Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 55

Baqeer complete - Chapter 55

Baqeer complete Chapter 55: Baqeer complete Chapter 55. ***** Kwanakin nan bata cikin nutsuwarta saboda ta daina samun Bello a waya ko zata kwana tana…

3,248 words

***** Kwanakin nan bata cikin nutsuwarta saboda ta daina samun Bello a waya ko zata kwana tana nemanshi wayarshi bata shiga, babbar damuwarta yadda kusan komai nata ya ƙare saboda dama ba wata sayayya suka yi mai yawa ba tunda dama a tsarinsu baza su daɗe a ƙasar ba shi yasa suka sayi kayan abinci na adadin kwanakin da suke saka ran zata yi anan kafin ta bishi to gashi kwanakin har sun haura ita bata bishi ba sannan kuma bai turo mata wasu kuɗaɗen da zata sayi wasu kayan buƙatun ba. Tana kwance a parlourn ta wurin yayi kaca-kaca don tun bayan barin Habi gidan bata ƙara saka tsintsiya da sunan shara ba, komai taci anan wurin take barin shi bata ɗaukewa don haka parlourn ya cika da ƙazanta. A gefe ga farantan da take cin abinci nan sun yi tsibi guda don ko su bata iya kawarwa sai dai idan tayi amfani da wani ta ɗora shi akan waɗanda ta tara, ga ledojin tarkacen kayan ciye-ciyenta nan da ribobin lemo da ruwan da take sha sun haɗa wata ƴar ƙaramar bola. Ita kanta idan aka kalleta ba za'a so sakewa ba don ga dukkanin alamu tayi kwanaki jikinta bai ga ruwa da sunan wanka ba, gaba ɗaya tayi biji-biji da ita duk ta fita daga hayyacinta. Tana kwance tana danne-danne a waya ga alama ita wannan bolar data haɗa bata damunta don chatting take yi da sababbin ƙawayen data yi tana murmushi don sai fasa mata kai suke yi suna cewa ai sun ɗauka da suka jita shiru kwana biyu ko har ta tafi ne babu labari. Turo ƙofar yayi ya shigo parlourn bakin shi ɗauke da sallama yana rataye da jakar matafiya a kafaɗar shi sai akwatin trolley da yake ja a ɗaya hannunshi. Sallamar da yayi ce ta maƙale mishi a maƙohgaro ganin parlourn kamar ba nasu ba, fita yayi ya duba yaga tabbas gidan ne dai ya shigo don haka ya koma ciki yana ƙarewa parlourn da alamu suka nuna kamar babu mutum ɗin dake rayuwa a ciki. A kwance akan doguwar kujera ya ganota. A fusace yace "Asiya miye haka?" Yana nuna tsakar parlourn da hannu. Wai sai a sannan tasan da shigowarshi cikin gidan don hankalinta gaba ɗaya ya ɗauku ga wayar da take dannawa ko kusa bata ji motsin shigowarshi ba. Miƙewa tayi tsaye fuskarta ƙunshe da mamakin ganinshi a daidai wannan lokacin da bata yi zato ba tace "Bello! Saukar yaushe?" Bin jikinta yayi da kallo sai yaji ranshi ya ƙara ɓaci, bsyan ƙazantar gidan har ma jikinta ba zata iya tsayawa ta gyara ba. Tsaki yayi kawai ya wuce ciki ya barta anan. Bin bayanshi tayi sai ta ganshi a tsaye yana ƙarewa ɗakin kallo. "Tafiya babu sanarwa Bello, hala kazo ka tafi dani ne. Kamar kasan dama na gaji da zaman ƙasar nan wallahi duk na matsu na bika ashe ma kai da kanka zaka zo mu tafi shi yasa bana samunka a waya." A fusace yace"Dallah Malama yi mini shiru, a hakan zan kwasheki na fita dake ƙasar waje kina zuba wannan uwar ƙazantar, kalli jikinka saboda Allah ki duba muhallinki kamar ba gidan amarya ba komai ya fita daga hayyacinshi tsabar ƙazanta." Kallon kanta tayi ta kalli ɗakin data manta yaushe rabon da a gyara a hakan ma wai shine mai ɗan dama don ba kasafai ta cika shigowa nan ɗin ba, cewa tayi "ya kake so nayi saboda Allah bayan nace maka zan nemo mai aiki saboda aikin yayi mini yawa bazan iya ba kaƙi amincewa." Ajiye kayan hannunshi yayi zai fita daga ɗakin tace "To yaushe zamu tafi don na fara shiri?"

Wani wulaƙantaccen kallo ya wata mata yace "Ina? Ai babu inda zamu don nima na dawo kenan," kawai ya fice ya barta a ɗakin. Bin bayanshi Asiya tayi da kallo hankali a tashe tace "Iyyeee.......Bangane ba ba inda zamu je a ina? Ni kaga bari nazo na tattara kayanmu." Tsaki yai kawai ya cigaba da tafiya, kallan mamaki ta bishi dashi ai ko za'a mutu sai ya fitar da ita daga kasar nan, tab ai bataga yban daya isa ya hanata ba....

Mukam mukace to ga fili ga doki🥴

*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA UKU*

{73}

Duk da Baqeer yasan zai yi missing ɗin Zee in ta tafi amma wata irin nutsuwa da jin daɗi yake ji, tabbas a matsayinta na mace tana buƙatar ta nemi mahaifiyarta sai dai in ita mahaifiyar ce ta nuna bata son zuwan nata, yau yana tashi ya tuna yau ne zata wuce, tun yanzu ya fara jin rashinta ya fara damunshi, wayarshi ya ɗauka ya tura mata text _Karfe nawa zaki wuce?_ Ba dadewa sai ga reply _11am In Sha Allah_ ajiyar zuciya yayi ya maida wayar, wani saƙon ne ya ƙara shigowa _In na dawo ina son jin amsar tambayar da nayi maka_ murmushi ne kawai ya bayyana a fuskarshi don shi kanshi amsar yake son bata, ganin bai yi reply ba yasa ta shiga wanka, tana fitowa ta shirya cikin atamfa anyi mata ɗinkin doguwar riga tasha kwalliya da stones tayi kyau sosai, bata son ɗaura ɗankwali hakan yasa tasa ƙaramin mayafi tayi rolling sannan tasa abaya buɗaɗɗiya a sama, fitowa tayi daga ɗakin, gidan yayi shiru kamar ba mutane a ciki, ita kaɗai tayi breakfast shi yasa kawai taci toast bread da tea, ji take yi komai baya yi mata daɗi a gidan, ƙofar ɗakin Mummy taje tana tafe tana tuno irin tsananin ƙaunar da Mummy take nuna mata, ta tabbatar wannan abinda take yi mata dole in taga ta shareta abun ya dameta. Hannu tasa ta murɗa ƙofar ɗakin ta tura a hankali, a duƙunƙune ta ganta tana bacci da alama sanyi take ji, bargo ta janyo ta lulluɓa mata cike da tausayin halin da suka tsinci kansu sai dai bata ji zata iya yafe mata yanzu kila dai in taje wurin Ummi ta dawo. Juyawa tayi ta fita bayan ta sanar da masu aiki akan su kai mata abinci anjima sannan in bata ci ba su sanar da Kabir. Motarta ta shiga tana ganin saƙon Daddy wai zai turo driver ya kaita da sauri tayi mishi reply akan ita da kanta take son zuwa don Allah ya barta. Tayi sa'a daya ce mata Allah ya kaita lafiya ta tabbatar ta kira shi in ta isa. Haka ta fito daga gida tana tafe tana tunanin yadda zata yi magana da mahaifiyarta don kuwa ita ko gidan da take aure bata sani ba, shekarun baya sukan je Dambatta amma tunda dangin mahaifiyarta suka fara tsangwamar Mummy sai taji sun fita daga kanta gaba ɗaya, hakan yasa ta tattarasu ta watsar dasu. Wayarta ta kalla wanda kiran Junaid ya shigo maimakon ta ɗauka sai ta kifa wayar ta cigaba da tuƙin ta, tana tausayawa Junaid sai dai ba zata sadaukar da kanta akan abinda tasan ba zai sanyashi farin ciki ba, ita mace ce da in har ba ta son abu to fa bata iya ɓoyewa, haka zalika in tana son abu kana iya gani a fuskarta, shi yasa har yanzu take mamakin yadda Baqeer ya kasa gane son da take yi mishi, ajiyar zuciya tayi ta cigaba da tuƙi ai ya dai yi ya gama in ta dawo zasu yita ta ƙare, bazata bari suyi ta tafiyar tatata haka ba.

***** Baqeer yau yana da appointment hakan yasa ya shirya da safe Tanimu yazo suka je, ga mamakinshi office ɗin Junaid aka kaisu, sunfi minti goma suna jira kafin yazo, nan yace Baqeer ya biyoshi, haka Baqeer ya gungura kekenshi suka nufi ciki, Junaid ya zauna yana sa Baqeer yayi gwaje-gwajen abinda ya umarceshi, kafin daga bisani shima ya zo da kanshi ya duddubashi, kallon Baqeer yayi bayan sun gama, fuskarshi sam babu walwala yace "Akwai wani abu ne tsakanin ka da Zainab?" Da mamaki Baqeer ya kalleshi, sai dai haka kawai yaji ya kasa bashi amsa a ganinshi wannan tambayar ba shi ya kamata yayi wa ba, Junaid ya ɗan kauda kai yace "Of course nasan ba kai bane kenan akwai wani?" Sake kallonshi yayi duk da zuciyarshi na son sanin me yake nufi da kalamanshi sai dai haka kawai yaji ba zai iya tambaya ba, Junaid ya sauke ajiyar zuciya yace "Baqeer please naga Zainab na ganin girmanka da kula da kai kamar yayanta me zai hana ka bincikomin wanda ke hure mata kunne yake neman hanata bin umarnin iyayenta?" Yanzu kam yanayin kallon da Baqeer yake yi mishi ya canza, kallo ne mai alamar tambaya wanda da alama Junaid ya fahimci kallon da yake mishi, ya ɗan miƙe tsaye yana sa hannu a aljihunsa yana cewa "Tana da gardama ne ban san ya zan yi ta fahimceni ba, wannan dalilin yasa nace yau a turoka wurina," ya ƙarasa maganar jiki a sanyaye, yana ƙoƙarin matsawa daga wurin yaji ance "Babu komai a tsakaninku kenan ko me?" Da mamaki ya waigo suka yi wa juna kallon kallo shi da Baqeer, kallon da su biyun kaɗai suka san ma'anarshi sai dai gaba ɗaya Junaid ji yayi ya kasa bada amsa, sai kauda kai da yayi wanda hakan yasa Baqeer ya tabbatar da amsar da yake son sani, a hankali ya saki siririn murmushi wanda da alama bai san sanda ya fito daga ƙasan zuciyarshi ba. Ba tare da yace komai ba ya fara tura kekenshi zuwa ƙofar fita, ina ma Zee tana nan ya ruga ya sanar da ita ƙaunar da yake yi mata? Dariya ma kalmar Junaid ta bashi wato ya binciko kanshi kenan ko me? Don ya tabbatar in har Zeey ba Junaid take kulawa ba to tabbas akwai sonshi a ranta kamar yadda yake sonta, ya daɗe yana ganin sonshi a ƙwayar idanuwanta sai dai in ya tuna soyayyarsu da Junaid sai yayi tunanin tausayi ne, wani tausayi ne ake tambayar matsayi? Abinda yaji zuciyarshi ta tambayeshi kenan, wani murmushi ya karayi ji yake yi tun yanzu ya ƙosa ma ta dawo ya fallasa mata abinda ke ranshi don wannan maganar dole sai gashi gata. Kamar ya kirata a waya sai ya fasa tunowa da yayi tana hanya, nan suka wuce shago, sun kammala ɗinki na biyu suka sake jera kayyakin da Salim ya kawo musu, suna yi yana ɗan sakin murmushi wanda yasa Salim kasa jurewa yace "Wai hala Zainab tazo yau?" Da mamaki ya kalli Salim yace "Me kake nufi?" Cigaba yayi da aikin yana cewa "To Malam Baqeer ai in dai aka ganka kana murmushi kwanan nan to tabbas akan Zeey ne." Nan da nan ya tamke fuska yace "Me kake nufi?" Dariya Salim yasa yace "Ah to ku za'a tambaya ai ba wani ba," yayi maganar cike da zolaya.

****** Mumy kam bata tashi ba sai karfe sha biyu don dama sai wajen goma ta sake kwanciya, ganin bargo a jikinta yasa tayi saurin miƙewa tana tunanin Senate ne ya shigo tana bacci, sai dai tana shiga ɗakin shi ta tabbatar ba shi bane, jiki a sanyaye ta juyo ta nufi ɗakin Zee don babu shakka in dai ba shi bane to Zainab ce, shiga tayi sai dai babu alamar Zainab a ɗakin ga dai ɗakin nan an gyarashi tas wanda hakan yasa tasan mai aiki ce tayi, fitowa tayi ta nufi kitchen tana kiran Karima wacce tasan sun jitu da Zainab. Da sauri ta fito ashe itama wurin Mummyn zata je ta kai mata breakfast tunda taga ta farka ta shigo don ta tattara kayan abincin, Mummy ta kalleta tace "Ina Zainab?" Kai tsaye tace "Ta fita Mummy tun ɗazu." Idanun Mummy na kanta tace "Ina?" Kai ta girgiza wanda hakan yasa Mummy juyawa don tasan dama ba zata san inda take ba, Kabir ta hango sanye da jeans da long sleeve shirt da key a hannunshi yana ɗan kaɗa su yadda ya saba, tayi saurin cewa "Kabir baka yi breakfast ba zaka fita." Waigowa yayi ya kalleta don shi bai masan me zai ce mata ba, neman juyawa yake yi tace "In har Zainab bata fahimceni ba kai dai bana ji ya kamata ka ƙi fahimtata, Kabir ka manta abubuwa nawa na ɓoye sirrinka? Sai ni don na ɓoye nawa sirrin ƙwaya ɗaya shi kenan sai ka kasa yafe mini?" Cak ya tsaya sai kuma ya waigo, nan da nan jikinshi yayi sanyi, ganin haka yasa ta tako inda yake tace "Kai bai kamata kayi mini haka ba, Kabir ka sani bazan iya furta kalmar bane shi yasa na ɓoye bawai don inaso ba, nasan nayi laifi amma sai ku duba zaman amanar da muka yi ko?" Murya cikin sanyi yace "Mummy na sani sannan zan huce ki bani kwana biyu don Allah, nasan dama Nabila ba da izininki tayi abubuwan nan ba." Kai ta jinjina alamar fahimta kafin tace "Zeey fa? Na duba bata nan." Tsaki yayi yace "Dambatta taje." Wayar Mummy dake hannunta ce taji tayi mata nauyin ɗauka wanda sai jinta suka yi a ƙasa, hannu yasa ya ɗauko ya miƙa mata sannan ya kalleta yace "Mummy?" Murmushin yaƙe tayi tace "Daddynku ya barta?" Ɗan wani motsi yayi da bakinshi yafin yace "It seems so, don ta tambayeni jiya nace ba zani ba." Kai ta jinjina kawai ta juya tana tafiya ƙafafunta na ɗan neman kasa ɗaukan ta, ɗaki ta shiga ta kalli abincin da Karima ta ajiye, hannayenta tasa a matse-matsin cinyoyinta kamar mai jin sanyi tana matsasu, tama kasa yin tunanin komai, wayar Zee ta kira sai dai da alama babu network ko wayar a kashe take don taƙi shiga, ajiyewa tayi tare da sake matse hannayenta.

^**** Tunda ta shiga Dambatta gabanta ke faɗuwa, yaushe rabonta ma da ƴan uwan mamanta? Duk laifin da suke yiwa Mummy ya kamata ace sun yi musu magana ne ba wai su janye jikinsu ba, wayar babban yaron ƙanin mamanta ta kira don numbershi kaɗai take dashi shima don ya kirata ne kwanaki akan za ayi family meeting in da hali suzo, shine lokacin data tambayi Daddy akan zata zo ya hanata daga nan tayi saving ta kira tace baza su samu zuwa ba, har kiran ya katse bai ɗauka ba, hakan yasa ta sake kira, yanzun ma kamar zai katse sai kuma taji ance "Hello?" Ajiyar zuciya tayi tace "Ya Adam kana ina? Gani a Dambatta." Duk da yayi mamakin zuwanta bai hanashi cewa "Dambatta? Ke ɗin? Sannan in kinzo menene nawa a ciki?" Hankali a kwance tace "Kaga don Allah kar mu tsaya shiririta kana ina? Sam na kasa gane garin gani dai kusa da wani shago, gefen tasha kazo sai muje gidan Hajiya Goggo daga nan ina so in ɗan yi ziyara." Ga mamakinshi kafin ma yace mata zai zo sai ji yayi tace "Kayi sauri ina jiranka," tana kaiwa nan ta kashe wayar tana kallon mutane nata hada-hada, murmushi tayi tana tunanin yanzu fa kowa da tashi rayuwar, kowa da matsalolinshi. Atm ta hango daga gefe ta gangara ta ciro kudi 100k tasa a jakarta, sannan ta sake dawowa, tana kokarin duba agoggo taji anyi knocking glass ɗinta, zugewa tayi ta kalleshi da yake shi ta sanshi har sanda tazo sallama zata tafi ƙasar waje shi yasa bata yi wani kokonto akanshi ba hakan yasa tace "Ya Adam shiga." Shiga yayi ya tamke fuska shi a dole yana son ta bashi haƙuri, Zeey ta hau hanya tana cewa "Ina zamu yi?" Samun kanshi yayi da nuna mata sai dai fuskar nan har yanzu babu wargi, har suka isa gidan Hajiya Goggo, parking tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tace "Muje?" Gaba yayi yana tafe yana muzurai, ita kam ko a jikinta. Daga waje yace "Hajiya Goggo ga Zainabu." Tana daga ciki tace "Zainabun Malam Lawi?" Zeey tayi saurin cewa "Hajiya Goggo taku dai." Mamaki ne ya kamata ta ɗan yaye labule don ganin wacece, Zeey ta sakar mata murmushi tace "Hajiya Goggo ina wuni?" Tamke fuska sosai Hajiya Goggo tayi wanda babu alamun wargi a tattare da ita, ta maida labulen tana cewa "Hala aurenki yazo ne kina tsoro kar azo biki aga babu dangin mahaifiyarki ko ɗaya." Zeey ta sani sarai basu kyautaba ta taho jikin ƙofar ta tsaya tana cewa "Hajiya Goggo kishiruwa tunda na taho bansha ruwa ba, sannan bikina bai zo ba da saura sosai." Hajiya Goggo bata tanka mata ba sai kuma can ta leko kamar an tunzuro ta tace "Kun gama tozartamu shine yanzu zaku dawo neman mu? Ace duniya da gaskiya? Kwanaki Kawu yana kan gadon mutuwarshi amma burinshi ya sakaku ke da Kabir a idanunshi, nan na wanki ƙafa ni da Altine muka je har gidan ku amma aka hanamu shiga aka koro mu wai mahaifinku ya hana mutanen Ɗambatta shiga mishi gida, haka muka tura a sanar da matar gidanku dalilin zuwan mu amma fir aka hanamu shiga, muka gaji da zama a waje muka dawo." Kalaman Hajiya Goggo ne taji sun ɗaure mata kai, mene? Ita dai a iya saninta sune suka je suka ciwa Mumy mutunci akan ta mallakesu, me suke nufi kuma yanzu? Adamu ne yayi saurin cewa "Allah in na tuna abun nan ji nake yi kamar naje har gidan dukanku nayi muku rashin mutunci don haka ki zo ki tattara ki bar mana gari." Zee gaba ɗaya kanta taji ya kulle, bakinta na rawa tace "Anya ba ciki kuka shiga ba?" Tsaki Dada tayi tace "Yaushe rabon da ko harabar gidan ku a barmu mu shiga? Ni ban masan kun koma gidanku na da ba sai da muka je wancan aka ce kuna nan to Allah ya taimakemu mahaifiyarku akwai wata ƙawarta a unguwar ita tayi mana kwatance muka je." Idanuwan Zee ne suka fara canza launi tsoro da fargabar abubuwan da take ji su zama gaskiya take, taya zata fuskanci abubuwan nan in har Mumy ƙarya tayi musu a karo na biyu? Hajiya Goggo ce ta katseta da cewa "Kuje can mu mun sallama ku ai ba ku kaɗai muke dasu a dangi ba." Bakinta na rawa tace "Gidan Ummy a taimaka a kaini," ta ƙarasa maganar muryarta na wani irin rawa tana jin har cikin jikinta na rawa, yanayinta da suka gani ne yasa suma ta basu tausayi, ta juya da sauri tana kallan Adamu tace "Don Allah….."

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA HUƊU*

{74}

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull