Baqeer complete - Chapter 49
Baqeer complete Chapter 49: Baqeer complete Chapter 49. ***** Har motar ta ɓacewa ganinshi bai daina bin hanyar da tayi da kallo ba. Wacece ita a wurin shi…
3,408 words
***** Har motar ta ɓacewa ganinshi bai daina bin hanyar da tayi da kallo ba. Wacece ita a wurin shi take tambayar shi, to wacce amsa zai bata? Zai fito ne ya faɗa mata gaskiyar matsayin da ya bata a cikin zuciyarshi ko kuwa zai ƙyaleta ne suci gaba da tafiya a yadda suke yi? Idan ya fallasa mata asirin zuciyarshi ba lallai ne ta amshi soyayyarshi ba don ido ba mudu ba yasan ƙima, ko ba'a faɗa mishi ba yasan daga babban gida ta fito, ko babu nakasa ita ɗin ba ajin shi ba ce to bare ga larurar dake tare dashi bayan haka bai manta da Junaid ba duk da taƙi amsa mishi shi yasan saurayinta, to ya isa yayi takara dashi a yadda yake ɗinnan? Yasan idan aka bata zaɓi tsakanin shi da Junaid dole shi zata zaɓa ta barshi saboda shine tsaran rayuwarta shine sa'an aurenta ba shi ɗan gidan Mallam Badaru da Umma Fatima ba. Kasa komawa cikin gidan yayi sai ya tafi can wajen da su Tanimu suke zama inda yake zuwa daa, bai samu Tanimu ba saboda yanzu akwai shagon da yake zuwa yana taya su ɗinki yace so yake yi hannunshi ya faɗa sosai kafin lokacin da Baqeer zai buɗe nashi shagon. Zama yayi cikin yaran da ya samu a wurin yana kallon duk abinda suke yi, tausayi yaran suke bashi don wasu a cikinsu basu fi shekaru biyar ba, yaran da basu wuce raino ba shine iyayensu suka tsige su daga jikinsu suka kawo su almajiranta babu ci babu sha kuma a haka suke iya bacci hankalinsu a kwance alhalin basu san a wane hali ƴaƴansu suke ciki ba, cikin ranshi yana ji inama shi wani mai faɗa aji ne da babu abinda zai hana bai daƙile kai yara garuruwa yawon almajiranta ba tunda in dai don karatu kowanne gari akwai makarantun allo me ya hana su barin yaran a kusa dasu idan har da gaske saboda karatun ake kai su ba don su yakice nauyin da Allah ya ɗora musu ba. Bai bar wurin ba sai da aka yi kiran sallar magriba, daga nan wurin masallaci ya wuce bai koma gida ba sai da ya sallaci sallar isha'i sannan ya koma. Yana shiga gida Dada ta tare shi da tambayar inda ya shiga tun ɗazu bai dawo ba. Ɗan murmushi yayi yace "Dada ni yaro ne da don na fita na daɗe ban dawo ba duk zaki bi ki damu, ina can wajen dasu Tanimu suke zama daga nan kuma na wuce masallaci kin san kuma ina tsayawa ɗaukar karatu duk bayan sallar magriba zuwa isha'i, abinda ya hanani dawowa da wuri kenan." Kwanukan abincin shi ta ajiye a gabanshi tace "Ni dai bana son daɗewar nan da kake yi a waje yadda rayuwar nan ta lalace babba ma ba tsira yayi ba bare yaro bare kai da ba lafiyar ƙafafu gareka ba." Jinjina kai yayi yace "To Dada In Sha Allah xan kiyaye," don yasan fa gaskiya ta faɗa mishi, yadda rayuwar nan ta lalace mutane ba abun yarda bane.
***** Sai da tayi nisa sosai da barin unguwar sannan ta samu wuri tayi parking ta ɗora hannunta akan ƙirjinta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi kamar wacce zata fasa ƙirjinta ta fito. Ita kuwa yau me ya shiga kanta ne? Me ya kaita furtawa Baqeer waɗannan kalmomin? Yanzu da wane ido zata ƙara kallonshi saboda Allah bayan wannan abun kunyar data tafka, wai wacece ita a wurin shi, inndai ba abinda take fatan ji daga gareshi zata ji ba me ya kaita yi mishi wannan tambayar. Idanunta ne suka kai kan gift bag ɗin daya bata ta janyo ta buɗe ta fito da kayan ciki, turaren Arden beauty (Elizabeth Arden) daya sabar mata da fesawa don tun daga ranar farko da yayi mata kyauta dashi ta bar turaren da take amfani dashi ta komawa wannan, ajiye shi tayi a gefe ta fito da abayar ai bata san lokacin da ta furta kalmar "wow" ba don sosai abayar nan ta tafi da ita, tayi mata kyau sosai kuma daga texture na fabric ɗin tasan ba ƙananun kuɗi ta kwasa ba. Irin waɗannan gestures ɗin na Baqeer ke sawa take ganin shima yana sonta kamar yadda zuciyarta ta afu a soyayyar shi, to amma idan da gaske yana sonta me ya hana shi furta mata duk tsawon lokacin nan da suka ɗauka tare, bai taɓa tambayar wani abu a kanta ba, bai taɓa nuna son yasan wacece ita ba duk da tana tsoron ranar da zai gano ita wacece amma tana ganin idan har akwai wannan son a tsakaninsu sanin asalin wacece ita ba zai zamo matsala ga tarayyarsu ba. Haɗa kayan tayi ta mayar cikin gift bag ɗin sannan ta ɗauki wayarta ta tura mishi saƙon sms. "I wanted to let you know how much I love the gift you gave me. Your thoughtfulness truly touched my heart. Thank you." Ajiye wayar tayi bayan ta tabbatar message ɗin yayi delivering sannan ta tashi motarta ta bar wurin, wani irin mixed feelings take ji a tattare da ita, ɓangare ɗaya tana jin takaicin kanta na yadda take kasa iya controlling emotions ɗinta akan Baqeer har sai tayi wani abu da daga baya zata zo tana dana sani a ɗaya ɓangaren kuma tana jin shauƙi da ƙaunarshi na daɗa ratsa dukkanin wasu sassa na jikinta, ta rasa me zata yi da Baqeer zai fahimci halin da take ciki, tana so duk ranar da Daddy ya ƙara yi mata maganar Junaid ace tana da makamar dafawa amma idan bata san a wane matsayi ya ajiyeta ba bata isa ta tunkari Daddy da zancen shi ba. Har ta ƙarasa gida bata da cikakkiyar nutsuwar zuciya, gabanta ne ya faɗi da taga motar Daddy fake a harabar gidan, yaushe ya dawo? Tayi wa kanta tambayar da bata da amsarta. Jiki a sanyaye ta fito daga cikin motar har ta ɗauki gift bag ɗin zata shiga da ita gida sai tayi wani tunani don haka ta mayar da ita mota ta ajiye, tasan yanzu tana shiga ciki za'a fara yi mata tambayar daga ina take tunda ba wai ta faɗawa Mummy zata fita bane, to a yadda ta fita ta bar gidan ma ai bata jin akwai wanda zai lura da rashinta a gidan yadda duka mutanen gidan basa cikin walwala. Har tayi hanyar ɗakinta don bata so kowa ya ganta bare asan dawowarta gidan sai ta fasa jin kamar hayaniya na tashi daga parlourn Daddy. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," tace haɗe da ɗora hannu aka ganin yadda Daddy yake dukan Kabir da wata sharɓeɓiyar dorina, a gefe ga Nabila a tsugune tana kuka sai Mummy dake tsaye hankalinta a tashe idanunta na tsiyayar da hawaye, tama kasa ƙarasawa kusa da Daddyn bare ta hanashi dukan da yake yiwa Kabir ɗin. A rikice Zainab tace "Daddy......"
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BIYAR*
{65}
Ta ƙarasa wurin da sauri tace "Daddy please!" Wani kallo ya watsa mata yace "Ban taɓa tunanin har dake za'a haɗu a tozartani ba, a cikin gidana? No way!" Ya sake maganar yana ƙara zubawa Kabir bulala, yana zaune duk uban azabar da yake ji na zafin dukan bai sa ya tashi ba don dama tunda Daddy yaji yasan abinda zai biyo baya sai ya wuce haka, kallon Nabila yayi wacce tayi ƙasa da kai tana share ƙwalla, tana cewa "Daddy don Allah kayi haƙuri na tabbatar shima yayi dana sani, don Allah Daddy….." kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata iya cigaba da abinda zata faɗa, ganin jini ta gefen wuyan Kabir yasa Mummy tace "Senate please ya isa haka." Hannu ya ɗaga mata tare da cewa, "Tashi ki koma ɗaki wannafatan umarni ne na baki." Mummy haka ta miƙe kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tayi ɗaki, ya sake ɗaga bulalan zai doki Kabir, Zeey tayi saurin tsayawa a gabanshi zuciyarta baza ta iya bari a cigaba da fasawa Kabir jiki haka ba, kallon Daddy tayi hawaye suka zubo mata tace "Daddy kar ka illatashi a zauna asan solution ɗin da za'a nema tunda mai afkuwa ta riga ta afku." "Kin matsa ko kema sai na zuba miki dukan a jiki? Ni zaku maida shashasha a gidana? To wallahi ba a gidan nan ba, babu wanda ya isa ya tozartani balle yaja mini mutane su fahimci gidana ma ban gyara ba balle in jagoranci mutane." Matsawa yayi daga inda Zeey take ya sake zubawa Kabir wani bulalar, ido ya runtse don shi kaɗai yasan me yake ji, saukar bulalar yaji sai dai ba a jikinshi ba, hakan yasa ya buɗe ido, ganin Zeey yayi a tsaye a daidai inda Daddy ya kai dukan, ya sani duk faɗan da suke yi da ita tana sonshi don kaf duniya su biyu ne a wurin mahaifinsu, kallon juna suka yi idanunta sun cicciko da ƙwalla don rabon da a daketa har ta manta, shi kanshi Daddy ganin Zeey ya daka yasa jikinshi yayi sanyi, kallonshi tayi tace "Daddy na roƙeka da Allah ka bar wannan dukan, sannan bafa abinda ya faru kake shakka ba tsoron siyasarka kake kaga mafita itace." Fuskarsa a tamke yace "Ba wani mafita shiryawa zata yi gobe ita da Mummy zasu je a cireshi, da hankalina babu wanda ya isa ya kawo min ɗan shege sannan ko an zubar bazan iya aura mata shi ba zan dai nemo mata wani ta aura, kai kuma wallahi in baka yi wasa ba gidan mari zan kaika aje can a rufe soko don wallahi baka isa ka lalatamin tafiyar nan ba." Kai kawai Kabir ya saukar ƙasa yana jin wani irin ƙunci a zuciyarshi. "Daddy zubarwa kuma?" Zee tayi tambayar cike da shakkun kalamanshi, wani kallo yayi mata ya yarda bulalar yace "ƙwarai kuwa don ba dai ni za'a haifawa cikin shege ba." Yana kaiwa nan yayi ciki yana sababi, wani kallo tayi wa Kabir wanda kana gani kasan na bacin rai ne sannan ta kamo Nabila suka bar wurin. Tun a hanyar ɗaki Nabila ke kuka har suka shiga ɗaki ta kamo hannun Zeey tace "Zeey tsoro nake ji don Allah kar a zubar ba gwara muyi aure a huta ba?" Kallonta tayi cike da tausayi kafin tace "Kin san Daddy ba zai yarda ba, ki kwanta ki huta In Sha Allahu komai zai tafi daidai. Nabila tana riƙe da ciki tana cewa "Ni dai bazan zubar ba sai dai na shiga duniya, Zeey ki taimaka min don Allah, akwai aure tsakanina dashi me yasa kuke haramta auren bayan ya halarta?" Tausayinta ne ya ƙara kama Zeey hakan yasa tayi ɗakinta jiki a sanyaye tana shiga ta kwanta akan gado tana jin kanta na wani irin sarawa, ga bayanta inda aka daketa har yanzu zugi yake yi mata, tashi tayi ta kalli madubi ta yaye rigarta ta baya sai ga shatin duka har ya fara tashi, nan da nan taji zuciyarta ta karaya, waya ta ɗauka ta kira Baqeer don muryarshi kawai take son ji. Har sai data kusa katsewa don yanata yankan ɗinki sam bai ji kiran ba wayar tana silent, da sauri ya ɗauka sanda idanunshi suka kai kan sunanta na motsi a jikin wayar, karawa yayi a kunnenshi yace "Assalamu Alaikum!" Cikin sanyin murya tace "Wa'alaikasalam da na ɗauka baka kusa." "Me ya sameki?" Tambayar daya jefeta dashi kenan, cike da mamaki tace "Me ka gani?" "Yanayin muryarki ya canja, meya faru?" Kwanciyarta ta gyara taja bargon duvet da aka yi gyaran gadon dashi tace "Abubuwa da yawa, ɗazu ma ganinka dana yi abu ne ya faru yasa na bar gidan, sai dai na yanzu yafi na ɗazu." Ɗan ajiyar zuciya ya sauke kaɗan yana cewa "Zancen ranan nan ne?" Tana ƙifta ido gun dauriya tace "Eh!" "Kenan solutions ɗin bai samu ba?" Ta kara cewa "Eh sannan yanzu abubuwan ma sunfi lalacewa zance ya ƙarasa kunnen Daddy." "How?" Ya tambayeta yana ajiye scissors ɗin hannunshi, ita kanta tambayar data yiwa kanta kenan how? Taya aka yi ya sani bayan lokacin da ta fita baya gidan? Sannan ta tabbatar Kabir ba shi zai sanar dashi ba to meya faru? Muryar Baqeer ce ta katseta da cewa "Baki san ya aka yi ba?" Miƙewa zaune tayi tace "Ya Baqeer bye zan kiraka anjima." Kai ya jinjina ga mamakinta ji tayi yace "Please ki kula da kanki." Cak ta tsaya saboda kalamanshi sun shiga jikinta, shi kanshi jin abinda bakinshi ya furta yasa yayi saurin kashe wayar don tabbas abinda ke zuciyarshi ne ya fito fili ba tare da ya shiryawa hakan ba, shafar sumar kanshi yayi sannan ya ɗan maida hankali kan wayar yana cewa "Allah ya warware muku abinda ke faruwa."
**** Zee kuwa miƙewa tayi ta sauko daga kan gado ta zauna akan sofa ɗin ɗakin tana nazari, ya aka yi Daddy ya sani? Waya sanar dashi? Don dai kaf cikin wanda suka sani bata jin akwai wanda zai sanar dashi, fitowa tayi daga ɗakin kai tsaye ta nufi ɗakin Kabir, a kulle taji shi sai dai tasan dama da ƙyar in zai barshi a buɗe, hakan yasa ta nufi ɗakin Nabila saboda ta tabbatar ba Mummy bace wannan kam bama sai tayi tunani akai ba. Nabila har yanzu na nan kwance a inda ta barta, zama tayi a bakin gado fuskarta a tamke sosai babu alamun wasa take kallonta, kafin tace "Aunty Nabs ke kika sanar da Daddy?" Gaban Nabila ne yayi wani irin faɗuwa don sam bata tsammaci tambayar nan daga wurin Zee ba, zama tayi ta kalleta tana goge ƙwalla kafin tace "Ba…." "Kar ki ce ba ke bace don Ya Kabir ba zai taɓa sanar dashi ba balle Mummy duk da kema bansa a raina zaki yi ba sai dai nafi tunanin ke akan su, na farko Kabir yasan in Daddy yaji shine zai shiga tashin hankali sannan mun yi dashi akan kwana biyu kenan gobe ne lokacin dana bashi, wanda nasan goben ma sai mun kai ruwa rana zai yarda a sanar." Cike da rawar murya tace "Nima ban sani ba mistakenly ne naje tura text ma Dr ashe Daddy na turawa ban kula ba, kin ga dukkansu D ne to ina kwance kaina na ciwo sam ban kula da wanda na turawa ba har sai da Daddy ya dawo ya kirani nan ya fara tambayata akan meya faru shine na sanar mishi, kema kin san wallahi a san raina bazan sanar dashi ba." Kallon zargi Zee kawai take yi mata, mistake? Ganin bata gamsu ba yasa ta ɗauko wayarta da sauri ta nunawa Zee text ɗin wanda a ciki ma Dr ta rubuta akan ya zata yi da ciki ƙarami ba wanda ya sani a gidansu tana kuma tsoron aji. Miƙa mata wayar Zee tayi kafin tace "A ina kika san Dr ɗin da har zaki yarda ki sanar dashi irin wannan babban sirrin?" Nan ma wata faɗuwar gaban ce ta kamata, mamaki take yi yaushe Zee ta fara wayau haka? Don a iya saninta ta yarda da ita in har ta faɗa mata abu bata taɓa bincike take yarda, anya bata yi ganganci ba kuwa wurin tura saƙon nan? To amma kuskure ne ai ba laifinta bane, kallon Zee take cike da rauni tace "Na sanshi don sanda nayi BUK yana level 5 ina level 1 to muna shiri sosai, bayan ya fara aiki ma duk yawanci abubuwana wurinshi nake zuwa." Kai Zeey ta jinjina alamun fahimta duk da ta rasa me yasa zuciyarta ke shakku akan abinda ke faruwa, miƙewa tayi ta nufi ƙofa ta waigo ta kalli Nabila sannan ta fita, ɗakin Mummy tayi, daga waje tana juyo sababin da Daddy yake yiwa Mummy yana cewa "Kina zaune a gidan nan har yaron nan yayi wa yarinyar nan fin ƙarfi? Ke kin san yadda na yarda dake na jingina amanar gidana a hannunki ashe da abinda zaki saka mini kenan? Tun yaushe nake sanar dake yaron nan sam ban yarda da wasu daga cikin dabi'un shi ba?" Mummy cike da tausayin Kabir tace "Senate ƙaddara ce fa Allah ya ɗauro mana wallahi ni nasan Kabir ba zai aikata abin nan da sanin shi ba, ka duba ka gani duk yawon da yake yi da ƴan matan da ke sonshi ka taɓa ji an kawo ƙararshi ance yana neman wasu? Ko kuwa duk matan dake sonshi za ace su basu kai Nabila bane? Allah shine shaidata ni nasan ba da saninshi bane sannan ita ma Nabilan ka daina bata gaskiya gaba ɗaya……." "Ba wani kema kin san Nabila dai bazata taɓa kai kanta wurin Kabir ba, yanzu me kike so ayi in har Inna taji? Bayan kece shaida dama tana jin haushin yadda na sakar miki kula da yarana. Tana ganin kamar ni na hanaki haihuwa." Kamo hannunshi Mummy tayi tace "baza ma taji ba, in har babu wani abu ka bari suyi aure, ita kanta Inna baza tayi faɗa ba in taji aure suka yi kaga ko haihuwa tayi a ƙalla za ace ai ta haihu da wuri ne tunda cikin nan ƙarami ne, ina tsoron garin zubar da ciki wani abun ya faru ne, sannan in tsautsayi yasa Inna tasan abinda ya faru daga baya wallahi har ƙara zata iya kaimu kasan yadda take ji da Nabila." Zama yayi a bakin gado ranshi na ƙara ɓaci shidai gaskiya ba dai aure ba, ba wai baya son Nabila bane sai dai gaskiya ba zai bari su ƙare a gidansu Inna ba, shi ya auri Mummy ne don babu yadda zai yi wanda daga baya ya maida ita class ɗin da yake so, amma banda Nabila don ɗan shi gaskiya sai dai ya auri yarinyar da zata taimaka mishi a siyasa, ba wai wacce ba'a sani ba. Kallon Mummy yayi don ba zai iya sanar da ita dalilinshi na ƙin auran ba sai cewa yayi "Ki shirya zan kira Dr Suhail kuje a zubar da cikin nan, salin alin ba tare da wani ya sani, kinga daga nan ta koma wurin Inna kawai ni zan nema mata miji na nunawa tsara ayi aurensu cikin rufin asiri." Mummy ta jinjina kai tace "Shikenan!" Jin haka yasa Zee ta bar wurin, ɗakin Kabir ta ƙara komawa don zuciyarta ta kasa nutsuwa, in har ita bayanta ya fashe haka da shatin bulala ina ga shi? Ƙwanƙwasawa tayi tace "Ya Kabir buɗe." Kamar bazai buɗe ba sai kuma ya buɗe bai jira ta shigo ba ya koma ciki ya zauna a bakin gado tare da haɗe hannayenshi waje guda, jingina tayi da jikin ƙofa tana kallonshi tace "Yanzu menene plans ɗin ka?" "Banda wani plan kema kin san sai abinda Daddy ya tsara." Cike da takaici tace "Kai ma Yaya why? In mace kake so me yasa baza kayi aure ba? Yanzu fisabillilahi me ka jawo mana?" Idanunshi da suka yi jaa ya ɗago ya zuba mata yace "Nake son mace a ina? Ke kinsan da a matse nake da tun kan ki dawo nayi aure, kawai bani da ra'ayin ajiye iyali ne yanzu." Ranta a ɓace da jin kalamanshi yasa tace "Ba kada niyyar ajiye iyali amma kana da niyyar yin fyade? Sannan a cikin gida? Ba kunya ba tsoron Allah, abinda Aunty Nabs ke ji...." Cike da ɗaga murya yace "Wai kowa ni yake ɗaurawa laifi? Ita fa? Ko don ina namiji shi kenan nine mai yin komai? Kuna ina sanda take biyoni har ɗakin nan don na kulata? Kuna ina sanda take nuna soyayyarta a gareni ina rejecting ɗinta? Kuna ina sanda nake korarta daga ɗakina amma take ƙin fita? Ko don ni ban bayyana abubuwan da take yi mini ba shi kenan kuma sai laifi yayi ta zama nawa?" Hankali a tashe Zee ke kallon Kabir tana mamakin jin kalaman dake fita daga bakinshi, kanta take ji yana wani irin sara mata, me take ji yana faɗa? Nabila? No way……..