Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 60

Baqeer complete - Chapter 60

Baqeer complete Chapter 60: Baqeer complete Chapter 60. ***** Bashir kam yana zuwa gida ya fesawa Jamila yaga Baqeer zai hau adaidaita, dariya Jamila ta…

2,683 words

***** Bashir kam yana zuwa gida ya fesawa Jamila yaga Baqeer zai hau adaidaita, dariya Jamila ta kwashe ta fito ta sanarwa Abu nan suka sake kwashewa da dariya, Abu tace "Ahaf ni dama nasan ko fili suka sata ba abinda zai tsinana musu yoo nakasashe dama me zai iya yi? Na tabbatar kuɗin haya ya biya a ɗan dakin daya samu hala sai ragowar suka juye a asibiti." Jamila tasa dariya tace "Ai jiya da naji Badaru na zazzagawa matar can rashin mutunci baki ga daɗin da naji ba." Umma tana yanka alaiyahu a falo sai dai yanda suke magana da ƙarfi yasa tana jin duk abinda suke cewa, murmushi kawai tayi don sam bata son kula wannan shirmen nasu, so take yi ma gobe tayi miya ta kai musu.

***** Miƙa yayi ganin ya kammala ɗinkin ya gunguro ya kashe injin daya kunna saboda ɗinkin sannan ya sauke ajiyar zuciya yana kallon kayan, wanda kyansu sai wanda ya gani, gashi colour na material din da irin colour ɗin yayi aikin shadarshi sabon yayi. Wayarshi ya janyo yana son jin yaushe zata dawo don babu shakka ya ƙosa ya sanar da ita sirrin zuciyarshi. Ganin saƙonta yasa yayi saurin kira, da ƙyar Zee ta ɗauka saboda yadda take sauke numfashi, hankali a tashe Baqeer yace "Meke faruwa?" Ta lumshe ido ta buɗe tace "ɗazu nazo gida baka nan kai da Dada." Da mamaki yace "Kin dawo? Meke faruwa?" Kai ta girgiza tace "Ba komai zan ware….." yanda tayi maganar kana ji kasan dauriya kawai take yi, kashe wayar yayi da sauri ya kira Salim, yana ɗauka yace "Salim don Allah kasan gidan su Zainab? Yanzu ba wasa nake yi ba kamar yadda ka saba ɗauka, gidansu na gaskiya nake so please!" Gaban Salim ne ya faɗi, meke faruwa? Ta ina zai fara? Bayan bai shirya ganin masoyan biyu sun rabu ba?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN*

{80}

Tunda ta dawo tana kwance a ɗaki zazzaɓi ya rufeta, da ƙyar ta daure ta kira Ummi a waya ta faɗa mata isowarta gida lafiya. Koda Ummin ta tambayeta lafiya taji muryarta tayi ƙasa sai ce mata tayi gajiya ce kawai da kuma bacci da take ji bata don yi saboda yamma tayi, nasiha Ummi tayi mata kafin suka yi sallama bayan Ummi ta bata Inaya sun gaisa. Komawa tayi ta kwanta kanta yana wani irin sara mata ga tunani da yayi mata yawa ta rasa menene gaskiyar duka abubuwan da taji a kwanakin nan, ta rasa maganar wa zata ɗauka ta mahaifiyarta ko kuwa ta Mummy da tayi musu riƙo na gaskiya tamkar ƴaƴanta shekara da shekaru. Tana kwance Kabir ya shigo ɗakin, shigowarshi kenan Mummy ta faɗa mishi dawowar Zeey shine ya shigo ɗakin don ya ganta. Ɗago kanta tayi taga Kabir a bakin ƙofa sai ta mayar ta kwanta. Ƙarasowa ciki yayi yace "Sai yau kika ga damar dawowa? Ai da kin sani kin yi zamanki acan butulu kawai mai manta alkhairi, shine Mummy tayi ta kiranki kika ƙi ɗauka saboda kin tafi wajen matar da tayi abandoning ɗin mu, ko kuwa laifin Nabila nata ne?" Murmushin takaici kawai Zeey tayi ta lumshe ido sannan ta buɗe ta zubawa Kabir tana kallon yadda yake wani cika yana batsewa duk don ta taka ƙafa taje wajen mahaifiyarsu. A sanyaye saboda kanta dake damunta da ciwo tace "Ya Kabir kenan, kai yanzu laifina kake gani don naje wajen Ummi? Kada ka manta mahaifiyarmu ce dake da hakki a kanmu, wacce taci kashi da fitsarinmu, ta kula damu tun daga haihuwarmu har zuwa ranar da aka rabata damu. Ka taɓa tsayawa ka tambayi kanka dalilin da yasa tun bayan barinta gidan nan bata ƙara waiwayarmu ba? Kai baka taɓa son ka san dalilin da yasa ta watsar damu ba kamar yadda muke tunani? Kama san cewa tun tafiyarta duk shekara sai ta aiko mana da ɗinkunan sallah amma ba'a taɓa faɗa mana ba bare a nuna mana kayan ko baza mu yi amfani dasu ba. Kasan sau nawa ƴan uwanta suka zo aka hanasu shigowa su ganmu? Watanni biyu da suka wuce Kawu ya rasu, yana jinyar ajali burinshi guda ɗaya shine ya saka mu a idonshi takanas su Hajiya Goggo suka zo don su faɗa mana aka hanasu shigowa, to ka faɗa min a ciki waye mai laifi, su da aka hanawa ganinmu duk lokacin da suka buƙata ko Ummi da aka rabata da yaranta tun suna ƙanana?" Da mamaki yake kallonta yace "What are you trying to say? Aka hanasu shigowa ko suke zuwa suna yiwa Mummy rashin arziƙi." Girgiza kanta tayi tace "Duk abinda kaji na faɗa gaskiya ne, Ummi bata yi abandoning ɗin mu ba duk tsawon lokacin nan muna maƙale a cikin ranta, akwai saƙonka a cikin kayana sai na tashi zan baka yanzu kaina yana ciwo. Idan ka fita ka rufe mini ƙofar ɗakin," taja duvet ta rufe har kanta don bata son yawan magana tana jin kanta kamar zai ɓalle ya faɗi ƙasa saboda azaba. Tana jin lokacin da Kabir ya tashi ya fita sai dai bata ƙara yi mishi magana ba har bacci ya ɗauketa.

***** Yanzu abubuwa da yawa sun yiwa Hadiza sauƙi saboda sana'ar markaɗe data kama Allah kuma yasa mata albarka a ciki saboda anan kurkusa dasu babu masu sana'ar markaɗen don haka kusan kowa ita yake kawowa shi yasa yini take yi a tsaye tana aiki, ɗan abinda ta samu kuma dashi take yin duk wasu ƴan buƙatunta har ma a ciki ta yiwa Umma ɗan alheri. Shi kanshi maigidan yanzu sam ba'a jin kansu saboda dama dai shi kuɗinshi ne ba zai cire ya bayar ba yanzu kuwa data daina tambayarshi abunshi sai aka zauna lafiya, a haka kuma har shima ya nemi wani abu ta ɗauka ta bashi duk dai don a zauna lafiya.

***** Tunda yaji Zainab bata da lafiya hankalinshi ya tashi, lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyanar mata da abinda ke zuciyarshi yana ganin batun ɓoye-ɓoye kuma ya ƙare lokaci yayi da zasu san matsayin juna idan yin yi idan barin bari amma ya gaji da raragefe zuciyarshi kullum bata da nutsuwa saboda bai san matsayinshi a wajenta ba. Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi yaga lokaci ƙarfe bakwai saura kwata na yamma, in banda yanzu dare zai yi da babu abinda zai hanashi zuwa wajen Zainab a yanzu amma In Sha Allahu gobe ba zata wuce ba ba tare da yaje ya ga a halin da take ciki ba. Koda ya koma gida sai ya samu kanshi da sanarwa da Dada batun rashin lafiyar Zainab ɗin ya kuma faɗa mata gobe zai je ya dubata. Cikin alhinin rashin lafiyar Zainab ɗin tace "Da kuwa ka kyauta don Zainabu yarinya ce mai mutunci da bata ɗauki rayuwa da girma ba, hausawa ma suka ce gaida me gaishe yadda ta ɗauki al'amuranmu da girma ya dace aje a gaisheta da jiki, wannan zuwa dubiyar ma kamata yayi ace harda ni za'a je." Girgiza kanshi yayi yace "Zan dai faɗa mata kina gaisheta amma kiyi zamanki, kinga bamu taɓa zuwa gidansu ba bamu san irin karɓar da za'a yi mana ba bare da ganin Zainab kasan ba daga ƙaramin gida ta fito ba." Tace "haka ne, to ka gaisheta kace ina dubata da jiki." Ɗakinshi ya wuce zuciyarshi fal tunani sam baya da nutsuwa sai dai yana jin ɗoki da farin cikin kasancewar gobe zai bayyanawa Zainab abinda yake ji a kanta a cikin zuciyarshi. Wayarshi ya ɗauka ya kirata yana so ya ƙara jin yanayin jikinta. A lokacin da ƙiran ya shigo ta idar da sallah kenan don tun dawowarta tana kwance bata motsa ba, shigowar Mummy ɗakin uku tana tarar da ita a kwance duk a tunaninta bacci take yi bata san tana jinta ba bata son yin magana da ita ne kawai. A kasalance tace "Ya Baqeeer," muryarta na rawa. Sai da yaji wani abu ya ratsa tun daga tsakar kanshi har zuwa tafin ƙafarshi saboda yadda taja sunanshi. "Ya jikin naki? Hope yayi sauƙi yanzu," Ya tambayeta cike da kulawa. "Da sauƙi Alhamdulillah, ya Dada? Nayi kewarta yau naso na ganta sai kuma nayi rashin sa'a ban sameku a gida ba." Ɗan murmushi yayi, duk da bata da lafiya amma tana tambayar Dada. Waɗannan halayen nata na daga cikin abinda yasa ta shige zuciyarshi tayi kane-kane ba tare daya shiryawa hakan ba. "Tana nan lafiya tace na gaisheki da jiki." "Wai faɗa mata kayi?" Ta tambayeshi da mamakin hakan ƙunshe a muryarta. "Ina dawowa gida na faɗa mata baki da lafiya gobe zanje na dubaki sai tace itama zata je, da ƙyar dai na lallaɓata ta haƙura amma tace lallai nace tana gaisheki da jiki," ya ƙarashe maganar yana dariya. Cike da jin daɗi take murmushi saboda kulawar da yake bata ya tabbatar mata tanada matsayi a gunsa, ajiyar zuciya yai yace "Magani fa? Kinsha?" Ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace "Nasha paracetamol." Kai ya jinjina yace "Zanzo naga ya jikin naki....." gabanta ne yai wani irin faduwa bata san sanda tace "A'a karka damu Ya Baqeer nasan gobe in na tashi zanji na ware." Mamaki yak da jin kalamanta sai dai ya alakanta hakan da kulawa ne tunda tasan halin da yake ciki, baisan batada lafiya ya ɗaga mata hankali kawai sai yace shikenan. Suna gama waya ya ƙira Salim yace dan Allah gobe yazo, Salim cike da zargi yace "Inzo? Badai maganar gidan su Zainab din bane?" Baqeer yace "Kai dai kazo ina jiranka." Kafin Salim yai magana ga kashe wayar. ***** Wannan karon shine karo na biyar daya ƙara kallon jikinshi, ɗinkin dake jikinshi kaɗai abin kallo ne, yayi kyau sosai da sosai. Wani sanyayyen murmushi yayi wanda ya ƙara sawa cikar zati da annurin fuskarshi ta bayyana "Ya Baqeer menene matsayina a wurinka?" Kalaman ta ne suka sake dawo mishi kamar a lokacin take faɗa mishi "Kasan rashin lafiyar me nake yi? Ko kuwa har yanzu zaka ce baka san komai ba?" Nan ma wasu bangare na cikin kalamanta suka sake zuwa mishi. "Yau zan sanar dake matsayin da kika taka a cikin zuciyata," yayi maganar yana sakin wani sanyayyen murmushi kamar ita ce a gabanshi. Salim ne ya saki baki ganin Baqeer yayi kyau caz kai kace wani ango ne yace "Wai ina zamu haka duk kabi ka dameni?" Kallonshi yayi yace "Gidansu Zeey zaka kai ni, bata jin daɗi ni kuma hankalina yaƙi kwanciya gashi akwai amsoshin da nake ganin baki da baki ya kamata na furta mata." Nan da nan tashin hankali ya bayyana a fuskar Salim hankali a tashe yace "Baqeer kayi mata waya mana tazo sai kuyi maganar, gani nake yi ba sai kaje ba." Wani kallo Baqeer ya yiwa Salim, me yasa a duk sanda yake son zuwa gidan su Zainab yake hanashi? Me yake ɓoye mishi ne da baya so yaje ya gani? Nan da nan ya tamke fuska sosai yace "Ko ka kaini ko na nemi wani ya kaini duk ɗaya amma dai yau nayi niyyar zuwa wajenta babu kuma abinda zai saka na fasa." Haka nan ba don Salim yaso ba suka shirya suka fita zuwa gidansu Zainab, adaidaita suka tara ga mamakin Baqeer sai yaji Salim ya ambaci sunan unguwarsu, wai dama Zeey ƴar unguwarsu ce amma shine bai taɓa saninta ba, gaskiya abun da mamaki duk da dai ba cika shiga sabgar mutane yayi ba watakila shine yasa bai santa ba tun da sai yanzu. Koda suka shiga unguwar kallonta kawai yake yi sai yake ganin duk ta canja mishi kamar wanda yayi shekaru bai shigo ba, kasa kallon layin gidansu yayi saboda wani ƙunci da yaji yana neman lulluɓeshi sai dai baya son yayi ruining musu wannan ranar shi da Zainab don haka yayi sauri ya kori duk wani tunani daga zuciyarshi sai na yadda gamuwarsu da Zainab zai kasance. Babu yadda Salim ya iya haka suka ƙarasa layin gidan, wani tunani yayi ganin ya kawoshi layin gidansu Asiya budurwar data yaudareshi bayan rasa ƙafafunshi, wacce ta juya mishi baya ita da amininshi, nan da nan kuma ya sake kallon layin yana tuno kalamanta data yi mishi farko-farkon haɗuwarsu a wannan layin. Ƙofar gidan da Salim yayi parking ya kalla, gabanshi ne ya fara dukan uku-uku yana jin wani tsoro da fargaba na yawo cikin ranshi, bakinshi ne ya fara rawa yace "Salim ba dai nan ne gidansu Zainab ba?" Ido Salim ya runtse don abinda yake ta gudu kenan tun farko shi yasa yaƙi kawoshi gidan, riƙoshi yaje yi da sauri ya ɗaga mishi hannu alamar kada ya taɓashi sannan yace "Please wheel chair!" Haka ya fito ya buɗe mishi ya hau kan kekenshi na guragu ya tura zuwa ƙofar gidan, duk wani turi ɗaya da zai yi sunan Zainab ne ke dawo mishi cikin ranshi, ba dai? Ba dai Zainab Sulaiman Karaye bace wacce ya sani? Ba dai itace Zeey ɗin da tayi kane-kane a cikin zuciyarshi ba? No No Zeey? Zainab? It can't be. A daidai jikin gate ya tsaya sakamakon kanshi da yaji yana wani irin juyawa, wani irin dum yake ji wanda yasa baya gani sosai, wayarshi ya ɗauka ya tura mata text akan yana waje, sannan ya kalli Mai Gadi yace "Don Allah ba nan ne gidan Sulaiman Karaye ba kuwa?" Hankali a kwance yace mishi "eh nan ne," tura kekenshi baya yayi jikinshi nayi mishi wani irin sanyi, zuciyarshi na bugawa akai-akai kamar zata fasa ƙirjinshi ta fito. "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, how? Ta yaya? Ta yaya Zainab ɗinshi take fitowa daga cikin wannan gidan? Kallonta yayi nan da nan kamanninta na yarinta suka fara dawo mishi tar a cikin kai, sai data bari sonta yayi tsamari yake jin duk wani bugun numfashin shi da ita yake yi sannan ya ganta a matsayin wacce ko a hanya baya fatan gamuwa da ita? Abubuwan da suka faru a baya a ta dalilin ta ne suka fara dawo mishi, kai kawai yake girgizawa yana tura kekenshi iya saurinshi. Ita kam tun sanda taga saƙonshi akan yana waje tasan shikenan komai ya ƙare, ita kam tasan rayuwarta ta ƙare. Baqeer shine jigon rayuwarta in dai har ya rabu da ita to tabbas rayuwarta tazo karshe. "Ya Baqeer!" Ta ƙira sunanshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, da sauri ta sha gabanshi ta tsugunna suka yi kai ɗaya tana hawaye tana cewa "Why? Please ka tsaya." Idanunshi sun kaɗa sun yi jaa sosai, kenan ita tasan shi wanene amma ta raina mishi wayau? Ba dai fansa ta ɗauka akanshi ta hanyar sace zuciyarshi ba? Gagarumin case ɗin da aka yi shekarun baya ne wanda har yasa suka bar unguwar yake dawo mishi kamar a lokacin abun ke faruwa wanda a dalilinshi komai sai da ya kusa tarwatsewa, how? Taya zata yi mishi haka?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA ƊAYA*

{81}

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull