Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 54

Baqeer complete - Chapter 54

Baqeer complete Chapter 54: Baqeer complete Chapter 54. **** Zeey kam bayan sallar Isha'i tana kwance kan sallaya bacci yayi gaba da ita, bata farka ba sai…

2,875 words

**** Zeey kam bayan sallar Isha'i tana kwance kan sallaya bacci yayi gaba da ita, bata farka ba sai asuba, haka ta tashi tayi sallah sannan ta zauna akan gado tana tunani, fitowa tayi ganin gari ya fara ɗan haske ta nufi ɗakin Daddy, sai dai da alama ma baya gidan, jikinta ne yayi sanyi hakan yasa ta juya, muryar Mummy taji tace "Auta bai dawo ba, da alama a guest house ɗinshi ya kwana." Bata tanka wa Mummy ba kawai ta koma ɗaki har ta zauna ta tuna gift ɗin da Baqeer ya bata hakan yasa ta fito taje motarta ta ɗauko ta koma ɗaki, anan kan sofa ta zauna ta buɗe jakar, idanuwanta ne suka sauka kan fabric ɗin nan, ta fara janyoshi ta wareshi, nan da nan tayi wani murmushin jin daɗi, abayar tayi mata kyau har bata san yadda zata kwatanta ba, a fili ta furta "My Baqeer." Ta ɗan rungume abayar, turaren ta ciro ta ajiye shi akan dressing mirror sannan ta ajiye abayar a bakin gado, agoggo ta kalla karfe takwas na safe gani take lokacin ma kamar baya sauri sam, saƙo ne ya shigo wayarta hakan yasa ta janyo wayar sai taga daga Baqeer ne, wani murmushi ta saki a fili tace "ɗan halak!" _Sending you good thoughts and hoping you believe in yourself just as much as I believe in you. Morning_ Sakon ta ƙurawa ido tana jin wani irin kewar Baqeer na shigar ta, dole zata bayyana mishi ƙaunar da take yi mishi don a wannan lokacin tana ji gwara tayi aure ta bar gidan don ganin Mummy ya fara mata wahala. Maimakon tayi mishi reply sai ta kwanta ta ɗaura wayar a saitin ƙirjinta ta rungume tana tunanin Baqeer a haka wani ɗan karamin bacci yayi awon gaba da ita.

**** Baqeer kuwa bayan ya tura mata ne ya sake karantawa, goshinshi ya ɗan riƙe yace "Ko dai saƙon bai kamata bane?" Sai kuma ya girgiza kai yace "Abinda ke raina ne sannan I think it's time to let her know abinda nake ji a kanta, in har bata yi gwara na haƙura kafin na ruguza abinda ke tsakaninta dasu Dada." Da wannan shawarar ya cigaba da exercise dinshi, gwada sauke ƙafar yayi yana ɗan neman yin amfani da ita ya tsaya tsaye, sai dai yaji ya kasa, ya sake nan ma ya kasa, dabara ce tazo mishi ya saukesu sannan ya riƙe head board na gadon ya ɗan sa ƙarfi gadon ya zame mishi kariya ya riƙe, yana tsayuwa ko second biyar bai yi ba ya faɗa kan gadon, samun kanshi yayi da dariya yace "Baqeeru da sauranka." Wayarshi ya sake janyowa Zee har yanzu bata yi reply ba, IG ya shiga ya sake posting na wasu flyers da yasa aka musu na adverts sannan yai shiru yana tunanin wani yankan ɗinkin maza daya fara, wani unique designs ne wanda bai taɓa ganin anyi ba, ya tabbatar in aka gama ɗinkin nan zasu samu mutane In Sha Allahu. Sai wajen goma Tanimu yazo suka je makaranta suna dawowa ya leƙa shagonsu suka sake gyarawa su biyu sannan ya ƙarasa yankan da yake yi, yanayi yana nunawa Tanimu yadda zai yi ɗinkin, basu gama ba sai karfe sha biyu, wani murmushi ya saki ganin ɗinkin ya fita sosai yadda ya tsarashi, Tanimu kam sai dariya yake yi bakinshi yaƙi rufuwa. Baqeer yayi murmushi yace "Muna needing styles kamar biyar kafin mu buɗe shago, na mata muna da su kawai ɗinkawa zamu yi sannan ina so na sayi wasu manyan electric sewing machine idan aka samu kuɗi, ina ganin daga nan zamu iya buɗe shagon." Tanimu yace "Allah ya ƙara daukaka ka, zuciyarka mai kyau ce shi yasa Allah ba zai barka haka ba." Fitowa suka yi suka shiga adaidaita suka yi hanyar gida, suna parking ya hau kan kekenshi sai ga motar Zeey tayo kwanar, bai san sanda ya saki murmushi ba, ya kalli Tanimu yace "Ka wuce gida ni zan ƙarasa, juyawa yayi shi kuma ya tsaya har sai da ta kashe motar, kafafuwanta ta zuro idanuwanta na kanshi shima haka, kafin ta fito ta maida kofar ta rufe. Kasa ɗauke ido yayi daga kanta ganin abayar daya saya mata ce ta saka, bai ƙara ganin kyan abayar ba sai yanzu da ta saka, tayi kyau har ya rasa me zai ce. Ido ta ɗan lumshe tana murmushi kafin ta fara takowa inda yake, sai data zo kusa dashi tace "Na sani nayi kyau kar mutanen waje su gane ka kasa ɗauke ido daga kallona." Tana kaiwa nan tayi ciki, a bakin ƙofa ta ɗan tsaya sannan ta waigo sannan tayi mishi murmushi tayi mai ƙaramin gwalo, sumar kanshi ya shafa yana jin wani yanayi wanda ba zai iya fassarawa ba, fuskarshi ya shafa sannan ya sake murmushi yabi bayanta. Dada ce take cewa "Zainabu na! Lale lale kai ina zaki haka kika sha kyau? Ba dai wurin saurayinki zaki ba?" Ta gefen ido ta kalli inda Baqeer ke tahowa tace "Ya riga ya ganni Dada yana gama ganina nazo kema ki ganni." Nan da nan yanayin fuskarshi ya canza, ya tamke fuska sosai da kayanshi daya bata zata je Junaid ya ganta? Dada ce tace "Shiga falo ki zauna bari na ƙarasa abu." "Dada kema ki dinga hutawa don Allah, ni kam na kai shekarunki bani ba girki." Dariya tayi tace "To ai gwara na motsa jikina bana son zaman haka nan, sannan yawanci kinga abinda nake fa ba mai wahala bane." Zeey ta nufi inda take har zata ce zata tayata ta tuna babu abinda fa ta iya hakan yasa tayi saurin yin kwana tayi falo, Baqeer ranshi a ɓace ya gungura yayi ciki yana kuncini, yana jin Dada na cewa "Wannan kai dai wallahi baka ji daɗi ba, matarka akwai aiki a gabanta." Bai tanka mata ba ya shiga, Zeey ce ta kalleshi ya ɗauka tana ciki sai ya ganta daga gefen ƙofa kaɗan tace "A dinga sakin fuska dai Ya Baqeer." Kallonta yayi duk da yana jin haushinta sai yaga kamar har ƴar ƙaramar rama tayi, jiki a sanyaye yace "Are you okay now?" Nan da nan yanayinta ya canza, ta girgiza kai alamar a'a tace "I'm not." Wani irin sanyi jikinshi yayi maimakon yayi ɗaki kamar yadda yayi niyya sai ya nufi cikin falo ya ja burki ya nuna mata kan kujera dake gefenshi kaɗan ya buga kaɗan alamar tazo ta zauna. Ƙarasawa tayi ta zauna ya kalleta yace "Meke faruwa?" Kallonshi tayi zuciyarta na zafi tace "Komai ma ya faru, komai da nake tunanin shine gaskiya ya koma ƙarya, yanzu ban san dame zan yarda ba." "Kin yiwa yayanki magana akan mahaifiyarku?" Kallonshi tayi tace "Itan ce ba neman mu take yi ba." "Kunji dalili daga wurinta? Ko ku kun taɓa nemanta?" Idanuwan ta ne suka sake yin raurau alamun son yin kuka tace "Ni naso zuwa wurin danginta amma abinda suke yiwa Mummy yasa naji bana so." Maimakon ya bata amsa sai ya kafeta da ido, kai ta sunkuyar da sauri cike da shagwaɓa tace "Me nayi kuma?" Shi kawai mamaki yake yadda sam basu da mai basu shawara yace "Ki samu time kije da kanki kiji me yasa ita bata nemanku, a matsayinta na mahaifiyarku." Kallon juna suka yi……

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA BIYU*

{72}

Kallon juna suke yi kowa yana kokowa da abinda yake ji a cikin zuciyarshi, a wannan lokacin kowanensu ji yake yi kamar ya fallasa asirin dake cikin zukatansu ko sun samu suji sauƙi sai dai kowanne da tunanin da yake yi dake taka musu burki wajen amayar da abinda suke ɗauke dashi. Zainab ce ta fara kawar da kanta tana sakin ajiyar zuciya, murya ƙasa-ƙasa tace "Taya za'a yi mu nemeta Ya Baqeer bayan tunda ta tafi bata ƙara waiwayarmu ba tayi aure ta haifi wasu ƴaƴan da take so mu ta manta damu." Murmushi Baqeer yayi yace "Zainab kenan naga alama baki san wacece mahaifiya ba baki san girmanta ba shi yasa kike faɗar haka, idan ita bata nemeku ba kenan ku ba zaku taɓa nemeta ba? Bayan haka kuma kun ji ta bakinta ne kun ji dalilinta na ƙin nemanku da zaku yanke mata hukunci? Haka nan uwa ba zata saki ƴaƴanta ta watsar dasu ba sai da wani babban dalili don haka dolenku ne ku bata dama ta faɗa muku nata side of the story ba wai ku ɗauki fushi don tunda ta tafi bata ƙara waiwayarku ba. Komai na rayuwa ɗan uzuri ne, idan ta rabu daku ku sai ku nemeta kuje inda take tunda itama tana da hakki a kanku, bayan haka ma baku san a wane hali take ciki ba watakila akwai dalilinta na rashin waiwayarku da bata yi ba tun bayan barinta gidanku." Jikinta ne yayi sanyi da taji abinda yace, cikin ranta dai ta ƙudurce In Sha Allah zata yi amfani da shawarar shi tabbas lokaci yayi da zasu nemi mahaifiyarsu wacce rabonsu da ita tun suna ƙanana don ita bata jin zata ganeta ma saboda ta bar gidansu lokacin bata fi shekara huɗu zuwa biyar ba. Har ta koma gida tana auna abinda Baqeer yace a cikin ranta, tana ajiye motarta ɗakin Kabir ta wuce. Murɗa handle ɗin ƙofar tayi ga mamakinta sai ta sameta a buɗe saɓanin kwanaki da sai tayi knocking kafin ya taso ya buɗe. Samunshi tayi yana kwance akan gadon shi yana danne-danne a waya. Zama tayi a bakin gadon tana kallonshi, ita sai taga kamar daga jiya zuwa yau ma har ya ɗan cicciko daga ramar da yayi ta tashin hankalin daya samu kanshi a ciki kwana biyu. Tashi yayi ya zauna yace mata "Kwanan nan fa kin fara damuna bini-bini sai ki shigo mini ɗaki kamar wacce kika bani ajiya na cinye ban biyaki ba." Hararar shi tayi tace "Au haka ma zaka ce? Yanzu daka samu ka fita daga waccen matsalar shine har kake da bakin yi mini wulaƙanci ko, ai shikenan ni na nuna na damu da kai amma kayi da ƴa." Dariya yasa yace "Allah ke ɗin ce kin fiye damu." Tashi tayi tace "Ai dai ka tsaya kaji abinda ya shigo dani kafin ka fara wulaƙancin ka daga yau kuma bazan ƙara zuwa inda kake ba." Da sauri ya riƙo hannunta ganin kamar tayi fushi zata bar ɗakin yace "kefa daɗina dake baki san wasa ba sam, dawo ki zauna ni wasa nake yi miki." Komawa tayi ta zauna ta zuba ido tana kallonshi kamar mai tunanin ta yadda zata fara faɗa mishi shawarar data yanke, sai da taga kamar ya ƙosa da jiranta sannan tace "Ya Kabir nace baka ganin ya kamata ace mun nemi Ummi kuwa? Tunda ta bar gidan nan fa bamu ƙara sakata a idanunmu ba sai ƴan uwanta dake zuwa lokaci bayan lokaci suma ba'a taɓa katarin sun zo sun samemu a gida ba." Wani irin kallo yayi mata yace "Wace Ummin kenan?" Itama kallonshi tayi tace "Har Ummi nawa garemu, of course Ummi mahaifiyar mu nake magana akai." A fusace ya tashi yace "Amma dai baki da hankali ko, matar da tunda ta watsar damu muna yara bata ƙara waiwayarmu ba tsawon wannan lokacin shine kike cewa muje wajenta, to muje wajenta muyi mata me bayan mun girma mun mallaki hankalin kanmu? Tunda ta nuna bata da buƙatar mu a rayuwarta ba shikenan ba muma bama buƙatarta a rayuwarmu sai kowa yayi rayuwarshi yadda yake so babu ruwan wani da wani." "Ya Kabir mahaifiyarmu ce fa." Katseta yayi yace "Mahaifiyar tamu, ki fada mini abu guda ɗaya da tayi mana da zai yi nuni da ita ce ta haifemu? Tunda ta bar gidan nan bata ƙara waiwayarmu taga a wane hali muke rayuwa ba, ko halin dana tsinci kaina a ciki ai laifinta ne idan da bata watsar damu tayi tafiyarta ba duk haka da bata faru ba." Da mamaki Zainab ke kallonshi tace "Ya Kabir wane irin laifinta kuma? Ita tace Nabila ta ƙala maka sharri saboda Allah." "Idan ma bata ce ba ai dai rashin zamanta damu ne ya janyo don haka ni babu inda zan je kema da zan baki shawara ki ɗauka da nace kada kije don bana jin ko ganinki tayi zata tuna dake don alamu sun nuna ta daɗe da mantawa da ta haifi wasu ƴaƴa data fita ta bari." Tashi Zainab tayi tace "Ni dai gaskiya to zan je don ban san dalilinta na ƙin waiwayarmu ba tun bayan barinta gidan nan zan je naji ta bakinta kafin na yanke mata hukunci, bayan haka kuma ita ɗin mahaifiyarmu ce da bamu isa mu canjata ba duk kuwa da gatan da wata zata nuna mana ba zai sa ta amsa sunan mahaifiyarmu ba." Daga haka tai hanyar fita daga ɗakin har taje bakin ƙofa sai kuma ta tsaya tace "Kunyi magana da Mumy?" tana jin lallai zata je taga mahaifiyarta don sai a yanzu tasan tayi wauta da duk waɗannan shekarun bata taɓa tunanin ya kamata taje inda take taga a wane hali take ciki ba, ba zata iya tuna abinda yasa ta fita ta bar gidansu ba amma tana iya tuna wasu daga cikin moments ɗin su masu daɗi da tsayawa a rai. Takan tuna lokutan da take fita dasu yawon shaƙatawa a motarta ita da Kabir suyi ta faɗa akan wanda zai zauna a gaba, wasu lokutan sai ta hanasu zama gaba ɗaya tace duk su koma baya babu mai zana a kusa da ita tunda faɗa suke yi. Tana shiga ɗakinta ta hau haɗa kaya a cikin akwati don ta riga ta sawa ranta zuwa Ɗambatta a gobe bata jin akwai wani abu da zai hanata zuwa. Sai da ta gama haɗa kayan tsaf sannan ta ɗauki waya ta kira Daddy don tunda ya fita ya bar gidan jiya bai ƙara waiwayarshi ba. Bata daɗe tana ringing ba ya ɗauka, a shagwaɓe tace"Daddy ina ka tafi tun jiya ban ganka ba?" Da kulawa yace "Raina ke ɓaci idan ina cikin gidan Zainab shi yasa na kauce har sai na huce don kada na yanke hukunci a cikin fushi daga baya nazo ina dana sani." Ɗaga kanta tayi kamar yana ganinta tace "haka ne kuma, Daddy dama zan faɗa maka ne gobe ina so zan je Ɗambatta na kwana biyu." Shiru yayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin yace "Ɗambatta kuma? Lafiya dai ko?" "Lafiya lau Daddy kawai dai ina so naje ne don Allah kada kace a'a," tayi maganar cike da shagwaɓa. Samun kanshi yayi da kasa musa mata duk da ba son zuwanta Ɗambattan yake yi ba bare da mutanen suka nuna mishi ba mutanen kirki bane su amma ba zai yiwu ya cigaba da hanasu zuwa wurin dangin mahaifiyarsu ko gunta ba don haka yace mata sai ta dawo amma kada ta daɗe. Da murnarta ta ajiye wayar har da ɗan tsallenta don bata taɓa tunanin Daddy zai amsa mata da wurwurii haka ba ta ɗauka hanawa zai yi kamar yadda ya sha yi a baya idan ta nuna tana son zuwa wurin mahaifiyarta. Ƙara ɗaukar wayar tayi ta turawa Baqeer saƙo. "In Sha Allah gobe zan je Ɗambatta, nagode da tunatarwa." Ajiye wayar tayi ta tashi tana ƙara duba ɗakin ko da akwai abinda take buƙatar ɗauka kada ta manta. Mummy ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, kallo ɗaya Zeey tayi mata ta juya ta cigaba da abinda take yi. Jikinta ne yayi sanyi ganin irin kallon da Zeey tayi mata. Ƙarasa shigowa tayi cikin ɗakin ta zauna a bakin gado tana bin yadda Zeey ta barbaza kaya a cikin ɗakin da kallo. "Wani wuri zaki je ne auta?" Ta tambayeta tana ƙara bin ɗakin da kallo. Ɗan taɓe baki tayi tace "Um," kawai ta cigaba da abinda take yi. Kallon Zainab tayi tace "kema kina jin haushina kamar Daddy ko? Shi yasa kika daina kulani." Wani irin kallo Zainab tayi mata da itama bata san tayi ba har ta buɗe baki zata bata amsa sai kuma taji ba zata iya ba kawai tayi shiru, har yanzu ta kasa gane dalilin Mummy na ɓoye musu Nabila ƴarta ce bayan duk wannan tsawon lokacin da aka ɗauka, to da ace haka bata faru ba baza ta taɓa sanar musu ba kenan ko me? "Ki bani dama nayi miki bayani," katseta Zeey tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tace "Bani zaki yiwa bayani ba Mummy don ba zamana kike yi ba a gidan nan mijinki ya dace ki yiwa bayani bani ba." Daga haka bata ƙara bi takan Mummy ba har ta gaji da zaman ɗakin ganin da tayi Zeey ba zata kulata ba yasa ta tashi jiki a sanyaye ta bar ɗakin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull