Baqeer complete - Chapter 2
Baqeer complete Chapter 2: Baqeer complete Chapter 2. Duk da faɗan da ta rufeta dashi bata saduda ba sai da ta ƙara cewa "Amma sai naji kamar kun ce Baqeer…
3,369 words
Duk da faɗan da ta rufeta dashi bata saduda ba sai da ta ƙara cewa "Amma sai naji kamar kun ce Baqeer yana asibiti, dan Allah ku taimake ni ku faɗa mini ba hakan bane ko hankalina ya kwanta, yau tunda Baqeer ya fita bai dawo ba bayan hakan ba sabon shi bane." ta ƙare maganar cikin rawar muryar da tashin hankali ya gama kassarawa. Har Jamila ta buɗe baki zata cigaba da zazzaga mata masifa sai Abu ɗaya kishiyar tasu ta ɗaga mata hannu alamar tayi shiru don haka Jamilar taja bakinta ta tsuke sai dai ranta fal ƙuna taso Abu ta ƙyaleta yau ta zazzaga mata rashin arziƙi saboda yadda tafi jin haushinta da kishinta akan Abu ganin yadda mai gidan ya ɗauki dukkanin wata soyayya ya ɗora akanta da tilon ɗanta sai kace fin nasu ƴaƴan yayi.
Muryar tausayi Abu tayi ta wani kwakkwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "Ashe baki ji ba ai da baza mu fara yin maganar nan har taje kunnenki ba amma tunda kin riga kin ji babu amfanin ɓoye miki," ta ɗan yi jim kamar tana juya ta yadda zata fara faɗa mata wannan mummunan labarin bare yadda taga duk ta matsu taji a wane hali ɗan nata yake ciki. Sai data gyara tsayuwarta sannan tace "Baqeer ne Allah ya aikowa da tsautsayi mota ta buge shi, yanzu haka su Alhaji na can asibitin Mallam Aminu Kano inda aka kai shi shi da Bashir, sai fatan Allah ya kiyaye gaba dai amma ga yadda nake ji kamar ance bai ma san a inda kanshi yake ba."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙara ambata tana mai fashewa da wani irin kuka duk da tunda Abu ta fara maganar take tsiyayar da ruwan hawaye dama "Yanzu Baqeer ɗin yana asibiti tun ɗazu aka rasa mai faɗa mini? Wayyo ni Allah ka tashi kafaɗun yarona alfarmar Annabi da Alqur'ani" ta ƙare maganar tana nufar hanyar waje da nufin tafiya asibitin taje taga halin da ɗan nata yake ciki, tsabar ruɗewa tama mance da ko mayafi babu a jikinta bare kuɗin motar da zata hau ta kaita asibitin.
Abu ce tayi hanzarin janyota ta dawo da ita tsakar gidan tace "Malama ina zaki? Yanzu da daren nan daga faɗa miki magana? Salon Alhaji yace waya faɗa miki kice mune bayan ya hanemu da yin hakan?" Kallon Abu tayi da kumburarriyar fuskarta data koɗe saboda kuka tace "Wallahi bazan iya zama ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba idan har ba zuwa nayi naga a wane hali yake ciki ba, don Allah kuyi haƙuri ku barni na tafi wallahi bazan faɗawa Alhaji a wajenku naji ba." Sai sannan Jamila ta saka musu baki don duk abinda suke yi kallonsu kawai take yi tunda Abu ta haneta da yin magana, cewa tayi "Idan dai kin tabbatar da baza ki faɗa mishi mu muka gaya miki ba sai kiyi tafiyarki don ko nice hakan ta faru da yarona nasan hankalina ba zai taɓa kwanciya ba idan ba zuwa nayi naje naga a halin da yake ciki ba, sai dai kuma kada ki manta ko mayafi babu a jikinki bare kuɗin mota ko kina tunanin akwai wanda zai yi miki kallon hankali a hakan da kike".
Sai sannan ma ta tuna ai ko sallar magriba bata yi ba ashe fa alwala ta fito zata yi taci karo da wannan mummunan labarin da yayi fatali da dukkanin wata nutsuwarta. Ɗakinta ta shiga ta fara zarya kafin ta ɗau ki hijab, zurawa kawai tayi ta tada sallah sai dai sam ba ka jiyo karatunta sai sautin kukanta, da tazo sujjadar karshe kuwa kasa miƙewa tayi kawai ta cigaba da kuka tana neman Allah ya tausaya musu ya tsagaita wahalar Baqeer. Da ƙyar ta iya sallame sallah, ko hijab ɗin bata cire ba ta jawo jakarta ta nufi hanyar waje kai tsaye, ba komai take ganewa ba, hakan yasa ta zura takalmin da take aiki dashi a tsakar gida kawai ta fita titi. Abu da Jamila suna hangota ta tagar window ɗin dakunansu, a tare suka saki wata dariya ta jin dadi dan tabbas sun san yau akwai kura a gidan nan, su dai iya kacinsu su buɗe ido su kwashi kallo. Mai adaidaita ta tare sannan ta shiga ciki tana tafe tana lazimi, har saida yace gasu a Aminu Kano. Idanunta ta sauƙe kan asibitin tana jin gabanta na faɗuwa, haka ta fito ta kira Bashir akan ya sanar da ita inda aka kwantar da Baqeer ɗin, a lokacin yana kwance dan ba'a daɗe da gama ɗaukar jininshi ba, hakan yasa yace ta kira Bello shima bai sani ba ya kashe wayar tare da jan wani tsaki haka kawai shi ba da hatsari ba an kwashe mishi jinin jikinshi, shi yasa sam baya kaunar Baqeer saboda a komai sai Baban ya nuna fifiko a kanshi. Bello ta kira cikin sauri, nan ya sanar mata zai zo ya ɗauketa daga inda take kasancewar asibitin da girma yake, sannan Baba ya hanashi komawa cikin ɗakin.
**** Zaune Baba yake gaban Baqeer wanda kallo ɗaya za kayi wa fuskarshi ka fahimci tsantsar damuwar dake ɗauke da ita, idanunshi na kan Baqeer yana kallon yadda yake kwance kawai baya ko motsi, numfashi kawai yake yi, hannayenshi ya riƙo zuciyarshi na sake karyewa yake magana "Baqeer ka taimakeni ka tashi, ka sani kai kaɗai ne burina, da kai kaɗai nake taƙama a duniyar nan, kaine wanda in na gani nake jin sanyi a raina nake kuma kyautata zaton nayi abin arziki na kawoka duniya da nayi, ka taimakeni ka farka kafin wannan taron naku, kada ka bari abinda muka daɗe muna shiryawa ni da kai ya tafi a banza……" Maganarshi ce ta maƙale jin sako ya shigo cikin wayarshi, duba wayar yai yaga sakon secretary na Gomna ne wanda yake sanar dashi sun turawa Baqeer kuɗi akan yayi siyayyar abinda zai buƙata in yaje Abuja yin gasar. Wayar ya maida aljihu ya sake damke hannun Baqeer yana ji kamar ranshi zai fito. Ƙofar da yaji an buɗe ne yasa ya kalli ƙofar tare da sakin hannun Baqeer, nan da nan idanunshi suka canza fuskarshi ta murtuke, rai a ɓace yake kallinta, sai dai ko bi takan shi ba tayi ba ta ƙarasa shigowa ciki da gudu tana cewa "Na shiga uku, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Baqeer?" Cike da tsawa Baba yace "Fatima ashe baki da hankali?" Cak ta tsaya daga inda take tana kallonshi a tsorace "Banda hauka da rashin tunani uban wa ya baki izinin zuwa asibitin nan?" Hawaye ne suka gangaro mata tace "Haba Alhaji, yanzu ta ina kake tunanin zan iya zama bayan naji ɗana yayi hatsari? Sannan kalli yadda aka nannaɗeshi da bandage wanda kana gani kasan……"Kuka ne ya kwace mata wanda ya hanata ci gaba da magana, nan ta ƙarasa jikin gadon tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, Baba yana tsaye yana saurarenta na wasu mintina kafin yace "Kin ganshi ai ko? To tattara ki koma ni bana son shirmen banza, ɗana ba abinda zai sameshi kuma bana so wasu mutane su sani balle a mana hassada da baƙin cikin da aka saba, kuma wallahi karna sake ganin ƙafarki anan in har ba ni nace miki kizo ba." Ɗago jajjayen idanunta tayi ta kalleshi cike da tausayi tace "Alhaji kar kayi min haka na rokeka da Allah ka barni na zauna kusa da ɗana dan Allah ka dubi wannan mahaifiyar." Hannu ya ɗaga mata alamar tayi mishi shiru dan Baba kowa ya sanshi akwai zafi, sam bashi da sakin fuska shi yasa yaranshi da matanshi kowa ke shakkarsa, "Wallahi kika bari na sake magana sai ranki ya ɓaci ni bana san shirmen banza, ce miki aka yi Baqeer rago ne irinki da zaki zauna kina kuka yana saurara? To ni bana son shirme ki koma can gida kiyi ta kukanki kina sharewa, yarona da izinin Allah ba abinda zai sameshi ki koma na miki alƙawari yana farkawa zan sa a kawoki." Hawaye kawai take yi kamar wanda ake zuba mata ruwa a cikin idanuwanta saboda yawan hawaye, da ƙyar take jan ƙafafunta ta fito daga ɗakin. Bashir wanda ya taso dan ya ga mai zai faru yana jikin ƙofa yana kunshe dariyarshi, jin alamun ana toshe baki yasa Fatima ta juya ta kalli Bashir, cike da raini ya nuna mata hannunshi yace "Jinina aka ɗauka aka sakawaa ɗanki." Hannun ta kalla ta juya ta kalli ɗakin inda jinin ke shiga jikin Baqeer, tace "Nagode Allah ya kara haɗa kanku." Juyawa tayi suka fara tafiya da Bello. Baba kuwa a ɗaki zirya ya shiga yi don a yanzu abin yafi ɗaga mishi hankali, "Kai Bashir shigo." Bashir dake waje abinda yaji Baban nashi ya faɗa kenan, da sauri ya shiga ciki yana sosa bayan ƙeyarshi. "Ka zauna da Baqeer duk wani abu daya faru kayi mini waya ka sanar dani dole zanje gidan Sulaiman Karaye bazan taɓa yadda da wannan iskancin ba, ni muna nan asibiti shi yana kwance a gida hankali kwance." Yana kaiwa nan ya juya bai ma tsaya ya jira mai Bashir zai ce ba, da sauri ya fito daga waje ya hango Fatima, nan ya ƙarasa inda take jiran adaidaita a mota ya tsaya kusa da ita. Ganinshi yasa ta buɗe gaban motar tana share kwalla ta zauna zuciyarta duk babu daɗi, "Kema yanzu kin fara daina jin magana ta ko? A wani dalili da zaki fito bada izinina ba?" Ta share kwalla tace "haba Alhaji kayi mini adalci mana, wacce uwa ce zata zauna a gida bayan taji halin da ɗanta yake ciki ba tare da taje ta ganshi ba? Sannan ka duba yadda Baqeer yake kamar wanda bashi da rai?" Hawaye kawai take yi tana jin zuciyarta na wani irin zafi, ya fahimceta sarai amma ɓacin rai da halin da yake ciki bazai barshi ya sauƙa daga fushin da yake ba. A ƙofar gidansu yai parking nan ta fita bai ko ce mata komai ba, tana sauka yaja mota ya nufi gidan Sulaiman Karaye.
***** Katon gida ne wanda a unguwar yana daga cikin manyan gidajen masu kuɗi, tun daga waje zaka gane kyan gidan saboda fitulu da aka saka suke haska layin gidan, ba wai kato bane gidan wanda baza'a iya kwatantawa ba, ba kuma cinye rabin layin yayi ba, gida ne dai babba daidai misali wanda za'a iya gina gida uku ko hudu na mai ƙaramin ƙarfi, kasancewar gidan sabo ne yasa yake sake ɗaukan ido. Alhaji Sulaiman Karaye ba wai bakon mutum bane don sun san juna shekaru masu yawa a baya. A gaban gidan yayi parking tare da sanar da mai gadi yana son magana da mai gidan. Kamar mai gadin zai musa sai ya fasa dan Alhaji Sulaiman ya sha sanar dashi duk wani dattijon dake son ganinshi to fa a sanar mishi kome yake yi zai bari ya saurareshi tunda bai san uzurin dake tafe dashi ba.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻
0020428430 Ishaq Fatima A GTBank
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
#BAQEER #AYUSHERMUHD #UMMASGHAR
BAQEER NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD
PAID BOOK
ƊANƊANO DAGA TAGWAYE SHAFI NA UKU
KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O? INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA. Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199 07068558096
{3}
Kishingiɗe yake akan kujera fuskarshi sanye da glasses yana karanta jarida, jefi-jefi yana ɗan kallon tv ɗin dake kunne a cikin falan, shigowar da tayi cikin parlourn ne yasa ya kalleta, sanye take da wani haɗaɗɗen lace wanda yabi jikinta ya zauna ɗas, baka ce daidai misali sannan tana da tsayi wanda hakan yasa ba'a ganin kibarta sosai, mace ce mai fara'a wanda fuskarta kullum a sake, murmushi ta sakar mishi tace "Diatinguished Senate ana sallama da kai." Rufe jaridar yayi yana dariya yace "Wai har kin bani matsayin?" Ta zauna a gefenshi tana cewa "Me za'a fasa? Ai kujera ka hau ta ka gama, sai da kai uban Zainab da Kabir." Kai ya girgiza yana wani irin murmushin jin daɗi yace "Ke dai Halimah wallahi baki da dama." Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye daga kan kujerar "Bari na leƙa naga wanene?" "Yana waje nace mai gadi yace ya shigo falon baƙi yace a'a." Waigowa yai ya kalleta yace "To me yasa?" Ta ɗan girgiza kai tace "Wallahi ban sani ba, ƙila kunya yake ji ko sauri yake." Bai ce komai ba ya ke kallanta, ta sake murmushi tace "Ai sai naga wajen ma kamar yafi ko?" Yanda ta kalleshi ne yasa ya saki fara'a yace "Wannan matar baki da dama, nafahimta kuma sosai yafi, bari na wuce." Nan ya fito yana sake tabbatar da fitilun waje da fatan a kunne suke, sannan ya taɓa aljihunshi ya tabbatar yana da wadatacen kuɗi, gate ya buɗe ya kalli mutumin dake tsaye a waje ya ɗan juya baya. Daga bakin gate ɗin yace "Assallamu Alaikum." Da sauri Baba ya juya suka kalli juna ido cikin ido, wani kallo suke yiwa junansu na wasu dakiku kafin Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya dake ya kauda kai yace "A'a Alhaji Badaru? Wai kaine dama?" Baba ya sake tamke fuska yace "Kira min yaronka kace ya gaggauta dawowa dan daga nan wurin ƴan sanda zan yi dashi." Nan da nan fuskar Alhaji Sulaiman Ƙaraye ta canza, yayi mishi wani kallo sosai yace "Wai kai har yanzu baka girma da wannan shirmen bane? Sai yaushe zaka girma ka daina magana kamar mara tunani? Ni yanzu kaf garin nan kana tunanin akwai wanda ya isa ya kama min ɗana?" Cike da masifa shima yace "Kai kana ganin nima kaf garin nan akwai wanda ya isa ya nemi halaka ɗana inyi shiru? Ka gaggauta sawa a ƙira shi ko kuma in tattaro dattijan unguwar nan in sanar dasu abinda yayi." Nan da nan gaban Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya hau faɗuwa mai kuma yaron nan ya sake jawo mishi? Waya ya ɗauko ya ƙira Hajiya Halima wacce har yanzu tana nan a zaune a falon tana jiran dawowarshi, ringing biyu ta ɗauka, tana ɗagawa tace "Senate kun shigo ne?" Yasa ƙiran a speaker sannan yace "Ina yaran nan yake?" Cike da mamakin yadda yayi maganar yasa tace "Yana ɗaki a kwance, tun safe yake ɗan fama da zazzabi shi yasa ko abincin dare bai ci ba." Kashe wayar yayi sannan ya kalli Baba yace "To ka dai ji yana gida, menene kake faɗa akai haka?" "Tunda yana gida komai yayi daidai, sai ka sa ya fito ya sanar dani a wani matsayi ya ɗauki ɗan adam da har zai buge ɗana a mota sannan dan rashin imani yaja motarshi ya tafi? Wallahi kai kafi kowa sani akan Baqeer ba abinda bazan iya aikatawa ba sannan duk wani abinda ya sameshi wallahi bazan yarda ba, hukunci kuma dole ne ya fuskanceshi daga hukuma." Da sauri Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya ɗaga mishi hannu yace "Ya isheni haka nan Malam! Kai banda ma saukin kaina har ka isa kazo ƙofar gidana kace zaka yi mini zancen banza? Sannan yaron nan ance maka yana gida tun ɗazu ko kana nufin karya muka yi maka? In zaka je ka nemi wanda ya buge maka ɗan ka kaje ka nema amma ba Kabir ba." Bai jira Baba yace komai ba ya sake cewa "Sannan kana tunanin hukumar ta isa ta kama yaran da bai da laifi ne tace zata hukuntashi?" Ya kalli mai gadi yace "Kabiru ya fita yau?" Da sauri yace "Ni rabona dashi tun jiya daya shiga yau ko masallacin daya saba zuwa bai fito ba" yayi maganar kanshi a ƙasa don kuwa yasan ƙarya ce ya shirga shi Kabir ɗin da kanshi ne ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura yace yau ya ganshi bare har aje ga batun fita. Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya kalli Baba ya ƙira wayar Kabiru itama yasa a speaker yace "Kana ina?" Cikin sanyin murya yace "Dad ina ɗaki inzo ne?" "A'a naji ance ka fita ne ɗazu." Ɗan nishi yayi yace "Ina zan je ni kam bayan tun dare nake kwance ina fama da zazzaɓi?" Kashe wayar yayi ya kalli Baba da duk jikinshi yayi sanyi, ba dai yaran nan basu ma gama tabbatar da wanda yai hatsarin ba? Hannu Alhaji Sulaiman Ƙaraye yasa a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mai yace "Tunda akan su kazo yiwa yarona sharri gashi ni mai iya baka ne kyauta abinda ya faru a tsakanin mu da ya riga ya wuce." Ganin Baba ya kasa ko motsi yasa ya saka mishi a aljihu ya juya ya koma ciki. Baba Badaru shiru yayi ya dafa kanshi yana da na sanin zuwa ƙofar gidan mutumin da tun asali basa ga maciji dashi, ganin zai shige cikin gidanshi ne yasa shi hanzarin bin bayanshi ya watsa mishi kuɗin daya saka mishi a aljihu yace "Kai dai kasan har abada ba zaka taɓa yin kuɗin da zan zo wurinka maula ba, me jiya ma tayi bare yau?" yayi wani matsiyacin tsaki ya juya ya bar wurin ya ƙarasa motarshi ranshi yana wani irin ƙuna da ɓacin rai, kanshi ya kwantar a kan sityarin motar yana sake tuno hannun Baqeer dake mane da bandage, fuskarshi ya shafa cikin tsananin tashin hankali, ya zai yi in har wani abu ya samu Baqeer? Kenan duk burin daya daɗe yana shiryawa zai tashi a banza? Kenan duk yadda ya sadaukar da komai akan Baqeer ɗin komai zai zo ya wargaje? Nan da nan ya shiga wani irin yanayin da yaji gaba ɗaya komai yayi mishi zafi, wayarshi ce tayi ƙara wanda yasa shi ɗauka. "Alhaji kana ina ne? Meya samu Fatima ne ta shiga ɗaki sai kuka take yi." Abu tai maganar cike da damuwa ita a dole bata san meya samu Baqeer ba. Tsaki yaja yace "Bana son shirmen banza, ita yarinyace da in tana kuka za'a nemeni a waya? Ko kuwa salon raini ne wannan?" Cike da dana sani na makirci tace "Kayi haƙuri Alhaji nayi kuskure." Kashe wayar yayi ya sakata a gefen mota tare da duba agoggon hannunshi ƙarfe sha ɗaya da rabi (11:30) na dare, asibiti ya koma zuciyarshi na sake ɗaukar zafi. Kai tsaye reception yaje ya cire kuɗi daga cikin wanda gomnati ta bashi dan shirye-shiryen gasar da Baqeer zai tafi ya biya kuɗaɗen da ake bukata sannan ya nufi ɗakin da aka kwantar da Baqeer, mamaki ne ya kamashi ganin Bashir baya ɗakin kenan da yace ya zauna yawonshi ya tafi? Alwala yayi tare da yin sallar isha'i a ɗakin sannan ya samun kanshi da dagewa da yiwa Baqeer addu'a akan Allah ya tashi kafaɗunshi a yau ɗin nan dan su cigaba da shirye-shiryensu tunda tafiyar nan dai matsowa take yi, ya daɗe yana addu'a kafin ya dawo inda Baqeer ɗin yake, shiru yayi yana tunanin yadda rana ɗaya rayuwa take neman juya musu baya, yadda komai yake neman rugujewa bayan ya daɗe ya kuma ɗauki shekaru masu yawa yana faman shirya ma zuwan wannan lokacin, yatsun hannunshi ne yaji alamun sun motsa, a zabure ya saki hannun ya kalli Baqeer dake kwance fuskarnan tayi fayau yace "Baqeer? Ka farka? Ni dama nasan bazaka bani kunya ba, na sani kai kaɗai ne wanda baka wasa da farin ciki na, Baqeer buɗe idonka ka ganni kaji ɗan albarka."