Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 53

Baqeer complete - Chapter 53

Baqeer complete Chapter 53: Baqeer complete Chapter 53. Wani irin kallo Daddy yake yi mata da yake sake ruɗa mata ciki take jin kamar ta saki gudawa a…

3,299 words

Wani irin kallo Daddy yake yi mata da yake sake ruɗa mata ciki take jin kamar ta saki gudawa a wando. Ƙasa-ƙasa yayi magana cikin wata irin masifaffiyar murya data ƙara ruɗar da Nabila yace "Cikin ƙarya kika yi shine kika lanƙayawa ɗana kika yi breaking trust ɗin dake tsakaninmu don kiyi tarnishing image ɗina." Girgiza kai take yi ta kasa magana saboda tsabar tsoron da ya kamata, ita wa ya aiketa ne ma yin wannan kasassaɓar gashi allura tana nema ta tono garma. Zama Daddy yayi akan kujera ranshi idan yayi dubu ya ɓaci, ya rasa wane irin mataki ma ya kamata ya ɗauka. Tsakanin jiya zuwa yau hankalin shi a tashe yake fata kawai yake yi ya kashe wannan matsalar data kunno kai cikin gidanshi ba tare da ƴan adawa sun ji ba su samu abun kawo mishi suka amma ashe wai duk wannan tashin hankalin daya shiga ƙarya ce kawai babu wani ciki a jikin yarinyar nan, to ita kuwa ribar me zata ci da tayi hakan ta ɗaga musu hankali gaba ɗaya. Ita dai Nabila na zaune a gefe dafe da kunci don har yanzu tana jin zafin marin da Daddy yayi mata tana sharɓar kuka. A cikin haka ne Dr ɗin ya shigo da nurse ta ɗebi jinin Nabila yace ta kai lab a gwada mishi yana so yaji if she's pregnant don in dai har akwai ciki to blood test yana nunawa komai ƙanƙantar shi kuwa. Zama yayi akan kujerarshi ya dubi Daddy yace "kayi haƙuri Yallaɓai bari a kawo result ɗin mu gani idan har akwai cikin blood test ɗin zai nuna, kasan test ɗin ne wani lokacin yana bada false positive to watakila itama irin shi ta gani tayi zaton akwai cikin amma ina tantamar cikin nan don scan ɗin da aka yi ya nuna mahaifarta bata taɓa ɗaukar ciki ba." Tsaki Daddy yayi yace "Ai tunda kace babu cikin na yarda da kai Dr ita dai tasan dalilinta na yin ƙaryar cikin da idan abokan hamayya suka ji zasu iya amfani dashi suyi tarnishing image ɗina," ya wurgawa Nabila wata uwar harara, babu shiri ta sunkuyar da kanta ƙasa idanunta na zubar da hawaye. Suna zaune a wurin nurse ɗin ta dawo da result ɗin test ɗin da aka yi, karɓa Dr yayi ya duba sannan ya kalli Daddy yace "Kamar yadda na faɗa maka ne Yallaɓai babu ciki a tare da ita watakila dai false positive ta gani a wancan test ɗin da tayi a gida shi yasa tayi tunanin akwai cikin, Allah ya kiyaye gaba." "Ameen Dr nagode," Daddy yace bayan ya miƙa mishi hannu sun yi musabaha. "Sai ki tashi mu tafi ai, mutuniyar banza da wofi," ya daka mata tsawa sai dai cikin ranshi yana ji ya samu nutsuwar da tunda maganar cikin nan ta fito bai samu ba tun ba da tace Kabir ne ke da alhakin cikin ba, ko baccin kirki bai samu yayi ba jiya don yana ganin kamar duk wani motsin su a idon abokan adawa suke yin shi zai iya jin maganar ta fita ta inda bai taɓa zato ko tsammani ba. Har suka je gida Nabila na sharar hawaye, bata taɓa tunanin asirinta zai tonu da wurwuri haka ba, ta ɗauka Daddy zai yi maganar aure ne a tsakaninta da Kabir don a taru a rufawa juna asiri ashe shi a wajenshi ba haka bane bata kai matsayin da zai aura mata ɗanshi ba sai m wani ɓoyayyen sirrinsu daya bankaɗa.

Suna zuwa gida Daddy ya fice daga motar a fusace ya shiga cikin gida, tun daga parlourn ƙasa yake ƙwalawa Mummy kira "Halima, Halima." Tana jin irin kiran da yake yi mata sai da gabanta ya yanke ya faɗi, ita yanzu gaba ɗaya Daddy ya zame mata abun tsoro daga taji muryarshi take shiga tsananin tashin hankali. Fitowa tayi jiki a sanyaye don bata san kiran me yake yi mata ba. Wani banzan kallo Daddy ya watsa mata yace "Dama kun haɗa baki ne da ƴarki (yadda ya ambaci kalmar ƴarki a kamar wanda yaga wani abun ƙyama) tayi ƙaryar ciki don kuyi tarnishing image ɗina ku kuma yi breaking trust ɗin dake tsakanina da ɗana?" Da sauri Zainab ta kalli Kabir don tunda Daddy ya fara yiwa Mummy ƙiran mafarauta duk suka fito daga ɗakunansu. "Ƙaryar ciki kuma?" Zeey tayi maganar ƙasa-ƙasa yadda babu mai iya jin ta. Cikin rawar murya Mummy tace "ƙaryar ciki kuma Senate? Kana nufin Nabila ba ciki ne da ita ba?" Sai da ya harareta yace "Koma menene ai da saninki yake faruwa tunda dai Nabila bata isa tayi abinda tayi ba idan har ba sakata aka yi ba." "Wallahi Senate babu ruwana," Mummy tayi saurin tarar numfashin shi. Nuna Nabila dake rakuɓe daga bakin ƙofa don ta kasa ƙarasa shigowa ciki ma yayi yace "to gata nan ashe ƙarya take yi babu wani ciki da take dashi, anyi mata scanninga ba'a ga komai ba har blood test aka yi duk sun nuna bata ɗauke da ciki." Da ƙarfi Kabir yace "I knew it, ni dama nasan babu wani abu daya shiga tsakanina dake don bazan iya tuna lokacin da abu makamancin wannan ya shiga tsakaninmu ba" ya ɗaga hannun shi sama in a fist. Dukkansu suka kalleshi, Daddy yace "Kasan da haka amma kayi shiru baka yi magana ba ka bari suke tayi mana yawo da hankali." Takowa yayi ya sauko daga matattakalar bene, sai da ya shigo parlourn sosai sannan yace "Ka bani damar da zan kare kaina ne? Ina ce kafi yarda da ita akan ni ɗanka na cikinka daka haifa don haka ka yarda da maganarta ba tare da kaji ta bakina ba kayi jumping into conclusion sai yanzu ne zaka zo kana cewa ban faɗa maka ba, to me zan faɗa maka bayan tun farko ka aminta da abinda ta faɗa maka?" Shiru Daddy yayi yana jin wani abu mai kama da dana sani na lulluɓeshi. Wani irin kallo Kabir ya jefawa Nabila yace "Kin sani tun farko ban taɓa nuna ina sonki ba, lokacin da kika zo mini da maganar soyayya na faɗa miki ba zai yiwu ba saboda ke ƙanwar Mummy ce ina yi miki kallon ƙanwar mahaifiyata saboda kallon da nake yiwa Mummy kenan don haka bazan iya aurenki ba, anyi haka ko ba'a yi ba." Bai jira jin ta amsa ba ya cigaba da cewa "Duk da haka baki haƙura ba kike biyoni har ɗakina duk wata ƴar dama da kika samu sai dai na ganki a cikin ɗakina har ta kai ga bana son zama a cikin gidan nan saboda takurar da kika yi mini duk da haka baki saduda ba daga baya ma sai kika ɓullo mini da wani abu mai girma duk da na nuna miki bazan iya ba baki haƙura ba sai da kika san yadda kika yi kika rinjayeni har na fara biye miki amma kin sani na sani wani abu makamancin wancan abun bai taɓa shiga tsakanina dake ba, ko a ranar da kika tuhumeni da yi miki fyaɗe ke kika kawo kanki har ɗakina kika yi ƙoƙarin tilasta ni akan sai na kusanceki naƙi a haka bacci ya ɗaukeni kawai sai farkawa nayi kika ce wai na gwada miki ƙarfi, duk yadda nayi ƙoƙarin son na tuna na kasa tunawa saboda babu abinda ya shiga tsakanina dake." Wani irin zazzafan huci ya sauke yace "Kije na barki da Allah ƙazafin da kika yi mini Nabila shi zai bi mini hakkina." Daga haka ya juya ya koma ɗakinsji yana share ƙwallar daya kasa tantance ta farin cikin jin cewa wani abu bai gifta tsakaninshi da Nabila bane ko kuwa ta takaicin sharrin data ƙulla mishi ne. Bin shi Zainab tayi sai ta sameshi zaune akan sofa ya dafe kanshi da hannayenshi yana sauke ajiyar zuciya. Zama tayi a kusa dashi ta dafa bayanshi tace "Kayi haƙuri Ya Kabir nasan akwai ciwo ayi maka sharri amma sai ka godewa Allah daya bayyana gaskiya tun ba'a je ko ina ba asirinta ya tonu, ni gaba ɗaya kwakwalwata ta kasa ɗaukan abubuwan dake faruwa, na rasa gane komai." "Hmm..." Kawai yace yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarshi, Nabila ta cutar dashi don a cikin ƴan kwanakin nan data taso shi a gaba da tashin hankali ko baccin kirki baya iya yi daya samu bacci ya ɗaukeshi kamar wanda ake yiwa raɗa sai zancen cikin nan ya faɗo mishi a cikin ranshi shikenan kuma sai ya nemi baccin ya rasa haka zai yi ta juyi har safiya tayi yana saƙe-saƙen abinda ya kamata yayi. Zama suka yi shiru kowa na saƙe-saƙe a cikin rai, nisawa Zeey tayi tace "Ya Kabir kasan me yafi ɗaure min kai kuwa? Yadda Mummy bata taɓa nunawa Nabila ƴarta bace sai ma nesanta kanta da take yi da ita bayan mu kuma ta riƙemu kamar ƴaƴanta amma ga tata ƴar ta watsar da ita a gefe, ko me yasa tayi hakan abun yana ɗaure mini kai." Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta sai dai bai yi magana ba, shima sai yanzu yake tunanin to me yasa Mummyn tayi haka? Shi yasan da ace ta fito ta faɗawa Daddy zai riƙe mata ƴarta kamar shi ya haifeta sai ta zaɓi data ɓoye tace ƙanwarta ce alhalin ƴarta ce, ko ribar ne zata ci data yi hakan oho.

***** Mayar da kayan data fara zubawa cikin akwati tayi a wardrobe ta shirya, komawa tayi ta zauna akan tabarma tana jan carbi sai dai lokaci bayan lokaci tana tuna tijarara da Badaru yayi mata, kome yasa ya hanata tafiya kuma bayan shi da kanshi yace ta bar mishi gidanshi. Wayarta ta janyo ta kira Baqeer, lokacin da kiran ya shiga wayarshi yankan ɗinki yake yiwa Tanimu don shi har yanzu hannunshi bai gama faɗawa ba ya dai iya taka keke sosai ya haɗa kaya amma yanakwar na ɗan bashi wahala. Ajiye scissors ɗin hannunshi yayi akan kayan da yake yankawa ya ɗauki wayar, yana ganin sunan Umma ya saki wani murmushi. Da sallama ya amsa wayar sai bayan ta amsa sallamar da yayi mata sannan suka gaisa. Tambayarshi tayi yadda ake ciki da shagon da yake son ya buɗe ganin har ya kusa kammala makarantar koyon ɗinkin. Nutsuwa yayi yace "Ai na faɗa miki mun samu shagon har an biya rabin kuɗin hayar, In Sha Allah zuwa ƙarshen watan nan akwai waɗanda na yiwa sketches zasu biyani da kuɗaɗen da wasu dana ajiye a banki nake so na zuba kekunan, a yanzu dai ni da Tanimu ne zamu fara zama a wurin sai munga yadda kasuwar ke tafiya kafin mu nemi wasu ma'aikatan kuma." Tana sauraren shi har ya gama yi mata bayani sai gyaɗa kai take yi cikin nuna gamsuwa da abinda yake faɗa duk kuwa da ba ganinta yake yi ba. "Allah ya taimakeka ya bada sa'a ya saka maka albarka a cikin kasuwancin da zaka fara. Allah ya kareka daga sharrin maƙiya da mahassada ya kawar da dukkanin wasu abun ƙi ya yalwata arziƙinka." "Ameen Umma," kafin yake cewa yana jin wasu ƙwallar tausayinta sun cicciko mishi a ido. Ko ƴaƴa nawa ne irinshi da suka yi dacen samun uwa ta gari irin Umma mai mayar da damuwar ƴaƴanta damuwarta, mai sayar da farin cikinta don ƴaƴanta suyi dariya, mai yawan kyautayi da tausayin ƴaƴanta wacce cigaban ƴaƴanta shine nata, gaskiya basu da yawa don kafin a samu irin Umma a cikin al'umma sai an daɗe. Har suka yi sallama bata daina yi mishi addu'a ba abinda yake ƙara mishi ƙwarin gwiwa da karsashi akan son ya ƙara dagewa wajen ganin ya cimma burinshi ko don ya saka farin ciki a cikin zuciyar Umma. Tun lokacin da ya faɗa mata ƙudirinshi akan sana'ar ɗinki da yake so ya fara ta duƙufa wajen yi mishi addu'a babu dare babu rana tana roƙa mishi alherin Allah akan abinda yasa a gaba, ita a yanzu bata da wani buri data sanya a gaba sai fatan ganin cigaban Baqeer, tana so taga ya zama wani abu a rayuwa shi yasa take jure duk wani wulaƙanci da take gani a cikin gidan har ranar da Allah zai iyakance musu wannan zama ta tafi ta barwa Badaru gidanshi din daga ranar daya kori Baqeer daga cikin gidan taji a ranta itama bata da muhalli a cikin shi...

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA ƊAYA*

{71}

Mummy ce ta ja Nabila ɗaki ganin su kaɗai suka rage a cikin falon, suna shiga tasa key ta rufe ɗakin zuciyarta na wani irin zafi, ta kasa waigowa daga jikin ƙofar, Nabila kam zama tayi a ƙasan ɗakin tana share ƙwalla kafin tace "Mummy ni dai don Allah ko ma menene kiyi amma ki sa a aura mun Kabir….." Wani irin waigowa tayi ta bita da mugun kallo kafin tace "Kabir? Ke yanzu kina ganin ko numfashin mutuwa kike yi Senate zai aura miki shi? Sau nawa ina ce miki ki bari? Ko kina tunanin ni ban san me nake yi bane?" Kai kawai ta sunkuyar ƙasa tana jin tsanar kowa na kamata, Mummy ce ta ɗan sauke ajiyar zuciya kafin tace "Ya aka yi kika san Inna ba ita ta haifeki ba?" A hankali ta ɗago ido kafin ta kauda kai gefe tana kallon wajen gado ba tare da tace komai ba, Mummy ta sake cewa "Ya aka yi kika sani? Don kaf garin nan babu wanda yasan sirrin nan, kuma saboda wannan sirrin tunda muka baro Nijer bamu sake komawa ba, ba neman ƴan uwan mu muka yi ba bare su san inda muka koma suzo, to ya aka yi kika ji?" Yanzu kam kanta ta dawo dashi wurin Mummy, ɗan nazari Mummy tayi don da Nabila na bala'in jin maganarta, sannan babu ruwanta kwana a gidan ma da ƙyar Zee da Inna ke sakata zuwa kafin shekaru huɗu baya da ta fara canza halaye, a gaban mutane ita mai tarbiyya ce amma in su biyu ne sai ta fara mata maganar raini. Da sauri ta kalleta tace "Ba dai sanda Inna tayi mini faɗa akan karatunki ba? Sanda Zeey bata daɗe da fara karatu a ƙasar waje ba akan insa Senate ya biya miki kema ki tafi?" Kanta ta sunkuyar. Mummy ji take yi kamar ta rufeta da duka, hakan yasa itama ta tsugunna a wurin da Nabilan take zauna ta sa hannu ta ɗago kafaɗarta ta riƙe da hannayenta biyu tana jijjigata tace "Yanzu hankalinki ya kwanta kin ɗauki fansar abinda kike so?" Wasu hawaye ne suka zubo mata, Mummy ta sake matsa kafaɗarta tace "Kin san baƙin cikin da kike sakani a ciki kuwa? Kin san halin da nake shiga a baya saboda ke? Amma na daure na nemar miki gata, ko kina tunanin da ban auri senate ba zaki yi school ɗin da kika yi? Zaki zauna gidan da kuke yanzu? Zaki samu mota da gatan da kike dashi yanzu?" Takaicin Nabila take ji wanda ji take yi baƙin cikinta duk ya gama nuƙurƙusarta. Sakinta tayi kawai ta miƙe tsaye ta fara ciro kayan Nabila tana zubosu ƙasa daga cikin akwati, Nabila da sauri ta sa gwiwoyinta a ƙasa tace "Mummy na tuba, na tuba wallahi kawai kishi nake yi yadda naga kina son su Zainab amma sam ba so nayi a tozartaki ba, sannan wallahi bansan abinda ya faru zai koma haka ba, don Allah ki yafe min." Wani irin ɓacin rai Mummy ke ji sai data watso kayan duka sannan ta ce "Tashi ki haɗa kayanki ki bar mini gida, kin ji na faɗa miki." Tana kaiwa nan ta fito daga ɗakin idanunta sunyi jaaa saboda ɓacin rai, abinda ta gina shekara da shekaru yarinyar nan ta lalata mata shi lokaci ɗaya yanzu ya zata yi, ta rasa wani tunanin zata yi kawai idanunta suka hango Zeey da Kabir sun fito daga ɗakin shi, baya tayi kawai sai ji tayi ta faɗi, da gudu Zeey ta taho inda take ta ɗagota tana tambayarta menene? Mummy a hankali take kallonta tana fitar da numfashi sama sama tana cewa "Jiri kawai nake ji, Auta abubuwan da ke faruwa ƙwaƙwalwata da zuciyata sun kasa ɗaukansu." Kama mata tayi ta kaita ɗaki har Mummy ta riko hannunta, zare hannunta tayi daga cikin na Mummy ba tare da ta amsa mata ba sannan ta fito daga ɗakin. Kabir na tsaye inda suka barshi kai kawai ya girgiza ya koma ɗakin shi, Zeey ma ɗakinta tayi sai dai da yake ɗakinta kusa dana Nabila ne tana jiyo kukanta daga ciki, kuka take yi sosai wanda yasa Zeey take jin komai ba daɗi ita dai sam ba zata yafe mata ba sannan bata son ganinta a wannan lokacin, sai dai kukan na ƙara ɗaga mata hankali ga magriba ta kawo kai, hakan yasa ba zata iya fita ba, waya ta ɗauka ta kunna karatun Qur'ani kawai ta haɗe kanta da gwiwarta wuri ɗaya, ta rasa wani tunanin zata yi, sam yanzu tsoron mutane take.

***** Nabila kam ta dinga buɗe makogaro tana kuka saboda Zeey taji sai dai ganin tayi kusan awa biyu tana kukan ba tare da tazo ba yasa ta daina don ji tayi har muryarta na neman dusashewa, haka ta kwashe kayanta ta dinga leƙawa sai dai gidan babu kowa kamar anyi mutuwa, su kansu masu aiki da alama sun fahimci akwai abinda ke faruwa a gidan don suma aikin gidan a hankali suke yi, ɗakin Kabir taje sai dai ta jishi a kulle haka taja akwatin ta fita idanuwanta duk sun yi ƙanƙanta. Motarta ta shiga ta bar gidan tana jin komai yayi mata zafi, takaicin abinda ta aikata ya isheta. Gida ta wuce kai tsaye, tayi parking sannan ta janyo manyan akwatinanta guda biyu tayi ciki, tana tafe kamar zata faɗi saboda wata irin yunwa da take ji, don kaf ɗin su tun breakfast babu wanda ya ƙara cin abinci. A zaune taga Inna tayi shiru da alama tunani take yi, har ta shiga da akwatinan bata tanka mata ba, ganin haka yasa ta dawo tace "Inna." Kallonta tayi cike da ɓacin rai kafin tace "Yanzu hankalinki ya kwanta? Kin ruguza farin cikin mahaifiyarki?" Zama tayi a ƙasa kusa da Inna tana maida ƙwallarta tace "To ni menene nawa Inna? Ta tsaneni ba tare da nayi mata laifin komai ba, ko abinci take ci idan nazo wuri haƙura take yi sannan daga baya naji wai bama Yayata bace mahaifiyata ce? Sannan ni da nake ƴarta bata damu dani ba sai su Zainab? Kina ganin yadda take yi musu bata iya ɓoye son da take yi musu." Cikin faɗa Inna tace "Wannan dalilin bai kai kiyi abinda kika aikata ba, tunda Halima ta kira ni a kan cikin ƙaryane, ke kin san rayuwar data shiga a baya saboda cikin ki? Kin san yadda tasha wahala? Ko kuwa kin san abubuwan da tayi saboda ta canza tabon dake jikinta saboda nan gaba ke kar kisha irin wahalar data sha?" Nabila ɗagowa tayi sai taji kuka ya ƙwace mata tace "Inna na tuba, don Allah ku yafe min, kishin su Zainab ne da son Kabir ya sani aikata hakan." Inna ba tace mata komai ba ta miƙe tayi ɗaki, nan ta ƙara durƙushewa tana rera wani kukan na tsananin dana sani.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull