Baqeer complete - Chapter 4
Baqeer complete Chapter 4: Baqeer complete Chapter 4. A fusace Baba ya kalli Dr yace "Bazai yiwu ba, ba abinda ya samu ƙafar yarona kuma babu abinda zai…
3,316 words
A fusace Baba ya kalli Dr yace "Bazai yiwu ba, ba abinda ya samu ƙafar yarona kuma babu abinda zai sameta nan gaba, me kuke san cewa? Kuna nufin bazai sake tafiya ba kenan? Yaran da zai zama abin kwatance nan gaba? Yaran da za'a ɗin ga nuna shi ana yabawa basirarsa? Sannan kucemin ya zama gurgu? Nakashashe? To baku isa ba wallahi." Baqeer ne ya sa hannunsa na hagu ya fara jan hannun Bashir dake tsaye kusa dashi, da sauri yace "Menene?" "Bashir taimaka ka daki kafata na tabbatar in wani ne ya daki kafa zanji, ka san ance in kai ne kai abu baka fiya ji ba, dan Allah...." Yai maganar cikin wani irin rauni wanda kanaji kasan shi kaɗai yasan abinda yakeji a ransa, lokaci ɗaya rayuwarsa ta zama wani abu da ko a mafarki bai taba kawowa ba. Bashir ne ya kalli Doctor ɗin wanda gaba ɗaya tausayin Baqeer ya hanashi magana tabbas Baqeer abin tausayi ne domin kuwa saurayi ne matashi ga buri dayawa a kanshi. Physio ɗin ne ya matso ya zare hannun Baqeer daga hannun Bashir yace "Baqeer furzar da iskar dake bakinka." Baqeer bai tankashi ba cikin ɗaga murya yace "Bashir ka taimaka ka daki kafaya dan Allah." Matsowa yai ya ɗan bugi ƙafar yana kallan Baba, Baqeer cikin ihu yace "Da ƙarfi Bashir ka taimaka kamin da ƙarfi banajin komai banaji! banaji!" Asiya ce ta saki ledar dake hannunta wacce ta siyo yoghurt zata kawowa Baqeer, idanunta ne suka ciko taf da kwalla dan tun dazu abinda ake a kan idanunsu akai, Habi ce ta kalleta cike da tausayi. Idanun Baqeer ne ya sauƙa akan Asiya dake tsaye, idanunsa sunyi wani irin jaa suna zubar da wasu zafaffan hawaye, kai ta shiga girgizawa tana jan kafafunta baya-baya, ta sake yin wani taku ɗaya baya tana sake girgiza kai. Habi ta fara ƙoƙarin riƙo hannunta sai dai Asiya ta juya a guje tana hawaye. Baqeer yana kallanta lokacin sai dai yanzu bata ita yake ba ta rayuwarsa yake dan tabbas tsoron abinda ke faruwa yakeyi.
Baba ne tsoro ya matsar da Bashir gaba ɗaya yanzu hankalinshi ya gama tashi ya tabbatar kafafun nan sun samu matsala, ya kalli Doctor yace "Yanzu in shine menene magani? Ai dai asibiti babu maganin da baku dashi, nidai karkuce ba magani." Ajiyar zuciya Doctor yai yace " Wannan result din MRI ne wannan ma X-Ray sannan wannan na CT Scan ne sannan munmai test na electromyography wanda ya sake tabbatar mana kafansa baya aiki." "Warkewa? Ita fa?" Baba ya katseshi. Hannu yasa ya ɗan cire abu daga idanunsa yace "Babu magani, sai dai yanda Allah ya bashi iko sai kuma shi da zai dage ya amshi kaddararsa ya fara rayuwa a haka." Baba ne ya shiga girgiza kai yace "Bazai yiwu ba, inalilahi wa ina ilaihi raji'un Allah bazai jarabeshi da hakan ba." Baqeer ji yai komai ya tsaya mai cak hawayen ma yanzu sun kafe nama yajin alamunsu, wani irin yanayi ya fara ji, kanshi na mishi wani irin zafi, hannun hagu yasa kawai ya cigaba da dukan kafarsa iya karfinsa, Physio ɗin ne ya sake riƙeshi yace "Baqeer fara addu'a." Kasa magana yai kawai idanunshi sun yi wani iri kamar wanda baya hayyacinsa, ƙafar kawai yake neman sake kaiwa duka. Baba hawaye kawai yakeyi, Bashir duk yanda bai damu da Baqeer ɗin ba sai daya samu kansa da kwalla, Baba ya kamo hannun Doctor ɗin yana hawaye yace "Zanyi duk abinda kukace amma dan Allah karkuce ba wata hanyar? Ta ina zai iya rayuwa a haka? Kasan yanda na ɗau ra duka burina akanshi? Doctor menai? Menene laifina? Dan Allah na rokeka da Allah ka taimaka mana. Ajiyar zuciya Dr yai cikin wani yanayi yake kallan Baba, jiki a sanyaye Baba ya matso ya rungume Baqeer su kaɗai sukasan abinda suke ji, zuciyarsu na sake wani irin zafi. Bayanshi Baba ya shiga shafawa a hankali, alamun lalashi, Baqeer wanda ko mutuwa akai baka ganin hawayensa saboda dauriyarsa yau shine yake kuka haka, shikanshi Baba bai taɓa ganin kukan Baqeer ba tunda ya mallaki hankalin kansa sai yau, yanzu kuma ga kukan ma ya kafe wanda yake ganin gwara kukan da wannan abin da yakeyi. Baba ne ya kalli Doctor yace "Hannunsa fa? Yaushe kake ganin zai warke?" "Ya danganta da yanayin saurin warkewar jikinsa, kawai dai karku tursasashi akan yai amfani da hannun yanzu ku bari hannun ya warke da kanshi tukun." A fusace Baba ya miƙe yace "To yanzu na gama gane bakin ciki kuke mana, Kai Bashir zo ka goya yayanka ko ka samu kujera mu turashi mu kaishi wani asibitin." Baba yai maganar cikin matukar ɓacin rai.
Ku kasance tare da Baqeer da yanda zai fuskanci canji mai karfi a rayuwarsa.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336 BAQEER NA
UMM ASGHAR DA
AYUSHER MUHD
RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA BIYAR
KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O? INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA. Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI - MAGANIN NONO MAGANIN HIPS - MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA - GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO - MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB - MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA - MATSI MAGANIN NI'IMA - MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU.....Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199 07068558096
5 Da ƙyar likitocin nan suka samu suka lallaɓa Baba har ya haƙura da ɗauke Baqeer ya mayar dashi wani asibitin da yake son yi bayan sun yi mishi doguwar nasiha da bayani kan cewa duk inda ma suka je abu ɗaya ne za'a faɗa musu ga kuma ƙarin kashe kuɗi tunda duk waɗannan tests ɗin sai an sake yi kuma mawuyacin abu ne results ɗin su fito ba irin na nan ba. Haka nan dai ya haƙura ba don yana so ba sai don tunanin irin kuɗaɗen da ya kashe tunda Baqeer ɗin ya kwanta a asibiti gashi har ɗan abinda gwamnati ta basu na shirin tafiyar Baqeer ɗin wajen gasar ya tasarma ƙarewa buƙata bata biya ba sai ma nakashewa da yayi, wannan abu yana yi mishi ciwo idan ya tuna yadda ya sadaukar da komai nashi don ganin Baqeer ɗin ya kai matakin da shi ya kasa cimmawa a rayuwa yanzu ga abinda ya faru yana ji yana gani mafarkin shi na neman tsayawa a mafarkin kawai ba tare daya cika burin shi ba.
Wannan takaicin yasa shi barin asibitin ba tare daya ƙara bi takan Baqeer ba da har wannan lokacin yake kukan baƙin cikin ƙaddarar data afko mishi don a ganinshi duk laifin Baqeer ɗin ne da baya iya zama a cikin gidansu yayi abinda zai fishe shi sai ya tafi yawon majalisa gashi nan yanzu asarar da ya janyo musu. Yana tafe a hanya yana ƴan mitocin shi kamar yana yi da wani har dai ya ƙarasa gidan, tun daga soro yake ƙwala kiran sunan Fatima hankali a tashe. A gigice ta fito daga ɗakin a tunaninta ko Allah yayi wa Baqeer ɗin rasuwa ne saboda irin wannan mahaukacin kiran da yake ƙwala mata gashi ya hanata zuwa asibitin ta zauna dashi sai dai idan lokacin ziyara yayi taje ta ganshi ta dawo shima kuma ba kullum ba.
Murya a shaƙe tace mishi "gani Mallam, ya wajen Baqeer ɗin? ina fatan dai lafiya?" Jikinta gaba ɗaya ya saki dama kuma tunda Baqeer ya gamu da tsautsayin nan ta ƙara yin sanyi fiye da da duk abinda ake yi a cikin gidan bata iya saka musu baki saboda hankalinta ba a kwance yake ba. Harara ya watsa mata kafin ya bata amsa murya a ɗage "ina fa lafiya bayan duk abinda na kashewa ɗanki duk don na inganta rayuwarshi yaje yayi sanadin da yanzu duk abinda na kashe ya tashi a banza, gashi can likitoci na maganar gurguncewa, kamar ni ace a gidana an samu nakasashe salon maƙiya su samu abun yi mini dariya akai". Kamar a mafarki taji maganar wai Baqeer ɗinta ya zama gurgu ba zai tashi ba, rigijib ta zube a ƙasa dafe da kirji saboda wani irin tsinkewa da zuciyarta tayi. Tama kasa buɗe baki tayi magana tsabar ruɗewa da tayi sai rawa da bakinta yake yi amma ta kasa cewa komai. Haka ya rufe ido yayi ta zazzaga mata ruwan masifa ba tare da la'akari da yanayin firgicin da take ciki ba, har yayi ya gama ya shige ɗakinshi tana nan zube a ƙofar ɗakinta ta kasa motsawa.
Abu ce ta kamata ta shigar da ita ɗaki ta kwantar da ita akan gado, su kansu kishiyoyin nata jikinsu yayi sanyi da jin irin ƙaddarar data afkowa Baqeer ɗin don haka aka rasa me magana a cikinsu haka kowacce ta koma ɗakinta suna juyayin wannan al'amari. Tashi tayi zaune jin da tayi ba zata iya zama ba alhalin tasan Baqeer ɗin nacan a wani hali saboda afkowar ƙaddarar nan a rayuwarshi a daidai wannan lokacin ba ƙaramin al'amari bane da dole yana buƙatar lallashi da tausayawa daga wurin makusantan shi gashi uban nashi da zai tsaya ya lallashe shi ya baro asibitin cikin fushi.
Hijabin sallarta ta ɗauka ta saka ta ɗauki ƴar purse ɗinta da take ajiyar kuɗi ta fice, kamar tayi wucewarta ba tare da ta sanarwa Mallam ɗin ba ganin irin tijarar da yayi mata a tsakar gida kamar Baqeer ɗin ne ya ɗorawa kanshi larurar sai dai kuma ba zata iya yin hakan ba don ba sabonta bane fita bada izininshi ba bare ma da yake cikin gidan a zaune ba wai baya nan ba. Daga bakin ƙofa taja ta tsaya ta ɗaga labulen ƙofar ɗakin tace mishi "zan tafi asibitin na zauna dashi tunda kai ka dawo". Da yake shima a ƙullace yake da ita ko musu bai yi mata ba sai ma ɗaga kanshi da yayi alamun amsawa, ganin hakan itama tasa kai tayi ficewarta zuciyarta cike da tausayin yaronta da mummunar ƙaddara irin wannan ta afko mishi da kuruciyarshi, tana tafe tana ɗauke hawaye da bakin hijabinta har ta samu adaidata sahu ta tara ta shige ba tare data tsaya sun yi dogon ciniki ba.
Lokacin data isa asibitin ta samu babu kowa a wajen shi sai shi kaɗai yana kwance yayi lamo abin duniya ya taru yayi mishi yawa, ya kasa gaskata wai shine ake cewa ba zai sake iya taka ƙafarshi ba, shikenan ana nufin ya zama nakasashe ya tashi daga mai lafiya ya zama gurgu. Yana kawowa nan a tunanin wasu hawaye masu tsananin zafi suka sulmiyo daga idanunshi, hannu tasa tana share mishi hawayen sai dai ita kuma ta kasa tsayar da zubar nata hawayen ganin tun ba ayi wata tafiya mai nisa ba mahaifin Baqeer ɗin daya kamata ace shine na farko wajen ƙarfafa mishi ya ƙarbi ƙaddarar data sameshi ya juya mishi baya. Abun nan yayi mata ciwo ba ɗan kaɗan ba. Sai da suka yi kukansu ya ishesu sannan ta tambayeshi ina Bashir yaje tunda tazo bata ganshi ba bayan kuma shi ne yake zaune a wurin shi yana jinyar shi.
"Tun bayan tafiyar Baba shima ya fita bai ce mini ga inda zai je ba" ya amsa mata da shaƙaƙƙiyar muryar data sha kuka ta ƙoshi. Zama tayi akan kujera daga gaban gadon ta riƙo hannunshi mai lafiyar tace "kayi haƙuri Baqeer, kowanne bawa da kake gani yana tafiya ne akan ɓigire na zanen ƙaddararshi, muhimmin abu a wajen mumini shine karɓar ƙaddarar a duk yanda tazo mishi, tunda kaga hakan ta faru da kai to haka nan Allah yake so ya ganka don haka nake horarka da yin haƙuri ka ƙarɓi ƙaddararka a yadda tazo maka In Sha Allah ba zaka taɓe ba. Allah yayi maka albarka ya tashi kafaɗunka." Baqeer ji yayi ya kasa cewa Ameen a fili, jugum-jugum suka yi a ɗakin gaba ɗaya kowa da abinda yake sakawa a ranshi, wayar tace tayi kara da kamar ba zata duba ba sai kuma ta ɗauko taga ƙanwar Baqeer ce mai bi mishi ke kiran, tayi aure tun shekaru biyar da suka wuce, tana ganin itace ta kalli Baqeer wanda ya ɗan kalli wayar shima, nan da nan wani abu ya sake taso mishi, kanshi kawai ya sake kwantarwa, cike da tausayi ta kashe wayar tace "Ka tashi kaci abinci, na siyoma alale mutumin ka." Kai ya girgiza a hankali alamar a'a kawai dan baya ji bakinshi ma zai iya tauna abinci. Ta sani sarai ba zai iya cin abincin ba amma dole ne ta karfafa mishi gwiwa, wannan wacce irin muguwar kaddara ce ta samesu?
****
Duk yadda Habi take yiwa Asiya magana ta kasa tankata, cike da takaicin abinda take aikatawa Habi ta fizgota tace "Asiya menene hakan? Ya zamu zo asibiti dubiya amma ki gudu? Bayan kin san yana bukatar wanda zai lallasheshi a wannan lokacin?" Fizge jikinta Asiya tayi tace "kinga Malama karki kuma tado mini maganar dubiya, hauka nake kina tunanin zan cigaba da soyayya da Baqeer? Ko baki ji me likita yace bane? Akan ba zai warke ba? Aure zanyi ko kula da gurgu?" Baki Habi ta saki mamaki ya sake rufeta tace "Asiya kina nufin yanzu daga yin wannan abin shine har kwakwalwarki ta tafi lissafin haka? Kin manta wanene Baqeer a gareki? Ko kin manta karatunki ma ba dan shi ba da baki karasa ba? Sannan shekara nawa yayi yana kula dake da duk wasu bukatunki?" "To saka shi nayi? Ko tilasta mishi nayi?" Ta faɗa tana cigaba da tafiyarta, gaba ɗaya Habi kasa motsawa tayi saboda mamaki, tana nan tsaye har Asiya ta shiga adaidaita ta ɗan ɗaga murya tace "Zaki zo mu tafi ko na tafi na barki?" Kasancewar tasan za'a mata faɗa a gida yasa ta ƙaraso ta shiga adaidaitar suka fara tafiya, sam Asiya bata ba ta fuskar magana ba hakan yasa ta yin shiru kawai suka cigaba da tafiya, suna sauƙa Habi tace "Lallai na yarda ɗan adam butulu ne, yanzu duk soyayyar da kike magana iya kacinta kenan?" Tsaki tayi tace "Da nace miki bana son shi ne? Ko kinji na faɗi haka da bakina? Sai dai ni ba auren jinya zanyi ba, kinfi kowa sanin kaf gidan mu babu wanda ya kai ni kyau da diri mai tsari ga karatu na nayi daidai gwargwado, ta ya ina planning na future ɗina magana ta sauya zuwa raino? Bana ɗaukan lokaci akan ajiye duk wani abu da zai kawo mini cikas a rayuwata, ba zanyi aure irin na gidan mu ba da za'ace babu dan haka karki sake yi mini maganar Baqeer." Tana kaiwa nan bata jira amsar Habi ba ta shiga ciki ranta a matukar ɓace. Gaba ɗaya Habi mamaki ne ke sake rufeta yarinyar da a saninta ko wayar Baqeer ne bata ji ba hankalinta tashi yake yi? Haka ta shiga gida jikinta duk a sanyaye, Inna ta gani zaune tana ɗaura tandar waina, da sauri ta ƙarasa ta gaisheta sannan ta cire mayafinta tana neman amsar aikin. "Waya taɓa Yayarki naga ta shigo rai a ɓace." "Shareta Inna kin san halinta ai ita wannan." Habi ta faɗa tana neman zama. "A wanke hannu kafin a fara." Dariya tayi ta miƙe tsaye tana nufar wajen famfo don ta wanke hannun.
******* Umma ce ta kalli agoggo ganin har azahar ta wuce ba Bashir gashi tun ɗazu Baqeer ke nemanshi ya taimaka mishi yaje banɗaki, ita dai wannan abu ya zasu yi da wannan sauyin? Baqeer ne ya kalleta muryarshi a karye yace "Umma dan Allah nemo wani ya taimakeni…." Ya kasa karasawa saboda yanayin da yake ji a ƙasan ranshi, tana buɗe ƙofa tayi kicibis da Salim, wata muguwar ajiyar zuciya ta sauke tace "Salim mun gode, dan Allah taimaki abokinka ka shigar dashi banɗaki." Gaisheta yayi sannan ya shiga ciki hankali a tashe, ganin Baqeer yayi ya dafa saman goshinshi da hannu, cike da tsokana yace "Wato an farka shine ka dawo da mulkin naka ko?" Kallonshi kawai Baqeer yayi yama rasa abinda zaice gashi a ɗan matse yake, jiki a sanyaye yace "Please Salim ga wheelchair can taimakeni naje toilet." Bai kawo komai ba ya ƙarasa da wheelchair ɗin yaja ya tsaya yana jiran Baqeer ya hau, sai dai ina duk yanda ya motsa ya kasa, mamaki ne ya kama Salim yace "Wai buguwar haka ta wahalar da kai?" Kai ya girgiza kawai yana ji yana magana to tabbas kuka zai yi, wai yau shine ya koma haka? Jikin Salim rawa ya fara ganin duk yanda yaso daga Baqeer ya kasa ɗaga ƙafar shi, Umma ta shigo ta taimaka da kyar suka sakashi akan kujera, babu abinda kowa ke yi sai hawaye sun kasa ko magana, haka Salim yaja shi banɗaki zuciyarshi na zafi sosai. Suna shigewa Umma ta sake fashewa da kuka a hankali ta ɗauki waya ta ƙira Baba, kamar ba zai ɗauka ba sai kuma taji ya ɗauka, bayan sun gaisa tace "Mallam dan Allah ko zaka kira Bashir yazo babu kowa a gun Baqeer sai yanzu da Salim yazo kasan yana bukatar namiji kusa dashi." "Wannan kuma ya dame ni ne? Ko kina son ce mini Bashir mai jinya zai koma? To ni bazan tilastawa yarona ba in yaso yaje ya zauna in bai so ba ra'ayinshi ne, ke a matsayinki na mahaifiyarshi kisan yadda zaki yi." Jin kalamanshi tayi kamar an watsa mata ruwan zafi tace "Mallam ka manta wanene? Baqeer ne fa?" Tsaki yayi yace "Da can bai san shi wanene a gareni ba sai yanzu? Sanda nake mishi faɗa kina ina? Sannan ki gagauta sanar dashi ya tabbatar ya fara rike pencil dan akan shi bazan sadaukar da burina ba, in bashi da ƙafa ai yana da hannun da zai yi zane, lokacin ni da kaina zan kai shi Abuja a keken guragun muje muyi komai tare, wannan shi kaɗai ne uzurin da zan sake yi mishi, kina zaune kin bar yaron nan ya lahanta kanshi kun cuceni daga ke har shi wallahi, sai dai bazan bari ku salwantar da abinda na dade ina fata nake addu'a akai ba shekara da shekaru." Yana kaiwa nan taji ya kashe wayarshi, daga banɗaki taji ihun Salim, da gudu ta tashi ta ƙarasa tace "Salim lafiya?" A tsorace ya buɗe ƙofar yace "Umma." Idanu ta zaro ganin Baqeer a yashe a ƙasan banɗaki…..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336 *BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHIDA*