Baqeer complete - Chapter 63
Baqeer complete Chapter 63: Baqeer complete Chapter 63. ***** Baqeer kuwa yana fitowa suka yi kiciɓis da Kabiru gabanshi ne yayi wani mugun faduwa, tunani…
2,782 words
***** Baqeer kuwa yana fitowa suka yi kiciɓis da Kabiru gabanshi ne yayi wani mugun faduwa, tunani yake ba dai shine wanda ya buge a mota ba? Don in bai manta ba ya bincika kuma ance mishi ƙafarshi ta samu matsala, kar dai shine ya zo kawo ƙara? Shi kuwa Baqeer kallonshi kawai yake yana tunanin Kabiru ne? Salim ne yace "Baqeer are you okay?" Kai ya ɗaga mishi alamar eh, wanda hakan yasa Kabir yaji sunan Baqeer gashi dama yasan yaron Badaru ya bige, innalillahi, yanda yaga Baqeer na mishi wani kallo ne yasa ya tabbatar abinda ya kawosu kenan? Bakinshi na rawa yace "Ba dai Dady kuka zo kawo wa ƙara ba?" Kallonshi Baqeer yayi cike da mamakin kalamanshi sai kuma yayi tunani kila ko yasan yana son Zainab ne hakan yasa yace "Eh, laifi ne?" Kabiru ya matso daf da Baqeer yace "Ka dai sani Daddy ba zai taɓa bani laifi ba sannan kai tsautsayi ne baka sani ba? Nasan nayi laifi amma kaima sanda kake tafiya me yasa baka duba inda kake takawa? Da sai ka fara samuna na baka hakuri in kuma kuɗi kazo nema na baka amma ba wai ka kawo karata ba," yanda yake magana kaɗai zaka san a ruɗe yake, kalaman da yake yi ba sai Baqeer yayi tantama ba don abinda yake son cewa a bayyane yake, murmushi Baqeer yayi wanda yafi kuka ciwo sannan ya sake kallon motarshi, tabbas motar can ce ya gani sanda ya bugu, idanun Baqeer ne suka canza yanayi ya ciji leɓenshi na ƙasa yace "Sanda ka kaɗeni me yasa baka tsaya kaga halin da nake ciki ba?" Kabir ya haɗiyi yawun bakinshi yace "Ban san mutum bane sai daga baya, amma…" hannu kawai Baqeer ya ɗaga mishi ya kalli Salim yace "Mu tafi," yayi maganar cike da raunin murya. Tafiya suke kawai zuciyar Baqeer na sake tafasa, sam ji yake kamar kanshi zai faɗo saboda tashin hankalin daya shiga, Salim kanshi ya kasa magana saboda mamakin abubuwan dake faruwa, lallai wannan soyayyar ta Zee da Baqeer kyanta shine kowa bai san kowa ba ayi a rabu a haka amma ina zasu kai wannan ɓacin ran da suka shiga da tashin hankali?
****** Zee kuwa Mummy ce ta rungume ta kawai kuka take yi tana cewa "Mummy yanzu Daddy yayi mini adalci? Yayi wa Baqeer adalci?" Shafa bayanta tayi tace "Kiyi hakuri Zee ni kaina bansan meke damun senate ba, sai dai ya kamata muyi mishi uzuri kin dai san yadda yake ji dake." Kallon Mummy tayi Mummyn tace "Yadda yake ji dake ne yasa yake haka, kiyi haƙuri zan sake yi mishi magana sannan nasan zai fahimceki in kika nuna son da kike yi mishi." Kallon Mummy tayi tace "Mummy kiyi mishi magana don Allah bazan auri kowa ba sai shi, in kuma ba haka ba Allah ya shirya zama dani har tsufana." Kai ta jinjina tana riƙe da ita tace "Na sani, anjima kije ki ƙara sanar dashi ra'ayinki ni ina tare dake ba kuma zan yarda ayi miki auren dole ba, menene a ciki don bashi da ƙafa? Sannan shi faɗan da shikenan bazai wuce ba ko me?" Cike da gamsuwa da maganar Mummy tace "Mummy nagode da kika fahimceni." Hannu tasa ta share mata hawayenta tace "In ban fahimceki ba wa zai fahimceki?"
****** Badaru cike da ɓacin rai ya sauke wayar da aka yi mishi wai yazo ya ɗauki nakasashen ɗan shi. Me ya kai Baqeer gidan Alhaji Sulaiman? Abu ɗaya ne yazo mishi tabbas Kabir ne ya buge Baqeer kila shine yaje ya nemi hakkinshi, ai kuwa in haka ne dole yaje yaci zarafin Alhaji Salaiman tunda dai saboda shi komai na rayuwarshi ya ruguje sannan yana neman inda zai sauke ɓacin ran da yake ƙunsa kwanan nan. Da wannan tunani ya baza rigarshi ya fito daga ɗakin Jamila.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA HUƊU*
{84} Yana tafe fakam-fakam yana saƙar wasiƙar jaki yana ayyana abinda zai yi da kuɗaɗen da zai karɓa a wurin Suleiman Ƙaraye na fansar abinda ɗanshi yayi wa Baqeer. Har ya gama tsara yadda zai kasafta kuɗinshi don wallahi sai an biyashi asarar da aka janyo mishi tunda dai ya tabbata ɗan nashi ne ya kaɗe Baqeer da mota kaɗewar da itace sanadin halin daya tsinci kanshi a ciki yanzu. Yana zuwa gaban gate ɗin gidan ya hau bubbugawa da ƙarfi kamar zai ɓalla ƙofar gate ɗin. A fusace maigadi ya taso yana cewa "Kai da Allah ana zuwa, haba mutane sam babu hankali kazo gidan mutane kana buga ƙofa kamar qanda yazo yaƙi." Yana buɗe ƙaramar ƙofar suka haɗa ido da Badaru dake tsaye sai faman hura hanci yake yi. Yana ganin shine ya tare ƙofar ya hanashi wucewa. A wulaƙance ya kalleshi yace "lafiya?" Don yasan zuwan nan na Badaru ba alheri ne ya kawo shi ba tunda kuwa kowa yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu da maigidan. Harararshi Badaru yayi yace "Kauce ka bani wuri na wuce, ni ba da kai zan yi ba da ubangidan ka zanyi don shine tsaran yina ba kai ba." Ƙin matsawa yayi ya bashi wurin kamar yadda ya buƙata sai ma cewa yayi "Tsaya dai anan naje na faɗa mishi kazo amma bazan baru ka shiga ciki ba alhalin wancan zuwan da kayi ka tayar da tarzoma ƙiris baka yi mini sanadin aikina ba."
Jayayya ce ta ɓarke a tsakaninsu Badaru ya dage sai dai a barshi ya shiga shi kuma maigadi yace ba zai shiga ba sai dai ya jira yaje ya sanar da zuwanshi idan ance ya shigo sannan zai buɗe mishi ƙofa ya shiga. Hayaniyarsu ce ta fito da Alhaji Suleiman daga cikin gida, tun kafin ya ƙaraso wurin ya shaida muryar Badaru. Yana zuwa yace "lafiya? Me kazo yi a gidana? Idan kuma nakasashen ɗanka kazo ɗauka tuni ya tafi". Wannan kalami na Suleiman Ƙaraye sai ya ƙara tunzura Badaru, a masife yace "Waya nakasa min ɗan nawa idan ba ɗanka ba? Kuma ni zuwa nayi a biyani fansar nakasa ɗana da kuka yi tunda dai ya tabbata ɗanka ne ya kaɗeshi don nasan babu abinda zai kawo Baqeer gidanka sai don a biyashi diyyar ƙafarshi da ɗanka ya nakasta mishi. Waya sani ma ko da gayya kuka nakasta shi don kunga ya taso da basirar iya zane yana daf da tafiya gasar da zata ɗaukaka sunanshi a duniya kowa ya san shi." A sakarce Suleiman Ƙaraye ya kalleshi yace "Har wani ɗa gareka da za'a yiwa baƙin ciki, tun wuri gara kaje ka nemi wanda ya nakasta ɗanka amma ba Kabir ba. Kada kaga kwanaki kazo har gida kayi mini hauka na rabu da kai wallahi idan na sake ganinka a ƙofar gidana sai na ɗaure haka har igiya tayi rara kuma ka faɗawa gurgun ɗanka babu shi babu ƴata ko yana da lafiya shi bai isa na bashi auren ƴata ba bare yana gurgu nakasashe." Mallam Bala rufe mini gate ɗin gidana sannan daga yau idan ka kuma bari mahaukacin nan yazo mini gida a bakin aikinka." Ya shige cikin gida yana bambamin faɗa kamar shi in banda raini ta yaya za ace wai ɗan Badaru ne ke son ƴarshi. Yana shiga Mummy ta taso tace "Senate me ya faru? Tun daga waje nake jiyo faɗanka." Zama yayi akan kujera, tsaki yayi yace"Wancan wawan mutumin mana wai yazo karɓar diyyar nakasta ɗanshi da Kabir yayi." Zama tayi a kusa dasi tace "Badaru wai? Har yanzu bai bar batun Kabir ne ya kaɗe ɗanshi ba duk da an faɗa mishi a ranar da abun ya faru ma Kabir bai fita ba? Wai shin meke damun shi ne?" Tsaki yayi yace"Waya san mishi mana, koda yake duk laifin Zainab ne data rasa wanda zata ce tana so sai ɗan shi in banda haka shi ya isa yazo ƙofar gidana yace zai kawo mini zancen banza." Dafa kafaɗarshi tayi tana shafawa a hankali zuwa bayanshi tace "Ka daina ganin laifin auta ni na tabbata yaron nan yaudararta yayi in ba haka ba ina shi ina Zainab ka kuma fa san mutane ba wani tsoron Allah suka cika yi ba yanzu haka ba haka nan ya barta ba shi yasa gaba ɗaya ta susuce akan shi don in dai ba aikin asiri ba ban ga ta yadda za'a yi auta ta so gurgu ba gurgun ma ɗan gidan Badaru."
"Ni dai na faɗa ko mutuwa zata yi bazan aura mata ɗan Badaru ba, ah ti gara ma ki faɗa nata idan zata haƙura su daidata da Junaid tun wuri daya fiye mata." Tashi yayi ya bar parlourn ranshi yana ƙara ɓaci wai kamar shi ace gurgu ne masoyin ƴarshi gurgun ma ɗan Badaru, Badaru dai da tun asali babu wata jituwa a tsakaninsu.
***** Shi kuwa Badaru ganin an rufe mishi ƙofa ya juya ya kama hanyar gidanshi yana jin takaicin kai kanshi gidan Suleiman Ƙaraye da yayi, shi da yasan wata maganar Baqeer yaje ɗauko mishi me zai sa yaje wannan gidan ya jiyowa kanshi kayan takaici da baƙin ciki. Ace wai duk faɗin garin Kano Baqeer ya rasa ƴar da zai ce yana so sai ta Suleiman Ƙaraye. Tun daga soro yake ƙwala kiran Fatima har ya shiga ɗakinta, tana kwance tana jan carbi bacci ya kwasheta bata sani ba. Kamar a mafarki taji yana ƙwala mata kira, tana buɗe ido sai ta ganshi tsaye a kanta sai huci yake yi. Tashi tayi zaune tana gyara ɗaurin ɗankwalinta daya zame tana bacci. "Mallam sannu da zuwa," tace mishi duk kuwa da taga alamun zuwan nashi bana lafiya bane. Yana daga tsayen yace "Ki faɗawa nakasashen ɗanki ya kiyaye ni wallahi ya fita idona in rufe in ba haka ba sai na wulaƙanta rayuwarshi, in banda rashin mutunci ya rasa ƴar mutumin da zai so sai ta Suleiman Ƙaraye salon ya janyo mini ƙasƙanci da wulaƙanci a wajen shi." Mamaki ne ya kamata tace "Shi Baqeer ɗin ne yake son Zainab?" Tsaki yaja yace "Na dai faɗa miki ki gaya mishi babu shi babu ƴar wannan mara mutuncin mutumin. Haba ƴaƴa sun zama kamar ƴaƴan Allah bani bau guda ɗaya na kirki a ciki kowanne da irin baƙin cikin da yake cusa maka." Bayan fitar shi Umma na zaune tana jin mamakin wai Baqeer ne yake son Zainab, to a ina ma suka haɗu da har ya ganta yaji yana sonta? Ta yiwa kanta wannan tambayar sai kuma ta tuna ashe fa Dada tace mata Zainab ɗin tana zuwa a lokacin abun ya ɗaure mata kai sai dai bata zurfafa tunani ba ashe su soyayya suke yi ba'a sani ba. Shi kuwa Baqeer me ya kai shi bayan yasan akwai daɗaɗɗiyar rashin jituwa a tsakanin iyayensu, ture batun Badaru ma tunda ya kori Baqeer daga gidanshi amma Suleiman Ƙaraye fa ita tasan babu ta yadda za'a yi ya bashi auren ƴarshi alhalin yqna ɗan Badaru. Nisawa tayi ta ɗaga hannayenta sama a fili tace "Allah gamu gareka, idan har akwai alkhairi a taraiyarsu Allah ka tabbatar ka kawar da fitina." Wayarta ta janyo ta kira Baqeer sai dai ta kasa samunshi, haka tayi ta gwadawa bata sameshi ba har ta haƙura ta ajiye wayar akan ta ƙara gwadawa zuwa anjima.
***** Tunda suka bar ƙofar gidansu Zeey hankalinshi yake a tashe, daga shi har Salim an rasa me yiwa wani magana saboda kowa damuwa ce danƙare a cikin zuciyarshi. Shi Baqeer ma abubuwan ne suka taru suka yi mishi yawa ya rasa tunani ƙwaya ɗaya da zai kama. Tun lokacin da yayi accident bai ƙara tunanin wanda ya bugeshi ba don a ganinshi babu amfanin da sanin mutumin daya kaɗeshi zai yi mishi sai yanzu yake tuna yadda accident ɗin ya faru. Tabbas Kabir ne ya kaɗeshi ya janye motarshi ya tafi ya barshi a kwance a wurin, duk da bai ga fuskarshi ba amma ya gane motar tabbas ita ce motar da yake hawa yana baɗesu da ƙura idan yazo wucewa. A daidaita Salim ya tarar musu suka shiga ba tare da sun faɗa mishi inda zasu ba, sai da suka fara tafiya sannan Salim ya faɗa mishi mariri zai kai su ai kuwa ya yanka musu kuɗin da zasu biyashi, amsawa kawai Salim yayi don baya cikin yanayin da zai tsaya yin jayayya dashi. Lokaci zuwa lokaci Baqeer yake sauke wata ajiyar zuciya, ga wata irin rawa da yaji jikinshi ya ɗauka ga alama dai zazzaɓi ne yake neman kamashi. Tashin hankalin daya tsinci a ciki ba zai faɗu ba, a yadda Zainab ta shiga ranshi bai hango ta yadda zai iya rabuwa da ita ya zauna lafiya ba. Wannan wacce irin rayuwa ce? Ace akan abinda bai taka kara ya karya ba, saboda wani saɓani daya shiga tsakanin iyayensu a shekarun baya za'a hanasu samun farin cikin su. Kallon ƙafafuwan shi yayi sai kuma yayi wani murmushi mai ciwo cikin ranshi yace 'What do you expect? Kana tunanin kowa ne zai ganka akan wheelchair ya amince ya baka auren ƴarshi.' Shi yasan ko babu matsalar kasancewar Badaru mahaifi a gareshi to wannan nakasar kaɗai ta isa tasa a hanashi aure to bare kuma ga babban ƙalubalen Mallam Badaru daya kasance uba a wajenshi abokin adawar mahaifin Zainab kuma. Har suka isa gida Salim ya taimaka mishi ya fita daga cikin adaidaitan ya zauna akan wheelchair ɗin shi, hannu yasa ya gara tayoyin ya shige cikin gida bai tsaya jiran Salim dake sallamar mai adaidata ba. Yana shiga ya wuce Dada dake zaune a tsakar gida tana gyaran zogale zata yi musu kwaɗo in anjima. Kan katifarshi kawai ya faɗa ya kwanta a rigingine yana kallon rufin ɗakin, wasu ƙwalla ne suka taru a idanunshi sai dai ya hanasu zubowa. Cikin ranshi yana jin ciwo da nakasar shi ta kasance abu na farko da zai sa a hanashi aure kamar mutane sun manta ai da ba haka yake ba ƙaddara ce ta afko mishi kuma babu wanda ya wuce ta faɗa a kanshi shima. Salim ne ya shigo ya zauna a gefen katifar yana kallon Baqeer da lokaci guda duk ya zabge ya rame kamar wanda ya kwanta jinya. Tausayin shi ne yaji ya kamashi, a cikin lokaci ƙanƙani matsaltsalun rayuwa sun saka shi a gaba daga wannan sai wannan kamar baza su wuce ba sai dai yasan komai mai wucewa ne kamar yadda wancan ya wuce haka nan wannan ɗin ma zai wuce sai dai shi kanshi bai ji daɗin yadda mahaifin Zainab yayi musu ba kamar ya manta Allah ne mai tsarawa kuma shi ya ƙaddari baqeer ɗin da kasancewa haka da zai zaunar dasu yana faɗa musu maganganu na ɓatanci son ranshi. Kallon Baqeer ɗin yayi yace "Kayi haƙuri Baqeer nasan abinda mahaifin Zainab yayi mana da ciwo amma haƙuri zaka yi please kada kasa abun a ranka yayi ta damunka, a yadda nasan Zainab na sanka nasan ba zata taɓa yarda a rabaku ba." Bai cewa Salim komai ba don shi kaɗai yasan abinda yake ji a cikin eanshi, wani irin ƙuna yake ji da bai san ta yadda zai iya fasaltaw ba. Yasan ba Zainab ba kowacce mace yace zai nema wannan nakasar ita zata zame mishi cikas don ya san babu uban da zai ɗauki ƴarshi ya bawa gurgu. Idan yayi wannan tunanin ne hankalin shi yake ƙara tashi, shi kenan shi nakasashe ba mutum bane da za'a dinga gudun shi irin haka kamar wani annoba.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*UmmAsghar Ce* *Da* *Ayushe Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BIYAR*
{85}