Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 48

Baqeer complete - Chapter 48

Baqeer complete Chapter 48: Baqeer complete Chapter 48. *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

3,255 words

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA UKU*

{63}

Badaru ne ya shigo gidan riƙe da kwankwaso don har yanzu bai gama warkewa ba, daidai Fatima zata shiga ɗaki kamar dama jiranta yake yi sai jita yi yace "Ai ba tun yanzu ba nasan dama kin rainani, in banda iskanci kina ganina shine ba zaki gaida ni ba zaki wuce? Fatima na kula fa kin gama rainani a gidan nan wallahi zaki kwashi kayanki ki bar mini gida." Kallonshi tayi maimakon ta bashi hakuri sai ji yayi tace "Sannu da zuwa," daga haka ta shige ciki, ƙwafa yayi yace "Munafuka kawai ai an yanka ta tashi yanzu kaf dinku kallon kowa nake yi." Abu tana jin haka tayi sum-sum ta shige ɗakinta ta maida ƙofar ta rufe, ya nufi ɗakin Jamila yana cewa "Munafuka kema daga ke har ɗanki kun kusa ku bar mini gidana." Jamila ta amshi ledar bread dake hannunshi tana sanabe tana cewa "Malam kai dai kada ka wahalar da kanka don Allah kaga dai ba dadi kake ji ba." Ciki ya shiga yana cewa "Ai ko ba lafiya gareni ba daidai nake dasu dukansu." Fatima kuwa tana shiga dakin ta saki murmushin jin daɗi tare da yiwa Allah godiya, account dinta da Baqeer ke turo kudi ta kalla, dubu dari ne a ciki don idan ya turo mata ba wani kashewa take yi ba gani take in mutanen gidan suka ga tana kashe kuɗi tabbas zargin ta zasu fara yi, ɗaki ta shiga ta kira Baqeer suka gaisa sannan tayi mishi godiya. Cike da jin daɗin dake bayyane a fuskarshi yake bata labarin shagon da zai kama, Umma wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo saman idanunta albarka kawai take saka mishi tace zata samu tayi miya sosai a aiko musu, nan shima yayi godiya suka yi sallama. Ƙwallar data tarun mata a ido tasa hannu ta share tare da yin hamdallah. Baqeer ne ya kalli Salim wanda ya saki baki yana kallon jakar gift bag da ya siya yasa abayar nan da turaren nan a ciki, ɗauke jakar yayi yana ƴan wurƙila ido yana cewa "Ahh lallai abu yayi karfi, ina ce dai ba a ɗinkin mata zamu ƙare ba?" Wani mugun kallo yayi mishi yace "Ka gama neman maganar ka kayan maza ma nake tunanin maida hankali sosai akai akwai abinda nake son yi." Dariya Salim yasa yace "Faɗa mini gaskiya ba dai so kake yi ka dinga yin na maza ba saboda baka son yiwa wasu matan ɗinki inba Zee ba?" Tsuke fuska yayi yace "A yaushe nace hakan? Sannan Zeey sai dai ka faɗawa saurayinta haka ai ba ni ba." Kai ya kau da yana shafar haɓa yana cewa "Adai gama waske-wasken za'a dawo dai inda aka barmu in ma mutum na neman sauƙi gwara ya fito ya faɗi abinda ke ranshi." Gyaran murya Baqeer y8ai yace "Yauwa muna magana akan sunan da za'a sa in nayi ɗinki." Matsowa Salim yayi yace "Ko zaka yi amfani da MBB ɗin ka don sunan nayi mini daɗi." Kai Baqeer ya girgiza alamar a'a sannan yace "Na gama amfani da sunan har abada, na farko na barwa wanda ya saci sunan shine last gift dana mishi a duniya, na biyu kuma bana son Baba ya gane nine da wannan sunan." Cike da fahimta Salim ya jinjina kai yace "Na Baba dai na fahimta amma banga dalilin barwa butulu irin Bello sunanka ba." Murmushi kawai Baqeer yayi don bai san me zai ce ba sai can yace "Ya kake ganin Muhammad B?" Salim yace "Yayi shima amma sai dai mu maida sunan Mohd kaga zai yi tsayi." Shiru Baqeer yayi alamun nazari kafin yace "MOHBAQ fa?" Tafi Salim ya fara yace "Perfect yayi sosai dama MBB ma kai kasa da kanka sai naga wannan ma yafi dadi Mohbaq Muhammad Baqeer kenan." "To shugaban yan washi bar zuzutawa dai." "To ko mu tambayi Zee am sure……" Jakar hannunshi ya kusa kwada mishi, dariya Salim yasa yana cewa "Ah to wai don ka tabbatar." "Kai dai nasan yanzu bakinka ba shiru zai yi ba kana matsawa zaka kira Habi." Yanayin fuskar Salim ne ya ɗan canza yace "Nifa kunsa mana ido babu abinda ke tsakanina da ita," kamar tasan abinda ke faruwa kawai sai ga kiran wayarta cikin wayarshi, kallon Baqeer yayi tare da saurin maida wayar aljihu wanda hakan yasa Baqeer cewa "Ya? Ta kira ne? Kuje kusha soyayyar ku ni babu ruwana." Fita yayi daga shagon da sauri yana cewa "Ba ita bace customer ne." Kallonshi yayi yana girgiza kai, kallon shagon yayi nan ya fara tura kekensa yana bin girman shagon da kallo don shaguna huɗu suka je gani sai wannan hankalinshi ya fi kwanciya dashi saboda girmanshi yana ganin in za ayi abu gwara ayi shi a wadace. Aunawa ya dinga yi abubuwan da ya kamata su siya na furnishing ɗin shagon, nutsuwa da kwanciyar hankali ke sake ratsashi, wayarshi ya kalla sai kuma yayi murmushi haka kawai yaji yana son jin ya take, text ya mata yace "Zafa a baki fail a exam ɗin ." Zeey lokacin tana zaune ɗakin Mummy sun yi shiru gaba ɗaya ta rasa me zata cewa Mummy, ita kam Mummy a kwance akan gado wani matsanancin ciwon kai take ji don gaba ɗaya jiya bata samu bacci ba, senate kuma da safe ya fita saboda wani taro da zai yi attending a Niger State, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kamo hannun Mummy ta riƙe gam cikin sanyin murya take cewa, "Mummy na bashi kwana biyu ya sanarwa Daddy da kanshi, sai dai yanzu an riga an shiga kwana ɗayan farko In Sha Allahu zamu samu mafita, sai dai an cuci Nabila ban san yadda zamu yi da baiwar Allahn nan ba." Kai Mummy ta girgiza itama ta ƙara rike hannun Zee tana cewa "Aikin gama ya riga ya gama, sannan in da lefin Kabir ita ma da nata laifin, tsorona Allah tsorona Senate ko Inna wani yaji abinda ke faruwa," ta ƙarasa maganar cike da damuwa, kallonta ta sake yi tace "Ya aka yi kika sani?" Wani abu ta haɗiya tace "Ta kirani jiya akan tana da ciki to da farko ban yarda ba amma da nazo na ganta sai na tabbatar, sannan ƙin faɗar wanene da kuma yadda nasan ba yawo take yi ba yasa na fara zargin Ya Kabir, naje wurinshi na bugi cikinshi sai kuma kalamanshi da actions ɗin shi suka tabbatar mini abinda nake zargi, Mummy taya Ya Kabir zai yi mana haka?" Wasu ƙwalla masu zafi ne suka taru a idonta. Mummy ta rungumeta tace "Babu komai Zeey mubi komai a sannu In Sha Allahu Allah zai kawo mafita." Kallonta tayi tace "Allah zai kawo mafita amma bazan bari a cuceta ba kin dai sani, dole ne Daddy yasan abinda ake ciki sannan Inna ma ki sanar da ita ko ni na sanar da ita, babu yadda za ayi tace tana da ciki a bar abu har sai ya girma kafin asan abun yi." Ajiyar zuciya Mummy tayi don tasan wacece Zeey akan faɗar gaskiya ko da mahaifinta ne sai tayi faɗa sannan in tana da ra'ayin abu babu mai canza mata shi akan wannan dalilin yasa sam bata da ƙawaye don bakinta baya shiru. Ganin Mummy zata lallaɓata yasa ta fito daga ɗakin ta shiga nata, kallon ɗakin tayi yayi kaca-kaca saboda Nabila bata gyara mata ba, fitowa tayi tasa mai aiki tazo ta gyara mata sannan ta amso abincin Mummy ta kai mata ta koma ta ɗauko na Nabeela ta kai mata, rungume juna kawai suka yi Nabeela na kuka tana shafar bayanta, sun daɗe a haka kafin tace "Ya isa Aunty Nabs In Sha Allahu komai zai tafi daidai." Kai ta girgiza tana cewa "Ta yaya? Bayan babu wanda zai fahimceni? Nice da cikin kuma ni aka ƙwacewa virginity? Sannan ni za'a bari da zagi?" "Kinyi PT ya nuna positive ne?" Kai ta ɗaga alamar eh kafin tace sau hudu ina yi amma still positive," ido ta ɗan runtse, Nabila ta kalleta tana hawaye tace "Zeey don Allah ki taimakeni tsoro nake ji ke kinsan ni wacece babu yadda za ayi na kula wani inba ta ƙarfi aka nuna mun ba." Hannu tasa a saman leɓenta tace "Na sani, ke dai kici abinci ki kwantar da hankalinki." Tana kaiwa nan ta fito daga ɗakin, jita yi komai na gidan ma bata so hakan yasa kawai ta shirya ta ɗauki wayarta ta fito ta faɗa mota tayi gaba.

***** Da mamaki Kamalu yake kallon yaron shagon Baba yace "Kai dan gidanku nida shagon mu zaka hanani shiga?" Yaron ya sake danne ƙofar ta ciki yace "Don Allah Kamal kar ka janyo mini matsala ka ga Baba saura kaɗan ya koreni don Allah ka bari in yana shagon kazo." Buga ƙofar ya fara kamar zai ɓalla ta hakan yasa mutane suka fara kallonshi, ƙwafa yayi ya juya yana masifa "yaron nan wallahi sai na tareshi a lungu nayi mishi dukan tsiya, sai ya san ni ya wulaƙanta ɗan banza ɓarawo kawai, ai kaine kake sata tunda ni kayan ubana gadona nake ci." Aljihunshi ya laluba yaga babu komai, ajiyar zuciya yayi ya hango wani mai babur wanda yake sak irin nashi, da gudu ya nufi mai babur ɗin dake cikin hold up, yana zuwa yace "Bawan Allah ɗan zo nan don Allah tambayarka zan yi." Me babur ya zabga mishi wani kallon banza yace "Sauri nake yi." Ya fara tuƙin shi, gudu Kamalu yasa yana bin babur ɗin sai dai duk yanda yake zabga gudu bai cimma shi ba haka ya dinga haki yana sauke ajiyar zuciya, haka ya ƙarasa gida da ƙafa saboda babu kuɗi a hannunshi ya gaji ya galabaita sosai ga wata azababiyar yunwa dake ƙara kamashi.

***** Zeey tana tada mota taga text ɗin Baqeer a hankali ta saki wani murmushi, a yanzu shi kaɗai take son gani, maimakon tayi mishi reply sai ta ajiye wayar ta nufi gidan Dada. Dada ta dawo daga maƙotansu kenan inda aka yi haihuwa kwanaki yau mai jego tayi arba'in zata koma gidan mijinta shine tazo gidan suka sha hira, tana ganin motar Zeey ta fara murna tana cewa "Lale da Zainabuwa ta." Fitowa Zeey tayi tana murmushi tace "Dada ta daga ina haka?" "Naje makota ne mai jego tayi arba'in baki ga yaron ba yayi ɓulɓul abinshi." Murmushi tayi tace "Dada kina son yara." "Saura naki ɗan, Allah yasa nayi wa ɗanki wanka ke da Baqeer." Ido ta zaro da sauri tace "Dada wani Baqeer ɗin?" "A'a Zainabuwa kwantar da hankalinki nufina da yaran ki da yaranshi ai ko tsugunawa yayi bazan bashi ke ba yadda kike ɗin nan sai namijin da yafi kowa mutunci zan bawa." Dariya Zeey tasa tace "Dada tawa Allah dai ya bar mini ke." Ciki suka shiga tana cewa "Mutumin baya nan ma sun fita shi da Salim…." Ganin takalminshi yasa tace "Ashe ma ya dawo, Baqeeru kana ciki ne?" Shafa addu'ar da yake yayi ya koma kan wheel chair yana cewa "Dada kin dawo?" Yayi maganar yana buɗe ƙofa, idanuwanshi ne suka sauka akan Zee, tana jingine da jikin bangon kusa da ɗakin, wani nutsuwa da farin ciki ne ya sauko mishi ya zuba mata ido yana cewa "Dada ban san kin shigo ba ai." Itama murmushin tayi tace "Dada kin kulle ɗaki ne hala?" Daga ciki tace "Zainabu bari ina zuwa abu zan ɗauko." Kallonta yayi yace "Ɗaki yafi dadi ai," Yayi maganar idanunshi na kanta. Tana kallonshi itama tace "Bani." Ido ya ɗan canza yace "Me?" "Mark ɗina," hannunshi yasa a aljihu ya ciro biro yazo daf da inda ta miƙo hannun ya fara mata zane, kallonshi kawai take yi tana murmushi, zanen ƙwarangwal yayi mata sama-sama, baki ta buɗe bayan ta kalla a shagwaɓe tace "Wato nice ma ƙwarangwal?" Biron yasa a gefen kuncinsa yace "Mark kika ce kuma baki ci komai ba." Ta turo baki tace "Allah a faɗa mini, please menene." Kiyi browsing ki gani, wayarta ta dauka ta rubuta ganin bata gane ba still yasa tace "Wani yare ne?" "Hmm arabic?" Nan ta sake rubutawa kurawa wayar ido tayi kawai sannan ta dago tana yi mishi wani kasalalken kallo wanda ya dinga ji komai na jikinshi na sagewa, tace "Wai da duk sorry ne aka dinga wahalar dani? Allah sai na rama an yi 1-0." Shima murmushin yayi yace "Anya ba 5-0 aka yi ba?" Jakar gift ɗin daya saya mata ya kalla yana son ɗaukowa yaji muryar Dada tana cewa "Zainabu share wannan kizo in nuna miki wani abu," Kallonshi tayi shima kallonta yayi sannan suka kalli Dada. Me zai gani? Album ne a hanunta da sauri yace "Dada wallahi a'a." Dariya tayi tace "Dalla kai dai ka koma ɗakin ka ni hotona zan nuna mata ba wani abun ba." Da sauri ya turo kekenshi, itama Zee ta nufo wurin tana dariya tana cewa "To Ya Baqeer ai dai hoton Dada aka ce ba naka ba."

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar ce* *Da Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA HUƊU*

{64} Zaman dirshan tayi ta baza hotunan a gabanta tana kallo tana dariya, yawanci hotunan Dada ne tana budurwa sai waɗanda suka ɗauka da mahaifin su Umma lokacin tana amarya. Haka Zeey ta sakata a gaba tana dariyar kwalliyarta harda ƙwalla. Tana cikin kallon hotunan ne taga hoton wani yaro an ɗaukeshi da kwanon fura a gabanshi fuskar nan tayi dagace-dagace da furar kamar wanda ya wanke fuska da furar. Ɗagowa tayi ta kalli Baqeer sai ta ƙara kallon hoton, can dai tace "Dada waye wannan?" Ta ɗaga hoton tana nuna mata. Dariya Dada ta saka kafin tace "Waye kuwa idan ba dunkum ba, kin san fa ci ne dashi yana ƙarami." Kallonshi Zeey tayi sai ta kwashe da dariya har da riƙe ciki tace "Wai Ya Baqeer ka ganka kuwa," hannu ya kai zai ƙwace hoton tayi sauri ta janye hoton tana cigaba da dariya. A gefe ta ajiye hoton ta cigaba da kallon hotunan sai dai duk da haka lokaci bayan lokaci sai ta juya ta kalleshi ta sake kwashewa da dariya. Har suka gama kallon hotunan bata daina dariyar wancan hoton na Baqeer ba, sai da ta tattare wa Dada hotunanta ta ɗaga wancan hoton tace "Dada ina son wannan, kin bani?" "Baki da dama Zainabu, duk hotunan nan ki rasa wanda zaki ɗauka sai wannan?" A shagwaɓe tace "Ni dai Dada shi nake so ki bani, kin ji?" Dariya tayi tace "Idan ma duka kike so ai zan baki bare wannan ƙwaya ɗaya." Juyawa tayi ta kalli Baqeer tayi mishi gwalo sai kuma tace "Ya Baqeer," shiru yayi ya rabu da ita. Tashi tayi ta koma kusa dashi tace "Ya Baqeer mana, please ka juyo ka kalleni magana zamu yi." Har cikin ɓargonshi sai da Baqeer yaji ƙiran nan da tayi mishi don tayi ƙasa sosai da muryarta sai tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa abinda yasa yaji wani abu ya tsirga mishi tun daga tsakar kanshi har zuwa tafin ƙafarshi. Kallonta yayi sai yaga itama shi take kallo, hoton dake hannunta ta ɗaga mishi tana dariya ƙasa-ƙasa tace "Ka tuna?" Gira ya ɗaga mata da sigar tambaya sai kuma yace "Me?" "Wannan hoton ka tuna lokacin da aka ɗauka?" Girgiza kai yayi alamar a'a don anyi hoton lokacin bai fi shekara biyu ba, ba zai iya tuna sanda aka ɗauka ba. Hannu ya miƙa mata don ta bashi hoton har ta miƙa mishi sai ta tuna ba lallai ne ya dawo mata dashi ba don haka tayi saurin janye hannunta tana dariya tace "Naƙi wayon nasan idan na baka ya tafi kenan ba dawo mini dashi zaka yi ba." Shima dariyar yayi "Da gaske zan baki gani kawai zan yi." Maƙe kafaɗa tayi tace "Ni dai a'a gaskiya."

Ɗan ɓata rai yayi kamar yayi fushi yaƙi magana, kallonshi tayi tace "Wai fushi kayi don nace bazan baka ba? To gashi," yi tayi kamar ta miƙo mishi sai da ya waiwayo yaga wayarta take miƙo mishi. Da mamaki ya kalleta yace " Me zan yi da ita?" "Oho," tace tana ɗaga kafaɗa, naga kamar kayi fushi ne shine na baka wayata a madadin hoton. Mayar mata da wayar yayi sai kuma yace "Ki ajiye wannan zan baki wani kinga wannan tsohon hoto ne." "Ni dai shi nake so sai dai idan zaka yarda na ɗauke ka wani a wayata sai na baka wannan." Girgiza kai yayi alamun a'a, cewa tayi "Shikenan ka huta sai ka bar min abuna tunda dama ba kai ka bani ba bare kace sai na dawo maka dashi." Cikin ranta kuwa cewa take yi 'me kike yi haka ne wai Zainab? Kada fa kiyi abinda zai fallasa asirin da kike ɓoyewa cikin zuciyarki'. Shiru suka yi na wasu ƴan mintuna, tashi tayi ta leƙa Dada a ɗaki tace "Zan tafi Dada sai an kwana biyu kuma," tashi tayi ta biyota tana cewa "Bari na taka miki." Koda suka fito daga ɗakin baya tsakar gidan, ƙofar ɗakinsni Zeey ta kalla tana tunanin daga tashinta shine har ya shige ɗaki, kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru, daga nan tsakar gidan suka yi sallama da Dada ta fita. Tsayawa tayi turus ganin shi a jikin motarta da gift bag a hannunshi, ƙarasawa tayi wurin tace "Kana nan ashe?" "Da ina kike tunanin zani?" Shima ya mayar mata da tambayar. Ɗaga kafaɗa tayi irin nima ban sani ba ɗinnan sai kuma tace "Ban sani ba ko ka shiga ɗaki ne." Miƙa mata gift bag ɗin yayi, bata karɓa ba sai cewa tayi "Me zan yi dashi?" "Karɓa mana, naki ne," hannu tasa ta karɓa sannan ta buɗe gift bag ɗin ta leƙa ciki sai taga kwalin turaren da yake yawan saya mata ne sai kuma fabric ɗin da bata san ko miye ba sai taje gida sannan ta duba ta gani. "Thank you," tace tana ɗan murmushi cikin jin daɗi, matsawa yayi daga jikin motar ya bata wuri ta shige. Har ta tayar da motar zata tafi sai kuma ta leƙo da kanta waje tace "Me yasa kake yawan yi min kyauta Ya Baqeer? Wacece ni a wurinka?" Bata tsaya ta saurari amsar da zai bata ba ta figi motar a guje ta bar wurin don gabanta faɗuwa kawai yake yi saboda kamar wacce aka matsi bakinta ta samu kanta da yi mishi wannan tambayar ba tare data shirya ba shi yasa tayi saurin barin wurin don bata son jin amsar da zata fito daga bakinshi ta zama akasin abinda take fata.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull