Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 61

Baqeer complete - Chapter 61

Baqeer complete Chapter 61: Baqeer complete Chapter 61. Da sauri Salim ya taho ya riƙe keken Baqeer da yake ta saurin turawa saboda yana son barin unguwar,…

3,160 words

Da sauri Salim ya taho ya riƙe keken Baqeer da yake ta saurin turawa saboda yana son barin unguwar, kallon Salim yayi wanda shi kanshi kallon shi yake cike da dauriya yace "Baqeer ina zaka kake wannan saurin?" Kallonshi yayi cike da mamaki da takaici, sai a lokacin ya kalli Zainab dake tsaye a inda ya barta, kanshi ya kauda da sauri sannan ya cigaba da tura keken, Salim ne ya kalli ledar dake hannunshi wanda ake ta murna za'a bawa Zainab, shafa bayan kanshi yayi yana tunanin abun yi. Wurin Zainab ya koma dake tsaye kawai tana share ƙwalla, ledar ya miƙa mata, amsa tayi tana kallonshi, muryarta na rawa tace "Salim please ka kula dashi." Kai ya ɗaga sannan yace "Ki koma ciki In Sha Allahu babu abinda zai faru." Ta ɗaga kai alamar to sannan tace "Nagode," tayi maganar tana juyawa, sai daya ga ta shige gida sannan yabi bayan Baqeer lokacin har ya kai ƙarshen layin, adaidaita ya tarar musu suka bar layin suna fatan babu wanda ya ganshi. Shi dai Baqeer tunda ya zauna bai ce komai ba, zuciyarshi ce kawai take tafasa, shi yasa ashe ko da wasa bata so tayi maganar data shafeta, hannayenshi ya dunƙule zuciyarshi na wani irin zafi, how? Taya zata mishi haka? Sai data bari ya gama mutuwa akan sonta? Shi a kanta zai iya rufe ido yace sai ita to amma me? Mahaifinta ya sani ko duniya za'a haɗu a bashi baki ba zai bashi aurenta ba, shi bai damu da yardar Badaru ba sai dai shi yasan da ƙafarshi ma mahaifinta ba yarda zai yi ba bare babu, kanshi kawai ya kawar yana kallon titi shi kuma haka ƙaddararshi take? Daga wannan sai wannan? Yanzu da yake sa ran komai yana tafiya daidai ashe yanzun ma wani abun zai ƙara ɓullo wa? Har suka isa gida babu wanda yayi magana, shi dai Baqeer kawai ya wuce ɗaki Dada tana jiyosu ta fito tana tambayar jikin Zainab, sai Salim ne ya tsaya ya bata amsa don Baqeer ɗakin shi kawai ya shiga ya kulle, jikin ƙofar kawai ya jinginar da kujerar shi ta wheelchair yana maida numfashi, komai ne yake sake dawo mishi kamar a yanzu ake yinsu, tashin hankalin da aka sakasu shida iyayenshi a dalilin ta ne yake sake dawo mishi, amma ya aka yii bai ganeta ba? A iya saninshi tana da ƙiba to yanzu ta zama siririya duk sai kamanninta suka canza, idanunshi ya runtse sai dai fuskarta ce tana mishi magana ɗazu kawai ke dawo mai. Wayarshi ce ta fara ƙara ɗagota yayi ya zubawa wayar ido wanda sunanta ne ke jikin allon wayar, ido ya rufe ya sake buɗewa yana kallo har ta katse, bata sake jira ba ta ƙara kira ji yayi zuciyarshi ta kasa jurewa, duk da yasan ba abu ne mai yiwuwa ba amma a ƙalla ya sanar da ita abinda ke ranshi, wayar ya ɗaga ya karata a kunnenshi sai dai ya kasa magana, ita ma a bangarenta da alama ta kasa magana don ajiyar zuciya kawai suka sauke a tare, ƙasan lebenta ta ciza da har yanzu bata jin daɗi tace "Ya Baqeer!" Ido ya runtse gam don kiran data yi mishi har tsikar jikinshi sai da yaji ta tashi, yawun bakinshi ya haɗiya yace "Why?" Wasu hawaye ne suka gangaro saman kuncinta tace "I'm really sorry wallahi da farko ba wai ɓoye maka nayi a sanina ba, lokacin da muka yi ta haɗuwa da farko coincidence ne don ban ganeka ba sai sanda naje wurin Umma naga ashe kaine, at that time I feel so bad na ganin abinda ya sameka." Wani murmushin takaici yayi yace "Kenan duk abinda ke faruwa ƙarya ne? Taya zaki bari sai da na gama kamuwa da sonki nake ji bazan iya rayuwa babu ke ba sai naji kece wacce ni nasan ko za ayi me mahaifinki ba zai taɓa amince wa ba." Ji tayi komai na jikinta ya tsaya ta sauke wata ajiyar zuciya tace "Ya Baqeer me kace?" Sam abinda ke ranshi ya faɗa wanda hakan yasa bai gane me take son ya maimaita ba, Zee ta daure tace "Ya Baqeer please me kace? I'm sure kunnena jiyo mini yayi zancen soyayya." Cike da takaici yace "Who cares Zainab? Ko kin manta ƙatuwar katangar dake tsakaninmu? Da so da rashinsa yanzu….." Katseshi tayi da sauri da cewa "I care, sannan for me that's all that matters, duk duniya babu wanda ya isa ya rabani da kai, kalmar so kawai nake jira naji daga bakinka kuma naji ba damuwa ta bane ko ma me zai faru." Yasan halinta ba abinda baza ta iya aiwatarwa ba sai dai shi a dalilin so ba zai taɓa saka yan uwanshi cikin matsala ba, especially Umma hakan yasa yace "Mun gama magana, bye." Ba tare da ya bari ta ƙara magana ba ya kashe wayar ma gaba ɗaya, yasan waye Alhaji Sulaiman ya kuma san akan ƴar lelen ƴar shi babu abinda ba zai aikata ba, shi kuma duk da yasan yana mugun sonta yana ji in har bai aureta ba ya haƙura da aure kenan, amma fa ba zai salwantar da rayuwar ƴan uwanshi saboda ita ba. Takaici ne ya kamashi kawai ya cillar da wayar kan gado yasa hannu biyu yana dafa kanshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi. Zee kuwa hawayenta ta share don tabbas babu mai rabata da Baqeer, ɗakin Mummy ta nufa lokacin tana zaune tana duba wasu takardu wanda da alama masu amfani ne, Zee na shigowa ta ɗan maidasu gefe kallo ɗaya tayi mata tasan akwai matsala, hakan yasa ta ware mata hannu ita kuma ta ƙara so ta shiga jikinta, duk kuwa da haushin Mummyn da take ji a yanzu neman me lallashinta take yi, kuka kawai ta saka tace "Mummy ki yiwa Daddy magana ni wallahi da wanda nake so sannan aurenshi nake son yi yanzu." Mummy cike da mamaki ta ɗagota tace "Shine wanda kike bani labari?" Kai ta ɗaga tana sake goge ƙwalla tana cewa "Shi Mummy bana ji zan iya rayuwa babu shi, don Allah ku barni na aureshi ni a yanzu ma a shirye nake." Dafata Mummy tayi tace "Shifa? Yace yana sonki?" Kai ta ɗaga cike da alfahari da hakan tace "Eh Mummy don haka ki sanar da Daddy." Kai ta ɗaga sannan ta shafi fuskarta tana goge mata hawaye tace "Zazzabi kike yi ne? Naji jikinki da zafi." Hannu tasa ta riƙe hannun Mummy tace "Ba shine a gabana ba Mummy ni dai ki mishi magana." Shiru Mummy tayi kafin tace "Ko ma menene kiyi ina bayanki, abinda kike so as always nima shi nake so, sannan ko ya yake ina bayanki, kawai dai ina tsoron magana ne kin san har yanzu bai sauko da abinda ke faruwa ba." Kallonta Zee tayi sai yanzu ma ta tuno da ashe itama fushi take yi da Mummyn tsabar ta matsu yasa tama manta. Neman miƙewa tayi da sauri Mummy ta riƙota tace "Zainab please ban da ke, ki tuna shaƙuwar dake tsakanin mu, nasan nayi muku laifi akan Nabila amma a matsayinki na mace ya kamata ki tausaya mini ki fahimceni." Kallonta Zee tayi tace "Zamu yi magana daga baya, don maganata akan su Ummi ne," tana kaiwa nan ta fito, ɗaki ta wuce tayi sallar la'asar sannan ta kwanta, tun ruwan tea babu abinda ta sha don bama ta jin shan komai balle taci wani abun, ledar da Salim ya kawo mata kaya ta bude tana kallon kayan da Baqeer ya ɗinka mata ta tabbatar yasha wuya kafin ya haɗa ɗinkin. Kuka ne kawai taji ya ƙwace mata don da alama abinda zuciyarta ke son yi kenan, ta zubar da ƙwallar har ta gaji, kuka take yi sosai tana rungume da material ɗin.

Daddy wanda shigowarshi kenan yake jiyo kukan Zainab, hankalinshi a tashe ya nufi ɗakin don ya tabbatar dangin mamanta ne suka sakata wannan kukan, kuma tabbas ba zai ƙyalesu ba har Ɗambattan zai je duk sai ya ci mutuncinsu, dama shi yasa ko da wasa baya son taje yanzu gashinan abinda ta jawowa kanta, ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa bai jira ta amsa ba ya tura ƙofar don zuciyarshi har wani azalzala yake. Rai a ɓace yace "Da da nake hanaki zuwa ai baki yarda ba yanzu da alama kin san amfanin abinda nake yi miki tunda gashi kema da kike tasu sun gwada miki halinsu." Kallonshi tayi ta ajiye kayan sannan tace "Ni ba saboda su nake kuka ba." Da mamaki yace "Saboda wa kike kuka to? Ko akan waccan shashashar Nabilan ne?" Kai ta girgiza tace "Ba'a kanta bane sannan Dady kada dai ka manta ƴar Mummy ce kake kiran ta shashasha." Tsaki yayi ta sauko ta tako gabanshi, kallonta yayi da son jin me ya faru don sai yaga gaba ɗaya ta canza, anya ma sun kular mishi da yarinyarshi kuwa? Tsugunawa tayi tace "Daddy surukinka nake so yazo ya gaisheka shine nake jira ka sanar dani lokacin da kake nan." Wani wulaƙantaccen kallo yayi mata yace "Ina da wani suruki ne bayan Junaid? Kin dai san bana son shirme ko?" Ta dake tace "Junaid ba surukinka bane sai dai in wata ƴar kake dashi daban da zaka bashi." Fuska a tamke yake kallonta, ɓacin ranshi ya fito bayyane a fuskarshi yace "Ke sam baki da kunya ko? Ni kike yiwa magana haka?" Dakewa tayi tace "Daddy yaushe kake gida? Zai zo ku gaisa?" Yatsa ya nuna ta dashi yace "Kin san Allah ranki kike so ya ɓaci, ki kawo mini wani ɗan iska gida ki gani." Mummy ce ta katseshi da cewa "Senate please! Ka tambayeta wanene? Ko kuwa ka ganshi bai yi maka ba ne? Ka jira kaga wanene mana in bai maka ba sai ka sanar da ita ra'ayinka." Tsaki yayi yace "Ke har kina tunanin zata kawo saurayin da zai kwanta mini? Har yaushe ma tasan mutane ta zauna dasu balle tasan abinda ya kamata?" Zee ce tace "Ban sani ba amma nasan abinda nake so, Daddy kasan bazan auri Junaid ba kuma babu wanda ya isa ya rabani da wanda nake so, abu mafi sauƙi shine ka amsheshi hannu bibi……" hannu ya ɗaga kamar zai kai mata mari, ko me ya tuna sai kuma ya fasa, ya dunƙule hannu tare da nunata yana fitar da iskar ɓacin rai yana cewa "ɗan gidan uban waye? Ko shima zaki ce baki sani ba?" Kai ta kauda tace "Na sani amma ba wannan bane a gabana." Rigarshi kawai ya kaɗa yayi ciki, zuciyarshi na azalzala, Mummy ce ta kalleta sannan ta jinjina mata kai alamun tayi daidai ita kuma tabi bayan Daddy. Ɗaki ya shiga ya zauna tare da buɗe ƙafa yana huci kamar zakanya, zama tayi kusa dashi tana shafa gefen kafaɗarshi tana cewa "Senate calm down, yarinya ce bata san meke faruwa ba, sai dai inaga don Allah kayi haƙuri ka bari yazo kaga wanene, in har bai yi maka ba kace bai maka ba, itama a lokacin na tabbatar bata da uzurin da zata ce a'a." Kallonta yayi yace "Sam ban san ya zanyi da yarinyar nan ba gaba ɗaya bata jin magana." Ta kwantar da kanta akan kafaɗarshi tana cewa "Yarinya ce kayi mata uzuri don Allah." Da ƙyar ya sauke wata ajiyar zuciya yace "Kice yazo kuma maganarta da Junaid yana nan har sai na gamsu da shirmenta na watsa mata ƙasa a ido, na tabbatar bata isa ta ƙara yi mini musu ba." Mummy ta fito ta shiga wurin Zee ta sanar da ita saƙon Daddy, sai dai duk da haka babu walwala a fuskar Zee, kwanciya tayi kawai tana ji zazzabin na sake rufeta, ya zata yi? Ta san Baqeer ko da ƙafar shi ba zai taɓa yiwa Daddy ba, balle in yasan ɗan wanene, tasan duk kuɗinshi yana ji ance ɗan Badaru ne to fa an rabu kenan balle ga babu kudi ga kuma babu ƙafa, pillow kawai ta janyo ta kwantar da kanta tana tunanin abinda zata yi. ***** Baqeer yana jiyo Dada nata mita akan tunda ya shiga ɗaki alwala kawai taga ya fito yayi bata ƙara ganinshi ba, sannan ga abinci ta bashi yaƙi ci, shi kam yana jinta don ko magana baya son yi, takaicinshi ɗaya rashin ƙafafuwan nan, haka yasa ƙafar a gaba yana ta ƙoƙarin takawa, sai dai daga ya tsaya a kanta sai yaji ya faɗi, yanzun ma sake gwadawa yayi ya faɗi, kanshi ya jinginar a jikin gado yana haɗiyar wani takaici da ɓacin rai, shi yanzu ko zai daki kirji yace yana son Zainab yayi yaya da ita? Hannu kawai yasa yana dukan saman ƙirjinshi da yake ji kamar wani abu ya tsaya mishi a wurin yaƙi wucewa, can ya janyo wayarshi ya kunna, saƙon Zainab ne ya shigo _Daddy yace kazo gobe da yamma ya ganka_ sake maimaita saƙon yayi, lallai Zainab da gaske take yi, shi yanzu ta ina zai iya zuwa? Wai anya ta tuno abubuwan da suka faru a baya kuwa? A dalilinsu? Abinda yasa har ƴan sanda suka shiga maganar? Badaru kuwa a ranar yayi mata iyaka da shiga gidanshi? Shima aka yi mishi iyaka da ko ganinta yayi kar ya sake yi mata magana? Dama can akwai ƴar tsama tsakanin iyayensu sai dai case ɗin nan shine ya kawo ƙarshen gaisawar da ake yi don kuwa tun daga nan komai ya wargaje, ashe Maryam sun cigaba da ƙawancensu saboda makarantarsu ɗaya, abinda yake so ta sani shi zai iya bijirewa Badaru amma ita fa? Inta bijire me auransu zai tsinana? Aure babu albarkar iyaye? Wai ma ta ina da kujerar guragu zai nufi Alhaji Sulaiman? ****** Abu ce ta kalli Kamalu tace "Ban gane lefe ka haɗa ba?" Dariya yayi yana shan robar kunun ayan daya siyo yace "Ai ke na kula baki fahimceni bane, aure zan yi don komai ya kammala kayan kwalliya ne ban siya ba sai abayoyi da jaka da takalmi." Katseshi tayi da cewa "Ba dai ka gama haɗawa ba dai zaka ce, wannan dogon lissafin da kayi ai yaci rabin kuɗin aikin." Kamalu ya ajiye robar kunun ayan yace "Ni dai don Allah ki bani ajiyar nan taki na saida na ƙarasa haɗa lefe na, kin dai ga suruka zaki yi sannan wannan surukar manya ce don haka kar ki wani damu da yawan kuɗin da kika kashe." Wani kallo tayi mishi tace "Ba dai wai zoben dana siya da gadon da aka raba mana kake cewa na baka ka saida ba?" Kai tsaye yace "Shi mana, to menene amfaninshi dama idan ba kadara ba?" Wani mugun kallo tayi mishi tace "Kaga bana son shirme, in zaka yi aure to fa ka haɗa komanka da kanka." Tana kaiwa nan ta shige ciki tana mitar rainin wayon da yazo mata dashi. ***** Bello kam gidan duk yayi mishi zafi bai isa ko falo ya fito ba Asiya zata haushi da masifa, duk ya rame ya jeme, abun takaici ta ƙi bashi key ɗin motarshi daya bata kafin ya tafi, don ya bar mata ne akan tayi amfani dashi tunda baya nan to yayi yayi ta bashi taƙi, sannan shi kunyar ma fita waje yake ji mutane su ganshi ga gida kullum datti, abinci wannan sai kame-kame yake ci, kallon mutunci ma taƙi yi mishi, gashi irin masifaffun matan nan ne da idonsu rufewa yake yi in suna bala'i. Yau kam ya gama gajiya da rainin wayonta dole ne ya taka mata birki, fitowa yayi a fusace ya shiga ɗakinta……..

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BIYU*

{82}

Yana shiga ɗakin ya ganta a kwance tana danne-danne a waya, ita ko damunta ƙazantar data haɗawa ɗakin bata yi, haushi ne yaji ya ƙara rufe shi, ayi mace bata san komai ba sai baƙar ƙazanta tun yanzu ma kenan da take ita kaɗai bata iya tashi ta tsaftace muhallinta ba ina ga idan ta fara tara yara kuma yana ganin wannan lokacin sai dai ya haƙura da zama gidan don yasan iska ba zata shaƙu a cikinshi ba. A fusace yace "Ya kuma isheki haka nan Asiya, na lallaɓaki iya lallaɓawa amma sam ba kya gani. To wallahi bazan ɗauka ba kuma ki fito mini da makullin motata tunda bada ubanki muka haɗa kuɗi muka saya ba." A fusacen itama ta tashi don dama irin haka take jira ranar da zai buɗe baki yayi magana ita kuma ta yagalgala shi son ranta. "Bello ubana kake zagi?" "An zagi uban naki idan kin ji haushi ki fito min da makullin motata, haba ya daga abun arziƙi yana nema ya zama na tsiya. Tunda na dawo baki barni na sha ruwa ya tsirga mini ba, ance miki nima daɗin dawowar nake ji da zaki sakani a gaba da masifa da bala'i kawai don ban fita dake ba ko da kin san ko hanyar airport ne banda Allah ya haɗaki dani da zaki bi ki isheni da masifa saboda baki fita ƙasar waje ba kamar yadda kika ci buri, ni da naga samu naga rashi kuma fa nace me?" Murguɗa baki tayi tace "Wannan kuma damuwarka ce ni dai ai alƙawari kayi min kuma baka cika ba don haka ka dinga ganin tashin hankali kenan idan har baka ciki ba, haka kurum bayan duk nabi ƙawaye da ƴan uwana na gama yi musu kurin ba'a ƙasar zamu zauna ba sai ka dawo kace wani wai kai ma koroka aka yi?" Ƙwafa yayi yace "Au haka ma kika ce? Shikenan mu zuba ni dake shege ka fasa kuma wallahi ki fito min da makullin motata kin ji na faɗa miki." Wata uwar harara ta danƙara mishi ta saki tsaki tana girgiza jiki tace "Na ƙarfi ne idan kana dashi ka ƙwata," tayi shigewarta banɗaki ta banko ƙofar ta rufe. Duk bala'in da Bello yake ji sai da ya kasa magana don kullum mamakin rashin arziƙi irin na Asiya take yi. Juyawa yayi ya fita daga ɗakin yana jin wani irin dana sani yana kamashi, shi wai waya aikeshi ne ma gashi yanzu duk yabi ya cakalkala al'amuranshi da hannunshi. Shi sai yanzu ma ya gane ashe ba wani so yake yiwa Asiyar ba kawai don tana tare da Baqeer ne yasa yake ganin kamar shima sonta yake yi ashe ba haka bane burinshi na son mallakar duk wani abu daya kasance na Baqeer ne yasa yake tunanin sonta yake.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull