Bakin ruhi complt by mrs sadauki - Chapter 21
Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 21: Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 21. "Barka da zuwa Sarkin matsafa " shi ne abin da ta furta,na amsa…
4,454 words
"Barka da zuwa Sarkin matsafa " shi ne abin da ta furta,na amsa da "yawwa" sai na ga tana kallon Nalado,sai ka gabatar mata da shi na ce "wannan shi ne abokina Nalado"
Ta ɗan yamutsa fuska kafin ta ce "na sani,amma ai shi ma sarki ne na wani yanki" Nalado na jin haka sai ya matso ya ce "sarki kuma?" Ta ce "eh na ga tambarin sarauta a saman goshinka sai dai babu tabbacin cewa za ka iya ɗaukar wannan kambun duba da baƙar zuciyarka mai cike da ha'inci da kuma zalunci ,saboda mene ka yi haka? Me yasa za ka cutar da wanda ya yarda da kai?"
Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da Nalado kafin ya ce "ki yi min afuwa ba zan sake ba" "Mene ne sunanki?" na tambaye ta don kawar da zancensu,ta maido dubanta gare ni kafin ta ce "Zinaru! Ya zancen maganarmu ka shirya auren nawa a yau ko kuwa?"
Muka kalli juna da Nalado sannan na basa labarin yadda muka yi da Zinaru,a cikin ƙwayar idonsa na hango tsantsar hassada saboda ya fahimci auren Zinaru da zan yi tamkar taka wani matsayi ne a duniyar tsafinmu.
"Na amince" na faɗa ba tare da wata shawara ba hakan kuma sai ya ƙara fusata Nalado saboda shi ɗin tamkar wani ubana ban taɓa ɗaukar wani mataki ba sai na basa shawara,kuma abin da ya zartar shi nake amfani da shi.
Zinaru na gama jin amsar da na bayar sai ta koma cikin ruwa ba tare da ta yi min bayanin yadda za a yi auren ya kasance ba.A ɗan hassale Nalado ya ce mini "ka yi hauka ne Maitama? Ka kuwa san yadda ruhikan ruwa ke da ƙarfin tsafi? In fa ba ka yi hankali ba wallahi za ta canza ka ne ta mayar da tsafinka wani iri"
Na ce "kar ka damu ,duk wani muƙami da wani matsafi zai buƙata ni na gama samunsa.Ko ka san girman tsafin da ke cikin rawanin nan kuwa? To bari ka ji in faɗa maka,ɗazu kafin ka zo har matattu na dinga gani suna yawo cikin gari sannan wai bayan wannan duniyar da akwai wata duniyar"
"Wata duniya kamar ya?"
"Ɓoyayyar duniya ce wacce aka killace domin matsafa,amma ilimin tsafinmu bai yi ƙamarin da yasa muka san da ita ba.Kai duk ba wannan ba,ashe akwai wuri na musamman da aka keɓe domin zuwa neman taimako ko kuma kiran wani dodo ko aljani,sai dai fa har yanzu ban san ta ina ake bi a je ba kuma ba a sanar da ni ba"
Nalado da yake babu abin da yake so a duniya irin tsafi sai cewa yayi,"in dai haka ne ya zama dole mu binciko ina ne aka keɓe wannan duniyar,ka ga mu je gida ka ɗauko rawanin sai mu je can bayan gari mu ƙaddamar da nufinmu "
Shawarar da ya bayar sai ni ma na ga hakan ne ya dace,kawai sai muka je gida muka ɗauki duk wani abu na buƙata kafin mu koma can bayan gari.Tuni duhun dare ya keto,haka muka kunna wuta kafin mu fara duk hatsabibin tsafi haɗi da kiran sunayen dodanni.Tun ƙarfe bakwai na maraice muke abu ɗaya amma har biyu na dare ba mu samu amsar abin da muke so ba,sai dai mun ci dambun kuturu ba gudu ba ja da baya haka muka ci gaba da fafutuka har wani abu mai kamar lula ya bayyana a gare mu.
Duk shiru muka yi muna kallon dunƙulallar lula kafin ta soma yi mana bayani da kanta,"ni ce girgijen tsafi mai amsa duk wata buƙata ta matsafa,ku faɗi ina za ku je?"
A lokacin guda ni da Nalado muka yi karon baki wurin cewa "ɓoyayyar duniya"
"Ku shafe ni sannan ku furta hakan" lular ta faɗa,sai muka kai hannu muka shafe ta kamar yadda ta ce nan ne fa muka tsinci kanmu a dajin sirri.Kamar yadda Maheer ya faɗa miki haka tattaunawarmu da Nalado ta kasance shi ya zaɓi ɓangaren duhu ni kuma na zaɓi.Da na shiga na abubuwan ban mamaki a ciki,ban taɓa yarda da fatale ba sai da na gansu a gabana birjit sai gudanar da lamurransu suke yi.Har na gama yawuce ko ina babu wanda yayi mini magana ko kuma ya nuna alamar ya san da wanzuwata.Fitowa na yi sai na tarar da Nalado a waje sai gumi yake fitarwa,da sauri na nufe shi na ce "ya dai lafiya?"
"Ina fa lafiya Maitama,babu irin tashin hankali da masifar da babu a nan ciki.Na ga abubuwan ban tsoro a ciki,haka kuma baƙaƙen ruhika suke shawagi yadda ka san ƙuda,babban tashin hankalina shi ne yadda wurin yake cike da duhu ga wari da ɗoyi " daga nan sai muka yanke shawarar mu fita zuwa duniyarmu,ta yadda muka shigo haka muka fita sai na ɗauki wannan lular sirri na saka a jaka kafin kowannenmu ya kama gabansa.Ina isa gida na zube kan katifa tare da soma yin bacci,mafarkin Zinaru na soma yi ga mu nan a ƙasan ruwa ana shagalin bikinmu bayan an kammala komai muka yi sunnar aure duk a cikin mafarki.Washegari tun da safe bugun ƙofar Nalado ta tashe ni daga bacci,ina buɗe masa ƙofa ya shigo yana zarar ido ko bari bai yi na yi wanka ba ya shiga koro min bayani "Maitama jiya bayan mun dawo sam ban yi bacci ba,bincike na duƙufa yi har sai da na samo asalin yadda ake gudanar da tafiyar da ɓoyayyar duniya.Ka ga aljanin da ke yi mini aiki ya bani wannan takarda mai ɗauke da harufan tsafin da ake furtawa domin kiran dodo ko aljani ko kuma wani ruhi.Duba ka ga hoton hatsabiban ruhika uku nan da ke can cikin wannan daji da muka tafi,kowanne kuma da bayaninsa"
Karɓa na yi na soma karantawa, takardar cike take da tashin hankali don manyan matsafan aljanai ne da suka tabka fasadi a cikin doron duniya. Nalado ya ci gaba da bayaninsa "zan je na kira wannan ɗin na ƙarshe,zan jawo shi izuwa duniyarmu "
Da sauri na tari numfashinsa na ce "a'a Nalado da akwai haɗari sosai kar ma ka gwada kiran ɗaya daga ciki.Ko ba ka karanta ka gani ba? In banda rarraba kan al'umma babu abin da suke so,kuma irin waɗannan da jinin mutane suke rayuwa"
Nalado ya karɓe takardar yana mai cewa,"ka ga ban abina,tun da ka ji na ce zan yi to tabbas sai na yi.Wato so kake na zauna ƙarƙashin ikonka kana mulka ta don ka mallaki abu mafi asiri a duniya?"
"Ba haka ba ne,na ce haka ne don tseratar da ahalinka da kuma al'umma daga sharrin shaiɗanun nan"
"Hahaha! Ni ma ai sheɗanin ne ka ga tafiyata" Nalado ya faɗa tare da ficewa,sai a lokacin na je na yi wanka.Duk a tunanina dole sai mun bi ta cikin lular sirri ne kawai Nalado zai iya kiran dodo ashe abin ba haka yake ba kana iya kiran su ko da a cikin ɗaki ne muddin ka kiyaye dokokin da ake bi.
Ranar da Nalado ya kira BAƘIN RUHI izuwa duniyar bil'adama haka garin ya ɗauki wani kalar ja tamkar garwashin wuta ,yayin da kuma zafi da hayaƙi suka turnuƙe ko ina.Dabbobi da dama sun rasa rayukansu haka ma jinin mutane ya salwanta,tsawon kwana uku ƙauyenmu na cikin tashin hankali a binciken da bokaye da matsafa muka ƙaddamar ne muka gano cewa an samu baƙuntar wani ruhi daga nan sai muka fara neman hanyar da za a samu maslaha sai dai fa duk hanyar da muka ɗauko ba mai ɓullewa ba ce.Wani tunani ne ya zo min a kai,da sauri na ɗauki hanyar tabki ina zuwa na yi tsaye ina kiran sunan Zinaru.Babu jimawa ta fito kuwa,kamar ta san dalilin zuwan nawa sai ta miƙo min wani littafi mai ɗauke da sunayen ruhika wanda ke Haule na san kin taɓa ganinsa a wurin Innarki sannan kuma kin yi amfani da shi wurin kiran dodon da ya haukata mijin antynki Aliya ko?" Papy na kawowa nan ya tsayar da bayar da labarin tare da tambaya ta,na jinjina kai na ce "eh haka ne"
Ya ce "to yanzu haka dodonki yana cikin duniyar nan,duk da cewa a cikin shawagin da yake yi ya gamu da wasu mutane masu aiki da baƙin ruhi sun mayar da shi tamkar yaronsu,amma ai lokacin da kuka je gidan Alhaji mai akwatin gawa kin gansa ko?"
"Eh da kuma ranar da na je can gidan Boss ya bayyana a daidai lokacin da Yasmine ta so cutar da mahaifiyarta" na faɗa. Papy ya ce "to wannan shi ne dodonki,shi ne protector ɗinki na farko ya kamata ki samu ki kira shi ku tsara abubuwa da dama don lokacin komawarki can gidanku yana dab da zuwa" yana faɗar haka sai ya matso kusa da ni tare da kamo hannuna ya ƙulla mini wani jan zare sai yayi kamar na saka awarwaro,"wannan layar ita ce za ta baki damar samun contact da ni,za ki dinga jin ci gaban labarina da Nalado a cikin kwanyarki a duk lokacin da kika buƙaci haka.Yanzu ki je Maheer ya mayar da ke gida,da dukkan alamu Hajiya na nemanki sannan yawwa gasar da za ku yi ta girke-girke da buƙatar ki fara gudanar da bincike tun yanzu don akwai masu aiki da tsafi wurin sayar da abincinsu wasu ma naman mutane ko na jakai suke amfani da shi"
"Na gode sosai Papy " na faɗa ina murmushi kafin kuma na ƙara matsawa wurin Maheer,shi ma haka ya saki murmushi kafin ya ɗora bakinsa kan nawa.Na sakankance sosai ina jin ɗanɗanon yawunsa amma ya janye bakinsa tare da ɗan ture ni,cike da mamaki na dube shi da idona da nake jin sun fara yi min nauyi.Ya banko min wata harara kafin ya ce "me? Ba ki jin abin da kike son ji ba? To sai ki tafi ko iskancin kike so a ci gaba da yi miki?"
Ji na yi tamkar na ƙurma ihu,sannan kuma gefe ɗaya ina mamakin yadda aka yi kuma ya canza lokaci guda.Zuciyata na tuƙuƙi na fice na bar masa ɗakin,ina sauka aka yi sa'a Hajiya ba ta falo sai na wuce sashenmu sai Yasmine kawai na tarar.
Na ce "ina sauran suke?"
"Suna kitchen za su fara training wai" ta bani amsa,da sauri na fita zuwa can.Duk suka zubo min na mujiya musamman ma dai Lubna wacce ke yi min kallon tsaf,banza na yi da su a dole aka ci gaba da yin aikin bayan mun gama muka koma ɗaki.
A wannan ranar kafin mu kwanta sai da muka tattauna ni da Aliya a kan za mu yi bincike mu gano restaurant ɗin da suke aiki da tsafi.Ina kwantawa kuwa aka nuna min wani gidan restaurant har guda biyu,ɗaya na wata bazawara ne ɗaya kuma na Hajiyarsu nurse Fatee ce.
Washegari bayan mun yi sallah ban yi nauyin bakin bai wa Aliya labari ba,bayan ta gama saurare sai cewa ta yi" da buƙatar mu ziyarce ta tun yanzu ba wai sai gari yayi haske ba,kawai ki tashi mu tafi"
"Lubna yau da buƙatar ki je restaurant ki sayar da abinci,mu kuma za mu je leƙen asiri don muddin ba mu yi haka ba ƙila ba za mu yi nasara ba"na faɗa ina kallonta,don kuwa suna a wurin muke yin hirar.Ta ɗan kawar da kai kafin ta ce "okay"
Ni kuma da Aliya tamkar wasu ɓarayi haka muka saci hanya muka fice,layar da ke ɗaure a hannuna ita ce ta yi mana jagora har zuwa gidan da muke da burin zuwa.
Ba mu nemi izinin shiga ba,don babu mai gadi sannan ƙofar a rufe take ruf Aliya ce ta buɗe ta da ƙarfin ikonta.Muna shiga a daidai lokacin da matar ke buɗe wata ƙatuwar jaka ta fiddo wasu yara guda biyu ga kuma wasu daɓeɓiyar wuƙa,tana ganinmu ta saki wuƙar ta faɗi ƙasa yayin da jikinta ya ɗau mazari.
Tana shirin guduwa ta hanyar yin nata tsafin sai ga gwagon birina ya bayyana tare da matse mata wuya ya cira ta sama.Sai a lokacin muka ƙarasa na duƙa na kwance yaran waɗanda ke ta sharara bacci da dukkan alamu an yi amfani da hoda ne yayin kama su.
Ido na ƙura mata yadda take hawaye,murya cike da takaici na ce "sauke ta ƙasa ta yi min bayani" nan ya sauke ta ɗin,sai ta ci gaba da yin kuka irin sosai ɗin nan kafin ta ce "don Allah ku tausaya ki yi mini rai kar ku kira ƴan sanda,wallahi ni ma ba laifina ba ne.Tun ina budurwa Allah yayi ni da shegen kwaɗayi ,ban cika son abincin gidanmu ba saboda mu talakawa ne amma makwabtanmu masu kuɗi ne sosai wannan yasa nake shiga nake taya matar gidan aiki.Tare da ni ake cin abincin breakfast,na rana har na dare in ma ban zo ba haka ake aika min.Ban taɓa sanin ita da mijinta Mayu ne ba sai bayan na yi aure ne maitata ta bayyana,sai na fara farautar mutane ina damƙe kurwarsu a haka har na fara ajiye yarana na kaina.Su 2 na haifa amma ko da wasa ban taɓa tunanin cinye su ba sai ƴaƴan mijina guda uku waɗanda matarsa ta farko ta bari sune kawai na dinga ɗaukar ɗaya bayan ɗaya ina sayarwa domin na samu na ciyar da nawa da kuma kaina.Bayan duk na kashe su sai na tuba na bar wannan mummunan aikin,amma ba a ɗauki lokaci ba na ƙara komawa cikin ƙazamar harakar saboda an tambayo ni kuɗin haya wajen na wata takwas,ga kuma ba mu da abinci a ƙarshe kuma aka kore mu daga gidan.Wannan makwabciyar tawa ita ce dama na dinga sayarwa da ƴaƴan kishiyata,yanzu kuma sai ta bani shawarar na buɗe restaurant ina sayar da abinci wannan hanyar na kawo kuɗi sosai ka yi arziki. Da na ƙi shi ne ta cinye mini ƴaƴana, sai a wannan lokacin na ɗauki shawararta na soma saida sassan jikin ƴan adam .Tun a satin farko na fara ganin canji yadda kowa ke yabon girkina,haka na dinga samun cusmer waɗanda suke ikirarin ba su iya cin wani abinci in ba nawa ba.Da haka nake yi musu wulaƙanci ina kyararsu amma ba su taɓa hassala ba saboda na riga na tsafe su ba cikin kansu suke ba" Aliya ta yi saurin katse ta da cewa "su wannan yaran nufinki yanka su za ki yi ko me?"
"Eh! A'a! Dama duk kullum ina sakawa,ba ni ce ke zuwa ina kamo su ba akwai mai kawo min su har gida" ba ta ida rufe bakinta ba Aliya ta yi saurin ɗauko wuƙa ta jefa mata ita cikin baki har sai da wuƙar ta ɓullo ta ta can bayan wuyanta.
"Aliya me kika yi ? Kisan kai? Kin fa kashe ta " na faɗa ina kallon yadda jini ke yi mata zuba tana kuma ɗaukar rai.
A hassale ta ce "to me za a yi mata HAULE ? Kina fa ji a gabanki ta faɗa ta sayar da ƴaƴan kishiyarta,sannan kuma ƴaƴan mutane ne take amfani da su domin bunƙasa business ɗinta.Ai ko a musulunci an ce duk wanda ya kashe a kashe shi"
Na ce "amma ai ba mu ne ya kamata mu yi mata hukunci ba,sai ki bari mu miƙa ta ga hukuma .Yanzu ya kike so mu yi da gawarta? Kin san muddin aka tarar da gawarta za a iya tsananta bincike kuma muddin labarin nan ya fita ina mai tabbatar miki ko Lubna na iya tona mana asiri"
Aliya ta ce "ai sai in an ga gawar ko? Ki cewa protector ɗinki ya ɗauke ta ya je jefawa karnuka ita su ci" tana faɗar haka sai na ga shawarar ta yi ,ina gama basa umarni kuwa ya ɓace tare da gawar matar.
Na ɗauki yaro guda Aliya ma haka kafin mu fito,direct asibitin su Maheer muka wuce da su.Dr Umar muka gani muka damƙa su hannunsa,sai da na leƙa ɗakin da aka shimfiɗe Dr Muhamud har yanzu yana bacci.
Hanyar toilet na bi don yin buƙatata,ina buɗewa na ga nurse Fatee a zaune tana kuka yayin da gefen wuyanta kuma ke ta tsiyayar da ruwan ciwo.Ido na ƙanƙance ina kallonta,kafin kuma na taka na isa gare ta ba tare da na ce mata kanzil ba na kai hannu kenan zan taɓa wuyanta na ji an wani fizgo ni ta baya...... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
32
Maheer ne ya jawo ni baya kafin cikin wata irin murya ya ce "kar ki manta aikinki a yanzu shi ne ki tursasa duk wani marar lafiya ya faɗa miki duk wani sirrinsa,da kike ƙoƙarin kai hannu jikinta kin me zai faru da ke ne?"
Ido kawai na zuba masa na wani lokaci kafin kuma na maida dubana ga nurse Fatee wacce ita ma take kallona,ba tare da na buɗa baki ba na yi mata tambaya ta ido "me ke damunki?"
A daidai lokacin da na yi tambayar,a daidai kuma wannan lokacin ne idonta suka fara fitar da hawayen jini.Ita ma ta idon ta soma yi min bayaninta dalla-dalla,"ban san taƙamaimai me ke damuna ba,kamar yadda wani sa'in nake manta wace ce ni.Abu guda zan iya cewa shi ne a duk lokacin da nake kusa da Maheer ina jin sassaucin azabar da ke ratsa ɓargo da ruhina,ina jin duk wata damuwata ta tafi wannan dalilin yasa na ɗauki son duniya na ɗora masa don na lura cewa shi ne maganin matsalata wacce na yi shekara da shekaru da ita amma ban san mece ce ba.
Tun ina jaririya a cikin tsumman goyo nake da aboki,in na ce aboki ba ina nufin irin abotar da kika sani ba a'a tawa haramtacciya ce domin Abbana shi ne abokina.A kullum yana zuwar min ta mafarki,yayin da kuma a zahiri yake shafar wuyana kusan kowanne dare ba tare da yayi mini wani abu ba.Ɓangaren Momyna ma kusan hakan ce ke faruwa,tana mugun sona kuma tana ra'ayina ta sha faɗa mini hakan da bakinta amma ban taɓa tunanin da lalata take sona ba sai jiya da ta zo min ido biyu ba a mafarki ba.A gabana uwar da ta kawo ni duniya ta yi tsirara tana neman na taimaka mata,amma sai na yi tamkar ina bacci na rufe idona.Bayan fitarta ne na take mata baya sai dai kafin na isa ɗakinta hankalina ya kai ga ɗakin sirri na Abbana,a tsaye na gansa yana tsafi ya kafa hotona yana ikirarin saura kwana biyu kacal ya rage yayi amfani da ni ya bada jinin budurcina ga dodon tsafi.Haka na kwaso jiki na zo asibiti sai dai na kasa sukuni,babu inda nake jin daɗi in ba a cikin toilet ɗin nan ba"tana kawowa nan ta yi shiru sai aukin kuka.
Na ce "shi kuma ciwon da ke a wuyanki fa?"
"Sirrin arzikin Abbana ne,ya bayar da gangar jiki ga tsutsa ne saboda yayi arziki mai yawa.Duk kusan sati biyu sai Dr Maheer ya zuƙe min ruwan da ke ciki,ashe duk kusan a banza ne ina da sauran jan aiki a gaba" ta bani amsa.
Na ce "bayan wannan babu wani abu da kike ganinsa ba normal ba ne?"
"Akwai ! Ina ɗaukar tsawon lokaci ban yi period ba,a kuma duk ranar da zai zo mini yi nake kamar zan mutuwa sai Abba ya bani wani magani da zarar na sha shi kuma ban ƙara sanin abin da ke faruwa,in kuma na dawo hayyacina iya wuni guda kawai jinin zai yi ya ɗauke"
"Kina jin zafi ko ƙaiƙayi ?"
Ta girgiza kai kafin ta ce "a'a sai dai wani zubin sai na ji tamkar al'aurata ta canza tamkar wacce ta haihu alhalin ban taɓa sanin namiji ba"
Bayan na gama saurarenta sai na juya na dubi Dr Maheer,sai kuma ya haɗe rai yana mai cewa "ki taimaka mata ta fito ku koma can ɗaki sai a duba ta"
Ba tare da na ce masa komai ba na kama kafaɗar nurse Fatee muka fito tare da komawa can inda ya ce. Allura ya ɗauko ya haɗa jinina da nasa kafin ya je ya yi wa nurse Fatee ɗurensa a daidai cikin ciwon nata.
Da sauri ya ɗan ja baya sakamakon wani baƙin abu da ya soma fitowa kamar zare,ba tare da tsoro ba na matsa tare da ɗaukar wani almakashi na dantse abin sai na ga yana motsi da dukkan alamu baƙar tsutsa ce.
Haka na ida ciro ta daga cikin jikin nurse Fatee,tsutsar na da mugun tsayi sosai.Kan wani abu mai kamar faranti na ɗora ta kafin na tofa mata yawuna,nan take ta soma ƙonewa ta koma hayaƙi.
Dr Maheer ya samu auduga ya soma matsa wuyan nurse Fatee,duk wata ƙazanta ta ida fitowa sai ya naɗe mata wurin tare da bata umarnin ta kwanta,babu jimawa bacci ya ɗauke ta.
Ya dube ni kafin ya ce "ki je ki tashi Dr Muhamud,sannan ita kuma Fa'iza ki ɗauki mataki kanta"
Na ce "a'a babu wani mataki da za a ɗauka kanta tun da har ta iya faɗin gaskiyar komai ,sai dai ban sani ba ko zan bai wa Dr Muhamud ɗin shawarar ya canza matar aurensa ko ya samo mata wata abokiyar zama"
"Ke ma kina iya basa shawarar ya ƙara da ke tun da na ga alamu da dukkan alamu sonsa kike"
"Kar fa ka manta ni matar aure ce"
"To ai ba son mijin kike ba,hasali ma kin tsane shi"
"Duk da haka dai amma ai ba za a canzawa tuwo sunansa ba"
"Kenan dai a gaske kina sonsa?"
"Shi so ko da wasa aka furta shi to ba zai tashi daga matsayinsa ba" na basa amsa tare da juyawa da niyyar fita na ji ya kira sunana sak irin yadda kowa ke kirana.
"Haule?" cak na tsaya ba tare da na juyo ba,shiru bai ce komai ba kawai na fice ina jin takaicinsa wato shi a kullum nuna mini yake ni ce ke sonsa shi ko oho.
Ɗakin da Dr Muhamud ke kwance na shiga,kallo ɗaya na yi masa na fahimci powersa kusan iri ɗaya ce da ta Aliya,hakan kuma na nufin ita ce za ta iya fiddo shi daga wannan balaguron ruhin da ya lula.Ina nan tsaye kuwa ta shigo tana mai cewa "an samu yaran can sun farfaɗo sai dai sun ƙi magana,ya kamata mu kai su gidan radiyo"
Ba tare da na bai wa abin da take faɗa muhimmanci ba ne ce "mene ne za ki yi masa ya farfaɗo?"
"Kina sonsa har haka HAULE?" Aliya ta jefo mini tambaya cikin wata irin murya mai sanyi.
Na ce "eh ai kin..." sauran maganar ce ta maƙale mini a maƙoshi ganin Maheer a tsaye ya jingina ga katangar ƙofar shigowa.Aliya ta juya ta kalle shi kafin kuma ta matsa kusan gadon Dr Muhmud,wasu abubuwa ta yi masa sai ga shi ya farka .Ɗaya bayan ɗaya ya kalle mu da idonsa waɗanda suka sauya daga na mutane zuwa na wata halitta can daban,muryarsa ba ta fita sosai ya ce "Fa'iza? Ni kika tsafe kika asirce?" sai kuma ya shiga yin magana cikin wani irin yare ba a ɗauki lokaci ba kuwa sai ga matarsa Fa'iza ta shigo kamar wata karya tana kuka haɗi da haushi.
Dr Muhamud ya ƙyalƙyace da dariya yana mai cewa "kin san wane ni ? Kin san wa kika taƙilo? Yau sai na kashe ki" ya furta haka tare da diro kan ƙafafunsa da kuma hannuwansa tamkar yadda dabbobin daji ke yi.Da wani mugun sauri Aliya ta shiga tsakaninsu tana kiran Dr Muhamud da wani suna wanda ba nasa ba da muka sani "Machi? Kar ka taɓa ta,kar ka yi wannan kuskuren ko ba komai ita ce ta yi silar buɗe ɓoyayyar idaniyarka ta uku"
"Evaliya? " shi ma ya furta kafin kuma su shiga yin wani yare da su biyu kawai suka san me suke cewa,can kuma Dr Muhamud ya miƙe tsaye yana karya wuyansa yana fitar da sautin ƙas.
Ya dube ni kafin ya kalli Maheer ya ce "na san Evaliya tun wasu shekaru da suka gabata,a lokacin ina ɗan jinjirina kafin iyayena sun tsince ni su wanke mini duk wani dattin ruhawaniya su mayar da ni ɗan wannan duniya.Yawan karatun Alkur'ani da kuma yadda suke gidan malaman sunnah yasa na manta wane ni amma yanzu na tuna.Ni ɗin ba ɗansu ba ne,mutum ne ni mai ɗauke da rigar aljan.Cikin jeji aka haife ni ,mutanen ɓoye suka fara rainona kafin su cillo ni wann duniyar shi ne har wata ta samu galaba a kaina" ya ƙarashe furicin yana mai matse wuyan Fa'iza,tsabar firgici yasa ta suma nan take sai da aka bata agajin gaggawa kafin kuma Maheer ya tisa ƙeyata mu nufi motarsa,Aliya ta zauna a baya ni kuma a gaba.
Muna tafe ne take basa labarin abin da ya faru da yaran nan biyu,da kuma yadda ta kashe matar kai tsaye.Ran Maheer ya ɓace sosai ya ce "me yasa kika yi saurin kashe ta ba ki bari aka ɗanɗana mata launukan azaba ba? Da a ce hannuna ta shigo na rantse miki cikin tukunya zan saka ta na dafa ta da ranta.Ban san me Mayu suke ji ba suke cin naman ƴan uwansu,amma na ....." ƙiiiiii! Ya fara ƙoƙarin jan burki kafin kuma ya tsaya cak daidai nan kuma wani ya faɗo jikin motar tamu.
Da sauri duk muka fita, Maheer ne ya ɗago shi .Kansa ya fashe yana fitar da jini sannan kuma ya suma,dakyar ya ja shi ya saka shi a mota kafin kuma mu shiga mu sake komawa can asibiti.
Maheer da kansa yayi masa aiki kafin ya bamu damar shiga ni da Aliya,na ɗan nutsu ina kallon matashin kafin na juya na kalli Aliya na ce "wannan fa da alamu ruhinsa a ɗaure yake"
Ta ce "eh to kusan haka ne,kin ga kamar ana farautarsa dai" Aliya na rufe baki muka ji wani irin yanayi ya ratso ɗakin.Ƙila su ba su taɓa sanin irin yanayin ba ko kuma ba su san me haka ke nufi ba,da sauri na ce "wane ne ya shigo babu gayyata? Ko ma wane ne ya bayyana kansa kafin ni na binciko shi" ina gama faɗar haka sai muka ji wani abu fuuuu alamun an fita da gudu.
Na ja ajiyar numfashi kafin na dubi Maheer na ce "da buƙatar mu ceto mutumin nan kafin su haukata shi,kana ga duk da mu uku ne wannan ruhin mai bibiyarsa sai da ya samu zarrar shigowa nan.Kana ganin yaushe zai iya farkawa?"
Aliya ta ce "in dai haka ne kawai mu tashe shi"
Maheer ya ce "in kun gama ku kira ni akwai aikin da zan yi" yana shirin fita na tsayar da shi na ce "amma don Allah in akwai kyandir ina so da kuma farar hoda"