Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 62

Baqeer complete - Chapter 62

Baqeer complete Chapter 62: Baqeer complete Chapter 62. ***** Baqeer kuwa tunda ya karanta saƙon da Zeey ta turo mishi yake saƙa da warwara, ta ina ta yaya…

3,670 words

***** Baqeer kuwa tunda ya karanta saƙon da Zeey ta turo mishi yake saƙa da warwara, ta ina ta yaya zai fara tunkarar Alhaji Suleiman a matsayin manemin ƴarshi? Shi yasan ko yana da lafiya ko ace ya cigaba da harkarshi ta painting Suleiman Ƙaraye ba zai bashi ƴarshi ba bare kuma da yake gurgu a yanzu wanda ya damu wata tawaya a jikinshi ga sana'ar ma yanzu yake ƙoƙarin ginata yasan babu ta inda zai fara tunkararshi a matsayin wanda yake son Zainab. Da yaga yawan tunanin da yake yi na neman saka mishi ciwon kai sai ya ɗauki waya ya ƙira Salim, tana fara ringing Salim ɗin ya ɗauka. Baqeer na jin muryarshi ya sauke wata ajiyar zuciya yace "Zainab na neman saka min ciwon kai Salim, wai kasan bayan dawowarmu saƙo ta turo mini akan naje naga mahaifinta gobe." "Daidai kenan, idan har da gaske kuke son juna dama ai kasan dole sai iyaye sun shigo maganar." A ɗan tsawace yace "Ka kuwa ji abinda nace Salim?" Yace "Ƙwarai kuwa naji ka kuma san hakan shine daidai kaje ka samu mahifinta kuyi magana shine zai san da gaske kake kana son ya baka auren ƴarshi." Wani zazzafan huci ya furzar yace "Wai ka manta waye mahaifin nata hala, Alhaji Suleiman Ƙaraye ne fa mutumin da kasan ko ina da lafiyar ƙafafu ba zai taɓa ɗaukar ƴarshi ya bani ba bare yaga naje mishi akan wheelchair." "Why do you lack confidence in your self Baqeer? Wannan abun da kake yi is an act of cowardice, idan har da gaske kake son Zainab bai kamata kaji tsoron haɗuwa da mahaifinta ba tunda kasan in dai har auren nata zaka yi dole ne ku haɗu." "Tabbas ina sonta sai dai wannan ba dalili bane da zai sa na kai kaina inda za'a wulaƙantani ba," yayi maganar yana jin wani ƙunci yana ƙara lulluɓeshi. Me yasa Zainab ta ɓoye mishi kanta gashi nan yanzu abinda ta janyo musu sun faɗa halin da ba lallai su iya fita ba. Nisawa Salim yayi yace "Idan har zaka ji shawarata ka shirya kaje wajen mahaifin nata baka san me zai faru ba, sai kaga Allah ya juya al'amarin yazo da sauƙi ba kamar yadda kai kake tsammani ba. Ina ganin hakan kawai zaka yi ka nunawa Zainab tabbas kana ƙaunarta kana kuma tare da ita a cikin kowane hali." Ɗan shiru yayi yana jinjina abinda Salim ɗin ya faɗa kafin yace "Shikenan Salim zan yi amfani da shawararka amma dai kasan bani kaɗai zan je ba ko? Sai kazo ka ɗaukeni mu tafi Allah ya tabbatar mana da alkhairi amma ni dai ina jinjina haɗuwar mu da Alhaji Suleiman Ƙaraye nasan zai yi wahala ya karɓe mu a matsayin manema auren ƴarshi." Murmushi Salim yayi yace "Ko kai fa? You have to be brave idan har da gaske kake son Zainab dole ka fuskanci dukkanin wasu ƙalubale da zasu iya kawo muku cikas wajen cimma burinku na zama mallakin juna. Goben zan zo muje In Sha Allah, kamar ƙarfe nawa zamu je?" "Ban sani ba gaskiya amma dai zan tambayeta naji sai na sanar maka." Da haka suka yi sallama da Salim yana fatan Allah yasa Suleiman Ƙaraye yayi musu bazata ya amince mishi ba tre da wata tangarɗa ba, sai kuma yayi wata dariya ta takaici don yasan abu ne mai wahala hakan ta kasance sai dai bawa baya cire da abinda yake so yana fatan kada su samu ko wacce irin tangarɗa daga wajen shi. Wayarshi ya ɗauka ya turawa Zainab message. _What time Daddyn yake son ganin mu?_ Ajiye wayar yayi ya kwanta yayi rigingine yana kallon ceiling, gaba ɗaya zuciyarshi bata yi mishi daɗi, shi yasan mawuyacin abu ne taraiyarshi da Zainab ta cigaba don shi yasan waye mahaifinta ya kuma san irin burin da yaci akan ƴarshi, shi yasan ba irin shi ne mijin da yake yi mata fata ba to amma ya zai yi da soyayyarta da tayi mishi wani irin kamu, soyayyar da tasa yake jin ashe da can ba son Asiya yake yi ba don bai taɓa jin yadda yake ji akan Zainab akanta ba. Zumbur yayi ya tashi zaune jin ƙarar shigowar text a wayarshi. Ɗaukar wayar yayi ya duba. _Ƙarfe huɗu zuwa da rabi haka_ kawai ta rubuto. Ajiye wayar yayi haka nan yake jin gabanshi yana faɗuwa, sai yake jin kamar ranar rabuwarshi da Zainab ce tazo don shi dai ya kasa yardar wa ranshi wai Suleiman Ƙaraye zai bashi auren ƴarshi ko ace yana da lafiya kuwa abu ne mai matuƙar wahala bare yadda kowa yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu shi da Badaru.

***** Umma na zaune a ƙofar ɗakinta tana gyaran kayan miyar da take so ta yiwa Dada da Baqeer miya Badaru ya shigo. Dama sallama ba al'adar shi bace don yace gidanshi ne daya gina da gumin shi babu sisin kwabon uban kowa don haka bai ga dalilin da zai sa don zai shiga ace sai yayi sallama ba. Ko ɗaga bata yi ta kalleshi ba tayi mishi sannu da zuwa tana cigaba da aikinta. Kallonta yayi sheƙeƙe ya taɓe baki yans lura da yadda ta bawa aikin da take yi muhimmanci kamar bata san da tsayuwarshi a wurin ba. "Wato Fatima ba zaki fito min da kuɗin filina ba ko?" Ɗagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuye ta cigaba da cire hancin tattasai cikin sanyin muryarta tace "Ai na faɗa maka abinda aka yi da kuɗin filin tuntuni bana jin za'a samu saura." Wani irin takaici ne ya lulluɓeshi, shi ya rasa ne ya yiwa Fatima da tayi mishi irin wannan muguntar ta sace mishi takardar fili ta kaiwa nakasashen ɗanta idan ma shi ɗin ta kaiwa da gaske don ga labarin da Bashir ya bashi bai kamata ace zai hau adaidaita ba idan shi ta kaiwa takardar filin ai sai dai ya sayi mota ana jan shi. "Ke dai wallahi Fatima muguwa ce azzaluma, sai Allah ya bi min hakkina a kanki wallahi," ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka, yana jin baƙin cikin filin nan da Fatima ta rabashi dashi. Ita kuwa ko kallonshi bata kuma yi ba haka ya gaji da tsayuwa ya shige ɗaki yana kumfar bakin kotu ce zata rabashi da Fatima idan har bata dawo mishi da kuɗaɗen filin ba tunda dai yasan an sayar gashi an faɗa mishi har an fara gini a wurin. Babbar damuwarshi jarin shi da yayi ƙasa bai san ta inda zai farfaɗo dashi ba, dama akan filin ya dogara to ashe waccan muguwar matar ta rabashi dashi yana zaune da baki buɗe shine bai sani ba.

***** Tunda ya tashi da safe yake jin faɗuwar gabanshi na ƙaruwa. Haka ya yini sukuku ko abinci kasa ci yayi haka Dada tayi ta fama dashi akan yaci abincin har ta gaji ta watsar dashi ta cigaba da ƴan sabgoginta. Ita bata san yadda yake ji ba shi yasa ta dameshi da batun wani abinci ko ance mata yana da ntsuwar da zai iya zama yaci abinci ne. Tun bayan azahar ya tashi ya shirya a cikin wata dakakkiyar shadda kalar light brown sai aka yi mata aiki da zare kalar coffee a irin waɗanda ya ɗinka ne, sosai yayi kyau ya fito cikakken namiji tsaf gashi dama tubarkallah Allah yayi mishi siffa irinta cikakken ɗa namiji gashi da wani irin kyau, sai abun ya haɗu da iya gayu da tsafta. Turarukanshi ya ɗauka ya feshe jikinshi dasu, wayarshi ya ɗauka ya fita parlourn Dada yana zaman jiran isowar Salim don ya matsu su bar gidan ko sun je suyi abinda ke gabansu yasan matsayin soyayyarshi da Zainab. Bai daɗe da zama ba Salim ya iso shima cikin shiga irinta Baqeer. Dada na ganinshi tace "Hala gaisuwar surukai zaku shi yasa kuka yi gayu haka." Murmushi Salim yayi yace "Ashe bai faɗa miki ba, mahaifin Zainab zamu je mu gaisar," shi kuwa Baqeer cewa yayi "da bama kwalliya sai zamu wani wuri." Harararshi tayi tace "Idan nayi magana daga kai har Zainabu kuce ba haka ba ashe ni kuka ninke baibai, to Allah ya tabbatar mana da alkhairi wallahi naji daɗi." "Ameen," Salim yace. Ƙara kallonsu Dada tayi tace "Ai gara ku hanzarta ku tafi kada suyi ta jiranku, idan kun je ku cewa Zainabu ina gaisheta akwai kuma tamu ni da ita zata zo ta sameni har gida naji dalilin wannan ƙunbiya-ƙunbiyar." Dariya Salim yayi yace "zan kuwa faɗa mata Dada, sai mun dawo." Tunda suka fito babu wanda yayi magana, shi dai Salim ganin kamar Baqeer baya cikin nutsuwa yasa yayi shiru da bakinshi ya ƙyaleshi yaji da damuwar shi, shi kuwa Baqeer tunanin bai san abinda zasu je su riske ba ne yafi tsaye mishi a rai, yasan zai yi wahala su samu karɓuwa a wajen mahaifin Zainab. Anan cikin unguwar suka tsaya a masallaci suka yi sallar la'asar, haka Baqeer yayi ta gaisawa da mutane suna yi mishi jajen abinda ya faru. Bayan sun fito daga masallaci Salim na turashi suka ƙarasa gidan su Zeey. Ciro wayarshi yayi ya ƙirata, tana ɗauka yace mata "Gamu a ƙofar gida." "Okay bari nazo na shigo daku," kawai tace ta ajiye wayar. Basu wani daɗe suna jiran ba sai gata ta fito cikin material ɗin daya ɗinka mata. Kallon-kallo suka hau yi zuciyoyinsu cike da bege da ƙaunar juna. Sosai Baqeer yaga ta ƙara yi mishi kyau gashi kayan sun karɓeta kamar yadda yayi hasashe. Salim ne ya katse kallon-kallon da suke yiwa juna yace "Hajiya Zeey barka da yamma." A kunyace tace "barkanmu dai, ku shigo." Tayi gaba suka bita a baya. A parlourn karɓar baƙin Alhaji Suleiman ta sauke su, sai da ta zauna suka ƙara gaisawa da Salim sannan ta kalli Baqeer ta sakar mishi wani ƙayataccen murmushi tace "Ya Baqeer ina yini," cikin wani salon magana da ita kanta bata san ta iya ba kawai dai ta tsinci kanta dayi. Lumshe ido yayi ya mayar mata da murmushin kwatankwacin irin wanda tayi mishi yace "I'm fine and you?" Karkata kai tayi tana dariya tace "Lafiya lau, sai dai fa ban yi tunanin da gaske zaka zo ba." "Me yasa?" Ya tambayeta yana tsatsareta da ido. Ɗan kawar da kanta tayi daga kallonshi da yake neman kassara mata jiki tace "Saboda jiya ka nuna min ba zaka iya pursuing ɗina ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina sonki Zainab har ban san yadda zan kwatanta miki ba amma ina tantama idan mahaifinki zai amince ya bani aurenki, kin dai san komai ba sai na faɗa miki dalili ba." "Kasancewarka tare dani ne abu mafi muhimmanci da nafi buƙata, ni kai kaɗai nake so kai kaɗai kuma zan iya aure don haka kada kasa damuwar komai a ranka In Sha Allah bazan bari kowa ya rabamu ba." Sun daɗe suna musayar kalamai kafin ta tashi ta shiga cikin gida akan zata faɗawa Daddy zuwansu. Kitchen ta fara shiga ta bada umarnin akai kayan motsa baki guest sitting room ɗin Daddy sannan ta shiga ɗakin Mummy tace mata ta faɗawa Daddy ga baƙin sun zo. Ɗakinta ta shiga tana addu'ar Allah yasa kada Daddy ya basu matsala don ita dai baza ta yarda a rabata da Baqeer ba domin kuwa shine farin cikinta dashi kaɗai zata iya rayuwa. Tunda Mummy ta shiga ta faɗa mishi baƙin sun iso yake baƙin rai, ya daɗe bai tashi ya shirya ba don sai da ya ɓata fiye da mintuna talatin kafin ya tashi ya canja kaya ya fita. Fuska a murtke ya shiga sitting room ɗin, Salim dake zaune akan kujera yayi saurin zamowa ƙasa ya zauna yana gaishe shi. Wani irin kallo Daddy yake yi mishi don ya ɗauka shine manemin auren Zainab ɗin. Shima Baqeer ya shiga gaisheshi cikin girmamawa. Kallo ɗaya yayi mishi ya mayar da kanshi wajen Salim yace "Kai ne mai san ƴata?" Girgiza kai Salim yayi yace "A'a bani bane abokina ne Baqeer," yace yana nuna Baqeer dake zaune akan wheelchair ɗin shi. Daddy bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba yace "What? Gurgun? Gurgun ne ke neman auren ƴata?" Yace yana nuna Baqeer da ya sandare a zaune da ɗan yatsa. Da gudu Mummy ta ƙaraso cikin parlourn don taga me yasa Daddy ihu irin haka.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*UmmAsghar Ce* *Da* *Ayushe Muhd*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA UKU*

{83}

Zee sam ta kasa zama sai zarya take yi zuciyarta ta kasa nutsuwa, Mummy ce ta riƙe hannayenta tace "Kar ki damu auta komai zai tafi daidai." A hankali ta jinjina kai alamar eh sannan tace "Matsalar nakasa da nace miki yana dashi ne bana so Daddy ya wulakantashi saboda wannan, nasan halinshi," ta ƙarasa maganar tana neman shiga falon, da sauri Mummy ta sake riƙota tace "Kar ki shiga shi kanshi Baqeer ɗin ba daɗi zai ji ba in ya ganki." Da mamaki ta kalli Mummy, ya aka yi tasan sunanshi? Don a iya saninta bata taɓa sanar da ita wanene wanda take so ba, baki ta buɗe zata yi magana suka jiyo muryar Dady daga falo yana cewa "Gurgu? Kai wannan wasa ne bana son shirmen banza da wofi, ni? Kamar ni gurgu mara ƙafa zai zo yace yana son ƴata? Uban waye ya tsaya maka da har ka rainani zaka tako kazo cikin gidana?" Baqeer kalaman Daddy sun kai shi maƙura sai dai wahalar da Zainab tayi dashi ne yake tunowa, hakan yasa ya daure don kalaman Alhaji Sulaiman ba ƙaramin ɓata mishi rai suka yi ba, gurgu ba mutum bane kenan ko me? Daddy yana hura hanci yace "Kai kaga mun yi maka kama da inda zaka zo da kekenka? Dalla fita ka bar min gida kafin nasa securities su fitar min da kai." Zee ce ta shigo ciki da sauri, daidai nan Baqeer ya saki wani murmushi yace "Ashe girma bai sa ka canza halayenka ba." Waigowa yayi ya zabgawa Baqeer wani mugun kallo yace "Me kace?" Kai kawai ya girgiza yana ɗagowa suka haɗa ido da Zainab, murmushin takaici da tausayawa kansu yayi, lallai daya sani da ya riƙe son da yake yi mata a zuciyarshi tabbas da yasan ƴarshi ce da ya gwammace ya nuna baya sonta a ƙalla zata auri wanda yake sonta wanda zai kula da ita kamar Junaid. Shi da budurwarshi ta gujeshi ma da wannan larurar ta sameshi ina ga Alhaji Sulaiman? "Me kace nace? Kai dalla ja keken guragunka ka bar min gida kaje can bakin titi nan ne ya dace da kai, ni ko mai gadin gidana gurgu bai kai yayi ba bare auren tilon ƴata," Yana kumfar baki yake maganar bai jira komai ba ya cigaba "In dai har Zainab zata kawoka a matsayin wanda take so to tabbas asiri kayi mata, wawan banza wawan wofi kai dai kayi asara wallahi....." Zee ce tace "Ni nake sonshi Daddy," tayi maganar idanuwanta na kan Baqeer, a fusace ya zabga mata wani kallo, fuskar nan tashi duk ta sake canzawa yana ƙara kumburota yace "Me kika ce?" Ta maida kallonta kan Daddy tace "Ni nace ina sonshi, laifi ne?" Baqeer ne ya katseta da cewa "Koma ciki." Kallonshi tayi kamar zata yi kuka, kai ya jinjina mata alamar babu komai, hannu tasa ta shafi fuskarta sannan ta juya, mamaki ya kama Daddy ganin duk gardama irinta Zee gashi tana abu babu musu, ai kamar an fusatashi yace "Waye ubanka? Sannan mema abokinka yace sunanka?" Baqeer ya haɗiyi wani yawu yace "Baqeer sunana." Yanayin Daddy ne ya canza zuwa mamaki yace "Baqeer?" Nan da nan ya tuno zuwan Badaru gidanshi akan ɗan shi yasa yaronshi hatsari, abinda ba zai iya tunawa ba yace ƙafar shi ta saku matsala ko bai faɗa ba? Don shi a trayuwarshi ma bai taɓa jin sunan Baqeer ba sai da Badaru ya sawa ɗan shi, bai mantawa sanda aka sa sunan har sai da yace menene ma'anar Baqeer? Kai ya girgiza don tabbas yasan ba dai ɗan Badaru ba. Cike da zargi Alhaji Sulaiman yace "Ba dai zaka ce min Alhaji Badaru ne mahaifinka ba?" Yanda Baqeer ya kalleshi ne yasa yayi baya ya zauna akan kujera, sai kuma ya miƙe yana haɗe yatsunshi yace "Wai yaron Badaru ne Baqeeru? Ka gaggauta fitar min daga gida ko sai nasa an kulleka, kai dan gidanku ni sa'anka ne? Ko nayi maka kama da wanda zaka zo ma kace kana son ƴa ta? Ba ma gurguntaka kaɗai ba yaron Badaru? Yaron Badarun ma ɗan iskan yaron da ka ja mana tashin hankalin da aka yi mana tsakani?" Cikin ihu yake maganar wanda yasa Zainab dawowa. Baqeer ne ya kalli Alhaji Sulaiman dake kumfar baki yace "Zan ƙara sanar da kaina, nine Muhammad Baqeer Badaru wanda yake son ƴarka Zainab......." Cikin hanzari Alhaji Sulaiman yayi kanshi a fusace don ranshi ya ƙara ɓaci yana ji zuciyarshi har wani tafasa take yi, Zainab har tayo ciki don ta tare sai taji Baqeer yace "Daddy!" Cak Alhaji Sulaiman ya tsaya, eh lallai Baqeer ya gama raina mishi hankali, yama rasa ta inda zai fara ci mishi zarafi, ya zai yi ya tozarta Baqeer yanda ya gama ci mishi mutunci, komawa yayi ya zauna ya kalli Baqeer kawai kafin yace "Daddy?" ya saki wani murmushin takaici sannan ya ɗauki waya ya danna, wani yake kira yace "Naga kasuwarku ɗaya da Badaru ko zaka kirashi kace yazo ya ɗauki nakasasshen ɗanshi da yazo bara gidana?" Yana kashe wayar ya kalli Baqeer yace "Daga Badaru har uwarka wannan karon sai na tozartaku mutanen banza mutanen wofi." Baqeer kallon Daddy yayi don kalamanshi sun kai shi bango, ƙasan leɓenshi ya ciza don duk yadda yaso ya daure da ɓacin ranshi ya kasa, abubuwan da suka faru baya ke sake dawo mishi tun kafin Alhaji Sulaiman ya tara musu jama'a gwara su bar gidan, kallon Salim yayi wanda gaba ɗaya kana kallonshi zaka san cikin takaicin abinda yake faruwa yake, kai ya ɗaga mishi alamar su tafi, shi kanshi Salim baya ji zai iya cewa Baqeer ya cigaba da zama, Zee wacce Mummy tayi saurin riƙeta ya kalla, ya kauda kai kawai ya fara tura kekenshi, hankali a tashe tace "Ya Baqeer!" Ta kira sunanshi tana tahowa inda yake bayan ta ƙwace hannunta daga cikin na Mummy, hawaye ne fal cikin idanuwanta tana zuwa inda yake suka zubo ta ƙara cewa "Ya Baqeer!" Wani murmushi yayi mata wanda kana ganinshi kasan na menene sannan ya cigaba da tura kekenshi, tana neman binshi taji Daddy yace "Wallahi kina fita sai dai ki nemi wani uban ba ni ba." Waigowa tayi da mamakin halayen shi ta zuba mishi ido tana tunanin ma me ya kamata tayi. Baqeer bai ko ƙara waiwayensu ba ya ja kekenshi kawai Salim ya turashi don ma suyi saurin fita. Zee hawaye tasa hannayenta ta share tana kallon Daddy da har yanzu bai gama masifar shi ba tace "Ka shirya ganina a cikin gidan nam har na mutu kuwa don Dady ka sanni ka kuma san kafiya ta, ban taɓa son wani ba sai Baqeer kuma shi kaɗai zan aura, in har kana son ganina nayi aure to ka taimaki kanka ka barni na aureshi." Tana kaiwa nan ta ruga ciki da gudu don ba ƙaramin wulaƙanta ta Daddy yayi ba, ta sani shekarun baya tana yarinya aka yi abun kuma babban abinda ya janyo saɓanin laifin tane da tayi magana tasan da abun bai kai haka ba, in bata manta ba tun daga case ɗin ta fara canza halayenta, ko rai zai ɓaci to fa zata faɗi abinda ta sani abinda kuma ke ranta. Daddy wani takaici ne ya ƙara kamashi ji yake yi ko sanda yaji Nabila ƴar Mummy ce ranshi bai ɓaci ba irin yau, kamar shi? Kuma a rasa ma wa zai ce yana sonta sai Baqeer? Lallai bai taɓa fuskantar ɓacin rai irin wannan ba, ga siyasar shi na kawo kai za'a tantance wanda zai hau takarar wato primary election, shafar suman kanshi yayi yana jin wani ɓacin rai, Mummy ce ta zauna kusa dashi tana shafa gaɓɓan bayanshi tana cewa "Calm down Senate, tsautsayi ne ya afka amma yanzu komai zai warware ai insha Allah, bansan ya aka yi wannan abun ya faru ba." Kallonta yayi idanunshi kaɗai sun isa kasan ɓacin ran da yake ciki yace "Kina ina har hakan ta kasance? Baqeer? Ni Zainab zata gayyatowa matsiyata cikin gida? Taya ma har ta ganshi har suka fara magana?" Kai Mummy ta girgiza alamun bata sani ba kafin tace "Ni kaina abun ya bani mamaki amma in ka duba laifin na yaron ne, taya zai so Auta? Ta yaya? Ai yasan haɗin ba ɗaya bane." Tsaki yayi yace "Zancen banza zancen wofi ni ko da ƙafar shi ai wallahi bai kai na bashi ƴata ba bare," ya ƙarasa maganar cike da ɓacin rai wanda yake ji kamar zuciyarshi zata fito, miƙewa yayi yace "Duk laifinki ne don kece kike barinta take fita, inba haka ba taya ma ta haɗu da shashashan can?" Yaja tsaki ya wuce ciki da ƙarfi ya rufo kofa. Mummy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe tayi ɗakin Zee zuciyarta duk ba daɗi, kuka Zee take yi sosai don abinda Daddy yayi ba shakka tasan shikenan Baqeer ya haƙura da ita don dama tasan tunda yasan wacece ita take tantama amma gashi ya daure yazo an tozartashi. Hawaye ta sake sharewa tana kallon wayarta, kiranshi take son yi amma bata san taya zata fara ba. Ƴar karamar ƙara ta saki daidai nan Mummy ta turo ƙofa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull