Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 3

Baqeer complete - Chapter 3

Baqeer complete Chapter 3: Baqeer complete Chapter 3. Motsi yaji yatsun nashi sun ƙara yi sai kuma idanunshi dake fafarniya alamun son ya buɗe su sai dai…

3,122 words

Motsi yaji yatsun nashi sun ƙara yi sai kuma idanunshi dake fafarniya alamun son ya buɗe su sai dai ya kasa saboda nauyi da yaji kanshi yayi mishi. Acan nesa yake jin ƙiran da mahaifin nashi yake yi mishi sai dai ya kasa tantance muryar waye yake ji, ƙoƙarin motsa ƙafafun shi yayi sai yaji ya kasa gashi dukkanin jikinshi yayi mishi nauyi tamkar wanda aka saka igiya aka ɗaɗɗaure shi kyakkyawan ɗauri irin wanda ake yiwa huhun goro. "Baqeer kana jina kuwa? Daure ka buɗe idanunka ka kalleni nine nan mahaifinka ko na samu nutsuwa nasan cewa wani mummunan abu bai sameka ba" Baban yayi magana muryarshi na rawa don hankalin shi sam ba'a kwance yake ba, fatanshi a yanzu kawai yaga Baqeer ɗin ya miƙe ya samu tabbacin cewa babu wani abu da ya samu ɗan nashi da ya ɗauki dukkanin wani burinshi na rayuwa ya ɗora a kanshi.

Kamar mai koyon yadda ake buɗe idon haka ya buɗesu a hankali yana jin kanshi yana sara mishi da matsanancin ciwo, hannunshi na dama ya ɗaga da niyyar dafe kan ko ya samu raɗaɗin da yake yi mishi ya ragu sai dai yaji shi a ɗaɗɗaure ko motsa shi ya kasa yi, a hankali ya juyar da kanshi ya kalli hannun sai ya ganshi a naɗe a cikin cast alamun anyi mishi aiki a hannun shi yasa ya kasa motsa shi abinda yasa shi wurga idanu yana ƙarewa ɗakin da yake kallo yana tabbatar da akan gadon asibiti yake, juyawa yayi ɗaya ɓangaren ya kalli hannunshi na hagu yaga babu abinda ya sameshi sai ya ɗaga hannun ya dafe kan nashi daya matsanta mishi da azabar ciwo. "Sannu Baqeer" Baba dake tsaye a kanshi yana kallon duk abinda yake yi ya faɗa. A hankali ya ɗaga mishi kai alamun amsawa don baya jin zai iya buɗe baki yayi magana. "Ciwo kan yake yi maka?" Baban ya tambayeshi ganin tunda ya farfaɗo yake riƙe da kan abinda ke alamta matsanancin ciwon da yake yi mishi.

Ƙara ɗaga mishi kan yayi don ko ƙwaƙƙwaran motsi baya son yayi idan ba ya zame mishi dole ba. "Bayan kan sai ina kuma yake yi maka ciwo?" Ya ƙara tambayarshi ba tare daya lura da yanayinshi ba da sam baya son yawan magana, shi dai burinshi ya tabbatar babu wani mummunan ciwo a jikin Baqeer ɗin ko ya samu a sallamesu da wuri ya koma gida ya fara shirin tafiya gasar da zai je. Da ido yayi mishi nuni da hannunshi mai karayar da shima ya matsanta mishi da ciwo.

"Sannu, Allah ya baka lafiya" yace tare da komawa kan kujerar dake gaban gadon ya zauna. Ji yayi gaba ɗaya ya takura da kwanciyar don sam bata yi mishi daɗi, ƙoƙari yayi ya gyara kafafuwan shi ko yaji daɗin kwanciyar sai yaji ya kasa motsa su, yayi-yayi ya motsa kafar yaji ya kasa, a hankali ya ɗaga kanshi ya kalli ƙafafun nashi sai yaga ƙafar shi ta hagu a ɗaure take alamun akwai ciwo a jikinta itama sai dai kuma sam baya jin tana yi mishi ciwo kamar yadda hannunshi ya matsanta mishi da ciwo. Cikin dauriya ya sake ƙoƙarin motsa ƙafar sai yaji ai kwata-kwata ma baya jinta tamkar ba'a jikinshi suke ba don sam baya jin wani feeling a ƙafafuwan nashi.

Gabanshi ne ya faɗi saboda yadda ya kasa motsa ƙafafun alhali gasu nan a jikin shi yana kallon su. Cikin rawar muryar data shaƙe saboda daɗewar da yayi bai yi magana ba yace "Baba wani abu ya samu ƙafafuna ne? Gaba ɗaya bana jin su na kasa motsa koda ɗan yatsana ne sai nake ji tamkar ba a jikina suke ba". Tasowa Baban yayi a ruɗe yace "kamar yaya baka jin su tamkar ba'a jikinka suke ba? Kada dai kace mini wani iftila'in ne yake neman faɗo mata bayan na karayar daka samu a hannunka hannun ma na dama wanda dashi kake amfani kana yin zane dasu". A gigice ya fice daga ɗakin ba tare daya ƙara kallon Baqeer ba dake kwance cikin tashin hankali don sosai ya tsorata da yadda Baban yayi magana. "Likita, likita" ya hau ƙwala kiran likita tamkar dai ya manta cewa a cikin asibiti yake kuma marasa lafiya ne a kwance a wajen da basa buƙatar wata hayaniya bare tashin hankali, har ya ƙarasa nurses station bai bar ƙwala kiran likita ba.

"Babu likita ne a kusa, don Allah kuzo ku duba mini yarona ya kasa motsa ƙafafun shi," yayi maganar a ruɗe abinda yasa nurse ɗin da tayi niyyar balbaleshi da masifa saboda hayaniyar da yake yi musu ta fasa don ta lura kamar ma ba'a cikin hayyacin shi yake ba. "Muje na gani" tace tana yin gaba ya bita a baya har suka ƙarasa ɗakin da Baqeer ɗin yake kwance. Har gaban gadon ta ƙarasa kafin tace "sannu ko, ina ne yake yi maka ciwo yanzun?"

Da hannu ya nuna mata kan shi sai kuma hannunshi mai karayar. "Ƙafar fa ko ita bata yi maka ciwon?" Ta ƙara tambayar shi. A hankali yace mata "Na kasa motsa kafafun nawa duka biyun kuma bana jin feeling ko kaɗan tamkar ba a jikina suke ba har mai ciwon, hatta ƴan yatsun kafata na kasa motsasu." Hannu tasa ta dafa shi tace "Yanzu fa? Ka ji saukar hannuna akan kafar taka?" Girgiza kai yayi alamun a'a. Da ɗan karfi ta matsa kafar ta ƙara tambayarshi "Yanzu fa?" nan ma yace mata bai ji komai ba.

"Ina fata dai ba wata matsalar bace ko nurse?" Baban yace gabaki ɗaya hankalinshi ya kai ƙololuwa wajen tashi don bai san ta yadda zai ƙarbi wannan ƙaddarar dake tunkaro rayuwarsu ta ƙarfin tsiya ba. Ɗan girgiza kanta tayi tace "A gaskiya dai bana ce ba amma bari naje na sanar da Dr duk abinda kenan zai sanar da kai, sannu Allah ya baka lafiya, ta cewa Baqeer sannan ta juya ta fita daga ɗakin cikin tausayawa yanayin da Baqeer ɗin ya tsinci kanshi a ciki. Bata jima da fita ba likitan ya shigo shima, a zabure Baba ya miƙe yace "Yauwa likita don Allah zo ka duba mini yaron nan yace baya jin ƙafafun shi tamkar ba'a jikinshi suke ba kuma ya kasa motsa su,"?yayi maganar cikin raunanniyar murya tamkar ya fashe da kuka.

Ƙarasawa yayi gaban gadon yace mishi sannu sannan ya hau taɓa ƙafarshi mai lafiyar yana jujjuyata tare da tambayar Baqeer ko yana jin feelings ɗin a yanzu yana girgiza kai alamun a'a. Ya jima yanavmatsa ƙafar yana jujjuyata waje-waje amma Baqeer yace shi baya jin komai. Juyawa yayi ya kalli Baba yace "Dole sai anyi mishi CT scan da MRI kafin mu faɗi wani abu akan rashin iya motsa ƙafafuwan nashi dama rashin jin alamun ƙafafun a jikin shi gaba ɗaya, In Sha Allah ba wani abun damuwa bane sai dai idan an yin zamu tabbatar daga inda matsalar take."

"To likita nagode" Baba yace wata irin zufar tashin hankali tana yanko mishi don a yanzu tunaninshi yafi karkata ga yawan kuɗaɗen da za'a kashe don ya tabbata wannan ƙaddarar data afko musu sai ta lashe maƙudan kuɗi kafin a samu akai gaci gashi kwanakin tafiyar su Baqeer ɗin sai matsowa suke yi shi yana kwance a gadon asibiti babu alamun zai warke bare har ya iya taɓuka wani abun arziƙi.

#Baqeer #Shalele #Asiya # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD

Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻

0020428430 Ishaq Fatima A GTBank Ki tura shaida ta +234 809 845 6130

KATIN MTN Ta👇 07043079282

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

BAQEER NA

UMM ASGHAR DA

AYUSHER MUHD

RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HUƊU

KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O? INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA. Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI - MAGANIN NONO MAGANIN HIPS - MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA - GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO - MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB - MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA - MATSI MAGANIN NI'IMA - MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU.....Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199 07068558096

4

Yau tsawon kwana huɗu kenan bata ji daga Baqeer ba duk kuwa da ya kamata ace tun kwanaki huɗun da suka wuce yazo wurinta don bai taɓa saɓa ranar zuwa wurinta hira ba a tsawon shekarun da sukai tare sai wannan karon, haka nan tayi fushinta na kwana biyu ta huce ganin ko a waya bai ƙirata ba bare ya bata haƙurin rashin zuwanshi wurinta. Ganin da tayi har kwana biyu bai nemeta ba yasa ta bawa kanta hakuri ita ta ƙira shi don a yanzu kam ta tabbatar ba lafiya ba don Baqeer bai taɓa ƙin ƙiran ta a waya na yini guda bama bare har na kwana biyu ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba sai dai kuma koda ta ƙira wayar tashi sai taji ta a kashe hakan yasa hankalinta ya ƙara tashi, haka tayi ta gwada kiranshi amma bata samu ba gashi yau har anyi wasu kwanakin biyu bata ji daga gareshi ba. Gabaki ɗaya ta tashi hankalinta don bata sani ba ko wata ce ta ɗauke mishi hankali yake nema ya juya mata baya, da kuwa ya cutar da ita cuta mafi muni kuwa don sai da ya bari ta zurfafa a cikin soyayyarshi sannan zai yi mata halin mazan zamani da yaudara da rashin cika alƙawari, da yin wannan tunanin sai taji wata irin zufa ta yanko mata gabaki ɗaya jikinta ya ɗauki rawa tana tunanin ta yadda zata iya rayuwa babu Baqeer a cikinta.

"Asiya, ke Asiya!" taji ƙiran mahaifiyarta daga tsakar gida. A sanyaye ta amsa sannan ta tashi jikinta babu karsashi ta fito, daga bakin ƙofa ta tsaya tace "Gani Inna." Ɗagowa tayi ta kalleta tace "Dan iskanci kuma daga nan zaki tsaya ba zaki karaso ba?" Cikin sanyin jiki ta ƙarasa kusa da mahaifiyar tata ta samu bakin turmi ta zauna ba tare da cewa komai ba. Kallon tsaf Innar tayi mata kafin tace "Ƙalau kike kuwa kwana biyun nan nake ganinki sukuku kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki?" Hawaye ne taji ya sulmiyo mata daga cikin idanunta tayi sauri tasa ɗan ya tsantsa manuniya ta ɗauke don kada Innar ta gani tace "Babu komai Innarmu, kawai dai kwana biyun ne bana jin daɗi." "Kuma shine zaki zauna da ciwo ba zaki faɗa ba a sama miki magani, shirun zai yi miki magani ne banda shiririta da shirme irin naki? Ga tuwonku nan ki ɗaukar muku sai kizo ki karɓi panadol idan kin gama idan jikin bai warware ba zuwa gobe sai Habi ta rakaki asibiti kiga likita don kin san bana son zama da ciwo."

Kwanukan abincin ta ɗauka ta koma ɗakinsu ta dangwarar dasu a gaban Habi ta koma kan katifarsu ta kwanta. Kallonta Habin tayi cikin mamakin yadda take cika tana batsewa, in banda ita ɗin mai haƙuri ce tana kai zuciya nesa da ba ƙaramin haurawa zasu yi ba. "Ba zaki ci bane kika dire mini kwanukan a gabana?" Ta tambayeta sai cewa tayi "Kici kawai ni na koshi." Daga haka bata ƙara yi mata magana ba ta buɗe kwanon tuwon ta hau zuba loma, sai da ta kusa cinyewa sannan ta ƙara ɗaga kai ta kalleta tace "Wai shin don Allah meke damunki gaba ɗaya kin rasa walwalarki kin koma wata sukuku dake, ko duk rashin samun Baqeer ɗin ne a waya duk ya sururutar dake haka?" Ajiye wayar hannunta tayi da mamaki ta kalleta tace "Ya aka yi kika san nayi ta nemanshi bana samunshi, wallahi gaba ɗaya na damu tunda bai saba yi mini hakan ba duk sai na damu nake tunanin ko wata ce ta ɗauke mishi hankali daga kaina yake nema ya gujeni."

Tasowa Habi tayi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kamo hannunta ta riƙe a cikin nata mai kyaun tace "Haba Asiya kada ki yiwa Baqeer gurguwar fahimta mana tunda dai kin san yaudara bata daga cikin halayenshi, tabbas akwai abinda ya faru daya hana mishi nemanki ko a waya ne ke kuma rashin nutsuwar da kike ciki ya hana miki tunanin neman wani daga cikin abokanshi kibi ba'asin rashin ji daga gareshi sai kika zauna kina ta zullumi da saƙe-saƙen abinda ba gaskiya ba."

Gaba ɗaya ta juyo ta rungume Habi cikin murna take furta "Nagode Habi da shawararki wallahi sam tunani na bai kai can ba, bari na kira Salim na tambayeshi nasan In Sha Allahu ba zai ɓoye mini komai ba." Wayarta ƙirar samsung galaxy s20 wacce Baqeer ya saya mata ta ɗauka ta nemo number Salim tayi dialing, ringing biyu sai gashi ya ɗauka da sallama suka gaisa a mutunce sannan ta tambayeshi abokinshi fa ta kwana biyu bata ji daga gareshi ba tana fatan dai lafiya. "Don Allah kiyi haƙuri wallahi laifina ne da ban sanar dake Baqeer na asibiti yayi accident ba, kuma a wajen aka ɗauke mishi a waya shi yasa ko kin ƙira ba kya samunshi." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" tace haɗe da fashewa da kuka "Garin yaya? Tun yaushe yayi accident ɗin? ina fata dai da sauƙi?" Ta jero mishi tambayoyin a jere ba tare da ta jira ya amsa mata ba.

"Eh to da sauƙi Alhamdulillah, ya samu karaya a ƙafarshi ta hagu da hannunshi na dama sai kuma ɗan buguwa da yayi." "Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, yana gida ko yana asibiti?" Ta ƙara tambayarshi har yanzu kukan da take yi bai tsaya ba.

"Yana asibitin Aminu Kano a male surgical ward."

"Allah ya sauƙaƙa mishi ya bashi lafiya, In Sha Allah zan je na duba shi" daga haka suka yi sallama a wayar tana yi mishi godiya. Bayan ta ajiye wayar ta yiwa ƴar uwarta bayani duk kuwa da cewa a gabanta tayi wayar ta kuma ji duk abinda Salim ɗin yace "Ko zaki faɗawa Innarmu ta tambayar mana Babanmu sai muje mu dubashi gobe?" Ta lanƙwasar da kai tana roƙon Habi don tasan ita ɗin ce kawai zata faɗawa Innar ta yarda ta tambayar musu Baban sabida ta iya tsari tsaf zata kalallame Innar har ta yarda.

Washegari ƙarfe 9 ta shirya zama tai akan gado ta matse hannayenta biyu tana addu'ar Allah yasa a barta ta fita dan itakam in bata gano halin da Baqeer yake ciki ba hankalinta bazai taɓa kwanciya ba. Habi ce ta buɗe labulen ɗakin nasu, tana ganinta ta miƙe da sauri tace "Ya ya?" Hannu ta miƙa mata tace "Kawo ɗari biyar." Harararta Asiya tai sannan ta ciro a jakarta tace "Gashi, an barni?" Kai ta ɗaga tace "Amma ance karmu daɗe saboda akwai aikin waina da Inna zatai anjima na biki da zamu tayata." Fitowa sukai tare da yiwa Inna sallama suka yi waje. Adaidaita suka hau Habi na tsokanar ta wai ta kusa ganin Baqeer hankalinta ya kwanta.

***** Physiotherapist ne tsaye gaban Baqeer ya dan ɗaga ƙafar tasa kaɗan, yace "Yanzu fa?" Wasu zafaffan hawaye ne suka sake zubowa daga idanun Baqeer, a hankali ya girgiza kai alamar a'a yana kallan Baba dake tsaye ya harɗe hanaye, wanda kana kallansa kasan yana cikin tsananin tashin hankali, da ɓacin ran abinda ke faruwa. Baqeer cike da kuka yace "Baca najin ƙafata gaba ɗaya,a jikina daga nan banajin komai zuwa ƙasa," ya ƙarasa maganar ya na nuna cinyarsa, sake kallan juna sukai da Doctor da Physio ɗin nan wanda ya sake duba takardun dake hannunsa dake ɗauke da result ɗin da ya fito, ya miƙa wa Doctor sannan ya ɗan ja gefe Dr Sajjad yace "Am sorry to say amma muna zargin kafafunsa sun kamu da cutar nan ta paraplegia." Wani kallo Baba yamai dake ɗauke da rashin fahimta. Dr Sajjad ya ɗan yi ajiyar zuciya ya cigaba "Paraplegia ciwo ne wanda yake bangaren paralysis, sai dai shi kasan mutum yake taɓawa daga cinyoyin sa zuwa ƙasa, wanda a dalilinshi mutum bazai iya tafiya ba, Ciwon yana faruwa ne sakamskon ciwo ko hatsari, to shi nashi hakan ya faru ne sakamakon buguwar da yai wanda wanda kashin bayansa ko kwakwalwarsa wani daga cikinsu ya daina aika sako zuwa jijiyoyin da suke kula da ƙasansa, da mun ɗauka ƙafa ɗaya ya taɓa sai dai yanzu da muka sake dubawa munada 95% tabbatarwa akan shine, idan ka duba wannan hoton na X-ray za kaga........"

Da ƙarfi Baba yace "Dan Allah Dr dakata, bazan kalla ba kuma ba zai yiwu ba badai Baqeer ɗina ba, duk wannan bayanan naka ni bawai ya dameni bane, dan babu wannan a tattare da yarona, ku dai kuje ku sake duba result ɗin, babu tantama wannan ba nashi bane, sai ku sake duba na waye ya fito shi ma ku nemo mai nashi, kai Baqeer sauko mu wuce gida bansan shirmen banza." Ya ƙarasa maganar yana nufar inda Baqeer ɗin yake. Jikin Baqeer ne ya fara karkarwa, nan danan ya shiga wani yanayi saboda duk yanda yake sake kokarin jan ƙafafunsa ya kasa, ya shiga girgiza kai yana wasu irin zazzafan hawayen wanda duk wanda ya ganshi zai tausaya mai, pillow ɗin bayansa ya cillar ƙasa da ƙarfi ya fara jan jikinshi ta wajen kafaɗar sa, ƙoƙarin sauƙowa daga kan gadan yake amma sam ya kasa banda wajen kafadar tasa da yake iya ja kafafunsa suna nan a tsaye cak, Bashir dake tsaye ne ya riƙe shi yace "Me kakeyi?" Fizge hannunsa yai da ɗan ƙarfi ya sa hannun hagu ya fara ɗago kafarsa ɗaya, jiyai ƙafafun sunyi nauyi ga hannunsa na dama wanda aka mai ɗori saboda karaya wanda hakan yasa bazai iya sa hannu biyu ba, wani irin ihu ya saka ya fara kuka mai sauti sosai, nan ya shiga dukan kafafunsa da hannunsa na hagu, duka yake iya ƙarfin sa wanda gaba ɗaya tausayinsa yasa kowa na cikin ɗakin yai shiru, jan jiki ya sake cigaba dayi da sauri Physio ɗin ya rikishi ya maidashi kan gadan, hannun damansa yaje ɗagawa nan wata azaba ta sake shigarmai, Baqeer hannun hangunsa yasa kawai a saman kansa ya fara dukan kan da karfi yanaji lalai rayuwarsa ta gama zuwa karshe.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull