Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 46

Baqeer complete - Chapter 46

Baqeer complete Chapter 46: Baqeer complete Chapter 46. ***** Mummy dake tsaye jikin ƙofar toilet tana jiyo wayar da Nabila ta yiwa Zainab, banda ƙoƙarin…

2,764 words

***** Mummy dake tsaye jikin ƙofar toilet tana jiyo wayar da Nabila ta yiwa Zainab, banda ƙoƙarin buɗe ƙofar babu abinda take yi ranta a matuƙar ɓace take cewa "Wallahi Nabila in baki fito ba jikinki ne zai faɗa miki." Tana daga ciki tace "Mummy bafa zan fito ba sai Zainab ta dawo babu abinda zaki ce mini har sai ta dawo gidan nan koma menene kiyi a gabanta, in ke kince a'a ita ai tasan da aure tsakanina da yayanta." Mamaki ya sake rufe Mummy, ɓacin ran dake fuskarta kuwa ba zai misaltu ba, ganin da gaske ba zata buɗe banɗakin ba yasa ta fita daga ɗakin kanta na wani irin sarawa, ɓangaren Kabir tayi don sam yanzu ya daina zaman gida, yanzun ma baya nan, anan falon ta zauna ta ɗauki waya ta kirashi, yana ɗauka tace "Kana ina?" Ina nan ƙasan layi akwai wani gidan abokina ina can." "Ka dawo yanzun nan," tana kaiwa nan ta kashe wayar tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta dafa saman kanta da take ji yana wani irin zafi kamar wuta, yanzu ita ya zata yi? Ta ina zata fara ɓullo wa abinda ke faruwa? Kalaman Nabila ne ke dawo mata, bayan ta sake mata magana akan ganin likita tace ba zata ba, har zata fita daga ɗakin ta sake kallonta tace "Nabila na roƙeki da Allah karki janyo mini abun kunya, don Allah kar kiyi abinda zai sa farin cikin gidana ya lalace, shi yasa tun farko naƙi sakar miki fuska ni nasanki fiye da yadda kika san kanki nasan wannan ladabin da kike yi a gidan nan wanda har kowa yake ganin baki da wani mugun hali ni nasan pretending ne, sai dai ban taɓa nuna miki na sani ba, fatana don Allah ki koma wurin Inna ki samu miji kiyi aure don Allah." Nabila taji tasa dariya da mamaki take kallonta tsoro ita kanta ya bayyana a fuskarta, tana kallon Mummy tace "Kinga rashin faɗarki bai daɗa miki da komai ba, yanzu burinki ya cika? Wacce baki yarda da ita ba ta tabbatar miki da mugun halin ta?" Yanayin Mummy ne ya canza tace "Me kike nufi?" Ƙafaɗa ta ɗaga mata tace "Idan Kabir ya dawo ki tambayeshi ni ba zanyi komai ba sai Zainab tazo, zan gani in zaki iya korata bayan abinda ya aikata." A tsorace Mummy take takowa tace "Tashi mu wuce gida wurin Inna…." Kafin ta ƙaraso shine ta shige toilet da wayarta, tana shiga tasa key daga nan shine ta kira Zeey. Ji take yi zuciyarta na wani irin zafi wanda ta tabbatar da za'a gwada jininta a lokacin tabbas da zai kai hawa 200/130 ga wani uban ciwon kai dake damunta, duk laifin Inna ne don ta dade tana nusar da ita zaman Nabila gabanta shine sam bata son yawan zaman nan da take saboda Kabir don tun tuni ta fahimci son Kabir take yi. Ya zata yi in da gaske take cikin ne kuma na Kabir ɗin ne? Ƙwaƙwalwar ta sam ta kasa yin wani dogon nazari don abubuwan da zasu faru a kan cikin nan Allah ne yasan yawansu, Daddy wanda ko da wasa baya son image ɗinshi ya ɓaci taya zai fuskanci abun nan? Ga Zainab wacce tasan ko me zai faru ba zata bari ace za'a tauye hakkin Nabila ba duk kuwa da yayanta ne mai laifi don haka take a kuma kan maganarta Daddy ya kaita ƙasar waje karatu saboda ya gaji da wannan halin nata. Kabir ne ya shigo tana nan a zaune, kallonshi tayi sai kawai taji hawaye sun zubo mata, nan da nan hankalinshi ya tashi yace "Mummy menene? Ƴan Ɗambatta sun zo ne?" Wasu hawayen ta sake yi tace "Ba gwara suzo kullum ba da abinda kake neman jawo mana Kabir meya shiga tsakaninka da Nabila?" Gabanshi ne ya8i mugun faduwa hankalinshi yayi wani irin tashi, jikinshi na rawa yace "Mummy wallahi nima ban sani ba." Wani abu ta haɗiya kamar zatasa kuka tace "Kabir ka janyo mana yanzu ban san yadda zamu yi da senate ba." Da sauri yasa gwiwowinshi a ƙasa ya riƙe ƙafarta yace "Mummy ki taimakeni a zubar wallahi ni bansan komai game da abinda take cewa ba, ni wallahi ban tuna komai ba, Mummy in Dady yaji ni nasan kasheni zai yi." Kallonshi tayi tace "Ta riga ta faɗawa Zainab." Idanu ya zaro yace "Kafin magana ta kai kunnen Daddy dkn Allah Mummy ki sakata a gaba muje a zubar ni wallahi ban san nayi ba." "Tana ciki ka gwada yi mata magana." Cikin sauri ya mufi ɗakin Nabilan ya ƙwanƙwasa tare da sanar da ita shine, da kamar ba zata buɗe ba sai kuma ta buɗe don bata son ɓacin ranshi, kallonta yayi yace "Nabila na roƙeki da Allah muje a zubar dashi, na ɗauka ke kanki baki tabbatar da ciki bane da?" Itama kallonshi tayi tare da riƙe cikinta tace "Na tabbatar ɗazu da safe, sai dai bazan iya zubar da ƙwan ka ba, ko da kuwa zan rasa raina." Tayi saurin rungumeshi kam tana cewa "Don Allah Kabir kar ka biyewa Mummy, da aure tsakanina da kai kada ka bari zancenta ya rabamu, ita tana ji kamar ta haifeku ne sai dai mu sa a ran mu ƙila ma rabon auren mu da zuri'armu ne yasa tazo a matsayin kishiyar mahaifiyarku." Janye jikinshi yayi yace "A wurun mu ita ce mahaifiyarmu kuma babu wanda zai nuna mata mu ba nata bane, bazan iya auren kanwar mahaifiyata ba na sanar dake a baya yanzu zan ƙara sanar dake, ko ba don Mummy ba babu soyayyarki a raina." Idanuwanta ne suka yi ja da sauri ta nufi gaban madubi ta fara zubar da kayayyaki ƙasa tana fasa su turare, cikin kuka take cewa "Haka kace? Haka kace? To lallai zaka tsinci gawata don bazan iya rayuwa babu kai ba kuma babu wacce ta isa tayi rayuwa da kai ina kallo sai dai duk mu taru mu rasa." Hannunta ya matso ya finciko ya matseta sosai ta yadda zata nutsu taji me yake cewa yace "Enough! Just listen to me, kin san kina sona kika sanar da Mummy kina da cikina? Kika sanar da Zainab? Haka ake so?" Cikin dauriya tace "Naga kai bazaka maida hankali wurin ƙwato ni ba shi yasa ni na furta don na raya soyayyar mu." Wata dariyar takaici yayi yace "Wallahi in har kika sanar da Zainab nine mai cikin wallahi magana bazan sake yi miki ba balle akai ga Shirmen zancen da kike yi na aure, na dai faɗa miki." Yana kaiwa nan ya fito tare da wucewa ɗakin shi. Yana fita ko minti biyar bai yi ba Zee ta buɗe ƙofar ɗakin Nabila tana haki da alama gudu tayi wajen shigowa ciki, kallonta tayi a zaune a ƙasa ga kayan kwalliya nan duk an zubar a ƙasa, wasu kwalaben turaren ma sun fashe da sauri ta ƙarasa ciki ta rungumeta, nan Nabila ta saki wani kuka, bayanta Zeey ta shiga shafawa hankali a tashe, da ƙyar ta samu ta daina kukan tace "Faɗa mini meke faruwa? Me naji kina cewa kamar wai ciki ne dake?" Kallonta tayi sai tayi murmushi tace "Ciki na ke min ciwo ji nake yi kamar bazan rayu ba." Kallon zargi ta tsareta dashi wanda hakan ya sata cewa "Allah da gaske nake yi wai ke da me kika ɗauka." Ajiyar zuciya Zeey ta sauke ta zauna a ƙasan tana cewa "Har hankalins ya kwanta dama na gama sanin in dai har kamar ke aka ce ciki gareki to tabbas wanda yayi cikin fyaɗe yayi miki don ko kusa da namiji ba kya zama bare har ta kai ki ga riƙe hannunshi to taya kenan zaki yi ciki, a hanya nasa a raina in dai shine to fyaɗe aka yi miki ko magani aka sa miki aka yi ba'a hayyacinki ba." Ƙeyarta ta talle tace "Lallai na kusa daina barinki kallon dramas ɗin nan da kike yi wato har kin tafi wani senario ɗin ma na daban? To ni ta ina zanyi ciki ke kin san ba maza nake kulawa ba." Yanayin Zeey ne ya canza ta sake bin ɗakin da kallo sannan ta tsare Nabila da ido sosai cikin kakkausar magana tace "No Aunty Nabila ɗazu ba haka kika ce mini ba, ce mini kika yi Zeey na shiga uku ciki ne dani kuma cikin……." Sai wayar ta yanke. Nan da nan gaban Nabila ya shiga faɗuwa, kallon Zeey tayi wacce yanayinta ya canza sosai tace "Haka kika ce am 100% sure." Yanayin Nabila ne ya canza gabanta ya shiga faduwa, kallonta sosai Zeey take yi itama yanayinta ne yake canzawa, meke faruwa? Aunty Nabila? How?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA ƊAYA*

{61}

"Me yake faruwa ne Aunty Nabs? Ni sai yanzu ma na lura da wasu changes a jikinki. Garin yaya hakan ta faru ke da ma ba wani yawan fita kike yi ba ba kuma wani kike kulawa ba da sunan soyayya, ta yaya hakan ta faru saboda Allah, kuma kada kice min ba haka ba ne ko wasa kike yi don ba irin wannan maganar bace ake wasa da ita." Ta tsurawa Nabila ido tana jiran jin amsa daga bakinta, ita sai yanzu ma ta lura taga duk ta ɗashe jikinta ya saki alamun dai lafiya bata wadaceta ba, to ita kuwa tana ina har Nabilan ta shiga cikin wannan halin bata sani ba, to wai shin ma wanene yayi wa Nabila haka ya keta alfarmarta don ita dai ta tabbata idan har da gaske cikin ne da ita to sai dai idan raping ɗinta aka yi don a sanin data yiwa Nabila babu ta yadda za'a yi ta kai kanta har ta yarda a keta alfarmarta da gangan. Ƙara kallon Nabila tayi sai taga itama kallonta take yi, tausayinta ne taji ya kamata ganin yadda lokaci guda gaba ɗaya ta canja, kamanninta sun sauya duk jikinta ya yamushe kamar wacce tayi sati jikinta bai ga ruwa ba. Wani irin kallo Zainab take yi mata cikin ranta tana ayyana 'kada dai ace' sai kuma tayi maza ta kawar da wannan tunanin. Har ta buɗe baki zata sake yi mata magana sai kuma taji ba zata iya ba don tunanin da tayi ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, fita kawai tayi daga ɗakin tana girgiza kai cikin ranta tana fatan kada Allah ya tabbatar da abinda zuciyarta ta saƙa mata yanzun nan.

***** Duk wani abu da Bello ya bar mata sun tasarwa ƙarewa gashi shiru har ana neman wata biyu da tafiyarshi tata tafiyar bata samu ba, tun yana yi mata daɗin baki da alƙawura akan akwai wasu shirye-shirye da yake yi yana gamawa zai yi mata shirin tafiya ta iskeshi har yazo ya daina sai ma wayarta da ba koyaushe yake ɗauka ba sai tayi ta kiranshi bata samu idan kuma tayi dacen samun shi to ba lallai ne ta samu ya amsa ba. Yanzu ma wayarta ta ɗauka ta danna mishi kira don kayan abincinta sun tasarwa ƙarewa dama kuɗaɗen da ya bar mata tuni suka ƙare saboda sayi banza sayi wofi data riƙa yi dole ta haƙura take cin abincin da Habi take girka musu. Har wayar ta katse bai ɗauka ba sai data ƙara kira sannan ya ɗauka daf da zata katse murya a cunkushe. Tana jin muryarshi ta fara masifa akan don me tana ta kiranshi yaƙi ya ɗauka, yana lallashinta ma yana ƙoƙarin yi mata bayani taƙi tsayawa ta saurare shi har sai da yayi spark ya fara yi mata masifa abinda bai taɓa yi mata ba tunda suka fara soyayya don haka bata san lokacin da tayi shiru ba tana mamakin wai yau ita Bello yake yiwa tsawa "Enough haba wai ke uwata ce?" Abinda ya faɗa kenan wanda ya sakata jin ta kasa magana. Shi ɗin ma ganin tayi shiru sai kuma ya sassauto yana cigaba da lallashinta akan akwai abinda yake shiryawa very soon itama zata biyoshi ta ƙara haƙuri kaɗan. A shagwaɓe tace "To ka turo mini wani abu mana kafin lokacin na faɗa maka kuɗaɗen hannuna fa duk sun ƙare." Kwantar da murya yayi yana bata haƙuri akan har yanzu ba'a fara biyanshi ba shi yasa bai turo mata komai ba tunda ya tafi shine ma dalilin da yasa har yanzu bai samu ya kama musu gidan da zasu zauna ba amma ana biyanshi zai ƙarasa shirin tafiyarta taje ta iskeshi don sosai yake missing ɗinta. Murmushi kawai take saki tana sauraren yadda yake ƙara fasa mata kai yana bayyana mata yadda yake jinta a cikin ranshi, basu ajiye wayar ba sai da katinta ya ƙare.

Yana sauke wayar daga kunnenshi ya saki wani dogon tsaki, yanzu har fargabar ganin kiran wayarta yake yi don yasan rigima kawai zasu yi shi yasa a mafi yawan lokuta yake ƙin amsa kiran nata don ƙarairayin da yake yi mata har sun fara ƙarewa ya fara rasa ƙaryar da zai yi mata akan dalilin daya hanata tafiya tuntuni bayan a yadda suka tsara bai fi yayi sati uku zuwa wata ɗaya ba zata bishi. Tunda yaje basu fara yin abinda ya kai su ba sai da aka yi musu wata test wacce da ita ne za'a tantance matakin da za'a ajiye kowanne daga cikinsu a lokacin basu fi sati ɗaya da tafiya ba, a wannan lokacin ya gane ba shi da wayo domin duk wasu zane da yake yi ada da taimakon Baqeer yake yi bai taɓa yin zane nashi na kanshi shi kaɗai ba tare da taimakon Baqeer ba don ko waɗanda yayi presenting a wurin gasar da tun asali Baqeer shi ne ya kamata yaje yayi munaƙisar da shi ya tafi a madadinshi da taimakon Baqeer ɗin ya zana su shi yasa har ya samu yin nasara a wajen gasar da tayi mishi sanadin tahowa bunƙasa ilimin shi a harkar zane sai dai tun ba'a je ko ina ba suka koreshi daga makarantar don sun ce baya da wata fasaha a harkar a taƙaice ma basu yarda takardun zanen da suka saka shi yin nasarar nashi ne ba, tun daga wannan lokacin yake gararanba yana buga-bugar neman yadda zai yi ya samu aikin da zai riƙe shi ko na taƙaitaccen lokaci ne ko ya tara abinda zai ishe shi ya dawo gida ya kama wata sana'ar don dai duk ɗan abinda ya tara ya tafi ne wajen shiryawa Asiya biki na garari na ƴan ƙarya irin wanda za'a daɗe ba'a daina zancen shi ba, to gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara ganin iyakar shi don zanen daya dogara dashi yake ganin shine zai zama silar arziƙinshi ya gane ashe shi ba komai bane a harkar idan har babu Baqeer a cikinta, a yanzu kuwa yasan ko giyar wake ya sha bai isa ya tunkari Baqeer da wani zancen daya danganci harkar zane ba bayan cin amana mafi muni da yayi mishi, ture batun auren Asiya da yayi bayan a irin son da yake yi mata da kuma tafiya wajen gasa a madadin shi tunda suka kai shi asibiti dama bai ƙara leƙa shi ba sai sau ɗaya shine kuma lokacin da yaji ƙaddarar data afka mishi yayi amfani da wannan damar ya tafi wajen gasar da yasan Baqeer ɗin yaci burin tafiya. A yadda abotarsu take da Baqeer yasan daya faɗa mishi cewar yana so yaje a maimakon shi tunda baya da lafiya wallahi ƙarfafa mishi gwiwa zai yi amma sai bai yi hakan ba ya zaɓi ya munafurce shi gashi abinda ya janyowa kanshi don yasan shi ba kowa bane idan har babu Baqeer. Baqeer ɗin da ya so shi da zuciya ɗaya ya aminta dashi ta inda bai ji ƙyashin koyar dashi duk wasu dabaru na sana'ar shi ta zane ba duk da ƙalubalen da yayi ta fuskanta daga wajen mahaifin shi akan baya son abotarsu amma ga da abinda ya saka mishi, tabbas bashi da kaico domin komai ya faru dashi shi ya janyowa kanshi.

*****

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull