu.

A hankali MAHEER ya juyo yana kallona da idonsa da suka canza kala suka koma baƙi ƙirin dukkansu babu ɗigo fari ko ɗaya.Tsoro ne ya kama ni wanda ban taɓa ji ya ziyarce ni ba,in dai na fahimta MAHEER shi ne BAƘIN RUHI a yanzu,shi ne wanda ya ɗauki alhakin dakonsa a gangar jikinsa.Tako ɗaya kawai yayi na gansa dab da ni,a hankali kuma ya soma yin wani abu mai kamar na zautatu haɗi da wangale bakinsa na ƙurma ihu ina shirin bazawa a guje sai aka banko ƙofa Aliya ce ta shigo tana mai yin wani furicin da yasa idonta suka ɗau haske tana mai cewa "A yau ƙarshen komai zai zo,ruhika biyu za su narke su zama babu.Queen Haulat wakiliyar FARIN RUHI tare da King Maheer wakilin BAƘIN RUHI ku zo zuwa ga duniyar Ruhaniya"

Tana gama wannan furici sai sarƙar wuyana ta faɗi ƙasa,dutsen tsakiya ya soma kawo haske yana mai fitar da wani kamar shatin zuciya amma an rabata gida biyu.Uwa Yabobo ce ta bayyana ita da Innarmu wacce ke miƙo mini wuƙa,na karɓa ina mai tsaga yatsana manuniya sai na miƙawa MAHEER shi ma yayi haka sai muka tara yatsun namu kan sarƙar jininmu ya dinga ɗiga a ciki yana haɗewa cikin juna.

Innarmu ta cire sarƙar wuyanta sai na ta zama tamkar murfin tawa sarƙar,haka ta haɗe su wuri guda ta miƙawa uwa Yabobo ita tana mai cewa "mun cika alƙawarin Baba Maitama"

Yayin da ita kuma uwa Yabobo ta ce "daga yau kowa zai karɓi hukuncin abin da ya aikata,adalci zai wanzu a duniyar Ruhaniya yayin da farin ciki da zaman lafiya zai yi wa duniyar ado" tana gama faɗar haka sai kuma ta soma yin wani furici ,farin abin nan da na ga ya ratsa jikina ya shiga lokacin da muka je dajin sirri,shi ne yanzu ya fita ya shiga sarƙa wacce take tamkar mayen ƙarfe zuƙo ruhi ne a aikinta.Haka ma wani abu baƙi ƙirin ya fita daga jikin MAHEER ya shiga sarƙar,uwa Yabobo ta yi sama kamar wata leda ta bi ta rufin ɗaki ta fita yayin da kuma MAHEER ya faɗi ƙasa babu numfashi,wanda yayi daidai da fara kukan Aliya......

/19, 10:09] Hlm: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

*The End*

Kukan Aliya shi ya tabbatar mini da abin da nake dai gudu ya zama gaskiya.Duk da ƙwaƙwalwata ta kasa ɗaukar lamarin amma gaske dai ne MAHEER ya mutu kamar yadda na gani a mafarkina,Innarmu ce ta shafa masa ido ita ma tana hawaye kafin ta zo ta rungume ni wanda yayi daidai da jin wani abu na rufe mini fitilun idanu ban sake sanin abin da ya faru ba sai tsintar kaina na yi a ɓoyayyar duniya wacce take cike da ɗumbin al'umma maza da mata,nagari da kuma mugaye.

Sun kasu kashi biyu,ɓangaren dama sanye suke da fararen kaya yayin da masu ɗaya ɓangaren ke sanye da baƙaƙe.Kaka Nalado na gani a gaban maƙarabansa tamkar shi ne dai ke wakiltar BAƘIN RUHI har zuwa yanzu,yayin da kuma Maitama ke sanye da fararen kayansa shi ma yana tsaye kan ƙafafunsa hannunsa riƙe da furen floris wanda aka rubuta saƙon maraba da zuwan ruhin MAHEER wanda ke dab da shigowa.

Kamar zararriya haka na tafi a guje ina kuka tare da zubewa kusan ƙafafunsa ina kallonsa da idon tausayi na ce "ta ya za ka yi mini haka duk da uwar wuyar da muka sha don ganin burinka ya tabbata? Me yasa sai MAHEER? Akwai wani aiki da ya kamata a ce yayi wanda bai cika ba? Ko da akwai inda ya yi kuskure? "

Kaka Maitama ya duƙa tare da kamo ni amma na zille na ƙi yarda ya ciro ni,a dole ya soma yi mini magana cikin taushin murya "jikata Haulat haka alƙalamin ƙaddara ya nuna,domin kawar da BAƘIN RUHI ana buƙatar hadiyar wani ruhin,kuma MAHEER shi ne jinina na kusa wanda ya kamata na bayar in kuma ba shi ba to ke ce ko kuma Aliyu sai dai kuma ruhin Aliyu ɗin ya gurɓata da duhun zunubi ba a buƙatarsa"

Wani kukan na sake fashewa da shi kafin na ce "na yarda na mutu domin MAHEER ya rayu"

Maitama ya ce "ruhi biyu ne da ke sai dai ki zaɓa cikin biyun wanne za a ɗauka sabo ko tsoho?"

Ba tare da na fahimci abin da yake nufi ba na ce "tsohon!"

Sai ya miƙo mini wata munduwa wacce aka ƙera da ƙarfen yin kuɗi ya ce "ki ɗora wannan a saman goshin MAHEER" na karɓa daidai nan na farka na samu kaina kan gadon asibiti.

Babu kowa ɗakin wannan yasa na yunƙura na tashi zaune da kaina.Wani abu na ji cikin tafin hannuna,ko da na duba sai na ga ƙarfen nan ne da Maitama ya bani sai yanzu ne kuma duk abubuwan da suka faru suka dawo mini a kai.Da sauri na dire daga gadon na buɗe ƙofa na fito,direct hanyar da za ta kai ni mutuware na nufa don na fi kyautata zaton can dai za a ajiye gawarsa .

A bakin ƙofar na hango Dr Muhamud sai rarrashin Aliya yake,shi ne ya fara ganina ya sanar da ita.Sai ta juyo,muna haɗa ido da ita sai na ga ta saki murmushi kuma kamar ta san abin da zai faru.Da sauri ta nufo ni tare da rungume ni"kin samo mafita? Wa kika bayar matsayin sacrifice?"

"Tsohon ruhina" na bata amsa,da wani mugun sauri ta sake ni tare da ja baya ta soma girgiza kai tana furta "a'a! A'a! Don me?"

Ban tsaya bata amsa ba na wuce ciki,ban wani sha wahalar ganin MAHEER ɗin ba.Na yaye zanen da aka rufa masa na ƙure kyakkyawar fuskarsa da ido kafin kuma hannu na rawa na ɗora munduwar kan goshinsa,nan take ta soma fitar da wani haske kafin sannu a hankali ta dinga nitsewa cikin koshin nasa har na bar ganinta sai hasken kawai shi ma zuwa wani lokaci sai na bar ganinsa.

Sama da minti biyu ina tsaye amma ko alamun numfashi babu a tattare da shi,tuni na sare kawai sai na faɗa jikinsa ina mai fashewa da kuka.Tsawon lokaci ina a haka kafin na ji hannunsa kan gadon bayana tare da amon muryarsa "H.lat!" ji na yi kamar an narkar da ni tsabar shock da kuma farin ciki.Na ɗago kai da sauri muna kallon juna kafin na kafa bakina kan nasa na shi yi masa sumbar fitar hankali.

"Haule?" na ji muryar da har abada ba zan taɓa mancewa ba, da sauri na saki MAHEER na juya na je da mugun sauri na ƙanƙame anty Aliya ina wani kukan.Ita ce ta jawo ni muka fito waje,yayin da kuma Dr Muhamud ya taimakawa MAHEER ya kimtsa suka fito.

Direct gidan Hajiya muka yi tsinke wacce ba ta san komai da ya faru ba sai yanzu da Innarmu ta bata labari.Babu jimawa aka haɗa family meeting ,an yi kuka sosai an zubda hawaye yadda Innarmu ta dinga zayyano irin matsalolin da muka fuskanta a gidanmu.

Dangi tamkar za su haɗiye ni haka suka dinga ririta ni,muna a tare sallah kawai ke sa mu tashi.Wuraren ƙarfe takwas na dare na haura can sama inda Aliya ta haɗa mini ruwan wanka masu ɗumi,yau wani sabon salo da ta ɗauko wai ita za ta yi mini wanka.

Haka na shiga bahon wanka,gashin kaina ta soma wankewa kafin ta soma yi mini maganar da sam ban fahimci abin da take son faɗa ba.

"Haule duniyar Ruhaniya da kike ganinta ta wuce duk yadda kike tsammani,yanzu ne za a baki sharuɗa sai kuma kin bi su amma kuma in kin tafi gaba sai ki ga ba ki tsira ba.Na so a ce kin yi haƙuri kin yi juriya ba ki yi saurin ɗaukar zaɓin da aka yi miki ba,don tuni na tsara nawa plan ɗin" sai kuma ta yi shiru.

Na ja numfashi kafin na ce "Aliya me kike son faɗa haka?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull