Bakin ruhi complt by mrs sadauki - Chapter 26
Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 26: Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 26. Yayi wata irin kururuwa wacce ta girgiza kaf illahirin…
4,472 words
Yayi wata irin kururuwa wacce ta girgiza kaf illahirin gidan,yayin da duk wani abu da ke na kwalba ya tarwatse ,bangon ɗakin ma wanda muke ciki haka ya tsage.
Da jajayen idonsa yake kallona kafin ya soma bajewa kamar wani hayaƙi yana bin iska,a daidai lokacin da BAƘIN RUHI ya mutu a daidai wannan lokacin ne kuma iyayenmu maza suka shigo ɗakin suna furta "Babaaa???" dakyar na ware idona na ga Kakana Nalado cikin jini yana kakarin mutuwa.
Muryarsa ba ta fita sosai yake cewa "Ibrahim na cire ka a cikin jerin ƴaƴana tun da har ka haifi annoba wacce ta yi silar mutuwata ta gaske sannan ta fitar da ruhin da ke bani duk abin da nake daga cikin gangar jikina.Ka sani ba zan taɓa yafe maka ba sai ka yi abu ɗaya tal ka maido da *BAƘIN RUHI* duniyar nan ka tarwatsa kaf zuri'ar Maitama,cikin jikin Haule kuma a cire shi ban ƙaunar haɗa jini da shi"shine furucinsa na ƙarshe wanda yayi daidai da soma fitar duk wani ƙarfin iko daga jikina yana koma can tushensa kamar yadda baƙin ruhin shi ma ya tafi can.
Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti, Innarmu na gefena yayin da nurse ke saka mini ƙarin ruwa. Innarmu ta saki murmushi ta ce "Haule kin tashi?"
Kai na jinjina mata alamar eh,sai ta furta "alhamdullah" haka na tsaya a kwance har sai da ƙarin ruwan ya ida sannan aka sallame mu muka nufi gida.
Tun da muka karyo layinmu na ga mutane sun cika wurin,haka muka ratsa muna ƙoƙarin shiga gida aka fito da gawar Kaka Nalado wanda tsofin garin ne suka ɗauko makarar suna tafe suna yin waƙoƙin tsafi.
Har zan kawar da kai sai kuma na ji Kawu Hamza na cewa "kar ki saki ki ƙara tako ɗaya don ba za ki shigar mana gida ba da cikin muguwar zuri'a ba"
Na tsaya cak ina kallonsa,nan kuma sauran ƴan uwansa suka taso su ma duk suka tsayu kan ra'ayinsa ina ji ina gani suka hana ni shiga har sai da Abbana ya zo ya ce "ina bada shawara a matsayina wanda Baba ya bar ma wasiyya cikar burinsa da ku bar surukar Maitama ta shiga gidan nan,ko ba komai ita ce makamin da za mu riƙe don cimma burin mahaifinmu " da kallo mamaki na bi Abba wanda yake jefo mini kallon tsana mai cike da son ɗaukar fansa, Innarmu ta ja ni zuwa ciki yayin da zuciyata ta kasa daina rawa fahimtar da sauran rina a kaba,zaune ba ta same ni ba.... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
39
Muna shiga ciki direct ɗakin Innarmu muka shiga,har bakinta ke rawa wurin tambaya ta "Haule me ya faru a ɗakin sirri?"
"Babu komai Inna kawai dai na mayar da BAƘIN RUHI duniyarsa wanda yayi dai da mutuwar Kaka Nalado kuma iyayenmu maza sun shigo sun gani shi ne Kaka ya ce wai Abba ya san yadda zai yi ya tarwatsa ahalin MAHEER"
"Da kika soke shi da wuƙa a ina ne kika daɓa masa ita?"
"Ga bayansa"
"Da matsala Haule,kin ga da ace a ciki ne ko a saitin zuciya to da ba zai taɓa yarda ya dawo duniya ba.Amma bari na duba na gani ko da kwai abin da ya kamata mu yi kafin lokaci ya ƙure " ta faɗa tare da fiddo wani ƙaton littafi shi ma mai hoton dodanni.
"Lissafa mini siffofin shi dodon wanda Kakanki Nalado ke dakon ruhinsa" Inna ta umarce ni nan na shiga yi mata bayani dalla-dalla har na gama sai ga shi kuwa ta binciko hotonsa.
Bayaninsa ta soma karantawa har ni ma ina ji,yadda tsarin yake ko da dodon zai sake dawowa a duniya a karo na biyu to ba zai zauna a jikin wanda ya taɓa haifar ɗa ba,sannan mutum ne zai je can dajin sirri ya jawo shi izuwa gare shi.
Bayan mun gama karantawa sai na ja ajiyar zuciya na ce " kenan in haka ne Abba ba zai taɓa yin nasara ba,kuma kin ga iyayenmu maza ma duk suna da ƴaƴa"
Innarmu ta ce " ai suna iya nemo wani Haule,ni dai burina shi ne mu kamata yayi mu je nemansa kafin su rige mu zuwa sannan da buƙatar mu jira zuwan Aliyu mu kwatanta masa yadda abubuwan nan suke da illa"
Ambaton sunan Yaya Aliyu yasa gabana faɗuwa don kuwa a yadda na gansa tare da su Boss tsaf zai iya yarda ya ɗaukar wa kansa jidali. "Innarmu yaushe Yaya Aliyu ya canza daga mutumin kirki zuwa irinsu iyayenmu maza? Shi ne fa Jagaba na ƙungiyar baƙin ruhi,kuma wai ni ce excelency hum"
Shiru Innarmu ta yi tana nazari kafin ta nisa ta ce "Allah ya bamu nasara ,bari na kawo miki abinci"
"Innarmu me zai hana mu haɗa kayanmu mu tafi?"
"Babu inda za ku je,in kin ga kin sake fitar da ƙafarki waje to ki tabbata banda rai ne Haule.Ke da komawa cikin zuri'ar Maitama sai kuma a lahira in kun haɗu,ke kuma ina mai gargaɗarki da kar ki saki ki yi kuskuren saka hannunki akan lamarin da bai shafe ki ba" ya nuna Innarmu yana wani irin watsa mata harara,sai na ga ta sunne kai ban san dalilin da yasa har yanzu tsoronsa take ji.Bayan ya fita ne ta ce "ki fara shirin karɓo dukkan power ɗinki a karo na biyu don zaune ba ta ganmu ba,sannan ina so ki san yadda za ki yi ki raba ta gida biyu ki bai wa mijinki wani kaso don da buƙatar ya tsaya kusa da ke sannan hatta ciwon da ke cikinki a yanzu jininsa dai ne zai warkar miki da shi"
Shiru na yi ina shirin magana Abba ya shigo ashe laɓe yake yi mana,wani makirin murmushi yayi kafin ya ce "da kyau! To ki sani yau Haule za ta bar wannan ƙasar yanzun nan ba sai gobe ba zan tura ta makaranta ta ci gaba da yin karatunta,dakon BAƘIN RUHI kuwa ita ce nan za ta ɗauke shi a yayin da ya ratsa gangar jikinta ya shiga na sadaukar masa da jinjirin cikinta matsayin hadiya" yana gama faɗar haka ya wani cakumo ni ya fito da ni waje,can ɗakinsa na baraya ya kai ni wani turare ya shaƙa mini wanda yasa na fita daga hayyacina ko da na farka a wani wajen na tsinci kaina.
Dakyar na iya tashi zaune na ƙarewa wurin kallo,ya fi kama da asibitin gargajiya don ga kwalaban magunguna,da kuma ganyayyaki nan birjit.Ina a haka wani dattijo ya shigo fari tasss da shi,kana ganinsa ka ga Bature .Cikin wani Yare tun na ƙarnin baya yayi mini magana amma ban gane me yake faɗa ba,can ya canza harshe zuwa French ya ce "ki aje esprit ɗinki wuri guda a yayin da nake yi miki Yaren duniyarki,za ki ga sarai za ki tuno da kin taɓa iya shi" yana gama faɗar haka ya canza harshe,sai da na nutsun ɗin kamar yadda ya ce sannan na fahimci abin da yake cewa ɗin.
"Mahaifinki ya kawo ki wannan makarantar ne,za ki ci gaba da karatunki na boko da kuma na duniyar Ruhaniya.Ya bada amanar ki ne a hannuna,shawarar da zan baki kar ki ma gwada tserewa don an zuba matakan tsaro ta yadda ba ki tunani, muddin na same ki da wannan laifin zan yi miki hukunci fiye da yadda kike tunani kin fahimta?" ya jefo mini tambayar daga ƙarshe,na jinjina masa kai alamun eh duk da cewa a ƙasan zuciyata ƙarya ne ina da burin tserewar.
Wasu magunguna ya bani na sha sannan ya buɗe ciwona ya zuba mini magani ya kuma rufe shi.Bayan nan sai ya ja ni muka fito harabar makarantar wacce take maƙil da students maza da mata har da ma waɗanda suka manyanta.
"Za ki je ki duba ko ina na makarantar ne ko kuwa hutawa za ki yi?" ya tambaye ni, kallonsa kawai na yi ba tare da na ce komai ba.
"Nadia?" ya ƙwala kiran wata budurwa wacce take tsaka da nunawa ƙawayenta nata salon tsafin,da sauri ta zo ta ce "na'am Mentor "
"Wannan Haule ce ki je ki zagaya da ita sannan ki nuna mata ajinku,ki ɗauke ta matsayin ƙawarki" ya faɗa yana wani shafar gashin bakinsa.
Nadia ta ce "to Mentor,mu je" ta kama hannuna tare da ja na,muna tafe a haka ta jefo mini tambaya "cikin jikinki an yi miki fyaɗe ne ko kuwa saurayinki wanda kike so yayi miki shi"
Da mamaki ta yadda aka yi har ta san ina da ciki na ce "ke ya aka yi kika san ina ɗauke da ciki"
"Ga hannunki cikin nawa shine kuma sai na kasa sani?"
"Gaske har da tsafi ake koyawa a makarantar nan?"
"Eh sosai,ni ma duk a ciki na koya ai"
"Iyayenki ne suka saka ki?"
"A'a kwaɗayina dai"
"Kamar ya kwaɗayi?" na tambaye ta a daidai lokacin da muka iso daidai wurin swimming pool ɗin makarantar.
Nadia ta yi tsaye tare da ɗaukar dutse ta cilla cikin ruwan kafin ta ce "kamar yadda kika ji sunana Nadia,shekarata ashirin da huɗu ina zaune a Libreville,labarina da zan baki bai da daɗi sam silar kwaɗayina lafiyar ƙwaƙwalwata ta taɓu yayin da kuma na rogaza gobena.Farkon lamarin ya faru a shekarar bara da na ci dambun kuturu na soma yaƙar talauci ta kowacce hanya a dole sai na yi kuɗi.Ni ɗaliba ce a University ɗin marayu,kasancewar na taso cikin maraici banda iyaye.Wata rana wata ƙawata ta bani labarin wani cele man da ke taimakon matasa domin cika burikansu,sunansa Jonas matashi ne mai ji da ƙurciya da kuɗi.Yana zuwa har nan University yana kawo taimakon abinci,ga waɗanda suke sha'awa kuwa har restaurant yake basu damar zuwa.
Ta ce mini in ina so zan iya zuwa ya taimake ni,da farko na ji tsoro amma yadda take zuzuta wutar taimakonsa yasa na amince,ta ce babu ruwansa yana iya ba mutum har 500k ba tare da ya nemi wani abu ba,tun daga maza har mata.
Lokacin da muka haɗu da Jonas sai na cika da mamaki a kallon farko da na yi masa na hango wani ɓoyayyen sirri a tattare da shi kamar dai wani malami mai aiki da aljanu ko ruhika haka.Sai kuma na ji yana zancen Bible da kuma bayanin duniyarmu da kuma ta Ruhaniya,gaba-gaba kuma sai ya canza yare zuwa na mutanen farko.A cikin ƴar hirar da muka yi ne ya ce mini ruhikan haske na gaske suna wanzuwa ne ta silar jini ba wai baiwa daga sama ba.Sam ban fahimci abin da ya ce ba,amma na watsar ganin ya bani kuɗi masu yawa kamar yadda na zo neman taimako.Tun daga lokacin muka zama kamar wasu ƙawaye ni da Jonas har na fara sonsa,wata rana sai ya bani wani zobe da aka ƙera da ƙarfen yin kuɗi,zoben baƙi ne siɗik bayan na saka shi a yatsana sai yayi mini bushara da cewa muddin na barsa a hannuna babu abin da zai iya samuna,amma kar na saki na cire shi.
Tun daga wannan lokaci kuma sai na koma ƙarƙashin kariyarsa,ya fitar da ni daga makarantar marayu ya saka ni ta ƴaƴan manya,sannan ya sayi gida ya zuba mini ƴan aiki masu kula da ni,sabbin kaya yawan shopping haka kullum yake yi mini su kamar wata sarauniya. Kwatsam wata rana ya ce mini zai yi tafiya domin wani taro na gamayyar kungiyoyin kuma so yake mu tafi tare na yi masa rakiya.Ya shaida mini cewa in na yi masa wannan rakiyar zai zamanto babban alkhairi a rayuwata.Sai kawai na yarda na bi shi,haka muka tafi har muka isa wani gida wanda ke tsakiyar daji babu komai sai ciyayi masu ƙamshi wurin yana da kyau sosai. Daga cikin wannan ɗaki akwai keɓaɓen wuri da aka yi wa penti ja haɗi da wasu alamomi na zanen ido da maciji.
Tsaya na yi ina kallon mutanen da ke a tsaye suna jiranmu,maza ne guda bakwai kowanne ya saka garkuwar fuska mai ɗauke da hoton dabbobi,na farko zanen Kada,na biyu maciji,na uku Giwa,na huɗu Mujiya,na biyar Biri,na shidda ɗin kuma Dragon ne.A tare suka kira ni da suna guda Mace mai jan ruhi. Daga nan kuma sai suka fara yin waƙe-waƙe cikin Yaren ƙarnin baya da ya gabata,can kuma Jonas ya kalle ni yana wani murmushi ya ce "kin shirya? Abin da zan baki a yau shine rigar kariyar mutuwa ce daga wannan ƙungiya tamu,amma sai kin yarda cewa daga yau ruhinki ba naki ba ne"
Ban iya cewa komai ba sai suka zaunar da ni tare da ɗauki wata baƙar kaza suka cire wuyanta,da jininta ne suka yi amfani wurin yi mini rubutu a ciki daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba.Lokacin da na dawo hayyacina tuni gari ya waye,ni kaɗai ce a ɗakin zobena ya dinga yin haske kamar ƙwan fitila.Sa'ilin da na tashi na yi tsaye gaban madubi sam babu alamun inuwata a ciki,da na nace kuma sai na hangi wasu idon a bayana tamkar wani ruhi dai ne ke rayuwa a cikin gangar jikina.A ranar Jonas ya zo ya maida ni can gida,tun daga wannan lokaci kuma wani sabon babin rayuwa mai daɗi ya buɗe mini na samu aiki ba tare da na gama karatuna ba,haka kawai sai mutane su dinga yi mini kyautar bazata sai dai matsalar shi ne da zarar dare yayi haka zan dinga jin wani kiɗa marar daɗi tare da amon gurɓataciyar murya suna faman jadadda mini "ruhinki namu ne! Ruhinki namu ne"
Kwatsam wata rana sai zobena ya ɓata wanda Jonas ya bani,a cikin wannan daren sai jikina ya soma yin wata kyarma da mugun ƙarfi.Sai ga Jonas ya bayyana a cikin ɗakina alhalin bai ma ƙasar,"kin karya alƙawarin alaƙa,ki shirya za su zo su tafi da ke" shi ne abin da ya faɗa kafin ya ɓace tun daga wannan lokaci na shiga uƙuba haka zan dinga ganin tsintsiya na shara da kanta,in na kunna tv sai ta dinga canza channel da kanta tana nuno mini abubuwan horror,haka zan dinga jin ana dariya haɗi da taɓi a cikin gida.A dole so ake a haukata ni, babu shiri na bar gidan na fito kan titi kamar wata zautata cikin irin haka ne na haɗu da Mentor shi ne ya kawo ni wannan makarantar tun daga wannan lokaci kuma komai ya dawo normal na rayuwata,sai kuma na fahimci dayawan mutane masu cewa za su baka taimako amma sai sun saka wani sharaɗi na daban ko su ce ka tura hotonka ko watan ranar da aka haife ka,ko kuma dai wani abu da ya danganci mallaki"
"Amma me yasa ba za ki koma can inda kika taso ba?" na jefa mata tambayar lokacin da muka gusa muka isa wani wuri mai cike da flowers. Maimakon ta bani amsa sai ta jefo mini tambaya "cikin jikinki na wane ne?"
"Me yasa kike son sani?" "Kawai dai! Kuma ƙila da taimakon da zan iya yi miki ke da shi don na ga tamkar kuna cikin tarko mai wuyar fita"
A cikin kalaman Nadia na ji ƙamshin gaskiya, wannan yasa na bata amsa kai tsaye "na mijina ne" sai na saki murmushi kuma saboda shauƙin son MAHEER da ya tsira mini.
Ta ce "amma me yasa aka raba ku aka kawo ki nan?" Nadia ta tambaye ni.
Na ce "labarin nada tsayi sosai,faɗa mini mene ne burinki game da makarantar nan?"
Ta kalle ni na tsawon lokaci kafin ta ce "burina bai wuce na canza wata baƙar aƙida ƙwaya ɗaya tal ba..."
"Nadia?" muryar Mentor ta katse ta,a tare muka juya sai yayi mana alama da hannu da mu zo da sauri muka nufe shi.
★A can ɓangaren MAHEER kuwa gida suka dawo shi da Aliya da niyyar za su ƙara dubawa su ga me ya dace su yi. Direct part ɗinsa ya wuce,wanka yayi ya canza kaya kafin ya ɗauko kayan Haule da ya taɓa cire mata ya saka mata nasa.Kan fuskarsa ya ɗora rigar yana shaƙar ƙamshinta yana jin wani feeling na bijiro masa haɗi da muguwar ƙaunarta.
Ya shagala sosai cikin shauƙi kawai ya ji hannu a saman jikinsa,da wani mugun sauri ya zabura tare da tashi zaune.Dama bai kashe ƙwan lantarki ba, da Ikilima yayi tozali jikinta har rawa yake ganinsa a cikin halin da ba taɓa gani ba sai a tunani ko a mafarkin da ta saba jawowa kanta tsabar fitina.
Ransa a mugun ɓace ya wanke ta da mari,amma tsabar ba ta cikin hayyacinta sam ba ta damu ba burinta guda kawai ta same shi su zama abu ɗaya wannan yasa ta soma ƙoƙarin warware ɗaurin rigar baccinsa.Sai da yayi mata mari na biyu ne ya hankaɗata can gefe kanta ya bugu ga didilin gado sannan kawai hankalinta ya dawo jikinta,murya na rawa take roƙonsa kan ya kusance ta saboda ita ɗin matarsa ce.
Rai a mugun ɓace ya ce "wai Ikilima hauka ne kike yi ko me? Wace irin giyar maye ce kika sha haka ? Wallahi in ba ki fitar mini daga ɗaki ba zan yi miki mahaukacin dukan da ba za ki sake taka ƙafarki ba in kuma kin yi gardama to mu zuba mu gani" ya faɗi haka tare da nufar ƙofar toilet amma da yake rabon wahala ce da ita ta riƙe ƙafarsa tana mai cewa "don Allah Baby ka taimaka ka rufa mini asiri na sha kayan mata ne na yi tunanin za ka kusance ni a yau" da ɗayar ƙafar tasa ya yi amfani da ita ya shure ta sannan ya taka ƙafarta yana cewa "jarababiya , wallahi ko mutuwa za ki yi ba zan taɓa zama ɗaya da ke ba ballagaza kawai"
Idonta na zubo da hawayen tausayin kanta ta ce "tabbas MATAR SHIGE( Saadiya Abdulrazaq) ba ta daraja amma ban taɓa tunanin a yadda muka jima muna soyayya za ka iya yi mini haka"
MAHEER wanda ya taɓa handle ɗin ƙofa ya juyo da sauri ya ce "ke da uban wa kuka yi soyayyar?"
Kamar suɓutar baki kuwa ta ce "ni da uban mai magana".... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
40
Da wata irin azama Maheer ya zo ya dinga ball da Ikilima ina jibgarta kamar ya samu jaka,bai taɓa sanin yana da siffa nan ba sai kuma a yanzu da ya soma jin idonsa na juya tafin ƙafafunsa na wani irin ɗaukar sanyi kamar ƙanƙara.Bai tantance ba ya rikiɗa ya zama maciji irin ƙaton nan na cikin ruwa,hankalin Ikilima kasa ɗaukar wannan lukutar masifar ta yi kawai ta suma a nan take.
Yayin da shi kuma MAHEER yayi amfani da bakinsa ya ɗala mata wani mahaukacin cizo a leɓenta na ƙasa.A hankali ya soma tafiya silululu har ya isa bakin mirror yana kallon kansa yadda ya rikiɗe ya zama macijin nan jawur da shi kamar jini.
Tamkar mayen ƙarfe haka yake jin wani abu na zuƙo maduban idonsa a cikin mirror ɗin,a cikin daƙiƙar da ba ta fi biyar ba shuɗaɗiyar rayuwarsa ta baya wacce ita ce silar halin da yake a ciki ya ziyarci kwanyarsa.
Internship/stage wanda a Hausa za a kiransa da gaɓar koyon aiki,shi ne silar canza rayuwar Maheer daga normal mutum zuwa mutum mai duniya biyu Ruhaniya da kuma zahiriya. A shekarun da suka gabata bayan sun yi shekaru biyu suna gwagwarmaya koyon aikin likitanci sai aka tura su wasu yankin da ke cikin ƙasarsu domin samun wayewa da kuma koyon aikinsu .
Ƙauyen Taguje,shi ne ƙauyen da aka kai MAHEER tare da wasu ɗaiɗaikun ɗalibai.A ranar farko da suka isa a ƙauyen direct gidan Maigari aka sauke su,bayan an basu masauki Maigari ya rabbato musu dokin ƙauyensa.Ba a duba madubi da dare,ba a yin busar fito da dare,haka kuma in mutum na son wanke kayansa an keɓance ranakun da ake zuwa tabki domin ɗebo ruwa ko kuma mutum ya je can ya wanke,yayin da kuma sauran ranakun an haramta tunkarar hanyar tabkin ballantana ma a je kusa da shi.
A yayin da Maigari ke wannan jawabin sai Maheer ya ji abin kamar abin tsafi wannan yasa bai yi nauyin bakin tambaya ba,"in kuma mutum ya kuskure ya je a ranakun da aka hana me zai faru da shi?"
Wani irin kallo Maigari yayi masa kafin ya basa amsa da "akwai haɗari mai girma a tattare da wurin,zai fi kyautatuwa dai ku kiyaye dokokin ba wai bincikar dalili ba"
Da yake Maheer yana cikin irin mutanen nan da ba su cika yarda da abubuwan almara ba sai cewa yayi "ko kawai dai camfin da kuka saba yi ne? Amma ai babu Aya ko hadisi da suka taɓa magana akan haka"
Maigari ya ce "a'a yarona,kai dai ka kiyaye kawai" ita ce maganar Maigari ta ƙarshe kafin ya bar wurin. Kwana biyu bayan zuwansu MAHEER ya fara aiki a wata ƴar ƙaramar asibiti da ke nan kusan gidan Maigari,tun ranar farko ya soma ganin abubuwan da sam ba su dace da tsarin hankali ba.Dare na yi duk fitilun asibitin aka kashe su aka kunna fitila aci balbal kamar yadda mutanen ƙauyen su ma da ita suke amfani.Shiru yayi yana nazarin abokan aikinsa yadda duk suka fara wani ɗari-ɗari,aikin ma kamar a tsorace suke yinsa.Yana cikin wannan nazari ne aka kawo wani tsoho a asibitin,ya galabaita sosai ta yadda dakyar yake numfashi ma.Kusan babu likitan da ya zo da sauri ya tarbi tsohon kamar yadda ake yi wa patient,Maheer kuwa mai zuciyar tausayi shi ne ya soma kula tsohon ya fara basa taimakon da ba a rasa ba kafin kuma ya dinga tambayar manyansa suna faɗa masa abubuwan da ya kamata yayi.Tsawon daren nan dai akan tsohon nan ya ƙare,sai wuraren sallar asubah kawai ya samu komai ya dawo normal.
Maheer na shirin fita tsohon ya tsayar da shi ta hanyar kamo hannunsa,ya juyo da sauri suna kallon juna nan ne ya lura idon tsohon babu ɗigon baƙi ko kaɗan duka fari fesss kamar madara.
"Kar ka ji tsorona,zan taimake ka kamar yadda ka taimake ni.Sai dai kafin nan ina so ka sa a ranka ka yarda tabbas akwai abubuwan magic da almara a zagaye a wannan duniyar.Ni nan da kake gani babban mugu ne,kusan kowa ya sanni a garin nan shi yasa ka ga babu wanda ya kula ni sai kai kaɗai kai ma don kana baƙo ne.A kullum fatan mutuwa suke yi mini,saboda ban taɓa aikin alkhairi ba amma yau ta silarka zan fara yinsa kuma a kanka.Ungo wannan " ya faɗa tare da miƙawa Maheer wani busashen goro wanda aka ci aka rage,ba tare da ya musa ba ya karɓa amma sam bai da niyyar ci.
"Ka tabbatar ka ci wannan goron,zai kare ka daga sharrin miyagun wannan ƙauye waɗanda idonsu tun tuni suke kanka saboda tambayoyin da ka yi wa Maigari da kuma ƙoƙonton da ka saka a ranka" tsohon ya sake faɗa.
Maheer ya ce "kenan kana nufin duk abin da Maigari ya faɗa gaskiya ne?"
"Eh babu shakka! Ko dai makaho ne kai? Ba ka ga yadda idona suke fari tasss ba?"
"A'a ba makaho ba ne ni,sarai na ga yanayin idonka kuma ban yi mamaki ba saboda halittar Ubangiji da yawa take" Maheer ya faɗa .
Tsohon yayi wata dariya kafin ya ce "sai dai fa a ƙauyen nan mutane sune gaba akan alhakin canza halittunsu,amma na san da sannu za ka fahimci komai don na san dole su neme ka"
Da ɗan mamaki MAHEER ya ce "su wa?" bai basa amsa ba tsohon ya soma jan numfashi yana yin wani irin girgiza kamar a mafarki a gabansa ya rikiɗe ya zama aigle 🦅 tare da buga fukafiki ya bi ta window ya fice. Wani irin bugawa zuciyar MAHEER ta yi da sauri ya ja da baya yana waro ido,dama lokacin tashinsa yayi bai faɗawa kowa abin da ya faru ba haka kuma babu wanda ya tambaye shi ina tsohon da ya yi wa aiki goron da ya basa kuwa cikin aljihun rigarsa ya jefa shi.
A saman hanyar komawa can gidan da Maigari ya basu haka MAHEER ya dinga jin alamun kamar wani na take masa baya sai dai babu kowa da zarar ya waiga.A haka har ya isa,yana shiga ya tarar da an yi bahaya a bakin ƙofar ɗaki wani ma har ya ɓata takalminsa waɗanda yayi wanka ya bar su nan.
Waje ya fita ya samo wani yaro ya wanke wurin sai ya biya shi,sai a lokacin kuma ya buɗe ɗakin ya shiga.Kan shimfiɗa ya kwanta yana tunanin abin da ya faru da shi a asibiti ,a haka bacci ya ɗauke shi sai ya soma mafarkin tsohon nan yana yi masa murmushi tare da ce masa "gwara da ba ka kwashe kashin nan ba da kanka,inda ka yi haka to tabbas ina mai tabbatar maka da ka tabka uban kuskure" yana gama faɗa masa haka sai ya farka,duk da haka MAHEER bai ɗauki abin da muhimmanci ba.
Yunwar da yake ji ma har ta fi damunsa fiye da tsafin da tsohon yayi a gabansa,jakar da ya zubo abubuwansa ya buɗe tare da fiddo cake ya ci ya kuma sha ruwan awa. Yana nan zaune abokan karatunsa suka dawo su ma aka shiga yin hira kowa na bada labarin ranar farkonsa a cikin asibiti amma banda Maheer wanda ya kafe wuri guda da ido.Ba komai yake kallo ba face wata tsuntsuwa baƙa ƙirin da ta yi tsaye cak wuri guda tana kallonsa da jajayen idonta.Shi ma ƙurin yayi mata,yana tunanin idon nan kamar ya san mai irinsu sai dai ya kasa tunawa.Sai da tsuntsuwar ta gaji don kanta sannan ta tashi ta tafi,shi ma sai a lokacin ya maida hankalinsa wuri guda aka ci gaba da yin hirar da shi sallah kawai ke tashinsu daga wurin.
Da dare bayan sun gama sallar isha'i suna zaune suna yin hira kawai suka dinga jin saukar faɗuwar abu a ƙasa.Kasancewar dare ne kuma babu wani haske sosai sai MAHEER yayi amfani da fitilar wayarsa ya haska,sai dai abin da ya gani ya kusa saka wayar suɓucewa daga hannunsa.
Ƙundulalin kawunan irin tsuntsuwar ɗazu ne zube birjit a ƙasa kamar an yi ruwansu,duk kowanne kai yana zubar da jini.A lokacin ne MAHEER ta ɗauki lamarin a gasken-gaske don yana mamakin ta ya aka yi duk kawunan tsuntsayen suka diro gidansu kuma ta sama? Sannan me yasa kafin hakan ya faru sai da irin tsuntsuwar ta zo har inda yake? Sam bai tsaya sauraren abin da abokansa ke faɗa ba ya nufi ɗaki.