Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 57

Baqeer complete - Chapter 57

Baqeer complete Chapter 57: Baqeer complete Chapter 57. Ummy ce ta janye jikinta daga jikin Zee tana sake maida wani abu daya tsaya mata a maƙoshi, har ga…

2,368 words

Ummy ce ta janye jikinta daga jikin Zee tana sake maida wani abu daya tsaya mata a maƙoshi, har ga Allah ta daɗe tana jiran wannan ranar sai dai yaran sun ƙi suyi hankali bare su waiwayeta, tayi kewarsu tayi tayi har ta haƙura, yarinyar ta kalla tace "Inaya me ake yi in aka ga baƙi?" Da sauri ta durƙusa ta gaida Zainab, rarrafowa inda take Zeey tayi tasa hannu ta rungumeta kawai tana hawaye, tari tayi tana cewa "Aunty ba nice Ummyn ba gata can." Zeey ta ɗago ta shafi gefen fuskarta tace "Sunan wannan cutie ɗin Inaya?" Kai ta ɗaga alamar eh sannan tace "Na gaskiya fa?" Ga mamakin Zeey sai ji tayi tace "Little Zainab!" Kasa fahimtar me take nufi tayi da sauri ta kalli Ummy wacce ta kauda kai sannan ta maida kallonta kan yarinyar tace "Sunanki little Zainab? Zainab sunanki kenan?" Kai ta jinjina tace "Eh!" Duk yanda Zeey ke neman dakewa ji tayi ta kasa kawai ji tayi hawaye nayi mata gudu a fuska, sunanta Zainab dama tasan sunan mahaifiyar Ummy ne data daɗe da rasuwa aka saka mata shi kuma Kabir sunan mahaifin Daddy, da yake akwai ƙannen Daddy da suka saka sunan mahaifiyarsu yasa shi bai saka ba, lallai sun yi rashin hankali ita da Kabir don gani ɗaya data yiwa mahaifiyarsu tasan lallai tayi kewarsu, babu shakka basu yi mata adalci ba sannan basu kyauta mata ba. Ummy tana kula da yanayin Zeey sai dai zafin da take ji yafi na Zainab ɗin, dakewa tayi tace "Ku shiga ciki kin sa yarinya a gaba kina kuka." Share hawayenta tayi suka shiga ciki, kallon cikin falon tayi wanda yake a gyare tas, ga hoton Ummy nan da saurayin nan na ɗazu da Inaya sai kuma mijin Ummyn, kallonshi tayi daga ganinshi yana da fara'a don a hoton ma yafi Ummyn sakin fuska. Zama tayi akan kujera, Adamu ya miƙe yace "Ni zan wuce, in kin shirya zan zo na kaiki ragowar gidajen yan uwa." Kai ta ɗaga a hankali tace "Nagode." Fita yayi, saurayin nan na dazu yace "Kece Aunty Zainab ta Kano?" Kallon mamaki tayi mishi, Inaya ma ta kalleta, yayi murmushi yace "Naga kamar ku ɗaya da Ummy shine na tambayi Adamu yake faɗa mini." Kai ta jinjina tace "Kai fa? Ya sunanka." Inaya da sauri tace "Ya Mubashir." Zeey ta shafi saman kanta tace "School fa? Ka gama?" Ya ɗaga kai yana cewa "Na daiyi diploma yanzu zan tafi Uni, BUK na samu admission." Cike da jin daɗi tace "Sai kazo gida ka zauna kaga in zaka je sai na dinga saukeka ko nasa a kai ka, in kuma ka iya mota sai na baka tawa…." "A hostel zai zauna," Ummy dake shigowa ta katseta, shiru tayi don bata ga alamar wargin da zata musa ba, kallonta Ummy tayi tace "Muje ɗaki." Ba musu Zeey ta miƙe suka yi ɗakin Ummyn, bayan sun shiga ta maida ƙofar ta rufe sannan ta samu kujera ta zauna, shiru Ummy tayi kafin ta samu bakin gado ita ma ta zauna, Zeey kanta na ƙasa tana ɗan murza tafukan hannayenta, shiru suka yi don da alama babu wanda ya shirya fara magana, can Zeey ta daure ta ɗago tace "Ummy mun sameku lafiya?" Yawun bakinta ta haɗiya kafin tace "Lafiyan mu kalau, Allah ya bamu ikon kaiwa wannan lokacin." Haka kawai Zeey taji kamar magana cikin magana Ummy tayi mata, miƙewa tayi tazo daidai kafafuwan Ummy ta zauna ta riƙe saman ƙafarta tare da kwantar da kanta daga gefe tace "Ummy mun yi laifi ki yafe mana." Ido Ummy ta runtse tace "Kina mace? In har ba'a barki kinzo ba ko waya baza ki iya yi mana ba? Mahaifiya dama ba a bakin komai take ba?" Kai ta girgiza tace "A'a Ummy kiyi hakuri wallahi zuciyarmu ce ke bamu tunda kika tafi kika barmu baki damu damu bane sannan alama ce ta kema ba kya son mu nemeki." "Bana son ku neme ni? Sannan tafiyar tawa ɗin yin kaina ne ko kuwa ba saki na aka yi ba? Kayan sallar da nake aika muku duk sallah kaɗai bai isa yasa kusan na damu daku ba? Ko kina tunanin har numberki data Kabir ban samu na kiraku bane?" Zeey kallon Ummy tayi jikinta ya shiga wani yanayi mai wuyar fassarawa, tana jin kamar an ɗauke ta an jefata cikin ruwa, ganin yanayinta kaɗai yasa Ummy tasan lallai ba'a taɓa ma basu kayan sallar ba kenan, dakewa tayi tace "Shi yayan naki yafi ƙarfin yazo ya gaida wacce ta kawoshi duniya kenan ko?" Bakinta taji ya fara rawa tace "Bai san na taho bane nan gaba in zan zo zamu zo tare." "Hmm! Ki tashi kije kiyi sallah kici abinci mayi magana daga baya." Kai ta ɗaga sannan ta tashi jikinta duk yayi wani mugun sanyi, daga ɗaki Ummy ta ƙwalawa Inaya kira sai gata da gudu tace "Rakata ɗaki sai kizo kiyi abinda na saki, sannan ki shirya ki tafi islamiya." Hannun Zee ta kama suka bar ɗakin, tana fita Ummy ta share ƙwallar data cika taf cikin idanunta sannan ta sauke ajiyar zuciya, Alhaji Sulaiman bai kyauta mata ba bai kuma yi mata adalci ba, ita mace ce mara son magana da hayaniya shi yasa ta dinga kauda kai sannan ƴan uwanta kullum ganin suna baƙin ciki da mitar abun yasa ta ƙara yin shiru, tana sawa a ranta in dai Kabir da Zainab suka girma tasan zasu nemeta bata san har zasu kai girma haka basu nemeta ba. Suna shiga ɗakin Zeey ta kwanta a kan gadon ɗakin ta kalli Inaya tace "Dakinki ne?" Tace "Eh amma bana kwana a ciki nafi kwana a wurin Ummy saboda Abbah ma baya nan a Abuja yake aiki." Kai ta jinjina tace "Ummy ma ance tana aiki ko?" Inaya tace "Eh vice principal ce a school ɗin mu." Cike da jin daɗi tace "Inyee wata taji daɗi, Inaya in aikeki ki siyo min paracetamol? Kaina ciwo yake yi." "Ummy tace na share falo na shirya na tafi islamiya." Kallon agoggo tayi tace "Uku kuke zuwa?" Kai ta ɗaga alamar eh, Zee tayi dariya tace "Jeki ki siyo mini zan yi miki sharar kinga kina dawowa sai dai kisa kaya." Inaya tayi dariya tace "To shikenan, Ummy baza tayi mini faɗa ba?" "Ai yanzu zaki dawo bazata miki ba." Ta ciro gudar dubu ɗaya ta bata tace "Ki siyo alawa daga nan." Inaya hankali kwance ta fita, Zeey tayi miƙa ta fito, falon babu kowa hakan yasa ta kalli ƙasa, da alama abinci taci don ga shinkafa nan ta zubar, leƙe-leƙe tayi har taga kitchen ta shiga ta ɗauki tsintsiya tana mamakin yadda aka yi basu da mai aiki, falo ta dawo tayi ajiyar zuciya tana tunanin ma ta yadda zata yi sharar don ita kam bazata iya tuna ma sanda ta riƙe tsintsiya da hannunta ba bare tayi shara, ko a ƙasar waje da vaccum cleaner suke amfani. Falo ta dawo kawai ta fara sa tsintsiya maimakon ta tattare inda aka ci shinkafar ai sai ta baza wurin ma shinkafar tayi ɗaiɗai, tana sharowa suna sake yin wani wurin, tsaki tayi tace "Ai ma na gama." Ta maida tsintsiyar har zata yi ɗaki taji Ummy na kiran Inaya, daga falon tace "Ummy na aiketa." Ba tare da ta amsa ba ta fito, a bakin ƙofar ɗakin ta tsaya tace "Kin aiketa kamar ya?" Ummy fuskarta kam babu fara'a, Zeey jita yi shakkar Ummy ta kamata a shagwaɓe tace "Abu na aiketa ta siyo min." "Ta fita bata sanar min ba?" Shiru Zeey tayi, kallon falon tayi wanda duk ya sake rikicewa bayan sanda ta shiga ɗakin kawai inda aka ci abinci ne yayi datti tace "Aikin dana sata bata yi ba shima?" Cike da zakwaɗi tace "Na riga nayi ai." Kallon falon ta kuma yi tace "Me kika yi?" Da mamaki tace "Shara." Ummy kallon falon tayi sai dai bata son nuna mamakinta da abinda idanunta suke gani ko dai gajiyace tasa ta kasa? Wannan amsar yasa ta tabbatarwa kanta shine dalili, Inaya ce ta shigo da gudu tana ganin Ummy tayi turus, Ummy ta tamke fuska tace "Wuce kiyi shara kisa kaya." Zeey kamar ta sake cewa tayi sai kuma tayi shiru tana kallon Inayan, har ta ɗauko tsintsiya a gaban Zee ta share tas sai ga shinkafa ta haɗu, mamaki ne ya rufe Zee tayi sum-sum ta shige ɗaki, baki ta taɓe tace "Ba komai ai ni ba dole sai na koya ba, ko aure nayi da mai aikina zani."

***** Yaye bargon da ya lulluɓa dashi tayi sai hura hanci take kai kace iskar gari take san shaƙewa, ta sa hannu a kwankwaso tana girgiza ƙugu tana cewa "Na rantse da Allah Malam baka isa ba ka tashi mu wuce ka sayi ticket mu tafi banga uban daya isa fa ya sani zama a ƙasar nan ba." Kallonta yayi cike da mamakin yanda ta rainashi yace "Wai ba na sanar dake nima koro ni aka yi ba? To in ma tafi dake muje ina?" "Oho sai ka nemo inda zamu." Miƙewa yayi yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin, caraf ta kamo bayan rigarshi yana ja tana ja yana ja tana ja, da ƙarfi ya fincike ai kuwa ya ƙarasa ɗaya ɗakin gudu-gudu sauri sauri yana shiga ya kulle yana haki wannan wani irin bala'i ne? To wallahi dole ya tsawatar mata ya nuna mata shi ba sa'an wasanta bane, kallon ɗakin yayi shima tayi kaca-kaca dashi, takaici da dana sani sun gama isarshi ace kai da gidanka baka da kwanciyar hankali, to shi yanzu kuɗin hayar gidan ma in ya ƙare bai san ya zai yi ba bare.

***** Mummy tun safe har dare ta kasa cin komai, gashi sai kiran Daddy take yaƙi ɗauka, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin Zainab na Dambatta. Ita kam bata san ya zata yi ba, wayar Inna ta kira don sam ta kasa samun nutsuwa. Inna ce ta ɗauka bayan sun gaisa tace "Inna na rasa ya zan yi Senate fa yaƙi dawowa gida." Inna ta sauke ajiyar zuciya tace "Halima ina tunaninki yake? Kin manta komai na rayuwarmu kece kike tsara mana yanda zamu tafiyar dashi? Ya kike neman maida kanki mara wayau? In ya tafi ki bishi inda yake mana." Ido Mummy ta runtse kafin tace "Zainab ma taje Dambatta, ina tsoron kada su faɗa mata wani abu in ta dawo ta sanar da babanta." Yanzu kam hankalin Inna ya tashi tace "To kiyi maza ki yiwa tufkar hanci amma ke garin yaya kika barta ta tafi?" Shafar fuskarta tayi tace "Ban sani ba wallahi kin san fushi take dani, Inna kinga abinda kuka ja min ko? Shi yasa nake ce miki ki bar yarinyar nan a wurinki yanzu ga abinda ya faru." Inna jiki a sanyaye tace "Kiyi hakuri Halima wallahi ni haushi nake ji ne in naga yaran can kun sadaukar da komai saboda su amma sam baki damu da Nabila ba." Ƙasan leɓenta ta ciza tace "Kema Inna duk gatan da Nabila ta samu dole sai ta samu sama da hakan? Yanzu wa gari ya waya?" Shiru Inna tayi don bata san me zata ce ba, kashe wayar Mummy tayi cike da takaici don a ganinta duk da sun zauna gidansu sirrin nan ba zai taɓa fitowa ba har abada. Miƙewa tayi ta shirya sannan ta kira drivern Daddy ta tabbatar inda yake kafin ta fito, kai tsaye driver ɗinta gidan Daddy inda suka taso ya kaita, har ta shiga falo baya nan sannan ta wuce ɗaki, yana kishingide a kan gado yana waya, yana ganinta ya kauda kai ya cigaba da wayarshi wanda tana ji ma tasan da Deputy Governor ne daga yanda yake yi mishi magana, zama tayi a gefenshi tana ɗan matsa mishi kafa, bai ko kalleta ba ya cigaba da wayarshi sai da suka gama sannan ya kashe, kusa dashi ta dawo ta jawo hannunshi tana matsawa tace "Senate please!" Wani irin kallo yayi mata yace "Ni Halima? Ni zaki munafurta? Shekara ba ɗaya ba ba kuma biyu ba ashe ke a soko kike zaune dani, wallahi ke kin san da badon ban san career ta siyata ta sake gurguɗewa ba da kin tafi gidan ku, amma nayi saki ɗaya bana son sake wani." Yatsa tasa da sauri ta rufe mishi leɓenshi, hawaye ne suka ciko mata tace "Senate kana tunanin a son raina na ɓoye maka? Wallahi a'a babu yanda zanyi ne, na daɗe ina son sanar da kai amma ban san ta ya zan fara ba, am so young sanda abin ya faru sannan ƙaddara ce ta afka min wanda har yanzu zuciyata ma tariyo mini abinda ya faru, in baka manta ba sanda Aunty ta fara barina ina shigowa gidan ku ba tausayi na bane ya kamata? Har nake zuwa ina tayata yan aikace aikace, ka tuna da kyau Senate a wani hali nake a lokacin?" Kallonta yayi don bazai iya tunawa ba amma yasan tabbas mahaifiyar Zainab ce ta jawota jikinta har wani sa'in take kwana a gidan saboda gidan da suke zaune ɗaki ɗaya ne shi yasa a lokacin da yace zai aureta aka dinga ganin wai cin amana zai yi wanda shi kuwa yasan so ne sannan da kyawawan halayenta da kuma guarantee da yake dashi na wanda zai kular mishi da family ɗin shi ya kuma ƙarfafa mishi gwiwa, abu mafi mahimmanci kalmar da ya fara girmama ta tsakaninsu sanda tace mai tana ji a jikinta zai zama governor nan gaba.

(Hmmm mudai kam bamu da bakin magana🥴)

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA BAKWAI*

{77}

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull