Baqeer complete - Chapter 58
Baqeer complete Chapter 58: Baqeer complete Chapter 58. Zee tana shiga ɗaki akan gado ta faɗa ta kwanta, me yasa Ummi ke yi mata faɗa akan abinda tasan ba…
3,139 words
Zee tana shiga ɗaki akan gado ta faɗa ta kwanta, me yasa Ummi ke yi mata faɗa akan abinda tasan ba laifi bane, in ma ba haka ake yanka dankalin ba a matsayinta na uwa ai haƙuri zata yi tayi amfani da wanda ta ɓare amma sai ta hauta da faɗa? Mummy ce ta faɗo mata a rai don tasan tabbas da ita ce sai dai ma tace "Auta sannu, da fatan hannunki bai yi ciwo ba?" Kallon yatsunta tayi wanda har peeler ɗin ta ɗan karceta kaɗan amma gashi ita Ummi sam bata damu da tasan ma a wani hali ta fere dankalin ba, daga nan ɗaki take jiyo muryar Ummi da alama ita da Inaya ne don tana iya jiyo yanda suke magana cikin farin ciki, fitowa tayi da son sanin meke faruwa, nan ta taradda Inaya ce data dawo daga Tahfiz ta taho da kyauta taci na biyu, nan itama ta fara murna, sallama aka yi da gudu Inaya tayi waje tana kiran sunan Daada, Ummi ta kalli Zainab tace "Baban Inaya ne ki tashi ki sanyo mayafi." Tashi tayi tasa mayafi ta dawo, yana zaune a falo ya sa Inaya akan cinyarshi fuskarshi ɗauke da fara'a yana tsokanar Inaya, ganin Zainab yace "Ah ah ah ai ina ji ance Zainab tazo nace lallai dole na samu dama nazo wannan satin mu gaisa." Kanta ta sunkuyar kasa sannan ta rusuna ta gaisheshi tace "Ayi hakuri bamu zo mun yi gaisuwa da wuri ba." Har yanzu fuskarshi ɗauke da murmushi yace "Ah to kun dai san kun yi laifi, sai dai ita rayuwa wanda ya gane kuskurenshi yafe mishi ake yi." Ummi ce ta kira Inaya wacce ta ruga da gudu zuwa kitchen, ba daɗewa sai gata da tire da ruwa da cup a kai, ta ajiye sannan ta zuba ta miƙawa Daada tana cewa "Daada ka siyo min doll ɗin da kace? Mai gashi?" Gashin kanta ya ɗan ja kadan yace "To gashi ita kuma bata da gashi ina ga naki za'a gutsire a sa mata ko Ummin mu?" Shigowa tayi falon tana cewa "Kun fi kusa dai, baza kuji bakina ba." Bayan ya sha ruwan ya kalli Zee yace "Wai haka Yaya Babba?" Zee kanta tsaye tace "A'a kam bamu yarda ba." Ummy ce ta kalleta fuska a tamke, Zee a ranta tace "Me kuma na sake yi ni sarkin lefi." Kallon Ummi yayi ya ajiye cup ɗin hannunshi yana cewa "Daga ji dai girkin Yaya Babba zamu ci don wannan ƙamshin ma sai naji ya fita daban." Ita dai Zee tayi ƙasa da kai sai take ganin kamar ma magana ake faɗa mata, Inaya ce tayi saurin cewa "Daada, Aunty fa tace mun bata iya girki ba." Wani kallo Ummi tayi mata wato har ma fariya take bata iya girki ba? Daada yayi dariya yace "Wasa take kin taɓa ganin babba kamar ta da bai iya girki ba?" Ita dai Zee sum-sum tayi ta bar falon don ji tayi bazata iya zaman ba, rai a ɓace ta ɗauki wayarta kawai idanunta ya gane mata kiran Baqeer har sau biyu, da sauri ta kira shi ta kishingida akan gado, har ta katse bai ɗauka ba, tana ƙoƙarin ajiye wayar ya kira, har ta kai hannu zata ɗauka sai ita ma taƙi ɗauka tana kallon kiran ya katse sai ta kira tana murmushi tana hasaso fuskar Baqeer, ga mamakinta ƙin ɗauka yayi har ta katse sannan ya kira. Cike da shagwaɓa ta ɗaga kiran tana ɗan gyara kwanciyarta, yace "Ƴar Ummi ana can ana zuba shagwaɓa ne?" Sakalce mishi tayi tace "Allah ni ina ji gida zan koma gaba ɗaya an takura mun a gidan komai nayi ba daidai ba." Yayi ɗan shiru kafin yace "Hmmm kamar me da me kenan?" Tace "Allah ni kawai komai ma, ciki har da girki." Ajiyar zuciya yayi yace "Ba dai wata a haka take son tayi aure bata iya girki ba? Kice akwai case a gaba." "Case? Kamar na me? Nifa Mummy tace ba sai na koyi komai ba ko aure nayi da mai aiki na zata kai ni Allah ni bana son takurar da ake yi mini a gidan nan." Cike da mamakin jin abinda take cewa yace "Ita Mummy haka aka koya mata? Ko haka aka yi mata?" Tambayar tazo mata a ba zata hakan yasa tace "Name?" Yana riƙe da wayar yace "Na komai, ko ita bata iya komai ba?" Kai ta girgiza kamar tana gabanshi tace "Ta iya amma nice bata so na wahala." Ya jinjina kai yana cewa "In kika auri talaka fa irin su mu?" Yayi maganar cike da bugar ciki, ido ta lumshe tana hango fuskarshi cikin ƙwayar idanunta tace "Da mai aiki na ai." Ya ɗan murmusa yace "To kuma irin mu ina muka ga inda zamu saka mai aiki? Sai dai ke bana ji zaki auri talaka watakila shi yasa ba kya wannan tunanin." Da sauri tace "Allah a'a!" Shafar sumar kanshi ta baya yayi yace "A'a me?" Ta gyara kwanciya tace "Ban ce komai ba." "A dai faranta ran Ummi kinga dai shekaru kuka ɗiba ba kwa tare sannan abinda take nuna miki gata take yi miki don ko ni bazan yarda matata ta zauna bata komai ba," yayi maganar cike da son jin me zata ce, sai dai kawai ji yayi tace "Umm!" Jikinshi ne yayi sanyi da Umm ɗin da tace amma ya daure yace "Yaushe zaki dawo? Dada nata tambayarki da alama missing ɗinki take yi." "Ita kaɗai?" Tayi tambayar itama tana son jin me zai ce, da yake ya dawo gida yana zane sai ya tura kujerarshi baya yace "Kila?" Zee tace "Kila kenan babu tabbas?" Kallon sketch na material ɗinta da yake yi yayi yace "Ko a tambayar miki?" Tace "In dai sai an tambaya na yafe kaga kenan ba ayi." "A'a ai sai anji ta baki ake fahimta," yayi maganar cike da zolaya, Zee ta ɗan motsa baki kafin tace "A'a wannan daga zuciya ya kamata ya fito." Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta cilla ta gefe tare da binta da harara tace "Allah sai na fanshe, ni kam anya Ya Baqeer na so na?" Ta tambayi kanta idanuwanta na kan wayar kamar wayar take tambaya, sai dai kalaman Baqeer na sake dawo mata, to ita ya zata yi? Gaskiya ko zata koya gwara ta koya a gidan su ba dai nan ba bata son abinda zata yi ace ba tayi daidai ba. ****** Inna ce ta shigo ɗakin rai a ɓace ta yaye bargon da take lulluɓe dashi cikin takaici tace "Baza ki fito kici abinci ba?" Maida bargon tayi saman kanta tace "Bana ci." Takaici ne ya sake rufe Inna tace "Wai na ɗauka zaki amshi laifinki ki nemi yafiya ashe shirme zaki aikata?" Kamar dama jira take ta tashi ta zauna a bakin gadon tana magana mai kamar ta kuka tana cewa "Inna wai menene laifina? Akwai aure tsakanin mu da Kabir sannan babu wani abu daya haramta, abu na biyu magana ta bayyana kowa ya sani to a barni na aureshi mana." "Anƙi a barki ki aureshin, nace anƙi a barki, ja'irar yarinya, yanzu duk kyawawan halin ki dama akwai wani halayenki da kike ɓoyewa wai har kece zaki yiwa kanki sharrin ciki? Cikin ma na shege? Ke kinsan me cikin shege yake nufi?" Nabila kamta ta sunkuyar tace "Nifa saboda a haƙura a bar mu muyi aure na........" Inna ce ta katseta da cewa "Kina ƙarasa maganar nan zan tsinkeki da mari, aure a gidan uban wa? To ki sani Halima tace shi ko a jikinshi sannan wacce ake so ya aura ma yaje ya ganta, sai naga abinda zaki yi, sokuwa wato ke ko tausayin mahaifiyarki ba kya yi." Inna tana kaiwa nan tayi hanyar waje, Nabila jan bargo ta sake yi zuciyarta na tafasa, in dai haka ne to lallai ba wanda zai zauna lafiya in har ita ba'a barta ta zauna lafiya ba, haushin kanta ne ya kamata tunowa da tayi bata san saurayin da Zee take so ba tabbas da ta kira Daddy ta sanar mishi don ta tabbatar bai san da wanda take so ba. ***** Ɗaki Mummy ta shiga ta ɗan fara kaiwa da komowa, hankalinta sam baya jikinta don ta kasa nutsuwa gashi dai Senate ya dawo gida amma fa yanda suke yi kamar da ya daina, hira wannan ba sosai yake yi da ita ba, to yanzu matsalarta yanda zata jawo Zainab daga Ɗambatta wanda ta rasa ta wani hali zata aikata hakan, baya tayi saboda jirin da taji ya ɗebeta, a hankali ta janyo wayarta tana sauke numfashi ta kira Zee, sai dai har tayi ringing ta gaji bata ɗauka ba, kiran Kabir tayi akan yazo. Ba daɗewa sai gashi don dama yana gida, duk da shima bai gama sakewa da abinda ya faru ba amma shi yayi mata uzuri ya tabbatar fyaɗe aka yiwa Mummy kuma ba da saninta ta aikata hakan ba yana ma gani Inna ce hala ta tursasata. Yana shiga ya ganta a kwance a ƙasa hankali a tashe yace "Menene Mummy?" Kai ta girgiza tana lumshe ido tace "Kabir ƙirjina keyi mini wani irin nauyi nama kira Zainab bata ɗauka ba." Hankalinshi a tashe yace "Bari na kira Dr, ta girgiza kai tace "Kar ka damu kawai dai gani nake in na ganku zan samu nutsuwa ne, In Sha Allahu ba komai. Ran Kabir a ɓace ya kira Zainab, sai dai lokacin ita bata ma ɗaki tana falo a zaune, cike da tausayin halin da Mummy ke ciki yake yi mata sannu.
******* Zee dake zaune a falo ce ta miƙe ta nufi kitchen inda su Ummi suke don dama abinda ya fito da ita kenan daga ɗaki, tana son bin shawarar Baqeer hannayenta na baya yana ɗan motsi dasu tace "Ummy dame zan taya ku?" Kallonta Ummy tayi kafin ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace "Me zaki iya daga abubuwan da muke yi?" Kallonsu tayi Ummy na yanka kayan miya, Inaya na tsinke zogale, cike da son jin bakinta Ummi tace "Ko zaki tayamu da wanke-wanke?" Ido ta zaro da sauri tace "A'a gwara abinda Inaya ke yi bansan taɓa kayan da aka ci abinci." Mamaki me ya kama Ummi kawai ta girgiza kai don bata san ma me zata ce mata ba, zama tayi babu kunya suka tsinke zogale sai wani daɗi take ji tana so taji Ummi ta yabeta, ita kam Ummi kasa tanka mata tayi don bata san me ma zata ce ba saboda takaici. Inaya ce ta shiga banɗaki tana fitowa taji wayar Zee na ƙara hakan yasa ta fito mata dashi ta bata, kallon wayar tayi ganin Kabir yasa ta ɗauka da sauri don ta haɗa su da Ummi su gaisa, shi kam tana ɗauka yace "Wato kinci moriyar ganga ko? A wani dalilin Mummy zata yi ta nemanki ki dinga ƙin dauka? Naji tayi miki laifi amma ai sai ki yi mata uzuri kiji dalilinta ko? Ko ba haka ake so ƴaƴa su yiwa iyayensu uzuri ba?" Zee ta kalli Ummy da ita ma kallonta take yi sannan tayi ciki da sauri, ba tare da ta rufe kofa ba ta shiga ɗaki tace "Ya Kabir me kake yi hakan? Sannan ai kaima kasan abinda tayi mana bata kyauta ba ko?" Tsaki yayi yace "In ta mutu kya yafe mata tunda wacce kika tafi wurinta itace ta raineki har kika kai girman haka, wannan halayen naku na mata shi yasa mata suke tsoron riƙe yaro da zuciya ɗaya." Hankalinta ne ya ɗan tashi tace "Bata da lafiya ne?" Cike da takaici yana haɗe fuska yace "Eh gata nan ana ƙoƙarin sa mata drip kada Allah yasa kizo kiga jikinta," yana kaiwa nan ya kashe wayar, Zee tace "Yaya! Yaya! Yaya!" Sai dai ya riga ya kashe, fuskarta tasa da hannaye biyu ta shafa, kallon bakin ƙofa tayi inda Ummi ke tsaye da alama biyota tayi da son jin meke faruwa, idanunsu ne ya haɗu da juna, Ummi tayi murmushin yaƙe tace "Kije kafin wani abun ya faru, na ɗauka ta daina wannan ƙananan shirmen ashe har yanzu bata san ta girma ba." Kalaman da taji Ummi ta furta kenan wanda yasa ta kallonta fuskarta cike da mamaki, ganin Ummi zata juya yasa ta saurin cewa "Me kike nufi da kalamanki Ummi? Kina nufin ƙarya Mummy take yi kenan ko me?" Waigowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "Ki koma ki tambayeta, sannan ki haɗa da tambayar da nima nake son sanin amsarsu, me ƴan uwana take cewa sun yi kamar yanda kika ce shine dalilin hanasu zuwa da Babanku yayi? Dan a iya sanina babu wanda ya taɓa zuwa don neman taimako gidanku duk zuwan da wani zai yi to fa lallai babban dalili ne ya kai shi saboda dukansu sun san waye Sulaiman, kayan da nake ɗinka muku shekaru kusan ashirin suna ina? Sannan number wayar data aiko min da sunan wayoyin ku nasu waye? Ahh abu na ƙarshe me da me muka yi da har Sulaiman ya aiko har Ɗambatta akan kar ya ƙara ganin wani daga cikin mu a gidanshi, in har ta sanar dake duka ina so ki sanar dani don mu san dalili," Ummi tana kaiwa nan tayi gaba zuciyarta na wani irin zafi don lallai abubuwan nan sun fara isarta shekaru nawa rabon data sa su a ido ace sati guda baza ta iya ƙyale mata ƴarta tayi mata ba? Zee kuwa ji tayi kamar an daskarar da ita kalaman Hajiya Goggo ke sake dawo mata, gabanta ne ya shiga faɗuwa ba dai yanzun ma ƙarya Mummy ta dinga yi musu ba duk yawan shekarun nan? Ji tayi kanta yayi mata wani nauyi nan da nan tasa hannu ta riƙe kanta tana sauke ajiyar zuciya.
****** Kamalu ne ya kalli yaron da yake bawa ajiyar kaya yace "Yauwa fito min da kayan nan inga ko sun haɗu." Nan yaron ya fito mishi da tulin atamfofin daya sace a shagon Badaru, dariya yasa sai kuma ya tamke fuska kamar wani mai aljanu yace "Matsalar babu lace bare shadda. Maida kayan yayi ya fito yana tunanin zuwa kasuwa ya ɗan yi samfe, sam bai kula da Salim dake tahowa ba da alama shago yaje, sai da Salim yazo daf dashi ya ganshi, kauda kai yayi yana neman wucewa sai ji yayi yace "Kai soko baka ganni bane?" Salim ya kalleshi ya girgiza kai cike da takaici yana cigaba da tafiyarshi, dariya Kamalu yasa yace "Saurayi soko da alama an kasaka ne shi yasa tafiyar ma kake yinta ba cikin hayyacinka ba, to ya zaka yi? Manya sun ƙwace maka wacce kake so." Duk yanda Salim yaso ya kauda kai sai da yaji dariya ta kwace mishi yace "Ah kace kai da Roshni abu ya kankama?" "Sosai, ba dai baƙin ciki kake yi ba?" Ya dan girgiza kai yace "Ni? Ai ban isa ba, na bar muku ai ku manya, yaushe ne bikin?" Kamalu ya maka mishi harara yace "Malam ba zuwa zaka yi ba, don mu ba kowane soko muke gayyata ba, kaje can in abokinka zai yi aure kaje." Dariyarshi ya sake guntsewa yace "Tab gaskiya kam ai da alama abokina yafi guarantee gwara na tsaya a ɓangaren shi," ya ƙarasa maganar yana tafiya, shi dai Kamalu ya bishi da harara yace "Wawa kawai."
****
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA TAKWAS*
{78}
Tunda taji wannan maganar a bakin Ummi kanta ya ɗaure ta shiga tunani, kada dai ace duk tsawon shekarun nan Mummy ƙarya take yi musu take nuna dangin mahaifiyarsu na yin tattaki takanas suna zuwa har gidansu kawai don suci mutuncinta duk don tana riƙon su. Tukuna ma tsaya, wacce magana taji Ummi nayi akan duk shekara sai ta aika musu da kayan sallah abinda ita ko Kabir wani bai taɓa sani ba, tasan farkon zuwanta tayi magana makamancin haka amma bata gama fahimtar me take nufi ba, ya Mummy take yi da kayan da take aika musu ko kuwa dai ɗan aiken ne baya kaiwa sai ya dawo yace mata ya kai? Tana ganin hakan nema don babu ta yadda za'a yi Mummy ta ɓoye musu abu irin wannan, wani ɓari na zuciyarta taji yace Mummyn kuwa? Har kin manta da ɓoye muku da tayi akan Nabila ƴarta ce in banda Allah ya nufa sai kun ji Inna tayi suɓul da baka ta fallasa sirrin da suke ta ɓoyo kina tunanin da zaku sani ne? Girgiza kanta tayi tana kasa gasgata wai Mummy ce tayi musu duk waɗannan abubuwan tasa suka ƙullaci mahaifiyarsu da gangan alhakin tasan duk abubuwan da take zaunar dasu tana faɗa musu ƴan uwan Ummin sun yi mata duk ƙarya ne. Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ita kuwa Mummy me yasa zata yi musu haka? Me zai sa ta hana ƴan uwan mahaifiyarsu kusantar inda suke? Laifin me suka yi mata da zata yi musu irin wannan cutarwa? Eh cutarwa mana tunda tasan duk abinda take faɗa musu ba gaskiya bane sai ma ƙara nesanta su da mahaifiyarsu da yake yi. Kawai sai taji hawaye yana zuba daga idanunta, tausayin Ummi ne taji ya kamata yadda suka rayu suna jin haushinta ashe babu laifinta ko ɗaya a cikin watsar dasu da suke zargin tayi. Tana zaune a wurin tana saƙa da warwara taji wayarta tayi ƙara, da kamar ba zata ɗauka ba sai kuma tayi tunanin ko Baqeer ne ya ƙirata duk da basu wani daɗe da gama waya ba abinda yasa ta janyo wayar don ta amsa kenan sai taga ashe Daddy ne yake ƙiran ta. Sai da gabanta ya faɗi cikin ranta tace Allah dai yasa ba wani abu ne ya samu Mummy ba. A sanyaye ta amsa wayar don bata cikin yanayi na jin daɗi, bayan sun gama gaisawa da Daddy yace mata ta shirya ta dawo gida gobe hutun ya isa haka nan. Murya na rawa tace "Amma Daddy..." Katseta yayi yace "Kiyi abinda nace Zainab, lallai gobe na dawo gida na iske ki bana son zamanki a wannan garin ya isa haka nan." A sanyaye tace mishi "to," tun yanzu tana jin kewar Ummi na lulluɓeta, ga kuma Inaya da suka yi wani irin sabo da yarinyar tasan idan ta tafi ba ƙaramin kewarta zata yi ba.