Baqeer complete - Chapter 47
Baqeer complete Chapter 47: Baqeer complete Chapter 47. Baqeer kuwa yana kwance akan katifarshi tunanin Zeey da halin damuwar data shiga a ɗazu ne suka…
3,375 words
Baqeer kuwa yana kwance akan katifarshi tunanin Zeey da halin damuwar data shiga a ɗazu ne suka tsaye mishi a ranshi, yasan ba ƙaramin abu ke damunta ba tunda har ta iya yin kuka a gabanshi bayan kasancewar ta very jovial mai yawan raha da son wasa da dariya. Wayarshi ya janyo ya tura mata text, "Are you okay?" Ya ajiye wayar a gefe ya lumshe idanunshi yana tunanin abubuwan da yake son yi idan ya gama makarantar koyon ɗinkin daya shiga, bai sani ba ko kuɗaɗen daya ajiye zasu ishe shi buɗe shago ya kuma zuba irin kekunan da yake so domin a tailoring school ɗinnan an koya musu amfani da kekunan yin designs kala-kala yana kuma son ya zuba su a shagon da yake son buɗewa sai dai matsalar kuɗi ce zata kawo mishi cikas. Ƙarar shigowar text ne ya katse mishi tunanin da yake yi. Cike da ɗoki ya janyo wayar yana doka murmushi tun bai ga abinda ta rubuto ba don dai ya tabbatar message ɗin daga wajen Zeey yake. "Am good" kawai ta rubuto. Ajiyar zuciya yayi sai dai har yanzu hankalinshi bai gama kwanciya ba da amsar data bashi. Kafin yayi typing reply wani message ɗin ya shigo. "Me kake yi har yanzu baka yi barci ba?" "Sketching?" Ta ƙara turo wani saƙon. "Nope" ya mayar mata. Sai kuma ya sake tura mata "Ke me kike yi har yanzu da baki kwanta ba?" "Tunanin assignment ɗin daka bani ne ya hanani barci." "Ya Baqeer ba zaka faɗa mini ma'anar assignment ɗin ba? Please👋." Murmushi kawai yayi, bai san lokacin da ya samu kanshi a halin da yake ciki ba amma dai ya sani a yanzu Zainab ita ce farin cikin shi, ba zai iya cigaba da rayuwar da babu ita a cikinta ba. Sai dai idan ya tuna ba lallai ne ta so shi a yadda yake ba ya zama gurgu, nakasashen mutum kamar yadda wasu suke kiranshi sai yaji hankalinshi ya tashi don ya tabbata tausayi ne kawai yasa ta shigo rayuwarshi bata jin abinda yake ji a kanta a cikin zuciyarshi. Emoji na dariya😆 ya tura mata kawai. Tana ganin abinda ya turo ta mayar mishi da emoji na fushi😠 ta ajiye wayarta tana murmushi. Kasancewarta tare da Baqeer na sakata cikin shauƙi yana bata nishaɗi shi yasa hankalinta bai kai kan abinda ke faruwa a cikin gidan nasu ba. Da yin wannan tunanin ta nemi duk wani farin ciki da ta samu kanta a ciki ƴan mintuna ƙalilan da suka wuce ta rasa. Bata so zuciyarta ta riƙa kaita wurin da bata so amma ta kasa yakice tunanin daya ginu a cikin zuciyarta sai dai abinda ta ganarwa idonta yasa ta kasa yakice hakan, bata so hasashen da tayi ya tabbata don tasan idan har ya tabbata hakan ne ba ƙaramin tashin hankali zasu shiga ba. Kai to su ta yaya ma zasu bari har hakan ya kasance? Tashi tayi ta fita zuwa ɗakin Kabir don suyi magana saboda gaba ɗaya hankalinta ya kasa kwanciya, gara taje taji daga bakinshi cewa tunaninta ba daidai bane ko ta samu kwanciyar hankali. Tana murɗa ƙofar ɗakinshi taji ta a kulle, knocking tayi ta haɗa da kiran sunanshi. Sai da ya tabbatar muryar Zeey yaji sannan ya taso ya buɗe ƙofar, murya a cunkushe yace mata "lafiya?" Ba tare daya bata hanya ta shiga cikin ɗakin ba. "To ka bani hanya na wuce mana ha'an, ni magana nazo muyi." Ta tureshi ta shige cikin ɗakin ta zauna akan sofa. Sai da ya leƙa yaga babu wanda ya biyota sannan ya koma cikin ɗakin ya mayar da ƙofar ya rufe da makulli. Zama yayi akan kujerar dake kallon wacce take kai yana kallon Zeey yana jiran yaji dame tazo ɗakin shi a wannan daren, itama kallon nashi take yi tana kokawa da zuciyarta akan ta tambayeshi ko kuwa dai ta ƙyale shi sai dai tasan ba zata samu nutsuwar zuciya ba idan har ba tabbatar da gaskiya tayi ba. Zamanta ta gyara ta ƙara nutsuwa saboda abinda take shirin faɗa mishi da tasan idan har zarginta ne kawai ba wai gaskiyar kenan ba sai sun samu gagarumin saɓanin da bata hango shiryawarsu kwana kusa ba. "Kai ke da alhakin yiwa Aunty Nabs ciki ko?" Kawai ta samu kanta da watsa mishi tambayar ba tare data shirya ba ko ta tsara ta yadda maganar zata fito ba. A firgice ya ɗago yana kallonta sai dai ya kasa buɗe baki ya amsa ko ya musanta zargin da tayi mishi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" tace haɗe da tashi tsaye hankalinta a tashe tana nuna shi da ɗan yatsa. "Kenan da gaske kai ne kayi mata ciki Yaya Kabir?" Da sauri yace "Zainab please! Ita ta faɗa miki? Sannan wai hauka nake yi da zan aikata hakan?" Wani irin kallo tayi mishi cike da tuhuma tace "Unfortunately I don't trust you, muje wurin Daddy a sakaku a gaba aji meke faruwa." Hankalinshi ne ya sake mugun tashi da sauri ya tsaya gabanta yace "Wai kece uwarta? Sannan nace ba ni bane a wani dalili zaki dage akan Shirmen tunaninki?" "In ma shirme ne in ma ba shirme bane muje gun Daddy kayi bayani." Tsaki yaja ya koma kujera ya zauna yace "Kanku ake ji ke da Nabilan, ai dai ni nasan ba ni nayi ba so ya rage naku ita zaki zubarwa mutunci ba ni ba." Yayi maganar cike da dauriya don kar ta gane halin da ya shiga. Saman goshinta ta shafa yanzu kam ta tabbatar akwai abinda ya shiga tsakaninsu, din a iya saninta in har Kabir bai san komai ba in ta faɗa abu na farko da zai tambaya shine ciki? Ciki ne da ita? How? Ta yaya? Tunda dukkansu sun san wacece Nabila sannan ya kamata ma ya ɗauki maganar tata a matsayin hauka amma ganin yadda hankalinshi ya tashi yasa ta gasgata tunaninta. Nan da nan taji hankalinta ya ƙara mugun tashi, tsoro ya ƙara kamata, cike da ɓoye tsoronta tace "Wallahi kai kasan bazan bar maganar nan ba, Ya Kabir kada dai kace mini fyade kayi mat……." Rawar da muryarta keyi ne yasa ta kasa ƙarasawa, ganin yanayinta ya taso da sauri ya ƙara dawowa gabanta, wani mugun kallo tayi mishi kafin yayi wani tunani ta sharara mishi wani irin mari tana yi mishi wani kallon tsana da ƙyama……..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BIYU*
{62}
Hanyar ƙofa tayi da sauri ya riƙo hannunta, kallonshi tayi kawai taji hawaye ya soma taruwa a idanunta, saman goshinta ta shafa sannan ta fizge hannunta tana cewa "Haba Yaya wannan wani irin son zuciya ne, taya zaka yiwa Mummy haka? How?" Kuka ne ya nemi k6wace mata kawai tasa hannu ta sake turashi baya, jikin ƙofa ya jingina ya sa hannu saman fuskarshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, ya zai yi da rayuwar nan? Kallonta yayi kamar zai yi kuka shima yace "Zeey sam nima ban san meya faru ba, ban tuna ba sam akan abinda ya faru kin dai san ba shaye-shaye nake yi ba." Wani mugun kallo tayi mishi tace "Ranar da ta taimaka maka ka dawo ɗaki hope dai ba ranar bane?" Kallonta yayi cike da rashin fahimta yace "Yaushe kenan? Don ni dai ban taɓa rasa hanyar ɗakina ba tunda dai kin san ba shaye-shaye nake yi ba." Hannu ta ɗaga mishi tace "Ta ina zan sani tunda ba ganinka nake yi ba, sau nawa ake neman ka a gida ba'a ganinka? Sannan ranar am sure abinda ta fara ce mini kenan da yake bata son aga laifinka sai ta wayance." Yanayinshi ɗauke da mamaki yace "Ban dai san me ya faru ba amma ni dai ba dai ni ta kawo ba sannan da kike magana haka ke kin san ma wacece Nabila ne?" Tsaki tayi tace "Malam bani hanya na wuce don wallahi baka isa ka tozarta Mummy ina raye ba, kai ko tausayinta ma baka yi? Ko duba yadda ta riƙe mu da amana baka yi ba? Kana gani abubuwan da take fuskanta akan mu a dalilin mahaifiyar mu da danginta, sannan kana ganin yadda suke faɗa da Inna akan mu, wannan wani irin rashin imani ne......." Ta ƙarasa maganar cikin tsananin takaici wanda kana ganin takaici a idanunta, taya zai yi haka? Shi kanshi kalamanta sun saka yaji jikinshi ya ƙara sanyi shi yasa duk wani abu da zai yi yayi ƙoƙarin yi ganin ya janye jikinshi daga kanta, amma yanzu yasan ba mai ganewa babu wanda zai fahimceshi. Ƙofa ta kama tana neman buɗewa da sauri ya ƙara maida ƙofar ya rufe yace "Ni kaɗai ne ɗan uwanki a duniyar nan, ki taimaki rayuwata ki jira na samu nutsuwa ni da kaina zan sanar in kuma har na wuce kwana biyu ban sanar ba na baki dama ki sanar wa Daddy ɗin, kiyi mini wannan alfarmar don Allah," ya ƙarashe maganar yana haɗe hannayenshi bibbiyu alamar roƙo. Hawaye ne ya zubo mata tace "Kwana biyu kaɗai Yaya don ba zai yiwu mu mata ace kullum muke ɗaukan laifi ba." Tana kaiwa nan ta fita, kasa ko motsi yayi saboda takaicin abinda ya aikata, tsanar kanshi na sake ratsa ko ina na jikinshi, taya zai yiwa Mumy haka? Nabeela da tun jin motsin Zee ta biyota duk abinda ya faru a ɗakin tana waje tana saurarensu, jin kalmar Zee na karshe yasa tayi saurin barin wurin tayi ɗaki tana shiga ta shige bargo ta fara kuka har da shesheƙa yadda za'a iya jiyowa daga waje. Ita kuwa Zeey tana fitowa jikin ɗakin ta tsaya tana jiyo kukan Nabeela, tabbas ba zata iya haɗa ido da ita ba, haka ta koma ɗaki kawai ta kwanta ruf da ciki, takaici duk ya isheta sai take gani kamar ma abinda ya faru laifinta ne tunda da bata dage sai Nabila ta zauna anan ba tabbas da bai haiƙe mata ba. Waya ta ɗauko tana son yiwa Baqeer magana amma bata son ɗaga mishi hankali don ta tabbatar dazu ta sanya shi cikin damuwa. Duk yadda Zee take da dauriya akan abu amma yau ji tayi ta kasa bacci haka tayi ta juyi sai wajen asuba bacci ya ɗauketa.
***** Habi ce ta kalli Asiya tace "Kinga tashi zan yi na koma gidan mu ba zai yiwu ki dinga yi mini abu kamar wata uwata ba." Cike da gadara tayi tsaki tace "Aikin banza gidan naku menene a ciki banda kunu? Ƙosai wannan ba kullum ake samu ba, amma nan kin samu banza sai ki dafa indomie ki soya kwai da dankali gashi nan duk kin cinye kayan abincin da My love ya siyo." Baki kawai Habi ta saki kafin ta tuntsire da dariya tace "Malama tashi daga baccin da kike yi, ke ɗin ƴar wacece? Kema ai ƴar kunun ce da shi aka raineki da shi kika girma." Yatsa ta nunata dashi cike da ɓacin rai tace "Wallahi ki shiga hankalinki dani, wai ni sa'arki ce ko kuwa don kinga na ɗaukeki kamar kawa kike son ki mayar dani marainiyar wayonki?" Harara itama ta zabga mata tace "Kinga kafin ma ki sallameni gidan kunu zan koma, gidan shayi asha da madara lafiya." Tana kaiwa nan ta miƙe ta fara haɗa kayanta a cikin jaka, takaici yasa Asiya jan tsaki ta koma ɗakinta tana cewa "Kiyi ki gama nasan dawowa zaki yi don yadda kika saba da cin mai maiƙo ba iya zaman gidan naku zaki yi ba, ta kalli wayarta cike da takaici don wallahi sai ta yiwa Bello wulakanci in har bai turo mata kudi yau ba, gaba ɗaya account dinta dubu biyar kacal take dashi ga kayan abinci da yawa babu, ita dai yayi sauri yazo ya dauketa su tafi don ba zata iya wannan rayuwar ba, rayuwar talauci da jiran sai an bata. Gara itama ta tafi daga can ko ta wataya ta ƙara zama babbar yarinya.
****** Cike da jin daɗi Baqeer ya kalli wayarshi, dubu dari hudu cif aka turo mishi. Wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo mishi yana jin wani yanayi a cikin zuciyarshi na nutsuwa da salama, ya zai yi da wannan jin dadin? Sujudush shukr yayi wa Allah na godiya tabbas Allah shine maji daɗin bawa, in har yaso ya tasheka babu mai durƙusar da kai, miƙewa yayi ya dinga exercise ɗin ƙafar shi kafin ya sake kallon wayarshi, sunan Zainab ya fara dubowa sai kuma ya saki murmushi ya kira number Salim nan ya sanar dashi an biya kuɗin sannan yace suzo da yamma suje a dubo shagon da suka ce zasu kama, sai suga abubuwan da suke buƙata tunda yana da ragowar naira miliyab ɗaya da rabi na kuɗin filinshi da aka sayar, cike da jin daɗi Salim yace ai gani nan ma zuwa wannan ai ba abun jira bane. Sallama suka yi cike da jin dadi dukkansu, anan ya turawa Umma dubu arba'in ya turawa Hadiza dubu ashirin ita da Maryam su raba sannan ya turo kekenshi ya fito falo wurin Dada. Tana ganinshi tace "A'a cukumi an fito?" Murmushi kawai yayi ya hau danna wayarshi, yana son kiran Zainab sai dai yafi so sai ya kama shagon har an zuba kekunan ɗinki kafin ya kaita taga wajen. Kallon Dada yayi yace "Dada menene bamu dashi a gidan nan yanzu Salim zai zo zamu fita sai mu sayo daga can." Ƙwalla ce taji ta taru a idonta, tunda Baqeer ya samu abun yi bai ƙara bari ta rasa wani abu ba a cikin gidan don kafin ƴaƴanta su kawo mata ya cire kuɗi ya sayo duk abinda yasan suna da buƙata, ita kuwa me zata cewa Baqeeru bayan ta cigaba da yi mishi addu'ar fatan alkhairi. "Shikenan daga tambaya sai kuka Dada, idan ba kya buƙatar komai ai sai ki faɗa ba wai ki zauna kina share hawaye ba." Maficin da take fifita dashi ta ɗauka ta jefa mishi sai dai yayi saurin kaucewa yana dariya, itama dariyar tayi tace "babu abinda muke buƙata Baqeeru, ka wadata mu da komai Alhamdulillah, Allah yayi maka albarka ya baka masu yi maka kaima." Murmushi yayi, sosai yaji daɗin addu'ar da tayi mishi har yana hango kanshi da Zainab a matsayin ma'aurata har ma ga ƴan ƴaƴansu data haifa mishi, wani irin farin ciki ne yaji ya kamashi cikin ranshi yana raya inama wata rana mafarkin shi ya tabbata ya zama gaskiya yana ganin da babu wanda zai kai shi farin ciki a duniya. A daidai wannan lokacin Salim ya shigo yana sallama, ganin Baqeer a zaune yana murmushi shi kaɗai don tuni Dada ta tashi ta bar shi a wurin. Zama yayi akan shimfiɗar Dada yace "mutumina irin wannan farin ciki haka, halan wasu kuɗaɗen aka sake turo maka." Tsaki yayi still murmushin bai bar fuskarshi ba yace "tun ɗazu nake zaune a wurin nan ina zaman jiranka, a ina ka tsaya?" "Kasan lokacin da ka kirani ina kasuwa to sai da na sallami wasu customers kafin na rufe shagon na taho. Ina dai ka shirya mu tafi?" Ɗaga mishi kai yayi kafin yace "eh, bari na ɗauko atm card ɗina. Sai dai a ina kake ganin ya dace mu nemi shagon? Da a tunanina ko nan unguwar sai kuma na duba naga nan ɗin yayi wajen gari da yawa ba kowa ne zai iya biyo mu nan ba shine nace bari dai na jira kazo sai muyi shawarar inda kake ganin yafi dacewa mu buɗe shagon, idan zai yiwu dai mu nemi wurin da yake center kasuwanci inda ko address muka bayar ba zai yi wahalar zuwa ba ba cikin lungu ko cikin unguwa ba, koya ka gani?" "Hakan shawara ce mai kyau, In Sha Allah ina barin nan zan yi mana survey zan kuma bada cigiya a wasu wuraren da nake ganin za'a samu wuri mai kyau, ko kuwa yanzu kake ganin zamu fita neman wurin?" "Eh akwai wasu shaguna da wani da muke koyin ɗinki tare ya faɗa mini su nake so muje mu gani daga nan zaka rakani shopping zan je nayi mana ƴan tsince-tsince." Komawa yayi ɗaki ya canja kaya sannan ya ɗauki atm card ɗin ya saka a aljihu ya fito, kallonshi kawai Salim ya tsaya yana yi domin sai yaga Baqeer ɗin gaba ɗaya ya canja mishi kamar wanda ake yiwa wankan inji, fatarshi sai sheƙi take yi tana glowing kamar ta jarirai ga wata ƴar ƙiba da yayi alamun ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali fiye da daa. Kantin da yake zuwa idan zai yi sayayya suka je, suna tafe suna ƴar hirar su duk akan yadda suke so shagon da zasu buɗe ya kasance. Sayayya yayi musu kamar yadda ya saba sai turaren Zeey da baya fashin saya mata duk lokacin da zai je sayayya irin wannan sai dai wannan karon ya haɗa mata da wata doguwar rigar abaya daya gani tayi mishi kyau, yasan idan ta saka a jikinta tabbas zata yi mata kyau shi yasa bai ji ƙyashin saya mata ba duk kuwa da cewa rigar tana da tsada don da yaga kuɗinta sai da ya jinjina kai amma Zainab is worth every penny he has, zai iya kashe mata ko nawa ne don yaga farin ciki a fuskarta.
***** Umma na zaune a tsakar gida wajen da suke yin girki tana ƴan aikace-aikacen ta, Abu da Jamila na zaune kowacce a ƙofar ɗakinta, ita dai Abu ƙulle-ƙullen magungunan matan da take sayarwa tana yi suna zunɗen Fatima dake ta kaiwa tana kawowa ba tare data kula da me suke yi ba, tana cikin aikin Hadiza ta kirata ta sanar mata da saƙon da Baqeer ya tura musu ta account ɗinta ita da Maryam, bata san lokacin da ta saki wani murmushin farin ciki ba tana godewa Allah daya kyautata rayuwar yaronta bai bar shi ya shiga garari ba bayan da iftila'in rayuwa ya afka mishi, faɗa mata tayi ai itama ya turo mata kuɗin, nan dai suka taya juna murna domun basu yi zaton rayuwar Baqeer ɗin zata inganta har haka ba a yadda suka ga ya cire rai da rayuwa a lokacin da ya samu accident sai gashi yanzu komai ya wuce ya fara zama tarihi. Murya ƙasa-ƙasa Jamila tace "ita kuma wannan lafiyarta ƙalau dai ko naga tana dariya ita kaɗai." Kallonta Abu tayi ta yatsina fuska sannan ta ɗaga murya don Fatima ta jiyota ba kamar yadda Jamila ta saukar da tata ba tace "kika sani ko albishir ta samu nakasashen ɗanta ya warke." Suka kwashe da dariya gaba ɗaya harda tafawa, kallonsu Umma tayi tace "Abu kenan, nakasa ai ba kasawa bace jarrabawar rayuwa ce kuma mun karɓeta a yadda tazo mana muna kuma fatan Allah yasa mun cinyeta sannan kuma fata nagari lamiri idan akwai rabon zai taka a gaba sai kuga ya warke tunda abun duk yin Allah ne amma ko a haka Alhamdulillah tunda ya tsira da ranshi da lafiyarshi. Ina kuma baki shawara ki rage yawan izgili don baki san me gobe zata haifar ba sai Allah tunda dukkanmu rayuwar ba a hannunmu take ba bare muce mun san yadda ƙarshenmu zai kasance." Miƙewa Abu tayi a fusace tace "aniyarki ta biki, wato tunda ɗanki ya zama nakasashe shine kike yi mana mugun fata to ta Allah ba taki ba." "Ameen Ya Rabbi, aniyar kowa ta bi shi," Umma ta mayar mata itama don taga alama matan nan na neman ƙure haƙurinta, duk kawaicin da take yi musu basa gani har sai sun sa ta tanka musu sannan hankalin su yake kwanciya.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari