Baqeer complete - Chapter 56
Baqeer complete Chapter 56: Baqeer complete Chapter 56. Bakinta na rawa tace "Gidan Ummy a taimaka a kaini," ta ƙarasa maganar muryarta na wani irin rawa…
2,382 words
Bakinta na rawa tace "Gidan Ummy a taimaka a kaini," ta ƙarasa maganar muryarta na wani irin rawa tana jin har cikin jikinta na rawa, yanayinta da suka gani ne yasa suma ta basu tausayi, ta juya da sauri tana kallon Adamu tace "Don Allah," da wani irin desperation a muryarta. Hajiya Goggo jikinta ne yayi sanyi da ga yadda Zeey tayi tabbas bata san abinda ya faru ba, Zeey kamar zata yi kuka tace "Ya Adam Kawun fa? Ko wurinshi zan fara zuwa?" Ya kalleta shima jiki a sanyaye yace "Ya rasu sai dai mu yi mishi fatan rahama, yanzu watanshi biyu kenan da rasuwa." Jikinta ne ya ƙara mutuwa nan da nan taji idanunta sun ciko da ƙwalla, muryar Hajiya Goggo ce ta katseta da cewa "Ɗauki jakar kayan naki ki shiga da ita ciki idan kin huta zuwa anjima sai a raka ki, yanzu bata dawo daga wurin aiki ba." Ba don ranta yaso ba ta tashi taja akwatin kayanta ta shiga ciki kamar yadda aka umarce ta, shiru tayi a cikin ɗakin tana tunanin rayuwa, ajiyar zuciya tayi ta sakawa ranta son ganin Ummy bata ɗauka zata kai wannan lokacin ba'a haɗata da ita ba, gashi bata son zama a nan kar ma ayi mata zancen abinda zuciyarta bata shirya ji ba. Tana shiga ɗakin ta samu wuri ta zauna sannan ta ɗauki wayarta ta kira Daddy kamar yadda ya umarceta tayi ta sanar mishi ta iso lafiya. "To, ki gaishe su," kawai yace ya kashe wayarshi. Sai taji bata ji daɗi ba da yadda Daddyn yayi a ƙalla dai ai ya tambayi lafiyar mutanen gidan ko ba zai ce a bawa Hajiya Goggo wayar ya gaisheta ba. Har ta mayar da wayar cikin jaka ta ajiye sai kuma tayi tunanin faɗawa Baqeer isowarta lafiya. Ɗan gajeren saƙon sms ta tura mishi ta mayar da wayar ta ajiye. Hajiya Goggo ce ta shigo ɗakin hannayenta ɗauke da kwanuka, ajiye kwanukan tayi a gaban Zeey tana kallonta, ta ɗauka zata tashi ta karɓar mata kwanukan sai taga har ta ajiye Zeey bata yi alamun zata taimaka mata ba. Zama tayi a bakin gadonta tace "Ke kaɗai kike tafe ina Kabirun ko shi bai yi niyyar zuwa ya gan mu ba?" Ɗan taɓe baki tayi tace "Yana gida." Daga haka suka yi shiru don babu wani sabo a tsakaninsu. "Ku kune kuke yada zumunci amma mu baza mu iya yadaku ba don mahaifiyarku mace ce ta gari mai son zumunci." Shiru kawai Zeey tayi don bata san me ma zata ce mata ba, Hajiya Goggo tace "Sai kici abincin kafin Adamu ya dawo sai ya rakaki wajen Innar taki." "Wacece kuma Inna nifa wurin Ummi nake so naje ba wata Inna ba," Zeey tayi maganar cikin rashin kulawa. Da mamaki Hajiya Goggo ke kallonta jin yadda tayi mata magana kamar wata sa'arta babu tausasawa bare ladabi. Tuni ta murtuke fuska tasha kunu don ita ba'a kawo mata wargi. "Uwarki nake nufi, ko sai ance Ummi zaki fi ganewa," ta mayar mata. "Au wai Ummin ce Inna sai kace wata tsohuwa," Zeey tace ba tare data lura da yadda Hajiya Goggon ta canja fuska ba. Tashi tayi ta fita ta bar mata ɗakin don idan ta zauna watakila ta iya kaiwa Zainab ɗin hannu don taga alamar baza su shirya da ita ba sam. Buɗe kwanukan abincin tayi tana yatsina fuska, dambun shinkafa ne wanda yaji zogale da gyaɗa sai ƙamshin soyayyen man gyaɗa yake yi. Mayar da murfin tayi ta rufe don bata cika son cin irin wannan abincin ba. Kwanon sha ta buɗe sai taga damammiyar fura ce data ji nono tayi fari tas gwanin ban sha'awa. Sai furar tasha don ta manta yaushe rabon da tasha fura irin wannan don yanzu zamani yazo an canza mata dandanon ƙauye, har wani lumshe ido take yi saboda garɗin furar da yake ratsata. Tana gamawa ta haye gadon Hajiya Goggo ta kwanta don sai taji gaba ɗaya gajiyar data kwaso ta haɗu da baccin da bata samu tayi ba kwana biyu sun saukar mata da wata iriyar kasala bacci kawai take so tayi. Babu daɗewa kuwa baccin ya sure ta, koda Hajiya Goggo ta dawo ɗakin sai ta tarar baccinta yayi nisa, tattare kwanukan data kawowa Zainab abinci tayi ta fita dasu cikin ranta tana mitar yadda ta bar mata kwanukan a wurin ba tare data kawar mata dasu gefe ba. Sai daf da la'asar Zeey ta tashi daga baccin daya ɗauketa bata shirya ba, fita tayi tsakar gidan ta ɗauro alwala. A tsakar gidan taga Hajiya Goggo tana ta ƴan kaye-kayenta, sai taji ta tuna mata da Dada haka itama take sam bata iya zama waje ɗaya. "Hajiya Goggo wai ba kya gajiya ne?" Ɗagowa tayi ta kalleta fuskar nan a tamke tace "Gajiya da me?" Ƴar dariya Zeey tayi tace "Da aiki mana, na lura ku dai tsofaffi ba kwa son zama waje ɗaya wallahi," daga haka tayi shigewarta ɗaki ta bar Hajiya Goggo da bin bayanta da kallo, lallai wannan ƴa lamarin ta akwai gyara, Hafsatu na da aiki a gabanta don ga alama gaba ɗaya an gurɓatawa yarinyar tarbiyya. Sallar azahar ɗin da bata samu tayi ba lokacin da take bacci da la'asar duk ta haɗa tayi. Bayan ta idar ta dade tana yiwa Kawu addu'a sannan tayi shiru yanzu kam Ummy take son gani, ɗaukan wayarta tayi ta kira Adam, da kamar ba zai ɗauka ba sai kuma dai ya ɗauka yace "Ya aka yi?" A shagwaɓe tace "Please mana Ya Adam, kai fa nake jira kazo ka kaini wajen Ummy ɗin." "Gani nan," kawai yace ya kashe wayarshi. Ajiye wayar tayi ta kishingiɗa tana jiran shi, tashi tayi ta fita tsakar gida wajen Hajiya Goggo ta zauna, ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba sai ma cigaba da tayi da jan carbinta ita kuma Zeey tana danne-danne a wayarta, ita duk ta gaji da zaman ma wallahi don ita dai bata saba zaman shiru ba nan kuma ta lura kamar kakar tata ba mai yawan son surutu bace. Ƙasan zuciyarta kuwa kokowa take yi da ita akan manta abubuwan dake faruwa, ƙurawa gefe ido tayi tana tuno yadda Inna ta tsangwemeta har yasa take tunanin ko haushinta take ji saboda Mummy ta sadaukar da komai saboda su ashe bata sonta ne saboda tana ganin Mummy na kula dasu ta bar ƴar cikin ta, ajiyar zuciya tayi tana tausayawa rayuwarsu shi yasa take jin tayi daidai zuwa ganin mahaifiyarta da tayi. Hajiya Goggo tana kula da yanayinta wanda ya sake tabbatar mata akwai abubuwan dake faruwa da alama maganar ce ba ta son yi. Sallamar Adamu taji ai kuwa da sauri ta miƙe yana shigowa tace "Yauwa Ya Adam kwaso kayana mu wuce don Allah." Hajiya Goggo tayi caraf tace "Ki kwaso kayanki dai." Bata musa ba ta shiga ta jawo jakar suka yi sallama akan zata dawo suka fita, iska ta furzar suna fita tare da dafa kirjinta ji take yi kamar akan ƙaya take, gani take yi duk wani motsi data yi Hajiya Goggo na kallonta. **** Wannan shine kira na bakwai da Asiya ta ke yiwa Bello amma yayi kunnen uwar shegu da ita, ganin da gaske bashi da niyyar amsa mata yasa tace "Kasan Allah Bello in har ba ka shirya karɓar tashin hankali mara misaltuwa ba ka sanar dani yaushe zamu bar garin nan, yau naji rainin hankalin da bazan iya ɗauka ba." Sake gyara kwanciyarshi yayi wani irin baƙin ciki na kwasar shi, yanzu fisabillilahi hakan shine auren? Ya gama sadaukar da komai saboda ita amma bata ma damu da halin da yake ciki ba? Gidan daya kashewa kuɗi ta maidashi kamar bola? Cike da tsiwa ta kama kugu tace "Malam magana nake yi maka kar ka maidani ƴar iska fa." Da alama shima yanzu ya kai bango don zama yayi ya kalleta sheƙeƙe yace "Kinga Allah in har baso kike yi mu samu babbar tangarɗa ba ki wuce ki gyara mini gida na, sannan nima da kika gani koroni aka yi a ƙasar dana je balle kisa ran zan kaiki don kin yi masifa, ki barni nima naji da abinda ke damuna ko kuma wallahi daga ni har ke muyi dana sani, don na kula sam baki da tunani," yana kaiwa nan ya gyara kwanciyarshi yana ji shi dai wannan aure duk shi ya janyo mishi talauci da ya lallaɓa ƴan kuɗaɗen shi ya tabbatar da har yanzu yana da kuɗaɗenshi amma ya biyewa wannan shashashar tasa duk sun kwashe kuɗin yanzu gashi nan ba ƙasar wajen ba aiki babu kuma kuɗin, don inda yake aiki ma anan Nigeria ganin shi ya zama celebrity ya kori kanshi da kanshi wai shi a dole ya girmi aiki a wurinsu. ****** Baqeer sam yau bai zauna ba daga shi har su Salim da Tanimu don sai yamma suka kamalla komai, ƴar karamar miƙa yayi yana kallon Salim yana cewa "Ya maganar abinda za'a yi mana printing ɗin?" Salim yace "Wallahi ban koma ba, jiya har naje zan shiga naga ƙaninka a waje shi da gang ɗin shi kasan ba kai gareshi ba yanzu sai yayi mini hauka cikin mutane shi yasa kawai na bar wurin ba tare dana ƙarasa ba." Kai Baqeer ya girgiza yace "Allah ya shirya Kamalu shi ko girma baya yi." Baki Salim ya taɓe yace "Kaima akwai taka dashi shi yasa duk ranar da ya ganka kai da masoyiyarshi to ka tabbatar kana da abun kare kanka don kuwa akwai yaƙi." Cike da rashin fahimta Baqeer yace "Masoyiyarshi? Ni me zai haɗani da budurwarshi?" Salim ya ɗan yi dariyar mugunta yace "Ai ba abinda ma bai hadaku ba, kai dai ka shirya kawai," yayi maganar yana hango abubuwan haukar da Kamalu yayi mishi akan Roshni lallai akwai drama ranar da zai ganga da Baqeer. Waya Baqeer yayi da mutanen da yake yiwa zane akan wasu sketch da ake so yace zasu samu ƙarshen satin nan, don shi kanshi kuɗin yake buƙata su gama shirya shagon sai ya fara shirin da yake son yi don tabbas wannan ƙudirin nashi yana fatan aiwatar dashi. **** A hankali Zee take bin gidan da kallo don dai kam ko a cikin gari ba za'a kira gidan da sunan gidan talaka ba don gida ne na masu rufin asiri, nan da nan kuma sai taji jikinta ya kara wani irin sanyi, lallai basu yiwa kansu adalci ba ace mahaifiyarsu bama su san wanda take aure ba? Basu san ya take rayuwa ba? Balle su san ƙannensu da aka haifa musu? Adam har ya fita ya ciro kayanta a bayan motar bata da alamar fitowa, ganin haka yasa shi yin gaba tare da ƙwanƙwasa ƙofar gidan, daga ciki wani saurayi wanda bai fi shekara 14 ba ya fito ya buɗe ganin Adamu yasa shi sakin dariya yace "Ya Adamu kai ne?" Murmushi yayi yace "Nine, Ummy ta dawo? Don tayi baƙuwa." Kallon motar yayi sannan ya kalleshi yace "Ta dawo tana ciki," tare suka shiga da Adamu, Zainab da ƙyar ta fito ta bisu a baya, ba dai yaron Ummy bane wannan? Waigowa yayi ya kalleta yace "Aunty ina wuni?" Bakinta cikin ɗan sarkewar murya tace "Lafiya ƙalau." Tsayawa suka yi a waje ganin yaron yayi ciki, Adamu yace "Muje mana." Ta girgiza kai tana cewa "Ka shiga zan shigo." Bai musa ba yayi ciki don yasan dole haɗuwar zata zo musu daban, gefe taja tana sauke ajiyar zuciya tare da fitar da iskar dake bakinta. Wayarta taji tana ƙara da sauri ta cirota tana fatan Allah yasa Baqeer ne, ai tana ganin shine ta ɗauka da sauri cike da shagwaba tace "Allah nayi fushi yau kuka zan tayi maka." Har cikin jikinshi sai da yaji shagwaɓar nan ya murmusa yana tuno kalaman Junaid yana cewa "Hmmm wata dai tana son yin kukan nan." Baki ta turo tace "Ya Baqeer ina gidan Ummy na kasa shiga." "Why?" Ta sauke wata ajiyar zuciya kafin tace "Wallahi ban sani ba kawai sai nake jin kamar ban shirya ba, me kake gani ya kamata nace mata in mun hadu? Ina wuni? Nice ƴarki ko…….." maganar tace ta katse jin kamar motsin mutum hakan yasa ta waigo, nan da nan taji zuciyarta ta karye da fuskar da baza ta iya kwatanta kamaninta ba, don Daddy ko hotunanta bai bar musu ba suma da yake basu damu da ita ba basu taɓa tambayarta ba, matar da ke tsaye jikin ƙofar falonta bata wuce shekara hamsin ba, tana da kyaun jiki amma kana ganinta kasan mahaifiyar Zainab ce don kamannin dake tsakaninsu ma ba'a magana, idanuwanta Zee ta kalla wanda take ganin tsantsar bege a ciki, Zeey wasu zafafan hawaye ne suka gangaro ta sulalo da hannunta ƙasa ba tare da ta katse wayar ba, kallon juna suke yi kafin Ummy ta haɗiye wani abu mai ciwo tace "Me kike yi a waje? Ki shigo mana." Kasa jure yanayin da take ciki tayi ta ƙarasa wurinta da sauri kawai ta rungumeta, don tasan babu wata magana da zata iya yi yanzu kam bayan ganin Ummy da idonta, hawaye ne suka zubo kuncin Ummy ta ɗan runtse ido. Yarinyar data rugu da gudu ta rungume Ummy Zee ta kalla, ta ɗauka tafi kama da Ummy don Kabir da Daddy yake kama itace kamarta daban amma ganin yarinyar yasa tasan ta fita don komai nasu iri daya ne da Ummin. A hankali yarinyar tace "Aunty ina wuni? Meya samu Ummyna?" Kallonta Zee tayi yarinyar bata fi shekara bakwai ba, wannan wani irin son kai suka aikata? Taya suka aikata hakan? Gaskiya daga ita har Kabir har Daddy basu yiwa kansu adalci ba.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN BIYAR*
{75}