Baqeer complete - Chapter 64
Baqeer complete Chapter 64: Baqeer complete Chapter 64. Kabir yana shigowa ɗaki ya shiga ya dinga zarya a cikin ɗakin, tsoro duk ya hanashi sukuni, daga…
3,113 words
Kabir yana shigowa ɗaki ya shiga ya dinga zarya a cikin ɗakin, tsoro duk ya hanashi sukuni, daga cikin ɗakin yake jiyo fadan Daddy akan zuwan Badaru, hankalinshi ne ya ƙara tashi ya leko ya ɓoye a jikin ƙofa yana ji Mummy na kareshi, Daddy ranshi a ɓace ya shiga ɗaki bai daɗe ba sai gashi da key ya fito ko kula Mummy bai yi ba yayi waje, taya ƴar yafi so a rayuwarshi zata janyo mishi ɓacin rai haka? Dan ƙaunar da Daddy yake yiwa Zainab a bayyane take kawai baya son nunawa ne amma ita kanta Zee ɗin ta sani. Yana fita Kabir ya fito kana kallon yanayin fuskarshi zaka san lallai yana cikin tashin hankali don idanuwanshi duk sun jame, bakinshi na rawa yace "Mummy yaron nan zuwa yayi maganar bugeshi da nayi ko?" Kallonshi tayi tace "Muje ciki." Tayi maganar tana kallon ɗakin Zee wanda taga alamun za'a buɗe, ɗakin Mummy suka yi yana shiga yace "Mummy meke faruwa? Zancen bugeshin da nayi ne?" Ajiyar zuciya tayi tana ɗan kallon ƙofa don basu rufe ba tace "Kabir ba wannan ya kawo shi ba sai dai yanzu in har aka san abinda kayi bayan abinda ya faru to lallai akwai gagarumar matsala." Cike da rashin fahimta yace "Ba hakan bane?" Hannu tasa ta shafi fuskarta tace "Gaisuwar surukai yazo Zainab yake so." Ido ya zaro hankali a tsananin tashe yace "What? Zainab? Bata da hankali ne zata ce tana son Baqeer? Gurgu ne fa? Sannan taya zata wulaƙanta mutane da yawa tace yaron nan take so?" Gaba ɗaya magana yake yi cikin ɗaga murya yana yi yana tafiya yana yarfe hannu don mamakin abun nan ya isheshi wai Zainab, Mummy ce ta kalleshi tace "A bar maganar Zee nasan shi yana sonta, yanzu me kake tunani zai faru in har tasan kai ka bugeshi, in har tasan kaine silar rasa ƙafar shi da yayi. Ƙofar da aka ƙarasa turawa itace tasa su waiwaya su kalli wurin, Zainab wacce jin fitar Daddy yasa ta fito don ta yiwa Mummy magana akan zata je ta bawa Baqeer hakurin wulaƙancin da Daddy yayi mishi kunnuwanta suka jiye mata wannan mummunan labarin, hawaye ne kawai suke gudu a saman kuncinta don kamar wanda ake korosu haka suke zubowa, Mummy da Kabir ma hankali a tashe suka kalleta, da sauri Mummy ta nufo inda take, hannu ta ɗaga mata alamun karta ƙaraso inda take sannan ta juya da sauri daga ita sai material ɗin ɗazu sai ɗankwalin kanta, ta fizgo mayafi da wayarta, kallon drawer ɗin gefen gado tayi ta ɗauki key ta fito da sauri, Mummy ce tace "Zainab!" Ko kallonta ba tayi ba tayi waje da gudu, mota kawai ta shiga mai gadi ya buɗe ta fita daga gidan da gudu, gudu kawai take don saura kaɗan ta buge wani mai yalo dake tura baro, birki ta taka da ƙarfi ta kifa kanta a sitiyari tana maida numfashin dake fita da sauri da sauri, da ƙyar ta iya buɗe ƙofa ta fito ta bawa mai yalo haƙuri sannan ta komo mota, tana tafe kuka kawai take yi. Ina zata kai son Baqeer da tausayinshi? Taya za'ace yayanta shine ya ja mishi abinda ya faru dashi? Hawaye kawai take yi tama rasa ta ina zata fara tunanin abun yi, tausayin Baqeer ne fal cikin ranta wanda take ji ya riga ya gama bin duk wasu gaɓoɓi dake jikinta. Bata san inda take jan mota ba don tuƙi kawai take yi, ga mamakinta sai ganin kanta tayi a ƙofar gidansu Dada, kanta kawai ta kwantar a kan kujerar ta runtse ido, to ita dama ina take dashi na wurin zuwa banda nan? Kasa fita tayi daga mota sai hawaye kawai da take yi, tafi minti sha biyar a haka sai kuma taji zuciyarta na son ganin Baqeer yanzu kam ta tabbatar babu ita babu shi don in har yasan Kabir ne ya ja mai nakasa to fa ita dashi kila har abada. Ciki ta shiga ta tsaya daga daidai ƙofar shiga tana goge fuskarta, sai dai idanuwanta kaɗai zaka kalla kasan tasha kuka, tana shiga taji Dada na faɗa tana cewa "Mutum sai kace yaro, komai aka baka kace baza kaci ba, in har kaje gaisuwar surukai ba'a dace zuwan farko ba ai haƙuri ake yi sai a ƙara gwadawa, to ni dai ga abincinka nan in kaga dama sai ka buɗe ɗakin," tana kaiwa nan ta ajiye kwanon a bakin ƙofa tana waigowa taga Zainab a bayanta, da sauri Zainab ta rungumeta kamar dama jira kukan da take so tayi yake kawai ta fashe da kuka. Kuka take yi wanda in kaji sai ka tausaya mata, shafa bayanta kawai Dada take yi cike da tausayin halin da suke ciki wanda ita aka barta a duhu bata san meke faruwa ba. Tun daga ciki yake jiyo kukan wanda ya ɗaga mishi hankali, saukowa yayi daga kan gado ya hau kekenshi zuciyarshi na wani irin zafi ji yake kamar yaje ya rungumeta ya bata haƙuri, turo keken yayi cikin sauri yazo daf da jikin ƙofa hannu yasa ya buɗe ƙofar din zuciyarshi ta kasa haƙuri da abinda yake ji, da yake tana rungume da Dada fuskarta tana kallon saitin ƙofar ɗakin, cike idanuwanta suke da ƙwalla take kallon ƙofar da aka buɗe sai dai bai leƙo ba. Dada ce jin shirunta yasa ta zareta daga jikinta tace "Ba komai In Sha Allahu zai yarda shima Baqeer ba laifi yayi ba Allah ya ƙaddaro mishi hakan," tayi maganar tana kallon inda Zee ke kallo, ganin Baqeer ya buɗe ƙofa yasa tace "Asha na manta na bar abu a kitchen," tayi maganar tana yin kitchen ɗinta dake waje. Zee a hankali take takawa har jikin bangon ɗakin tsugunawa tayi ta ɗauki kwanon abincin da Dada ta ajiye, ba tare da ta miƙe ba ta ɗago suka haɗa ido, idanunshi yayi ja sai dai ita idanunta cike suke da hawaye wanda suka sauko daidai sanda ya kalleta, sharewa tayi tana murmushi tace "Mantawa nayi ban tambayeka ya ka ganni ba bayan kaji wacece ni," tayi maganar cikin hawayen da take ta ƙoƙarin tsaidawa, yanayin maganarta kaɗai zai sa kasan lallai tana cikin babban damuwa, murmushin yaƙe yayi yace "Shi yasa ban ganeki ba Abulele." Ta jinjina kai tana goge fuskarta tare da yin wata dariya mai cike da ban tausayi tana cewa "Me na canza?" Shima murmushin yayi yace "Komai, sai dai da alama ba kya cin abinci ne yasa kika rame haka." Ta ƙara yin ƴar ƙaramar dariya tana jan hanci tace "Randa na fara ganinka nima ban ganeka ba." Kai ya jinjina don yana ji in har yayi magana zata fahimci rawar da muryarshi keyi, ta sadda kai tace "Da wannan, da kuma girma," tasa hannunta kan hannun kujerar guragun, kai ya sake jinjinawa yana cewa "Umm!" Hannu biyu tasa tana maida kwallarta tare da goge ƙasan idanunta tace "Da alama bazan ƙara ganinka ba ko?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, ta haɗiyi wani abu mai ɗaci tace "Hmm na sani, amma kayan da aka bani an bar mun ko?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, gaba ɗaya tausayin kansu ya isheshi. Murmushi tayi ta miƙa mishi kwanon abincin da ɗaya hannunta na dama wanda tasa kwanon a saman cinyarta, hannu ya kai ya amsa yasa a jikinshi. Kallon juna suka yi ta miƙe tsaye tana haɗiyar wani abu mai ɗaci wanda ta rasa daga ina yake ziyartar makogwaronta, da sauri ta juya baya don ji take baza ta iya riƙe hawayenta ba, Ya Kabir bai kyautawa Baqeer ba, an san da tsautsayi, ya zata yi ta sanar da Baqeer akan Kabir ne ya janyo mishi zama gurgu? Dada dake kitchen duk jikinta yayi sanyi ita kam meke faruwa da har yayi zafi haka? Ta ɗauka kawai dai iyayenta ganin gurgu ne shi yasa suke jinkirin basu ita amma yanzu ta fara tunanin akwai abinda yafi haka. Zee ce ta waigo suka haɗa ido da Baqeer kowannensu abinda zuciyarshi ke aika mishi daban, saƙo ne mai zafi da ƙuna wanda muhimmancin junansu da ƙaunar da suke yiwa juna ya tarwatse lokaci ɗaya. Kasa jurewa tayi kawai ta juya da sauri ta fita, ƙofar kawai Baqeer ya maida ya rufe ya jingina da ƙofar tare da runtse ido, ta ina zai fara? Lallai babu inda soyayyarsu zata kai, laifin da ya aikata aka kulle Badaru a cell sai da yayi kwana ɗaya ana biyun aka sallameshi kaɗai ba zai bari a bashi aurenta ba. Abubuwan da suka faru a baya ne suke dawo mishi…….Itama Zainab tana shiga mota taja tana tafe abubuwan da suka faru ke dawo mata. Tuna Baya……
Asalin iyayen Alhaji Suleiman ƴan Ƙaraye ne sai dai zama daya dawo dasu cikin garin Kano. Mahaifinshi mai kuɗi ne don babban ɗan kasuwa ne a kasuwar kantin kwari. Shi kuwa asalinshi ɗan cikin birnin Kano ne, anan unguwar aka haifi iyayenshi da kakanninshi anan suka taso suka girma har suma suka yi nasu gidajen anan cikin unguwar, bai san wani wuri da zai kira da asalinshi ba bayan nan. A rayuwar Badaru babu abinda yake ƙauna irin karatun boko gashi Allah yayi mishi baiwa da iya zane, tun yana zane akan ƙasa ko ya samu gawayi ya zane sumuntin dakalin gidajen mutane har ya fara sayen pencir da littafi yana yin zanen akan takarda. Yaso mahaifin shi ya barshi yayi karatun boko inda zai faɗaɗa ilimin shi akan harkar zane mahaifin nashi yaƙi, babu irin roƙon da bai yi mishi ba amma sam yace ɗanshi ba zai je makarantar boko inda ake koyawa yara kafurci ba.
Haka nan ya haƙura ba don ranshi yaso ba sai don babu yadda zai yi, sai dai duk da hakan bai rabu da yin zane ba yana yi yana ajiyewa a cikin kayanshi ba don zasu yi mishi wani amfani ba sai don zanen yana sanya shi nishaɗi shine abu guda ɗaya da yake ƙaunar yi a rayuwa. A farko farkon rayuwarsu Badaru da Suleiman Ƙaraye abokai ne saboda gidajen iyayensu dake maƙwabtaka da juna sai daga baya abotar tasu ta fara ja baya saboda shi Suleiman yana ganin Badaru bai yi karatu ba don haka bai kai yayi abota dashi, ba to shima Badaru da yake ya kasance mutum ne mai tsananin zuciya yasa ya janye jikin shi daga Suleiman don ba zai ɗauki ƙasƙanci da cin fuskar da yake yi mishi ba duk suka haɗu a hanya ko wani wuri dai haka. Haka dai suka sake abokai kowa yana yi da daidai shi ba kowane lokaci suke gaisawa ba sai ta ƙure. Ana cikin haka ne Badaru ya haɗu da wata yarinya daya mato a soyayyarta, son Uwani yake yi bil haqqi da gaskiya. Kullum sai yaje zance wurinta saboda baya iya yin kwana ya yini bai sanyata a idanunshi ba. Kusan kowa dake unguwar yasan da soyayyar Badaru da Uwani saboda ita ma anyi dace bata kula kowa sai shi, duk wanda zai je wurinta yace yana sonta a take zata sallamesu tace akwai wanda take so, tace dole ta taya Badaru kishin kanta saboda bai rageta da komai ba, komai ya samu nata ne, kafin ya yiwa kanshi hidima sau ɗaya yayi mata sau goma don haka take tattalin farin cikin shi take gudun abinda zai ɓata mishi rai.
Ana haka har iyaye suka shiga maganar aka yi musu baiko. Tuni Badaru ya tayar da ginin gidanshi, yana ta shirin aurenshi da Uwani da aka saka rana har shekara biyu zuwa lokacin ya gama ginin da yake yi. Wata rana Suleiman na zaune a majalisar da suke zama shi da abokanshi Uwani tazo wucewa. Yana ganinta yaji ta kwanta mishi don haka ya nemi sanin gidansu a wajen abokanshi anan suke faɗa mishi ai budurwar Badaru ce don anyi musu baiko ma ranar auren kawai ake jira a ɗaura. "Ai dai baca riga an ɗaura ba ko?" Yace yana kallon abokinshi da yayi maganar. Da kai ya amsa mishi. "Ku zuba ido kuyi kallo ni na faɗa muku ba dai yarinyar can ta auri Badaru ba idan har ban sameta ba sai dai duk mu taru mu rasa gaba ɗaya." Wannan alwashin da yaci ne yasa yana tashi daga wurin bai dire ko ina ba sai a ƙofar gidansu Uwani yasa aka yi mishi sallama da ita. Da farko ta ɗauka Badaru ne yazo duk kuwa daba lokacin zuwan shi bane sai data fito taga wani mutum da bata taɓa gani ba. Haka dai Suleiman yayi amfani da wayewarshi irin ta ƴan boko ya tsara Uwani, tun tana ƙin kulashi har tazo bata san lokacin da ta fara son shi ba. Haka tayi ta yiwa Badaru halaye har dai daga ƙarshe ta fito ta nuna mishi ita fa ba zata aureshi ba don ta samu miji ɗan boko daya ƙware a iya gayu da ƙwalisa. Hankali a tashe Badaru ya baza neman saurayin da ya hurewa Uwani kunne har take neman guje mishi, anan yake jin ai Suleiman ne saurayin da take cewa tayi ɗan boko, baƙin ciki kamar ya kashe Badaru don a rayuwa idan akwai wata da yake so to Uwani ce, shine Suleiman zai je ya hure mata kunne ya rabashi da ita. Itace ya ɗauka ya nufi majalisar dasu Suleiman ke zama, yana zuwa wurin ya ɗaga itace zai kwaɗa mishi aka tattare aka hanashi. Badaru ya ƙara harzuka yana masifa yaa cewa Wallahi yau ko shi ko Sulaiman dan sai sunyi kunar bakin wake. Hankalin Sulaiman ya tashi ganin da gaske Badaru yakeyi zai halaka su, nan fa aka fara bashi baki. Haka yayi ta ɗurawa Suleiman zagi yana cewa sai yaga bayanshi tunda ya rabashi da masoyiyarshi tace bata son shi bayan daf ake da ɗaura musu aure. Wannan abun da Suleiman yayi wa Badaru ne yasa suka ƙara ƙullatar juna ƴar gaisuwar da suke yi ma tuni suka daina.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA SHIDA*
{86}
Wani abun Allah shi kanshi Suleiman ɗin da yayi ƙwacen budurwa sai kuma yazo bai auri Uwanin ba duk da tsananin son daya samu kanshi yana yi mata don da farko da niyyar yaudara yaje mata bare da yaji ance ita ce wacce Badaru zai aura sai yaga ai kawai bari yaje ya tarwatsa abun amma tun tafiyar bata yi nisa ba ya afkawa sonta mai ƙarfi. Sai kuma Mahaifin shi yace ba zai aureta ba saboda ta fito daga ƙaramin gida ma'ana iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne shi kuma yana ganin ai ɗanshi yafi ƙarfin yayi aure a irin wannan gidan. A haka Uwani tayi ba wan ba ƙanin karatun ɗan kama. Ita bata auri Badaru ba da yaso ta da dukkan gaskiyarshi saboda ta samu Suleiman ɗan gayu ɗan boko da take ganin yafi Badaru komai yace yana sonta, a ganinta irin wannan damar sau ɗaya take zuwa a rayuwa idan tayi sake ta rasashi ba ƙaramar asara zata tafka ba. Sannan ita bata auri Suleiman ɗin ba don iyayenshi suna ganin yafi ƙarfinta. Sai kuma daga baya ta dawo wajen Badaru shi kuma yace taje ya barwa Suleiman.
A Ɗambatta makarantar da aka turashi bautar ƙasa ya haɗu da Hafsatu a lokacin tana aji biyar na secondary shi kuma yana ɗaukarsu darasin English. Suleiman yana ganinta yaji ta kwnta mishi a rai, tun bayan rabuwarshi da Uwani bai sake gain macen data shiga ranshi farat ɗaya ba irin Hafsatu. Bai ɓata lokaci ba ya gabatar mata da kanshi ya miƙa mata ƙoƙon barar soyayyarta. Sai aka yi dace itama ya kwanta mata don haka bai sha wata wahala ba wajen yaɗa manufarshi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fara soyayya, babu daɗewa iyayen Suleiman suka nema mishi auren Hafsatu don koda suke a ƙauye ta fito daga babban gida irin wanda mahaifin Suleiman ke so don haka aka saka rana bayan ta gama makaranta da sati biyu. Anan unguwarsu mahaifin shi yayi mishi gini mai kyau a jikin gidan shi, kasancewar Suleiman tilon ɗanshi yasa yake gatata shi fiye da ƙima. A wannan lokacin matan Badaru uku, Jamila ce uwargida sai Abu sannan ya auri Fatima daga baya saboda daga Jamila har Abu ƴaƴa mata suke ta haifa mishi shi kuma namiji yake so shi yasa ya kasa haƙuri yana ganin kamar su ɗin basu da cikin haihuwar ƴaƴa maza. Fatima na zuwa ta samu cikin Baqeer wanda tsiransu da Kamalu wata uku ne itama Abu ta haifi ɗa namiji. Tunda Fatima ta haihu Badaru ya ɗauki son duniya ya ɗorawa Baqeer komai ya samu Baqeer, tun bai fara cin abinci ba ake sayo mishi kayan ƙwalama ya hana asauran ƴaƴanshi idan Fatima tayi magana yace ba haka ba wani sa'in har burin Allah ya isa yake mata in dai tabawa wani abu. Wannan bambancin da yake nunawa ne yasa sauran matan suka tsani Fatima da ƴaƴanta don Badaru ya fifita su akan su da nasu ƴaƴan don ko da Abu ta haifi Kamalu bai nuna wani farin ciki ba sai ma cewa da yayi sai yanzu zata haifa mishi namijin bayan ya riga ya samu, ranar suna baiji kunyar yankawa Baqeer katan rago ba shi kuma Kamalu aka yanka dan akuya karama. Tunda Badaru ya ƙyalla ido yaga Baqeer yayi gadon baiwarshi wajen iya zane yayi ta murna yana alfahari dashi yana jin shine zai cika mishi burinshi da nashi mahaifin ya daƙile mishi tun bai yi nisa ba, hakan yasa ya hana Baqeer sakat yana koya mishi dabarun yin zane, ko wasa Baqeer bai isa ya fita ba sai Badaru yace bayan ya bashi aiki bai yi ba shine zai ce ya biyewa yaran banza suna shashanci. A komai sai ya nuna bambanci don komai na Baqeer daban yake a wajen Badaru. Makarantun daya saka su daban su suna zuwa ta yaku bayi shi kuwa mai tsada mai kyau, haka ko wajen sutura ba iri ɗaya yake ɗinka musu ba, komai na Baqeer yafi kyau da tsada. Wannan bambancin da yake nunawa ne yasa ƴan uwanshi suka tsaneshi idan ka cire Hadiza da Maryam babu mai san shi a cikin ƴan uwanshi kowa haushin shi yake ji.