Baqeer complete - Chapter 50
Baqeer complete Chapter 50: Baqeer complete Chapter 50. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
3,309 words
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA SHIDA*
{66}
Girgiza kai kawai take yi ta kasa gasgata abinda kunnenta ya ke jiye mata, ta yaya ma za'a yi ace wai Nabila ke bibiyarshi, Nabila dai data sani wannan mai yawan nutsuwar da kamun kai wacce kullum idan Daddy zai yi mata faɗa da ita yake yin kwatance yace tayi kwaikwayo da kyawawan halayenta ko yace bata ganin yadda Nabila take girmama manya ga son aiki saɓanin ita da bata iya komai ba sai son jiki ga rashin iya magana, kai ba zai taɓa yiwuwa ba ba dai Nabila. Wani irin kallo tayi mishi ta juya zata bar ɗakin sai jin muryarshi tayi yace "Kenan kin fi yarda da ita akan ni ɗan uwanki?" Juyowa tayi ta kalleshi ya ɗaga mata kai yace "Ribar me zan ci idan nayi mata sharri akan abinda bata yi ba, ki yarda dani Zainab wallahi ita ta riƙa bibiyata idan kin lura zaki ga na rage yawan zama a gida to wallahi duk saboda ita ne, ko ƙarfe nawa zan kai a waje idan na dawo gida zan tarar da ita tana jirana ko ta shiga ɗakina ta laɓe kuma duk a hakan ban taɓa gwada nemanta da wani abu ba saboda babu son ta a zuciyata don haka ban taɓa jin sha'awar kasancewa da ita ba, ita ta fara nemana da wannan rayuwar a cewarta romance kawai zamu yi, tun ina kaucewa har nazo na biye mata kuma wallahi ni ban yi mata fyaɗe ba tunda dai kin san bana shaye-shaye bare tace na sha wani abu daya fitar dani daga hankalina har na afka mata ban sani ba. Please Zainab ki yarda dani idan har da gaske cikin dake jikinta nawa ne ki yarda to ba fyaɗe nayi mata ba da yardarta da amincewarta komai ya faru." Gaba ɗaya fuskarshi ta koma kalar tausayi, lokaci guda duk ya rame yayi wani iri alamun yana cikin tashin hankali mai girma wanda sam bata kula da hakan ba sai yanzu. Ita tama rasa tunani guda ɗaya da zata yi, gaba ɗayansu daga Nabilan har Kabir ɗin kowa idan ya tara maka zance sai kaji shine mai gaskiya. Fita tayi taje ta ɗauko first aid kit ɗinsu ta dawo ɗakin sai ta samu ya cire rigar jikinshi ya kwanta akan cikinshi, gaba ɗaya bayanshi ya kwaye tsabar dukan da Daddy yayi mishi. Hankali a tashe ta ƙaraso cikin ɗakin tace "Me yasa ka tsaya yayi maka irin wannan dukan kamar ya samu jaki baka gudu ba?" Zama tayi akan gadon ta wanke mishi ciwukan tana yi tana mitar don me yasa zai tsaya Daddy yayi mishi irin wannan dukan gashi nan duk ya farfasa mishi jiki. Shi dai yana jinta halin damuwar da yake jin kanshi a ciki ne yasa ya kasa amsa mata.
Haka ta wanke mishi duka ciwukan sannan ta tashi ta fita da first aid kit ɗin, kitchen ta shiga tasa masu aiki suka dama mishi oats ta ɗauka ta kai mishi, da ƙyar ta matsa mishi ya tashi ya sha sannan ta ɓalli paracetamol ta bashi yasha har jikinshi ya game da zazzaɓi me zafi sai rawar sanyi yake yi, rufe shi tayi da duvet ta fita ta rufe mishi ƙofar ganin alamun shi kamar bacci yake son yi.
***** Shi kuwa Daddy yana barin ɗakin Mummy ɗakinshi ya koma abun duniya ya taru yayi mishi yawa, shi yanzu ya zai da abun maganar da Kabir yake neman janyo mishi ace kamar shi ɗanshi yayi wa ƙanwar matarshi ciki. Tashi yayi ya hau zagaye a tsakar ɗakin shi yana neman mafita, gaba ɗaya yana cikin tashin hankali, tension yayi mishi yawa, ga yawon campaign daya sako shi a gaba ko zaman gidan baya samun yi soaaigashi Kabir yaje ya ɗauko mishi wata maganar. Tunani yayi tun kafin maganar cikin nan taje kunnen Inna tace dole sai Kabir ya auri Nabila gara ya nemo mishi mata yayi maza ya aurar dashi. Kai gaba ɗaya ma zai aurar dasu ya huta haka kurum ba zasu janyo mishi magana ba, dama uban Junaid ya daɗe yana so suzo a saka rana shine yake watsar da zancen saboda yafi son a samu fahimtar juna sosai tsakanin Zainab da Junaid ɗin amma yanzu tunda haka ne zai basu dama su fito a tsayar da rana kawai ayi bikin cikin ƙanƙanin lokaci, babu mai janyo mishi matsala a harkar siyasar da yake ganin akwai nasara a cikin tsayuwarshi takara. Wayarshi ya ɗauka ya ƙira mahaifin Junaid, bayan sun gama ƴan gaishe-gaishensu irin na tsofaffin abokai da suka aminta da juna yace mishi dama akan batun auren Junaid da Zainab ne idan sun shirya su fito a tsayar da rana don baya son abun ya ɗauki lokaci so yake yi ayi auren tare dana Kabir kafin lokacin zaɓe yayi. Sosai baban Junaid yaji daɗi don dama abinda suke ta fata kenan suga auren tilon ɗan nasu da matar da yake matuƙar so. Suna gama waya ya ƙira Junaid yayi mishi albishir, duk da maganar tazo mishi a bazata sosai yayi murna don bai taɓa tunanin Zeey zata sauko da wuri ta amince mishi aurenta ba ganin yadda ko wayarshi yanzu ba koyaushe take amsawa ba. Yana asibiti lokacin da Babanshi yayi mishi wayar haka ya sallami sauran patients ɗin shi akan ba zai iya dubasu a yau ba sai dai su dawo gobe ya tafi gida zuciyarshi cike da ɗokin son ganin Zeey.
Fitowa Daddy yayi yana ƙwala ƙiran Zainab lokacin ta fito daga ɗakin Kabir kenan, sai da taji gabanta ya faɗi saboda irin ƙiran da yake yi mata. A parlourn shi ta tarar dashi a tsaye ya goya hannayenshi a baya sai kaiwa da kawowa yake yi, tashin hanakalin da ya samu kanshi a ciki yasa ya kasa zama a wuri ɗaya, idan ba gani yayi ba ya samu mafitar wannan badaƙalar da ƴaƴanshi ke neman sakashi a ciki ba hankalinshi ba kwanciya zai yi ba. Zainab na zuwa tace "Gani Daddy," bayan ta zauna akan kujera tana kallon yadda Daddyn ya kasa zama a wuri ɗaya sai fama zagaye yake yi a cikin parlourn kamar mai yin parade. Kallonta yayi ya nunata da yatsa yace "Ina fata kun gama daidaitawa da Junaid don mun gama magana da mahaifin shi zasu zo mu tsayar da ranar aurenku nan ba da jimawa ba." Shiru tayi ma ta kasa magana jin yadda maganar tazo mata a bazata, ana cikin wancan case ɗin me ya kawo wannan? "Tashi kije," taji muryar Daddy kamar daga nesa yana bata umarni. Sai sannan ta dawo cikin hayyacinta tace "Wani irin aure kuma Daddy bayan na faɗa maka bana son shi, ni dai gaskiya bazan aureshi ba." A fusace yace "Na dai faɗa miki aurar dake zan yi kuma banga uban da ya isa ya hanani ba, ruwanki ne ki koyawa kanki son shi ruwanki ne ki ƙi aure ne dai ke da Junaid babu fashi." Ya fice daga gidan a fusace ranshi yana tafasa. Tashi tayi a guje ta shige ɗakinta tana kuka. Mummy da fitowarta kenan daga nata ɗakin taga wucewar Zainab ɗakinta tana kuka ta bita ɗakin hankali a tashe tana fatan ba wata matsalar bace ta sake kunnowa kuma. Tana shiga ta ganta ta kifa kai akan gado sai gurshaƙen kuka take yi, tambayarta tayi abinda aka yi mata take irin wannan kukan. Ɗagowa tayi ta kalli Mummy fuskar nan tayi jawur idanunta sun yi kozai-kozai alamun taci kuka ya isheta tace "Wai Daddy ne yace sun gama magana da Baban Junaid zasu saka ranar aurenmu dashi bayan tun da farko na faɗa mishi ni bana son shi amma yaƙi yarda kuma ma Mummy ni ina da wanda nake so me yasa ba za'a barni na aureshi ba." Zama Mummy tayi a bakin gadon tasa hannu tana shafawa Zainab baya kamar mai lallashin wata ƙaramar yarinya tace "To me yasa baki faɗa mishi ba?" Sai cewa tayi "Bayan bai bari nayi magana ba ya fice yana masifa ni kuma wallahi babu mai yi min auren dole haka kurum." Shiru tayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin tace "Ai kin san ko kowa bai tsaya miki ba ni zan tsaya miki, ba Daddy ba koma waye babu mai yi miki auren dole idan har ina raye wanda kike so shi zaki aura, haba wane irin auren dole sai kace muna zamanin iyaye da kakanni." Kanta ta kwantar akan cinyar Mummy tana jin wata irin nutsuwa na ratsata don tasan ko kowa bai goya mata baya ba Mummy na tare da ita. A shgwaɓe tace "Mummy bai fa ce yana so na ba." Tsaki Mummyn tayi tace "Ke ba sai ki faɗa mishi ba tunda dai ba haramun bane ba kuma ace dole sai namiji ne zai fara furtawa mace soyayya ba, babu batun wani ɓoye-ɓoye yadda zamanin nan ya canja don kin faɗa mishi kina son shi ba laifi bane." Haka Mummy tayi ta ƙarfafarta tana nuna mata ta kwantar da hankalinta don ba zata taɓa bari ayi mata aure da mijin da bata so ba abinda yasa ta samu ƴar nutsuwa ke ab don tasan tunda Mummy tace haka ita tasan yadda zata yi tasa Daddy ya haƙura da batun aura mata Junaid. Tana kwance tana saƙa da warwara akan shawarar da Mummy ta bata na ta fara furtawa Baqeer cewa tana son shi sai dai kuma zuciyarta ta kasa nutsuwa da yin hakan tana ganin kamar bai dace ba a matsayinta na ɗiya mace da aka sani da kunya da kawaici ta fara bayyana mishi asirin zuciyarta, to sa ma ace tayi hakan idan shi baya jin irin abinda take ji akan shi ba fa kenan ta zubar da ƙimarta ta ɗiya mace ta fallasa mishi asirin zuciyarta yazo yace baya sonta bata san a wane hali zuciyarta zata kasance ba, tana jin watakila ma bugawa zata yi don bata ga ta inda zata iya rayuwar da babu Baqeer a cikinta ba. Mummy ce ta shigo ɗakinta tana faɗa mata Junaid na guest sitting room yana jiranta. A fusace ta tashi zaune tace "Mummy me yazo yi a wurina kuma? Please Mummy kice mishi ya tafi wallahi na tsane shi bana son ganinshi, shine bayan duk faɗa mishi da nayi tayi akan ni bazan aureshi ba a matsayin aboki kawai na ɗauke shi yaje ya turo Babanshi zasu sa ayi mini auren dole to wallahi bazan aureshi ba, idan shi maye ne sai dai ya cinye kanshi da kanshi amma ni nafi ƙarfin nacin shi wallahi." Hannayenta Mummy ta riƙo tace "Duk wannan faɗan da kike yi ai shi ya kamata kije ki yiwa ba wai ki zauna anan kina yi ba alhalin bai ma san kin yi ba, zuwa zaki yi kija mishi kunne kice ya fita sabgarki don ba aurenshi zaki yi ba tunda dai kin tabbatar ba kya son shi to gara ya kama gabanshi tun wuri yasan nayi don nasan harda yawan ganinshi yana zuwa wurinki da Daddy ke yi yasa ya bijiro da maganar aurenki da shi kamar wacce muke neman kai dake, ni an faɗa mishi idan zaki tabbata babu aure zan damu ne, a yadda nake jin ƙaunarki a cikin zuciyata ban ƙi muyi ta zaman mu a cikin gidan nan ba don bana son tuna akwai wata rana da dole zamu rabu kiyi aure." Tashi tayi tana jinjina kai, tabbas harda fuskar data sakarwa Junaid yasa kowa ke tunanin soyayya suke yi bayan tasha faɗa cewa ita ba zata aureahi ba saboda a aboki kawau take kallonshi ba wai masoyi ba. Haja ta fita fuska kozai-kozai ko ruwa bata sa ta wanketa ba Tana shiga sitting room ɗin babu wata gaisuwa babu komai kawai Zainab ta rufe shi da masifa tace "ai dai kasan ba sonka nake yi abotar ma kuma na fasa don haka tun wuri gara kaje ka samu su Daddy ka faɗa musu ba zaka aureni ba don wallahi idan ka yarda ka aureni ka aurar wa kanka tashin hankali, haba bana son naci wallahi. Ka dai san nasha faɗa maka ni bazan aureka ba amma ka nace akan magana ɗaya, to tun wuri kaje ka faɗa musu ka janye don ni dai bazan aure ka ba, to na auri sa'ana nace na auri wa ma?"
Idan ka kalli Junaid a wannan lokacin sai ya baka tausayi gaba ɗaya ɗokin da yazo dashi ya gama gabanshi, ashe bada yardar Zeey iyayensu suka yanke musu wannan hukuncin ba. Ɗan zamowa yayi daga kan kujerar da yake zauna yace "haba Zainab don Allah kada ki bari son da nake yi miki ya tafi a haka, kema kin san ina son ki tun kafin iyayenmu suyi tunanin haɗamu, please ki bani dama na nuna miki irin son da nake yi miki, bana buƙatar sai kin soni son da nake yi miki kaɗai ya ishemu ba sai kin so ni ba har ƙarshen rayuwarmu," tsaki tayi ta mishi wani irin wulaƙantaccen kallo tace "Ai ni zama da wanda bana so ne ma ba zan iya ba kwata-kwata, shawara kuma ta rage ga mai shiga rijiya don ni dai na gama magana," daga haka ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi anan.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BAKWAI*
{67} Tana fita daga falon ɗakinta ta nufa nan da nan kuma tausayin Junaid ya ziyarci zuciyarta, ta sani bata kyauta mishi ba sai dai babu yadda zata yi don kuwa babu abinda zai sa ta aureshi, duk wani abu da Daddy zai yi sai dai yayi amma ita dai babu mai tilasta mata aurenshi, Baqeer take so kuma yanzu ta sani shine jigo na rayuwarta ko da ba zata iya furta mishi ba zata jira lokacin daya shirya sanar da ita abinda ke ranshi akanta. "Kina tunanin yana sonki ne?" Tambayar data zo kanta kenan ji tayi abin duniya ya isheta, pillow ɗin dake kan gado ta ɗauka ta cillar ƙasa, wani irin takaici na ƙara kamata, sallar magriba tayi sannan ta zauna tana jin yunwa amma ɓacin rai ya hanata neman abinci. Junaid kuwa da ƙyar ya iya kwasar ƙafarshi ya bar gidan don ji yayi kamar an ɗebi ruwan sanyi an kwara mishi, mota ma da ƙyar ya iya shiga yayi zuru yana tunanin ta yadda zai yi ma ya kunna motar yaja ya tafi gida, yafi minti goma a ciki kafin ya daure yaja motar sai dai tafiya kawai yake yi babu wani laka a jikinshi. Mummy ce ta turo ƙofar ɗakin riƙe da tire na abinci, Zee tana ganinta ta sake jan bargo ta rufa, zama tayi kusa da ita tace "Auta tashi don Allah kin dai san bana son wannan halin ko?" Kallonta tayi cike da shagwaɓa tace "Allah Mummy ba wai naso wulaƙanta Junaid bane kawai dai nasan in ban faɗa mishi maganganu ba bazai ƙyaleni ba." Kai Mummy ta jinjina tace "Hakan shine daidai in har kasan abu ba zai zama alheri ba to tabbas kar ma ka soma bawa mutum false hope, shi Daddynki muƙaminshi yake dubawa sai dai ni farin cikin ki nake dubawa, Nabila ta ruguza mana farin cikin gidan nan ba zan yarda ke ma a ruguza miki farin cikin rayuwarki ba." Ƙanƙame Mumy tayi tace "Na sani duk duniya babu mai sona sama dake, ke kaɗai ce gatana shi yasa a koda yaushe nake alfahari da kasancewarki mahaifiyata." Shafar saman kanta tayi tace "Nice zan yi alfahari Zeey baki san yadda nake farin cikin kasancewa tare da ke bane." Ɗagowa tayi kaɗan tana kallonta tace "Wannan sakaliyar ƴar taki da bata iya komai ba?" Kuncinta taja tace "Sai me? Sannan menene zai sa ki koyi wani abu bayan muna da kuɗin da zamu yi providing ɗinki with everything you need? Burina kiji daɗin rayuwa bawai ki wahala ba, ko aure ki kayi na faɗa miki zan haɗaki da mai kula da komai naki babu abinda zaki yi sai hutawa." Dariya taɗan yi kaɗan tace "Mummy ni kam tambaya, Aunty Nabila tana son Ya Kabir ne?" Yanayin Mummy ne ya canza ta ɗan janye kaɗan tana cewa "Bana son zancen yarinyar nan sam, sannan gobe da safe zamu je asibiti daga can wurin Inna zata koma." Cike da rashin jin daɗin kalamanta Zee tace "Mummy me yasa ne sam ba kya tsayawa ki fahimci halin da take ciki? Yanzu tun bayan faruwar abun nan kin duba ta? Kinji ya take ciki? Kin tambayeta halin da take ciki?" Mummy ta kalleta jiki a sanyaye tace "Ba sai na tambayeta ba don kuwa bana son jin komai, ni zamanta a gidan nan ma ba so nake yi ba, balle yanzu da ta gama ja mini cin mutunci." Mamaki gaba ɗaya sai sake rufe Zeey yake yi kawai ji tayi bazata iya magana ba, hakan yasa ta sake jan bargo ta rufa, Mummy ta yaye bargon tace "Tashi kema kici abinci, ai Zabba'u tace kin sa an yiwa Kabir abinda zai ci amma ke baki yi tunanin kice ayi miki ba." "Aunty Nabila fa? Taci abincin ne?" Mummy ta tsuke fuska sosai tace "So kike muyi faɗa?" Shiru Zeey tayi kawai tana kallonta, ajiye mata abincin tayi sannan ta shafi gefen kanta ta fita, ga mamakinta Nabila ce tsaye a ƙofar ɗakin kamar dama jiranta take yi ta fito, yi tayi kamar bata ganta ba sai jita yi tace "Ki gama kauce-kaucen dole zaki dawo kibi bayana." Wani kallo Mummy tayi mata tace "Ke yanzu laɓe ma ba abin kunya kika ɗauke shi ba naga alama, ki haɗa kayanki da safe daga asibiti gidan Inna zan kai ki." Da sauri tace "Babu fa inda zani don ina nan har sai anyi aurena da Kabir." Wani banzan kallo Mummy tayi mata tace "Waye zai yi miki auren?" Da mamaki tace "Wa kuwa in ba Daddy ba?" Tsaki Mummy taja tace "Na kula har yanzu hankalinki bai dawo jikinki ba, mutumin da yace a zubar da cikin jikinki shine kike tunanin zai aura miki ɗanshi? To ki buɗe kunnuwanki kiji da kyau in ma bacci kike yi ki farka Senate duk yadda yake yabon kyawawan halayenki a wurinshi baki kai ya aura miki ɗanshi ba," tana kaiwa nan ta cigaba da tafiya cike da takaicin shirmen Nabila, shi yasa take ta nuna mata a'a amma ita sam ta kasa ganewa. Nabila kuwa kasa ko motsi tayi har Mummy ta ƙule bata iya cewa komai ba, ɗakinta ta nufa hankali a tashe ta fara cin babban farcenta na hagu jikinta har karkarwa yake yi saboda tsoro, ta shiga uku, yanzu ya zata yi?
(Umm Asghar da Ayusher kam muka ce muma bamu sani ba🥴)