Baqeer complete - Chapter 51
Baqeer complete Chapter 51: Baqeer complete Chapter 51. ******** Baqeer kam da Zee ya kwana a ranshi yana tashi asuba bayan yayi sallah yayi addu'oi kiran…
3,449 words
******** Baqeer kam da Zee ya kwana a ranshi yana tashi asuba bayan yayi sallah yayi addu'oi kiran wayarta yayi haka nan yaji zuciyarshi baza ta iya jira gari ya waye ba tare da yaji muryarta ba, Zeey ita ma tayi sallah kenan don ta ɗan makara kaɗan saboda tunanuka da suka yi mata yawa, ganin kiran Baqeer yasa tasa a ranta zata tambayeshi matsayinta da safen nan don ta samu ta yiwa Daddy bayani akwai wanda ma take so, ajiyar zuciya tayi sannan ta kishingiɗa akan gado ta ɗaga wayar. Shiru suka ɗan yi kaɗan kafin yace "Ba sallama?" Tace "Assalamu Alaikum!" Yace "Wa'alaikissalam kin ware yanzu?" Ta ƙara gyara kanta tace "Bayan baka damu dani ba baka kira da daddare kaji ya nake ba." Da sauri yace "Inji wa?" Sai kuma yayi shiru, kallon wayar tayi cike da mamakin kalamanshi don ta tabbatar daga ƙasan ranshi ya fito tace "To ba haka bane?" "Umm!" Tace "Umm?" Yace "Eh to shikenan? Seriously na ɗauka kin kwanta ne." Murmushi ta saki kamar yana ganinta tace "Guess what?" Yace "Me?" Tace "kayi guessing kai dai." Ɗan nazari kaɗan yayi yace "Kun samo solution?" Ta girgiza kai tace "Nope! Abinda ya shafeni ne ni da kai." Nazari ya sake yi yace "Menene?" Ta ɗan sake rage murya tace "Wasa nake yi." Murmushi yayi sosai yace "Na manta wa nake waya da ita ashe." Shiru suka ɗan yi kowa da abinda ke ranshi kafin yace "Is everything alright?" Ta ɗan yi shiru kafin tace "A'a komai ya sake wargajewa, sai dai ina fatan komai ya tafi daidai." Jiki a sanyaye yace "In Sha Allahu komai zai tafi daidai." "Jiya Junaid yazo," ta faɗa cike da son jin me zai ce, Baqeer kuwa nan da nan ya haɗe rai, ai bai tambayeta zancen saurayinta ba bare tace amsa ta bashi tunda ya tambayeta, shiru yayi hakan yasa tace "Ya Baqeer kaji me nace?" Cikin dakakkiyar murya yace "Eh!" Shiru tayi don yadda ya amsa yasa ta rasa me zata ce, can tace "Akwai abinda nake son faɗa maka amma ba gobe ba sai dai ko jibi." Cike da son jin menene yace "Kuma sai a bar ni da tunani har kwana biyu?" Kallon wayar tayi kafin tace "Ni wacece a wurinka wacce in nace zan faɗa maka magana baka so ta daɗe ban sanar maka ba?" Shiru yayi yana son cewa "Muradin zuciyata, wacce zuciyata ke bege a koda yaushe," sai dai ganinshi a keken guragu da irin ƙatuwar motar da take hawa da ƙatuwar mota da aikin Junaid yasa yaji ya kasa cewa komai, shi a wa? Jin shiru yasa Zee jikinta yin wani mugun sanyi, muryarta cikin sanyi tace "Kayi tunani jibi in mun haɗu ka faɗa mini in har baka san matsayina a wurinka ba to a gabanka zan goge number wayarka sannan ni da gidan Dada kuma shi kenan har abada don banga amfanin cigaba da tarayyarmu ba." Tana kaiwa nan ta kashe wayar, kifa kai tayi tana tunanin wannan shine mafitar data dace da ita, wai ita yarinyar da bata yarda da so ba ita ke zubar da ajinta akan ɗa namiji? Bayan tasan duk ranar da yasan ita wacece shikenan alaƙarsu ta ƙare? "Ya Allah!" Ta furta a fili tana jin wani yanayi a cikin zuciyarta.
***** Umma cikin baccinta taji kamar ana ƙwala mata kira, ita ba yara ƴan makaranta ba balle ta tashi da safen nan, ga sanyi da ake a gari, abin mamakin ma daga waje ake kiran nata ba ciki ba. Fitowa tayi da sauri tana cewa "Malam lafiya? Allah dai yasa ba wani abun ne ya faru ba?" Wani banzan kallo yayi mata yace "Yau wai ba girkinki bane?" Mamaki ya kamata wanda ya bayyana a fuskarta tace "Girki nane amma kiran na menene?" Da hannu ya nunata yace "Kinga bana son shirmen banza da wofi ki fito yanzu kisa a siyo wake da mai don ƙosai nake son ci da kunu." Baki ta ɗan buɗe kaɗan tace "Malam haka kawai da safe kace ƙosai zaka ci da kunu? Ina ma masu shagon suka buɗe?" "Eh lallai wuyanki ya isa yanka, to a cikin kuɗina na kujeru da kika cinye ki ciro kisa a siyo wake da mai, sannan ayi mini kunu wallahi in lokacin fita ta yayi ba ayi ba za'a gamu da ɓacin rai na." Kallonshi tayi jiki a sanyaye tace "Malam kaji tsoron Allah rabona da in ganka ma a ɗakina har na manta balle kuɗin cefane da zaka bani ranar girki na, kana son cewa har wannan lokacin kuɗin kujeru muke ci?" "To in ma ba na kujeru bane da alama kuɗin sata ko haram kike ci tunda ke dai ba kudi gareki ba ba kuma sana'ace dake ba, ni dai na faɗa miki in fito inga abincin da nake so," yana kaiwa nan ya shiga ɗakin Jamila yana cewa "Zan koya miki hankali da kaina, ina zaune zaki ɗauki jakarki ki bar mini gida."
**** Ƙarfe bakwai Mummy ta haɗa breakfast a kan dining, Daddy ne ya fito fuskarshi sam babu walwala wanda kana gani kasan ba wani baccin kirki ya samu ba, zama yayi sannan ya kalleta yace "Bani wayata na kira Kabir." Miƙa mishi tayi tana cewa "Senate ka saki ranka please kaga dai akwai important meeting da zaka yi yau." Murmushi kawai yayi baice komai ba, sai kiran Kabir da yayi yana zama ya kira Zeey itama. Kallonsu yayi yana cin haɗin soyayyen dankali da kayan ciki wanda yasha attarugu da tattasai da albasa sai ƙamshi ke tashi, fuskar nan tashi babu walwala yake cin abincinshi, babu alamun zasu ci don dukkansu da alama cikin ɓacin rai suke, Daddy ne ya kalli Zeey yace "Jiya kin dai ji me nace miki ko?" Kanta tsaye tace "Naji amma ba abinda zai sa na aureshi bayan tun farko na faɗa maka ni bana son shi." Wani kallo yayi mata sannan ya kalli Kabir yace "Ka shirya anjima kaje gidan Alhaji Nafi'u kaga yarinyarshi mun riga mun gama magana auren ku zan haɗa nayi ƙarshen wani watan kuma wallahi duk wanda yaƙi bin umarnina zai gamu dani." "Daddy me kake cewa? Taya zan yi aure a cikin wannan yanayin? Ana wannan case ɗin?" Kallonshi yayi yace "Wani case kenan?" Da mamaki Zeey da Kabir suka kalleshi, ya cigaba da cin abincinshi yana cewa "Oh wai tsautsayin daya afka kan Nabila? Baiwar Allah ƙaddara ce ta afku mata amma da zarar yayarta ta fita da ita komai zai dawo daidai." Zeey bata san sanda tayi wani murmushin takaici ba tace "Na ɗauka ma daka kira shi haƙurin dukan daka yi mishi ka farfasa mishi jiki zaka bashi sai ma kazo da wani zance? Taya ma zaka ce yayi aure? Ita kuma Nabila fa" Tamke fuska yayi sosai ya tashi yana kallon Kabir wanda shima kallonshi yake yi, babu tsoro yanzu ko shakkar Daddy da yake dashi a da, yace "Na dai faɗa maka," yana kaiwa nan ya fita daga falon, shima Kabir fita yayi ya bar gidan ma gaba ɗaya. Mummy ce ta kalli Zeey wanda gaba ɗaya suma yanayinsu babu daɗi sai dai basu da ta cewa, haka ta fito ita da Nabila suka shiga mota suka bar gidan suma. A hanya Nabila tace "Saukeni." Mummy ta kalleta tace "Kema kin san baki isa ba, tun kafin ki ja mana matsala gwara ki kwantar da hankalinki aje a cire cikin nan, kafin ma ki lalata rayuwarki don Kabir ma aure zai yi." Gabanta ne yayi wani irin faduwa tace "Aure?" Mummy bata kulata ba sai cigaba da jan mota da take yi, Nabila ta fara sakin wani irin ihu tana jijiga ƙofa kai kace zararriya ce tana ihu tana cewa "Buɗe ni, buɗe ni ko wallahi na ce satoni kika yi." Tsoron abinda Nabila ke yi yasa Mummy yin parking ai kafin ta gama daidaita motar ma Nabila ta fita, adaidaita ta shiga ta wuce gidan Inna tana tafe tana kuka kai kace wani ne ya mutu. Tana shiga gida tun a tsakar gida ta ƙara buɗe maƙogwaro tana zabga ihu, Inna daga ciki ta jiyo ihu cike da tsoro ta fito, mamaki ne ya kamata ganin Nabila nan ta rungumeta tace "Nabila? Menene?" Kuka sosai take yi kamar ranta zai fita a cikin kukan tace "Inna na shiga uku, Kabir yayi mini ciki ta ƙarfi sannan yanzu mahaifinshi yace aure zai yi mishi da wata bani ba." Jikin Inna ne ya fara rawa da sauri tayi baya tana maimaita kalmar ciki? Ciki? Ina zan sa kaina da wannan abun kunya a karo na biyu? Baya tayi saboda jin wani duhu ya mamaye mata idanuwanta, jikinta har rawa yake yi take cewa "Kaini gidan wallahi ba zai yiwu ba, kaini gidan yanzun nan Nabila." Da yake abinda take so kenan da sauri ta fito dama tace mai adaidaita ya jirata tunda tasan Inna dama dole taje gidan, haka suka juya gidan Inna sam ta kasa nutsuwa zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, kanta na wani irin zafi. A falo suka samu Mummy don dama tunda Nabila ta gudu ta dawo gida, ta zauna a falo tana tunanin abun yi ko dai ta tashi taje wurin Inna ne tayi mata bayani? Ai kafin ma ta bawa zuciyarta amsa taji ance "Shashashar banza shashashar wofi wallahi kin yi asara ke dai kam baki ji daɗin halinki ba, ki sadaukar da komai naki kiƙi haihuwa dashi amma ƴarki ƙwaya ɗaya baza ki iya amsar mata hakkinta ba? Jininki guda ɗaya dake duniya shine ba zai iya kula miki da ita ba?" Mummy a zabure ta ɗago ta kalli Inna waigawa tayi da sauri tana fatan babu wanda ke wurin sai dai me? Daddy ta gani tsaye a bakin ƙofa don har yayi nisa ya tuna ya bar wasu takardu ya kuma kira number Mummy bata ɗauka ba, jikinta ne ya fara rawa, me zata gani Zeey na tsaye a jikin ƙofar ɗakinta don jin hayaniya yasa ta fito, wasu zafafan ƙwalla ne suka zubowa Mummy shikenan rayuwarta ta ƙare……..
(Baki a sake muka kalli juna, meke faruwa? Me Inna ke nufi da kalamanta? Tana son cewa Nabila ƴar Mummy ce ko kuwa dai kuskuren harshe ne tayi?)
ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA TAKWAS*
{68}
Gaba ɗaya parlourn ya ɗauki wani irin shiru na wasu ƴan mintuna, sai a sannan Inna ta ankara da ɓaramɓaramar da tayi. Hankali a tashe Mummy ke kallon Daddy, wani irin kallo yake yi mata daya ƙara sawa jikinta yin sanyi. Baki ta buɗe zata yi magana sai dai ta rasa ma me zata ce. Ƙarasa shigowa cikin parlourn Daddy yayi yace "Me nake ji Inna tana faɗa Halima?" Jikin Mummy ne ya ɗauki rawa sai girgiza kai take yi ta kasa cewa komai. "Da gaske ne Nabila ƴarki ce da kika haifa ta cikin ki ba ƙanwarki ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar, Mummy dai babu baki sai ido. Wata irin gigitacciyar tsawa yayi mata yace "magana nake yi miki ki buɗe baki ki amsa mini shin Nabila ƴarki ce ko ƙanwarki?" Gaba ɗaya sai ta sake rikicewa don tunda take da Daddy bata taɓa ganin fushin shi irin wannan ba, in banda hawaye babu abinda ke kwarara daga idanunta. Wani irin kallo Daddy yake yi mata sai ya juya ya kalli Nabila dake tsaye a gefen Inna yana ganin kamanni na zahiri tsakanin Mummyn da Nabila kamannin da bai taɓa tsayawa ya lura dasu a tsakaninsu ba saboda duk lokacin nan a zaman ƙanwarta take a wajenshi. Hannu yasa ya tura hular daje kanshi baya ta faɗi a ƙasa. "Lahaula wala ƙuwwata illa billah,' kawai yaje ambatawa. Tuni ya manta da batun meeting ɗin da zashi da mantuwar da yayi ta dawo dashi gidan har yaji wannan mummunan zancen mai kama da almara. Ƙara kallonta yayi sai yaga gaba ɗaya baƙinta yake gani, cikin wata irin masifaffiyar murya da duk wanda aka yiwa amfani da ita sai ya ruɗe yace "duk tsawon shekarun da muka ɗauka tare baki yi tunanin akwai wata rana da zata zo ba da zan iya sanin cewa ita ɗin ƴarki ce shi yasa kika zaɓi ki ɓoye mini?" Cikin rawar murya tace "Senate," hannu ya ɗaga mata alamun baya son jin komai daga bakinta. Juyawa yayi ya kalli Inna yace "kun san cewa Nabila ba ƙanwarta bace ƴarta ce amma kuka rufeni baku taɓa sanar dani ba? Akwai wani abu da kuke ɓoyewa ne?" Gaba ɗayansu suka yi shiru ita kanta Inna a yadda taga Daddy ya birkice musu a yau wani irin mugun tsoronshi ne taji ya kamata. Wani tunani ne ya ɗarau a ranshi sai ya waiwaya ya ƙara kallon Mummy yace "kun ma je inda na turaku kuwa?" Ɗan shiru tayi tana tunanin to ina ya turasu, aka kuma ta tuna ashe fa asibiti yace suje a zubar da cikin jikin Nabila. Da kai ta amsa mishi don a yadda take jin bakinta yayi mata nauyi baza ta iya furta kowacce kalma ba. A fusace yace "baku je saboda kema kina son Kabir ya auri ƴarki?" Murya ba rawa tace "ba haka bane Senate, wallahi ba haka bane zan kaita." "Da dai ya fiye muku don na faɗa miki Kabir ba zai auri Nabila ba ba a gidana za'a yi wannan kwamacalar ba ace ɗana yana auren ƴar matata wacce kowa yake yiwa kallon ƙanwarta, mun riga mun gama magana da Alhaji don haka tun wuri gara ku san yadda zaku yi da cikin nan, ba kuma naso maganar ciki ta ɗara parlourn nan kin san idan ta fita ba ƙaramar illah zata yiwa kujerar da nake nema ba don haka ku kiyaye." Nabila na jin abinda Daddy yace ta zube a wurin tana birgima tana ihu akan ita dai a bar mata cikinta kada a zubar tsoro take ji. "Rufe mana baki mutuniyar banza, duk bake kika janyo mana ba da baki je kin bashi kanki ba hakan zai faru ne?" Inna tayi mata tsawa tana jin wani irin ɓacin rai na ƙara taso mata ɓacin ran da bata taɓa nuna tunanin zata ƙara jin kwatankwacin shi ba tun a shekarun baya da wani abu mai kama da wannan ya faru dasu. Rarrafawa Nabila tayi wajen Daddy tace "Don Allah Daddy kada kuce sai an cire cikin nan wallahi tsoro nake ji ance mutuwa ake yi a wajen zubar da cikin, ka aura mini Kabir ɗin yadda asirinmu zai ƙara rufuwa in yaso sai ka aura mishi waccan ɗin ni na amince." Wani irin kallo yayi nata yace "Zancen banza kenan ko ki amince ko kada ki amince Kabir aure zai yi, maganar aure a tsakaninku kuma na haramta shi, ki tashi kuje a zubar da cikin kamar yadda na ce, ni zan samo miki miji daidai ke amma ba Kabir ba." Haushin Nabila ne Inna taji ya kamata ganin yadda Daddy yake nanata ba zai aurawa ɗan shi ita ba ita kuma sai faman naci take yi kamar shi kaɗai ya rage autan maza. A fusace tace "Tunda yace ba zai aura miki ɗanshi ba ai sai ki haƙura muje a zubar da cikin don ba zan ƙara yin rainon shege ba, na dai yi ɗaya ba zan ƙara yin na biyu." Da wata irin ƙaƙƙarfar murya kamar ba tata ba Mummy tace "Inna!" Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta, wai ita yau me yake damunta ne da take ta faman fallasa asirin da suka binne cikin ransu shekara da shekaru, asirin daya rabo su da ƙasarsu ta haihuwa duk don su samu su lulluɓeshi ba tare da kowa ya san shi ba. "Don't tell me cikin shege kika yi kika haifeta Halima? No wonder itama tayi following footsteps ɗinki, tabbas barewa ba zata yi gudu ba ɗanta yayi rarrafe." Daddy yayi maganar ranshi na ƙara ɓaci sai dai kuma bai yi mamaki da jin cewa Nabila shegiya bace don yasan haka nan baza su ɓoye ita wacece ba inba don suna gudun asalinta ba. Zeey da tunda aka fara maganar nan take hawaye ta kalli Kabir fuskarta ƙunshe da mamakin abubuwan da suke taji yau ɗinnan. Ji tayi ba zata iya cigaba da tsayuwar ba don haka ta koma ɗakinta tana kuka, wannan wacce irin kwamacalar rayuwa suke ciki. Ace wai Nabila ƴar Mummy ce ta cikinta ba wai ƙanwarta ba kamar yadda kowa ya ɗauka. To ita kuwa Mummy me zai sa ta ɓoye musu irin wannan sirrin mai girma haka? A ganinta ai ko ta ɓoyewa kowa bai kamata ace su ta kasa faɗa musu ba tunda dai ai sun zama ɗaya yanzu tana ganin babu wani batun ɓoye-ɓoye kuma a tsakaninsu. To amma idan har Nabila ƴar Mummy ce me yasa take yawan kyararta tana yi mata faɗa alhalin ita ba haka take yi mata ba? Sam fa babu wata jituwa tsakanin Mummy da Nabila yadda take yi ma kamar haushinta take ji komai tayi sai tayi mata faɗa har ita tana mamakin yadda aka yi sam babu jituwa a tsakaninsu kamar ba ƴan uwa ba to ashe ma uwa ne da ƴarta sune basu sani ba. To ko dai haka duk iyaye mata suke idan ta duba taga yadda tasu mahaifiyar tayi watsi dasu tunda ta bar gidansu bata ƙara waiwayarsu ba sai ma ƴan uwanta dake yawan zuwa suna ɗagawa Mummy hankali duk don akan ta riƙesu kamar ƴaƴanta bayan ita data haifesu tayi watsi dasu ta manta ma tana da wasu ƴaƴa data fita ta bari. Kwanciya tayi tama rasa abun dake damunta, ta rasa tunani guda ɗaya da zata yi a cikin kanta. Har yanzu ganin abubuwan da suka faru take yi kamar almara ko a cikin shirin film. Wayarta ta ɗauka ta rubutawa Baqeer text. "Komai ya kwance min Ya Baqeer na rasa ya zan yi." Ko minti biyu bata yi da ajiye wayar ba reply ɗin shi ya shigo yace "Are you okay? Me ya faru?" Hawaye ne ya zubo mata don ganin reply ɗin shi ya sata jin wani irin rauni ya lulluɓeta. "Nothing was as it seems Ya Baqeer. Rayuwar nan gaba ɗaya ƙarya ce mutanen duniya mayaudara ne." Hankalinshi ne yaji ya tashi don haka yayi saurin kiranta, tana ganin shine ta ɗauka sai ta fashe mishi da kuka. Tashin hankalin shi ne ya ƙaru sai cewa yake yi "Zainab menene? What happened? Are you okay?" Ita kuma kuka kawai take yi don a yanzu tana buƙatar yin kuka a inda za'a rarrasheta, ga matsalar rashin sanin matsayinta a wajen Baqeer ga matsalar auren da Daddy yake son ya ƙaƙaba mata na dole gashi Mummyn data kasance mata abar jingina a duk lokacin da take cikin damuwa ta sameta da ɓoye musu sirri mafi girma a rayuwarta a yanzu bata san wane matsayi zata ajiye ta ba kuma. Sai data yi kukanta ya isheta sannan tayi shiru, shima tun yana rarrashinta har yayi ahiru ya ƙyaleta tayi kukan sosai don ya lura kamar akwai abinda yake damunta. Sai data tsagaita da kukan sannan yace "Are you okay?" Ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa sai kuma ta tuna ashe fa baya ganinta don haka ta buɗe baki tace "Eh," cikin dakusashiyar murya. "Me ya faru kike irin wannan kukan Zainab?" Ya ƙara tambayarta. "Ashe mutanen duniya maƙaryata ne mayaudara Ya Baqeer? Ashe zaka iya zama da mutum na tsawon wani lokaci ba tare da kasan gaskiya guda ɗaya a kanshi ba?" "Me ya faru? Waye ya yaudareki? Is it Junaid" Ya ƙara tambayarta muryarshi a cunkushe yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarshi, shi yasan dama Zainab tafi ƙarfinshi zai yi wuya ta iya son shi ko yana da lafiyar ƙafafu bare kuma a yadda yake ɗinnan. "No, its not him," tace tana girgiza kai sai kuma tace "Thank you for lending me your shoulders to cry on," ƙit ta kashe wayarta ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. Duk da ta yarda dashi tana ganin kamar bai kamata ta kwashe abinda yake faruwa a cikin gidan su ta faɗa mishi ba, tana ganin kamar wannan wani sirrinsu ne da ba kowa ya kamata yaji ba,