Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 59

Baqeer complete - Chapter 59

Baqeer complete Chapter 59: Baqeer complete Chapter 59. Tashi tayi jikinta yayi wani irin sanyi ta nufi ɗakin Ummi, tana tsaye a gaban wardrobe ɗinta tana…

3,925 words

Tashi tayi jikinta yayi wani irin sanyi ta nufi ɗakin Ummi, tana tsaye a gaban wardrobe ɗinta tana neman abu Zainab ta shigo ta zauna a bakin gado. Juyowa tayi ta kalleta sai taga tana share hawaye. Cike da kulawa tace "wani abu aka yi miki kike kuka?" Girgiza kanta tayi sai kuma tace "wai Daddy ne yace na koma gida gobe." Murmushin takaici tayi tace "ke kuma shine kike kuka? Gidan naku ne ba kya son ki koma ko ya aka yi?" Gaba ɗaya sai ta fashewa Ummin da kuka don bata gaji da ganinta ba, da ta ɗauka cewa bata da buƙatar Ummin a rayuwarta domin Mummy ta cike mata dukkanin wasu gurbi na uwa don haka nema bata damu da rashin Ummin a rayuwarta ba sai yanzu da ta zauna da ita na wasu ƴan kwanaki tasan ashe lallai babu wani giɓi da wani zai cike maka na mahaifiya kowacce irin kulawa yake yi maka kuwa, ashe ita uwa matsayinta daban ne, ganinta gata ga Ummin kaɗai wata irin nutsuwa da farin ciki yake sakata wacce duk tsawon rayuwarta bata taɓa tsintar kanta a ciki ba. Zama Ummi tayi a kusa da ita ta kamo hannayenta ta riƙe cike da tausasawa irin ta uwa tace "ai bamu rabu ba kenan Zainab, tunda kika zo kika ga wuri nasan idan kin tafi ma zaki sake dawowa. Kada ki saɓa umurnin mahaifinki ki shirya ki koma kamar yadda yace ga waya nan ai zamu dinga gaisawa kin ji?" Ɗaga kai tayi alamun amsawa sai dai har wannan lokacin bata daina kukan ba. Haka Ummi tayi ta lallashinta tana bata baki har ta samu ta sassauta kukan da take yi. "Tashi kije ki wanke fuskarki kada Inaya ta shigo ta tarar dake kina kuka," ɗan murmushi tayi sai ta tashi ta koma ɗakin Inaya inda aka sauketa tunda tazo anan suke kwana ita da Inaya. Da dare suna zaune a ɗakin Ummi tana haɗa mata kayanta tana yi tana mata ƴar nasiha ita dai Zainab tana saurarenta sai dai bata jin daɗin tafiyar da zata yi ta bar Ummin, bata gaji da zama da mahaifiyarta ba duk da ba wani sakewa take samu daga Ummin ba komai tayi sai tayi ta mata faɗa tace bata iya ba hakan bai sa taji zata gujewa zama da Ummin ba. Inaya na maƙale da ita tunda Zainab ɗin ta faɗa mata gobe baza ta dawo daga school ta isketa ba. "Aunty Zeey idan kin tafi yaushe zaki dawo?" Ta tambayeta. Ɗan shiru tayi tana kallon Inaya da duk tayi wani iri kamar tasa kuka, kawar da kanta tayi daga kallon Inayan tace "In Sha Allah bazan daɗe ba zan dawo kin ji," ɗaga mata kai tayi alamun amsawa. Ummi na kallon duk abinda suke yi ita kanta bata jin son tafiyar da Zainab ɗin zata yi saboda tana son zama da ƴarta ta koya mata hidimar kula da gida da ba'a koyar da ita ba to amma ya zata yi tunda ubanta yace lallai ne ta koma.

***** Maryam yau ta samu kanta cikin tsantsar farin ciki sakamakon ƙiran ta a waya da Baban Aareef yayi yace mata yana tafe da kyakkyawan albishir wanda ta daɗe tana jiran samuwarshi ta tanadar mishi tukuicin da zata bashi. Duk da ta kasa iya tuna menene wannan abu da ta daɗe tana fatan samuwarshi amma ta samu kanta cikin ɗoki da son sanin abinda ta samu da yasa maigidanta kasa jira ya dawo kafin ya faɗa mata, tasan dai ko menene abun alkhairi ne. Tashi tayi ta ƙara kimtsa gidan ta shiga kitchen ta shirya mishi kyakkyawan abinci, stir fried spaghetti tayi sai chicken salad da sharma milk (kunun shinkafa). Haka ta jere komai akan table sannan ta shiga tayi wanka tayi kwalliya cikin atampa julius holland da aka yi mata ɗinkin straight gown, sosai kwalliyarta tayi kyau kayan suka bi jikinta suka kwanta suka fitar da duk wasu curves na jikinta. Dawowa tayi parlour ta zauna, ƙamshin turaren wutan data saka ya haɗu dana jikinta da sanyin ac ya bada wani sassanyan ƙamshi mai kwantar da zuciya da sanya nutsuwa. Tana zaune taji shigowar motarshi don dama yace mata zai biya ta school ɗin su Aareef ya taho dashi shi yasa yau bata fita zuwa ɗaukarshi ba. Tashi tayi taje ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran shigowarshi. Da fara'arta ta taresu ta karɓi jakar hannunshi. "Sannu da zuwa Daddy," tace tana rausayar da kai gefe. Ɗan rungumota yayi a jikinshi cike da kulawa. Sai da ta cirewa Aareef uniform tayi mishi wanka ta bashi abinci sannan ta koma wajen Babanshi. Taimaka mishi tayi ya cire kayan jikinshi ya shiga wanka bayan ta haɗa mishi ruwan wankan. Fito mishi da kayan da zai saka tayi ta feshe su da turare ta ajiye akan gado sannan ta koma parlourn wajen Aareef don bata cika son barinshi ya zauna shi kaɗai ba sai yaje yayi mata wata ɓarnar bata sani ba.

Bayan ya fito daga wankan ya shirya sannan ya fito parlourn, direct wajen dinning table ya nufa itama tashi tayi ta bishi, yana zama ta ɗauki plate tayi serving ɗin shi abinci ta ajiye a gabanshi, kujerar dake gefen damanshi taja ta zauna yana cin abincin shi suna ƴar hira har ya gama cin abincin ya tashi ya koma wajen kujeru ya zauna ita kuma ta tattare wurin ta mayar da kayan kitchen sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi suna taya Aareef kallon tashar cartoon, duk ta ƙosa ya faɗa mata albishir ɗin shi kuma sai faman ja mata rai yake yi. Sia da ya gama wanata sannan yace ta ɗauko mishi jakar laptop ɗin shi a ɗaki, tashi tayi taje ta ɗauko ta kawo mishi ta koma wajen zamanta ta zauna. Buɗe jakar yayi ya fito da wata takarda ya miƙa mata, hannu biyu tasa ta karɓa tana karantawa. Ai tun bata gama karanta abinda ke jiki ba tasa ihu tana ɗan tsallen murna daga zaune, shi dai sai dariya yake yi yana jin daɗi cikin ranshi saboda farin ciki da ya yasa ta. Offer ce ta aiki daya daɗe yana nema mata sai yau Allah ya nufa ta samu. Sosai ta nuna farin cikinta da samun wannan aikin itama ta samu ta tallafawa Umma ba komai sai an jira Baqeer yayi ba ga kuma Hadiza a gefe da itama take buƙatar taimakonsu don ma yanzu Allah yasa albarka a cikin markaɗen da take yi bata rasa abinda zasu ci abinci ita da yaranta har ma tayi wasu ƴan buƙatun nata a ciki. Sai murna take yi ta kasa ɓoye farin cikinta, ƙasa yayi da murya don baya son Aareef dake kusa yaji ne zai ce yace mata "sai murna kike yi har yanzu baki bani goron albishir ɗin ba," wata ƴar dariya tayi cike da kissa tace "kai ma kasan goron albishir ɗin ka na nan na tanadar maka sai mun shiga daga ciki," ta amsa mishi tana lumshe ido. Haka suka zauna cikin farin ciki har lokacin sallar magriba yayi ya tashi ya fita masallaci, tashin Aareef tayi suka shiga ciki sai da tasa shi a gaba yayi alwala ya fara sallar sannan ta tafi ɗakinta tayi sallar itama. Tasan Baban Aareef baya dawowa sai yayi sallar isha'i tukunna, turaren quta ta ƙara kunnawa gidan tana jin daɗi cikin ranta don tuni ta cire rai da smaun aikin nan ganin an daɗe ana nema ba'a dace ba ashe rabonta ne a gaba shi yasa tuntuni bata samu ba sai yanzu. Tare suka fito daga masallaci shi da Baffa, suna tafe a hanya suna ƴar hira ta tsakanin ɗa da mahaifi anan ne yake faɗa mishi batun samun aikin da Maryam ɗin tayi. Wani kallo Baffan yayi mishi yace "Kai yanzu daka sama mata aiki ka gama yarda da ita ne?" "Ban gane ba," ya tambayi Baffan nashi da mamaki. "Eh ka gama yarda da ita ka tabbatar baza ta ci amanar ka ba ka amince ta fita aiki inda zata je tana cuɗanya da wasu mazan? Wai me yasa baka yin abu da tunani ne? Baka yi shawara ba babu komai kaje ka nemawa mace aiki matan nan da ba amana ce dasu ba kana zamanka lafiya lau aje a yayibo cuta a saka maka ko a kawo maka ɗan da ba naka ba cikin gida. Ka dai yi tunani wannan maganar aikin a barta gara ta zauna a cikin gida ta cigaba da kular maka da gidanka kai kuma ka fita ka nemo ka kawo mata tunda ai Alhamdulillah komai da take buƙata ka ɗauke mata shi to me take nema da har sai ta fita aiki zata samu." Shiru yayi yana jinjina maganar da Baffan ya faɗa, sai yaga kuma haka ne fa wasu matan basu da kamun kai suna fakewa da fita aiki suna yawon banzar su, duk da yasan Maryam yasan bata daga cikin irin waɗannan matan to amma maganin kada ayi kada a fara gara kawai a haƙura da aikin tunda Allah yasa bata fara ba. Sallama yayi wa Baffa bayan sun shigo harabar gidan ya nufi part ɗin shi shima ya shige nasu.

Aareef yayi bacci har ta kai shi ɗaki ta kwantar dashi dama kuma da wuri yake kwanciya saboda school da yake zuwa. Tana parlour a zaune tana kallon wani korean series lokacin daya shigo, zama yayi shima suna cigaba da kallon tare. Kamar daga sama taji muryarshi yana cewa "Hmm ina ganin batun aikin nan a haƙura dashi don mun yi magana da Baffa ya nuna mini illar fitar mace aiki sai kuma naga haka ne don haka ki haƙura kawai tunda ma baki nemi komai kin rasa ba bare ace dole sai kin fita nema." Baki a buɗe take kallonshi tace "Ban gane a haƙura ba, aikin da kia kayi mini alƙawari kuma sai yanzu bayan na gama sa rai tunda ka kawo mini offer zaka ce a barshi?" "Eh haka nace a bar maganar fita aiki babu ita, kawia ki zauna ki cigaba da kula da gida," daga haka ya tashi ya shige ɗaki ya barta tana jin wani irin ƙunci ya mamaye zuciyarta, ita kenan komai zata yi sai da yardar uban miji idan bai amince ba duk yadda ta kai da son abu sai dai ta haƙura?

****

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA TARA*

{79}

Haka Maryam tasha kukanta ta gaji don tasan tunda suka riga suka tsara to fa babu canji babu kuma yanda zata yi, takaicinta ma data juya taga yana bacci kamar ma bai san halin da take ciki ba, haka ta kwanta tana share ƙwalla har bacci ya ɗauketa. Da safe ta fito kitchen don haɗawa Areef abun breakfast, Baffa ta hango a falo yana zaune yana karanta jarida, takaici da tsanar abinda yayi mata ya kasa barin fuskarta, a ɗan dakile ta gaisheshi, bai ko kalleta ba ya amsa yana cewa "Ina dai ba haka kike gaida naki mahaifin ba?" Kallonshi tayi kawai takaici yasa ta wuce kitchen don tasan ko ƙara ta kai laifin ma kanta zai koma, shi yasa abubuwa da yawa da ya shafeshi bata iya sanarwa.

**** Da safe Zee ta shirya, Inaya sai binta take yi duk inda tayi, Daada mijin Ummi kanshi bai ji daɗin tafiyar nan ba, da kanshi yaje shago ya siyo shadda da atamfa da turare ya bata wai ita da Kabir, haka tayi godiya tana yi tana kallon Ummi wacce yanayinta kaɗai zai sa kasan tabbas dauriya kawai take yi, Zee ce ta maida ƙwallar dake neman zubo mata tace "Ummy na manta akwai saƙo da zan baki, don Allah muje ɗaki." Bata tanka mata ba tabi bayanta zuwa ɗakin suna shiga Zee ta rungumeta tana hawaye tace "Ummi zan dawo ki yafe mana don Allah." Jikin ta ne yayi wani irin mugun sanyi, ta ɗan shafi saman kanta kaɗan dln mace ce mai kawaici bata so Zainab ta gane halin da take ciki, ɗan zareta kaɗan tayi tace "Nasan ba son zama kike yi anan ba tunda ina saka ki aiki, sai dai Zainab ki sani a matsayin ki na mace ba rainon nan ya kamata ace anyi miki ba, duk gatan da kike dashi kina buƙatar kisan yanda zaki kula da kanki da mijinki idan kinyi aure." Kai ta sunkuyar cikin ɗan sakalci tace "Zan gyara In Sha Allahu." Kai Ummi ta ɗaga sannan tace "Sannan maganar Kabir," sai kuma tayi shiru, tausayin Ummi ne ya ƙara kamata, babu shakka ta daɗe tana missing ɗinsu, tun daga jin sunan Inaya take dana sanin abinda suka aikata. Ummi ce ta katseta da yin murmushi kaɗan tace "Ba sai kin yi mishi magana ba, Allah ya bashi mace ta gari." Kallonta tayi tana son bata labarin Nabila sai dai bata son ɗaga mata hankali, kai kawai ta jinjina tace "In Sha Allahu zai zo ma, amma Ummy me yasa….."sai ga Inaya ta shigo hakan yasa ta kasa tambayar abinda ke bakinta, haka ta kamo Inaya suka fito har mota suka rakata taba Mubashir number ɗinta sannan ta bashi ragowar kuɗin hannunta, Ummi tasa hannu ta amsa ta cirar mai 3k ta bashi ta maida mata ragowar tana cewa "Banda sakalci ya ba aikin da yayi zai samu kudi da yawa haka kawai? Wannan yana daga cikin abinda yake lalata yara." Ita dai Zee bata ce komai ba don bata san ma me zata ce ba. Haka ta kamo hanya zuciyarta duk ba daɗi don sai data dade tana share hawaye a hanya saboda yanda take jin takaicin halayensu, sai dai tana buƙatar ta koma don taji meke faruwa, me Mummy ke ɓoye mata sannan ta sanar da ita dalilinta na aikata abubuwan data aikata. Ajiyar zuciya tayi ita kam kwanan nan rayuwa take yi amma kamar ba rayuwa ba, ji take kamar mafarki take abubuwan dake faruwa da ita, ace komai na rayuwarsu ya canza lokaci ɗaya? Abinda suka daɗe suna ginawa su gane wai ashe duk ƙarya ne? Gefen kanta taji yana ɗan sara mata hakan yasa ta gangara gefen titi tare da ciro paracetamol ta haɗiyi guda biyu, kanta ta kwantar saman kujera tana sauke ajiyar zuciya, wayar Baqeer ta kira don haka kawai take jin muryarshi take son ji, sun dawo daga makaranta kenan don sun ma kusa gama makarantar, suna tafe yana tunanin abubuwan da ya kamata suyi dan ƙara bunƙasa shagonsu, yana ƙoƙarin shiga adaidaita sahu sai ga motar Badaru tazo wucewa, Bashir ne a ciki yana ƙoƙarin yin parking ya fito su kuma sun shiga adaidaita sun yi gaba, wayar Zee ce ta shigo hakan yasa ya ɗaga cikin ragaggiyar murya wanda ko kana kusa inba kunne ka kai kusa dashi ba baza kaji me yake cewa ba yayi sallama. Zee ta amsa a hankali tana lumshe ido, ji take yi ina ma dai ta ganshi a gabanta? Ji take missing dinshi na neman rikitata, murmushi yayi yace "Ya Ummin?" Tunani tayi akan tana son yi mishi surprise hakan yasa tace "Tana nan lafiya, mun fito siyan abu ne dasu ni ina mota." Ya jinjina kai yace "Shine aka ɗan tuno mutumin nan?" Tana murmushi tace "Ba gwara ni na tuno mutumin ba? Shifa?" "Ke nan dai gori ake yiwa mutumin?" Tana murmushi tare da riƙe gefen kanta dake ciwo tace "Uhm hmm sai ya canza in zai iya." Kai ya ɗan girgiza yace "Zan baki mamaki, sannan ki shirya kar kiyi mita akan na dameki da kira." Cike da neman magana tace "Wa? Kai ɗin? Allah Ya Baqeer baza ka iya ba." Da mamakin kalamanta yace "Dalili?" Ta dan wurƙila ido tace "Saboda ban san matsayina a wurinka ba, sannan a yanda kake bana ji in zaka iya aikata hakan." Kallon Tanimu yayi bai son fallasa abinda ke ranshi a gabanshi da ya sanar da ita abinda ke ranshi, murmushi yayi yace "In kin dawo zan sanar dake, sannan get ready kema inji nawa amsar." Wani irin energy taji yazo mata ta runtse ido tana jin wani shauƙi na ratsata, ji tayi baza ta iya cigaba da wayan ba don tabbas so take ta ganta kawai gaban Baqeer, hakan yasa tace "Su Ummi sun fito sai ka kirani." Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta sha ruwa sannan ta cigaba da tuƙi, tana jin wata nutsuwa na ƙara saukar mata, ina ma tana da wanda zata sanar wa halin da take ciki, Nabila ce ta fado mata ta girgiza kai tana neman kauda ta daga ranta. A bangaren Baqeer kuwa murmushi yayi suna zuwa gida yaga Dada na ƙoƙarin fita yace "Dada ina zaki?" Tace "Dubiya zani wallahi ƙawata ce bata jin daɗi," tayi maganar cike da kulawa, cike da ɗan jimami yace "Kuma wai Dada ƙawa kuke cewa da girmanku?" Gyara zaman mayafinta tayi tasa takalme yi tace "To in bamu ce ƙawa ba kuliya kake so muce? Ha'a yau ni naji abinda yafi karfina, ku dai baku isa mu faɗi abu ba sai ace mun girma da faɗar hakan." Dariya yayi kaɗan yace "Hajiya Dada tamu ke dai yanzu sai kin dawo. Kallon mamaki tayi mishi da alama yana cikin farin ciki don wannan zolayar da biyu yake yin ta. Ɗaki ya shiga ya kalli shaddar daya ɗinka yana jiran ta dawo yayi expressing abinda ke ranshi, ƙasan leɓenshi ya ɗan ciza kaɗan ganin bai gama yi mata ɗinkin material ɗin ba, abinci kawai yaci ya fito ya tafi shagonsu. Zee kuwa da yake daga Dambatta zuwa cikin kano ba wani nisa gareshi ba yasa ta iso da wuri, kallon jikinta tayi atamfa ce doguwar riga sai mayafi da tayi rolling a saman kanta don bata sa ɗankwali ba, fuskarta babu komai sai mai da lip gloss, madubi ta ciro bayan ta shigo layin ta gyara fuskarta, wayarta ta kalla wanda kiran Mummy ke ta shigowa ga na Kabir, bata jin amsawa kuma ba mai sata amsawa, tana gama gyara fuskarta ta fito ta nufi gidan, ganin gidan a rufe yasa tasan basa nan don basa rufewa in dai har ba fita zasu yi ba, baki ta turo ta koma mota, text tayi mishi tace "Ya Baqeer ɗazu naji kamar kana hanya ka koma gida?" Sam bai kula ba don hankalinshi na kan kayanta da yake haɗawa, gashi electric yake amfani dashi to a wahale yake yi saboda kafarshi in ya daɗe yana amfani da ita sai yaji tana yi mishi ciwo, bai san kowa ya tayashi yi mata wannan ɗinkin don yana ji wannan shine ɗaya daga cikin hanyoyin da ya shirya don yin confession na soyayyarshi. Ganin bai yi mata reply ba yasa ta kai hannu zata kira shi sam bata kula da kiran Mummy daya shigo ba kawai sai ji tayi hanunta ya taɓa, ganin ta riga ta ɗaga yasa ta gaisheta, Mummy cikin muryar marasa lafiya tace "Zainab kina can? Hankalina yaƙi kwanciya don kuwa Daddynki yaje Abuja shi da mahaifin Junaid ina tsoron kar suje daɗin tafiya tare yasa suyi arrangement na auranki." Hankali a tashi Zee tace "What? Mummy gani nan zuwa," tayi maganar tare da shiga mota da sauri, wayar Junaid ta kira bai jima ba ya ɗauka tace "Junaid yanzu zan zo office ɗin ka don haka ka fito waje." Tana fadar haka ta kashe wayar, ji take a wannan lokacin babu abinda ba zata iya ba, don zuciyarta ta gama shiryawa tsaf don amsar abinda Baqeer zai sanar mata wanda tasa a ranta in har yace ba soyayya yake sonta dashi ba to fa ita zata sanar dashi soyayyar take so. Bata wani jima ba ta isa, a waje ta ganshi yana tsaye sanye da suit yana duba agoggon hannunshi, da alama jiranta yake yi, a kusa dashi tayi parking, ta jikin kofar inda take ya tsaya ta zuge glass ta kalleshi, tausayinshi ne ya kamata don tabbas tasan ya dade yana binta da soyayyarshi, murmushi ta sakar mishi tace "J har ka fito?" Kai ya ɗaga mata alamar eh yana kashe mata ido yana cewa "Ya zan yi sanyin raina ta kirani?" Kai ta kauda tace "Kai dai wallahi ka fiya neman magana, J please bana son nayi hurting feelings ɗin ka shi yasa na fara tsayawa a nan inyu maks magana, kada kaji ba daɗi in kaji abinda zance don tabbas in har aka ƙara maganar auren mu zan bayyana abinda ke raina, wancan karon na faɗa maka maganganu wanda har yanzu ina jin ba daɗi ." Kallonta kawai yake yi yadda kai tsaye take rejecting ɗinshi ko da wasa bata taɓa tsayawa tayi reconsidering ƙaunar da yake yi mata ba, mota ta tada tayi mishi sallama, har zata zuge glass yasa hannu yace "Baqeer kike so?" Kallonshi tayi sai dai bata ce komai ba, mamaki ne ya kamashi, how? Zainab? No way, don yayi tambayar ne saboda abun na damunshi sai dai yanayinta yasa shi shan jinin jikinshi, hannayenshi ya zare kamar mara laka taja mota tayi gaba hankalinta a kwance. Gida ta nufa kanta na ƙara sara nata ga wani sanyi da ke ratsata, ciki ta shiga janye da akwati, tun daga falo take jiyo ƙamshin turaren wuta, kiciɓis suka yi da Mummy tana riƙe da kasko, kalaman Baqeer ne suka faɗo mata, ita Mummyn haka aka raineta? Yawun bakinta ta hadiya, Mummy cikin hanzari ta ajiye kaskon ta rungume Zainab, tana sauke ajiyar zuciya tana cewa "Auta nayi missing ɗinki, banda lafiya nace bari na tashi nayi wani abun saboda na samu sauƙi a raina, ji nake rashinki a gidan nan duk gidan ba daɗi, kallon Mummy kawai take kafin tace "Na ɗauka saboda kina son zama ke kaɗai a gidan kike hana ƴan uwan mahaifiyata zuwa?" Gaban Mummy ne yayi wani irin faɗuwa a tsorace ta kalleta tace "Me kike nufi?" Muryar Zee na rawa tace "Sun ce rabon da su shigo cikin gidan nan sunfi shekaru goma, iya kacinsu bakin gate, amma ni a sanina sau sama da biyar kina cewa sun shigo sun yi watsi da kaya akan sai kin basu wani abun saboda kwacemu da kika yi." Mummy fuskarta ɗauke da mamaki tace "Haka suka ce? Wallahi sharri suke yi mini, Auta ba dai kin yarda dasu sama dani ba?" Idanuwan Zee ne suka yi jaa sosai tana kallon Mummy tace "Naji ace wannan ƙarya ne, kayan da mahaifiyarmu ke ɗinko mana shekara da shekaru fa? Mummy I just….." ta kasa ƙarasa maganar saboda raunin da muryarta tayi. Mummy ta kamo hannunta da sauri tace "Wannan mahaifinku ne ya hana ba ni ba, sannan zancen farko sharri suke yi mini, ki tuna sau nawa kina zuwa kina ganin gidana a hargitse? Sannan mai gadi ba a gabanki a farko yace sun shigo ba?" Zee ce ta kalleta don ita kam bata son wannan abubuwan dake faruwa sai ma ta kasa gane mai gaskiya dame ƙarya, ga ciwon kanta dake ƙara ƙaruwa. Ganin jiri na neman ɗibanta yasa ta wuce ɗakinta da sauri tana shiga ta kulle ƙofa ta sulale jikin ƙofar ta zauna tana dafa kanta iduwanta a rufe.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull