Baqeer complete - Chapter 52
Baqeer complete Chapter 52: Baqeer complete Chapter 52. ***** Badaru na zaune a kasuwa wani abokin shi da suke harkar kasuwanci tare ya kawo mishi ziyara.…
3,204 words
***** Badaru na zaune a kasuwa wani abokin shi da suke harkar kasuwanci tare ya kawo mishi ziyara. Bayan sun gama gaisawa yace "Mallam Badaru ashe yaronka ya fara gina filinshi dake unguwarmu babu labari? Nace to Badaru mantawa yayi bai faɗa min za'a fara ginin ba bayan muna haɗuwa kusan kullum a kasuwa, ai irin wannan sai ka sanar dani yadda zan saka muku ido sosai a harkar ginin ba wai naga an fara ba bayan tare dani aka yi duk wasu shige da fice har Allah yasa aka sayi filin." Tunda ya fara magana Badaru yake kallonshi fuska ƙunshe da mamakin jin cewa wai an fara gini a filin Baqeer. To ta yaya ma za'a fara gini a wajen ba tare da an sanar dashi ba? Kada dai ace Kamalu sayar da filin nan yayi shine har aka fara gini bai sani ba. Ai da yin wannan tunanin ya miƙe zumbur ya zari makullin motarshi ya fice daga shagon ba tare daya tsaya yayi wa abokin nashi bayani ba duk kiran da yake ƙwala mishi kuwa bai sa ya tsaya ba sai ma sauri da yake ta faman zambaɗawa yana fatan yaje gida ya iske Kamalu yau babu me rabasu sai dai Allah. Kamar wanda zai tashi sama haka ya kwaso mota a guje, hukuncin Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya. Ko tsayawa ya daidata parking motar bai yi ba ya fita da sauri har yana cin tuntuɓe da wani dutse Allah dai ya kiyaye bai faɗi ba. Yana shiga cikin gidan da Abu ya fara cin karo ai kuwa ya kai mata damƙa yace "ina Kamalu yake? Ina yake nake tambayarki?" Jiki na rawa don ta tsorata da yanayin data ganshi a ciki fatanta dai Allah yasa ba shagonshi ya ƙara zuwa ya ɗebo mishi wasu kayan ba. "Mallam lafiya?" Wata uwar harara ya zabga mata yace "ina fa lafiya ɗan iskan yaron nan ya kassarani yaje ya sayar da filin nan har an fara gini a wurin." "Kamalun ne ya sayar maka da fili Mallam? To yayi me da kuɗin?" "Oho nima na sani zai wuce yawon iskancin shi zai tafi da kuɗin." "Gaskiya Mallam ka daina cewa shi ya sace maka fili tunda dai ba ganinshi kayi ya ɗauka ba, ko kuwa wani ya gaya maka ya ganshi lokacin da ya ɗauki takardun filin?" Tsaki yayi yace "Har sai wani ya faɗa mini, ki gaya mini duk gidan nan akwai wani ɗa daya gagara ne bayan shi? To wallahi ki faɗan gaskiya ko na tsine mai." Shiru tayi dan mamakinshi ya hanata magana, sai cewa yayi "Kin gani kema kin san gaskiya." Umma ce ta fito daga ɗakinta jin abu na neman kaiwa ga tsinuwa yasa ta fito tace "Takardun fili dai ni na ɗauka na kaiwa mai filin ya sayar yayi amfani da kuɗin." "Ke kika sace mini takardun filin fa kika ce Fatima?" Girgiza kai tayi tace " Haram, ni ban sace maka komai ba takardar filin Baqeer na ɗauka don nasan ko nace maka ka bani ba bayarwa zaka yi ba kuma mai filin yana da buƙatar kayanshi shi yasa ni kuma na ɗauka na kai mishi." Baki buɗe yake kallonta don ya rasa wane mataki ya kamata ya ɗauka a kanta. "Habawa ashe shiyasa kike da kuɗi? Kudin sata kike ce to wallahi Fatima ki karɓo min takardar filina in har ba barauniya kike san zama ba, idan kuma ba haka ba wallahi zan yi matuƙar saɓa miki akan takardun nan zaki iya bar min gidana." Murmushi tayi tace "Filinka ko na Baqeer kuma idan kace na bar maka gidanka sai me tunda ka iya korar ɗan cikinka bayan ka gama cin moruyarshi ma bare ni da ka sameni da girmana," daga haka tayi shigewarta ɗaki ta barshi anan da sakakken baki.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA TARA*
{69}
Abu bata san sanda dariya ta ƙwace mata ba, ganin wani mugun kallo da Badaru ya watsa mata yasa tayi saurin cewa "Malam to yaya? Kamalu dai sai ka nemi yafiyarshi watakila ma atamfofin su ke sata ba'a sani ba." Ai kuwa tana kaiwa nan ya hayayyaƙo mata don dama a wuya yake saboda kalaman Fatima, a fusace yace "Gurgun ne kike nufi zai je kasuwa yayi sata? Ko kuwa kina son cemin shi yaron shagon nawa bai san Kamalu ba? In Baqeer ɓarawo ne shima Kamalun ɓarawo ne aikin banza ka haifi yara taron ɓarayi a gida ni dai kam banji daɗin haihuwa ba." Jin yanda ya rufeta da masifa yasa tayi sum-sum ta shige ɗaki, maimakon ya koma ciki sai ya nufi ɗakin Fatima yana masifa "Kina ina munafukar banza da wofi, ni Fatima har kin yi idon da zaki yi mini sata? Ni? Ni?" Tana daga cikin ɗaki ko motsi bata yi ba yi tayi ma kamar bata san me yake yi ba, ai kuwa ya ƙaraso cikin dakin yana hayagaga yana cewa "Eh lallai idanunki sun isa yanka, to tashi maza ki bar mini gida na." Maimakon ma ta bashi amsa gani yayi ta janyo hijabi ta saka ta jawo akwatin ta a ƙasan gadonta na ƙarfe tana neman watsa kayanta ciki, wani tunani ne yazo mishi in har ta tafi shikenan bashi ba kuɗin filin nan don ya tabbatar kuɗin na hannunta ko Baqeer amma ko yaya in ya ajiye Fatima ai dai ko banza zai iya ƙwace kuɗin shi a hankali, wani kallo yayi mata kafin yace "Kina sa ƙafa kika bar gidan nan Allah ya isa." Da mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a idanuwanta ta kalleshi, idanuwanshi sun yi jaa saboda tsabar masifa ya sake yi mata wani muzurai don ta ƙara shakkar shi sannan ya fita, kai ta girgiza don baƙin ciki ya isheta taso ta tarkata ta tafi duk da itama bata son tafiya har sai Baqeer ya zama abinda Badaru da kanshi zai yi ƙwallar da na sani, amma da zaran ta tattara ta koma wurin Dada tasan neman faɗanshi kaɗai sai ya sa ya bita har can, sannan wannan kishiyoyin nata masu gulma tasan bazasu barta ba haka zasu yi ta sawa ana musu leƙen asiri, amma da tuni itama tayi yaji don ba abinda yake zaune da ita a gidan. Badaru kam ɓacin ran da yake ciki ne yasa ya fito waje, yana ƙoƙarin fita Kamalu na shigowa, daga ɗan gefe kawai ya raɓa yana neman wucewa ba tare da ya yiwa Badaru magana ba, kamar ya shaƙo wuyanshi ya kifa mai mari yake ji amma baƙin ciki ya hanashi gashi yana tunanin haukar yaron nan kar yasa ya ƙara bigeshi wanda ya tabbatar a rashin kanshi zai iya aikatawa, shi dai kam bai yi sa'ar yara maza ba, duk yanda yake kulafucinsu gashinan duk sun zo babu wanda yayi mishi rana. Tafiya kawai yake yi don bai masan inda yake saks ƙafarshi ba, yanzu filin nashi da gaske Fatima ta sace? Mai zai yi mata da zai ƙuntata mata? Don wallahi bataci bulus ba, dama ɗanta ya cireshi daga sahun yaranshi don shi kam babu abinda zai yi da Baqeer to yaranta mata ma aikin banza duk ba wani jin dadi suke yi ba, ƙwafa yayi yana waigawa suka haɗa ido da Suleiman Ƙaraye yana zaune a cikin mota a baya ya sauke glass yana sauke wani irin numfashi na ɓacin rai, don yau shi kaɗai yasan ɓacin ran da yake ciki wanda yake jin ƙwaƙwalwarshi ma ta kasa tunani mai kyau, wani kallon-kallo suka yiwa juna sannan yace wa driver ya hanzarta su tafi bai son tsayuwa a wurin. Badaru ya ƙara tamke fuska ya juya ya cigaba da tafiyarshi abun takaicin ma shine sai yake ganin kamar kowa yana cikin farin ciki ne banda shi.
******* Tsugunnawa Bello yayi ya haɗe hannayenshi alamun roƙo yana murza hannun yana cewa "Sir plz help me," yayi maganar cikin roƙo, wani kallo suka yi mishi mutanen dake zaune a office ɗin, ɗayan wanda kana gani kasan bature ne, ya kalleshi yace "Am sorry but you have to go back to your country, we brought you here to sponsor you but unfortunately you couldn't pass any test and at the end we realised everything you said was false." Gabanshi ne ya ƙara faduwa, sam ya manta karatunsa da passport ɗinshi suna daban-daban ya saka, su sun yi visa da sunan Muhammad Bello Bala, sai dai bayan yazo ya faɗi gwaje-gwajen da suka yi mishi suka tausaya mishi akan to ya kawo karatun degree da yace yayi in yaso su nema mishi wani aikin, sai dai yana kawowa suka ga Bello Bala Jogana, wannan dalilin yasa suka ce sato takardun yayi, duk yadda yake fahimtar dasu bai sa sun fahimceshi ba, gashi maganarsu ta turanci da sauri suke yi shi kuma ba fahimtarsu yake yi sosai ba. Wani ne ya kalleshi yace ya shirya wai ƙarshen satin nan zasu maidashi gida in kuma ya cigaba da zama zasu lalata mishi permit ɗinshi na zama wanda ko aiki bai isa ya samu ba. Haka ya fito ya shiga masaukin da aka bashi da ƙyar kanshi na wani irin sarawa saboda ɓacin rai, zama yayi a bakin gado ya zuba tagumi yana tunanin abun yi, gaba ɗaya bai yi nisa da tunani ba sai ga wayar Asiya. Wani ƙululun baƙin ciki ne ya kamashi ya ɗaga fuskarshi a tamke, ba tare da yace komai ba. "My love baka turo mini kuɗin ba bayan mun yi magana rannan, sannan Habi ta tafi wai ta gaji so take ta koma wurin Inna, shine nake so in ka turo kuɗin zan ɗauki masu aiki biyu kafin ka zo ka ɗauke ni don sam zaman garin nan ya isheni wallahi," ta ƙarasa maganar cikin kashe murya. Wata irin iska ya furzar yace "Ni kam Asiya hala baki san komai ba sai kisan kuɗi ko?" "Ba dai suma cewa zaka yi ba zaka bani ba?" Ranshi ne ya ƙara ɓaci don dama ƙoƙarin danne ɓacin ranshi yake yi, a fusace ya kashe wayar don yana ji kamar idan ya cigaba da yi mata magana to lallai zai iya furta kalmar sallama don shi dai ta gama kai shi bango tunda yake da ita bata taɓa tambayarshi ya yake ba? Yana da kuɗin da take so ko babu, amma a iya saninta da Baqeer lokacin suna soyayya kullum ta Allah in suka yi waya da safe sai ta tura mishi text na soyayya wanda a zamanshi da ita har suka yi aure bata taɓa yi mishi text ɗin soyayya ba, sai na godiya in yayi mata wata kyautar.
******
Baqeer shiru yayi yana tunani meke faruwa da Zee? Don da alama akwai abinda aka yi mata sosai sannan menene laifinshi? Kashe wayar data yi ya tsaya mishi a rai yana ganin kamar shima ya ɓata mata rai, tambayar data yi mishi na son sanin matsayinta shi ke sake dawo mishi, ko dai ya sanar da ita yana sonta ne? Iya kaci in bata sonshi tace a'a sai dai baya son ya zama sanadiyyar rabuwar zumuncin Dada da ita sannan Maryam da ita. Shafar sumar kanshi yayi sannan ya turo kekenshi zuwa waje Dada ya kalla dake saka maggi cikin ɗan wake yace "Dada yau kuma ɗan wake kika yi?" "Ina fa aiko mini aka yi daga maƙwabta, ga naka can kaima na ragema, yanda yayi daɗi nake ta tunani ina ma Zainabuwa zata zo." Murmushi yayi yana ɗaukan kwanon yana cewa "To ai sai ki aika mata ni dai ci zan yi don ya bani sha'awa." Wani kallo tayi mishi tace "Nikam Baqeeru son Zainab kake yi ko?" Gabanshi ne ya faɗi ya maida murfin kwanon ya rufe yana cewa "Dada me kike nufi? Wani irin so ana zaune ƙalau?" "In ba haka bane abar maganar amma ni haka kawai nake gani." Sake buɗe kwanon yayi yana cewa "Ku dai tsofaffi da son zancen aure kuke," yayi maganar yana kifkif da ido.
******
Mummy ce ta goge hawayenta, Inna na gefenta itama tayi shiru tana tunani, daurewa tayi tace "Aikin gama ya riga ya gama yanzu abun yi zaki yi tunani ai ke mai wayau ce sannan ba kya rasa mafita duk abinda ya shige miki duhu. Wani kallo ta yiwa Dada cikin magana mai ɗan sauti tace "Kin san da haka shine kika biye mata kuka zo kuka janyo mana tozarci? Sannan sanda kika yi magana sam babu alamun mamaki a fuskarta dama ta sani ne ko me?" Inna ta kalleta yanayinta ya ɗan canza tace "A'a banaji gaskiya." Mummy ta girgiza kai tana tuno abubuwa da dama da Nabila take faɗa mata especially akan Zainab lallai ta sani kawai dai nunawa take yi kamar bata sani ba, Inna ce ta katseta da cewa "Bana ji gaskiya da ta sani da ta nuna." Kai Mummy ta girgiza tace "Ta sani shi yasa ta ƙwallafa rai da Kabir so take yi ta tozartani." Wani kallo Inna ta zabga mata tace "Kada ki kuskura ki yi mata wannan ƙazafin, zan ɗauketa mu koma gida ke kin san me zaki yi ki shawo kan komai," tayi maganar tana miƙewa, har ta kai ƙofa Mummy tace "Shi yasa nake cewa ki dinga sawa bakinki linzami yanzu don Allah me kika ja mana?" Tayi maganar tana bin Inna da kallo. Waigowa tayi ta kalleta sai bata ce komai ba kawai ta fita ta ja ƙofar. Mummy ta share ƙwalla tana murza bayan hannunta tana cewa "Duk abinda na gina shekara da shekaru rana ɗaya mahaifiyarka ta ruguza ma shi? Da wani ido zan kallesu? Da kuma wani ido zasu kalleni?" Saman kanta kawai ta riƙe tana jin takaicin abun nan.
Daddy duk yadda yake ƙoƙarin ƙwaƙwalwarshi ta ɗauki abinda ke faruwa ya kasa, har ya tafi zai je guest house ɗinshi ya fahimci ba zai iya zama ba tare da an cire cikin nan a gabanshi ba. Nan yace driver ya sake maidashi gida don meeting dai an gama shi tuni dama guest house zashi, suna zuwa suka ga su Inna sun fito zasu tafi, cewa yayi su tsaya a gabansu bayan sun tsaya ne ya kalli Nabila yace "Shigo!" Kallon Inna tayi a tsorace Inna ta kalleshi tace "Alhaji kayi haƙuri don Allah." Magana zamu yi da ita ke ki wuce gida zan ajiyeta in mun gama, haka ta shiga motar a tsorace don babu alamun wargi a fuskar Daddy balle ta bashi hakuri, gaba ta shiga kusa da driver ko sake kallon Inna bai yi ba balle ya sa a kaita gida, sai driver daya kalla yace "Muje asibitin Zahir" daga haka bai ce komai ba, gaban Nabeela ne ya faɗi ta waigo hankali a tashe zata yi mishi magana, wani mugun kallo yayi mata wanda ya sata maida kanta gaba, gabanta na wani irin faɗuwa wanda take jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito. Idanu kawai take ƙiƙƙiftawa akan titi, a hankali zufa ke ɗan karyo mata tana jin wani dummm bata gama fahimtar me ke faruwa da jikinta ba sai gani tayi an zo asibitin don dama ba wani nisa gareshi ba zuwa gidansu. Fitowa Daddy yayi sannan ya kalleta yace "Wuce gaba saboda bana son a ganeni kiyi gaba ina binki a baya, sannan wallahi kika kuskura kika yi wani abu ko magana da zata sa hankalin mutane yazo kan mu sai ranki ya ɓaci." Bakinta na rawa ta ɗaga kai don tasan bata isa tayi magana ba, haka suka wuce tana tafe ƙafafuwan ta na sake yin sanyi, nauyinsu na ƙara tafiya, kuzarinsu na ƙara raguwa. Waya yayi mishi ya sanar dashi ya iso hakan yasa ya turo secretary ɗinshi akan ta shiga dasu, sun shiga suka sake gaisawa, Nabila na takure gefe ɗaya kamar ƙuli, bayan sun gama magana ya sanar dashi ciki gareta yana so a cire mata, ƙanwar matarshi ce sai tsautsayi ya afka mata tayi ciki, ya ɗan jinjina abun sannan ya umarceta da tazo su shiga ɗan kewayen cikin office ɗin kaɗan don yayi scanning wanda zai bashi damar sanin taimakon da zai yi mata ba tare da matsala ta afku ba. Nabeela ta sake kallon Daddy wanda ya sake haɗe rai yace "Magana ake yi miki ko?" Ta ƙarasa wurin kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, idanunta kuwa nan da nan suks fara zubar da ƙwalla, keɓantaccen guri ne a cikin office ɗin ansa labule an kulle ta yadda na waje ba zai iya ganin meke faruwa ba, haka ta gyara zaman skirt ɗinta ta hau saman gadon da Dr ya umarceta ta hau, hawayenta ya kasa daina zuba, haka tana gani ya fara sa mata gel sannan yasa abun scanning akan cikinta, mamaki ne ya kamashi ganin duk inda ya duba a mahaifarta babu ciki babu alamunshi, da mamaki ya kalleta yace "Ya aka yi kikasan kina da ciki?" Gaban Nabila ne ya faɗi tace "Na'am?" "Kinyi pt ne?" Yawun bakinta ta haɗiya da ƙyar tace "Eh!" "Kuma positive ya nuna?" A tsorace ta ɗaga kai. Cike da mamaki ya sake yin scanning yace "Amma babu alamun ciki babu ma alamun mahaifarki ta taɓa ɗaukan ciki." Daddy dake zaune mamakin kalaman Dr ya kamashi a fusace ya miƙe yace "Me kake nufi?" Dr yana scanning yana cewa "Gaskiya bata da ciki ban san ya aka yi kuka yi tunanin tana da ciki ba." Tsoro ne ya rufe Nabila tayi saurin durowa daga kan gadon ta zube ƙasa tace "Dr ka duba sosai wallahi ciki gareni, don Allah kada kace babu, don sai dai in zubewa yayi ban sani ba……" A ƙufule Daddy ya yaye labulen ya kalleta yace "Kina son kice mini cikin da kika ce kina dashi minti goma sha biyar da suka wuce shine ya zube ba tare da kin sani ba?" Dr ne ya kalli Daddy yace "Yallabai ka kwantar da hankalinka bari muyi bincike." Yayi maganar yana fita daga office ɗin, wani gigitaccen mari taji an ɗauketa dashi wanda yasa ta ƙarasawa ƙasa riƙe da kuncinta…….
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN*
{70}