Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 45

Baqeer complete - Chapter 45

Baqeer complete Chapter 45: Baqeer complete Chapter 45. Bayan yayi sallar asuba ya daɗe yana addu'oi tare da godewa Allah da al'amuranshi suke sake…

2,946 words

Bayan yayi sallar asuba ya daɗe yana addu'oi tare da godewa Allah da al'amuranshi suke sake daidaituwa, ji yake yi sai yanzu ne ma ya cika namiji tunda da kanshi yake neman kuɗi ba wai Baba ne yake tsaye akanshi ba, yayi karatun Alkur'ani sannan ya ɗan yi exercise na ƙafar shi, yanzu sosai yana jin ƙafar a jikinshi dkn har yatsun ƙafar shi ya fara iya motsawa, bayan ya gama komai ya dubi agoggo karfe bakwai da rabi gashi yau babu makaranta hakan yasa ya kwanta akan gado, wayarshi ya sake janyowa don tun kafin ya tashi yaga sakonta yace sai ya gama abinda yake zai yi mata reply. Fuskarshi ɗauke da murmushin da shi kanshi bai san yana yi ba ya rubuta "In kina so ki sani kizo wurin Dada ta sanar dake!" Ya kifa wayar tare da sa hannunshi a bayan kanshi, mamaki yake yi wai shine yake murmushi haka kawai inya tuno Zeey? To shi ya san tafi ƙarfinshi ya kuma san bai cancanci mace kamarta ba yana gurgu sannan ita me yayi mata? Ita kuwa abubuwan data mishi har ba zai iya ƙirgawa ba, a hankali yake lumshe ido yana buɗewa a haka bacci yayi gaba dashi. Can cikin baccinshi yake jiyo muryar Maryam ita da Hadiza, mamaki ne ya kamashi hakan yasa ya miƙe tare da duba agoggo karfe sha ɗaya na safe, haka ya tashi ya shirya sannan ya ɗauki wayarshi saƙonta ya gani akan in tazo kyautar me za'a mata? Ba tare da dogon tunani ba ya maida mata "Ƙawarki tazo kizo ku gaisa!" Yana kaiwa nan ya fita wurinsu Maryam wanda ganinshi yasa duk suka saki fara'a, wani irin jin daɗi ne ya kamasu don Maryam karyar ma tayi akan zata je wani taro a makarantarsu Areef ta samu ta gudo ganin Baqeer, har ga Allah bazata iya cigaba da daɗewa haka ba tare da ta ganshi ba, ita kuwa Hadiza dama ba hanata zai yi ba in dai yaji ba shi zai biya kuɗin adaidaita ba, haka suka shiga ɗakin Dada suka gyara shi tsaf sannan suka gyara na Baqeer suna tsokanarshi akan yanzu ya zama tailor don haka ɗinkin su na sallah na wuyanshi, murmushi kawai yayi yace "Ai ku kuma yanzu shikenan kun samu pass ku shirya har na mazajenku ma sai ai muku," ya ƙarasa maganar yana duba agoggon jikin wayarshi ya kamata Zeey tazo gashi ya ce mata Maryam na nan amma shiru, zuciyarshi tana so taga yanayin yanda zasu yi magana ita da Maryam har ya samu yaji ya alaƙarsu take daga nan ya bugi cikin Maryam akan me ta sani akan Zeey.

A bangaren Zee kuwa tunda taji labarin Maryam na nan ta san babu ita ba zuwa don tabbas in taje tasan shikenan Baqeer zai san ita wacece daga nan kuma alaƙarsu tasan tazo ƙarshe, gashi tana son ganin Baqeer, tsoro ne ya shiga yawo a zuciyarta kenan a haka zasu cigaba da alaƙa a sirrance? To alaƙar mecece tsakaninsu? Kanta ta kwantar saman pillow don bata san amsar da zuciyarta ke nema ba, Mummy ce ta turo ƙofar kallonta tayi bayan ta zauna kusa da ita tace "Ni kam yiwa yaron nan waya kice yazo ina son ganinshi don tabbas bazan taɓa yarda ya maida mini auta ta haka ba." Zeey ce ta dago tana kallonta aranta tace "Kema in kin san wanene ba barina zaki yi ba." Amma a fili sai cewa tayi "Mummy ban taɓa shakkar abu ba irin alaƙata tsakanina dashi, ban san matsayina a wueinshi ba, ban san ya zata kasance ba in har ya san ko ni wacece, Mummy shikenan rabuwa zai yi dani ko?" Da mamaki tace "In yasan ke wacece kamar ya? Akwai wata alaƙa ne tsakaninki dashi?" Kai ta kauda da sauri sannan tace "Ba haka nake nufi ba kawai dai kinga bai san komai nawa ba." Kai Mummy ta jinjina tace "Taso muje falo so nake muyi magana akan matar Kabir ina ga is time yayi settling Daddynki yana tunanin Zinnira ɗiyar oganshi." Saman goshinta ta ɗan daka tace "No wonder ashe neman auren dole kuke yi mishi shi yasa jiya ya dawo cikin wani yanayi, Mummy please ku ƙyaleshi ya zaɓi matar da yake so da kanshi." "Cikin wani yanayi kamar ya?" Tayi tambayar tana kallonta, baki ta taɓe tace "Aunty Nabs dai ta kareshi amma ni ban yarda ba am sure wani abun yayi ashe kune." Mummy bata ko tsaya jin ƙarashen maganar ba ta miƙe don dama maganar auren da take cewa yayi saboda Nabila ne tabbas bazata yarda da wannan haukan ba. Ƙofar ɗakin ta buɗe da karfi, akan kujera ta ganta a kishingiɗe tana danna waya, duk fuskarta ma taga ta sake ɗashewa, a fusace tace "Uban me ya haɗaki da Kabir har Zainab ta ganki?" Ta sani sarai bakin Zeey bazai yi shiru ba hakan yasa ta miƙe zaune tace "Bafa komai abu kawai na……." Yunƙurin amai ta fara yi, nan da nan Mummy hankalinta ya ƙara tashi, a fusace ta kalleta tace "Wuce muje asibiti wallahi bazaki ja mini abin kunyar da za'a dinga nuna ni ba sannan Kabir aure zan yi mishi don haka ki tattara ki bar gidan nan, na dai faɗa miki." Tana kaiwa nan ta juya, ga mamakinta Nabila biyota tayi waje tana dafa bango alamar jiri take ji, Mummy ce ta kalleta tace "Meye hakan kike yi? Ki koma ki kwashe kayanki yau zan maida ke da kaina ma…." Ƙarar data saki ne yasa Mummy tsayawa ta saki baki tana kallonta, Zeey ce ta fito da gudu tazo inda take, Nabila na ganin Zeey ta sulale a ƙasa tana riƙe ciki, hankali a tashe Zeey ta ƙaraso ta ɗagota tana cewa "Menene Aunty Nabs?" Hawaye ne ya zubo mata tace "Zeey ni kam tsintata akayi a titi hala? Wannan wace irin ƙiyayya ce ke tsakanin ya da ƙanwa? Ki taimaka ki kaini gidan Inna shi yasa sam bana son zuwa gidan nan, Mummynki ke kaɗai take son gani a gidan nan na gaji da gidan mu ayi ta wulakantani Zeey…" Fashewa tayi da wani irin kuka, Zee ta kalli Mummy cike da rashin jin daɗi tace "Wai don Allah Mummy me yasa kike haka? Sai kace bare? Ƙanwarki uwa ɗaya uba ɗaya tilo amma kin kasa kyautata mata?" Takaici ne ya rufe Mummy ganin yanda Nabila ke kuka wiwi, muryar Daddy suka ji yace "Ke Nabila tashi ki koma ciki ke kuma ki zo ina son magana dake." Bin bayanshi tayi don takaici ma ya hanata magana amma duk abinda za ayi sai dai ayi dole Nabila ta bar mata gida. Haka Daddy ya sata a gaba yana faɗa, jinshi kawai take yi don shi a duniya duk abinda zaka ce akan Nabila baya gani shi a kullum gani yake yi ma ba kowa ne ya kaita tarbiyya ba, yana gamawa ya fito ya shiga mota ya bar gidan zuciyarshi duk babu daɗi. Da ƙarfi driver ɗinshi ya ja birki ganin motar data kawo kai, wanda har saida Sulaiman Karaye ya ɗan bigi kujera kaɗan, driver ya juya yana bashi hakuri sannan ya kalli motar, kafin driver ɗin ya fita har shi mai ɗaya motar ya fito yana tafe yana riƙe ƙugu, glass ɗin ya ƙwanƙwasa hakan yasa drivern ya fita waje yana cewa "Yallaɓai kayi haƙuri ban kula ka taho bane." Wani kallo yayi mishi sannan yace "Eh da kasheni kayi ma kenan haƙuri zaka bawa iyalina? Ko?" Zai ƙara magana idanuwanshi suka kai kan Sulaiman dake zaune, wani mugun tamke fuska yayi yace "Da walaki ai tunda ka ɗauko ɓarawo ai dole dama idanunka ba zasu kula da hanya ba, aikin banza wallahi da kun bigeni da sai na kai ku ƙara wurin ƴan sanda, munafikai kawai." Sulaiman ne ya zuge glass yace "Ka tabbatar kaje asibiti an baka gado dkn da alama ƙusumbi ne ya fito a bayanka, kai Mamman mu tafi don Allah." Badaru takaici ya rufeshi yace "Kasan Allah ka shiga hankalinka dani, kafi kowa sanin tsaf zan ma tijara ni ba kunya gareni ba." "Tunda tsufa yayi gardama dama kai kam menene ma baza kayi ba?" Mamman ne ya shiga suka ja mota suka bar Badaru yana ta masifa da zage-zage, kwankwason shi ne yayi ƴar ƙara ya ja tsaki yace "Wallahi Kamalu sai kasan kayi dani."

***** Zeey kam da ƙyar ta samu ta lallashi Nabila ta daina kuka hakan yasa ta koma ɗaki takaici yasa ta ɗau key kawai tabar gidan tana ganin kiran Mummy amma taƙi ɗauka, Baqeer kawai take skn gani amma tsoron haɗuwarsu da Maryam take, ganin yamma ce yasa ta ɗauki waya tayi mishi text tace "Wani abu ya riƙeni kaɗan amma zanzo, suna nan dai ko?" Reply ya mata akan sun tafi, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta sauke tare da yin hamdallah sannan taja mota tayi gidan idanunta taf da ƙwalla, sam bata son wannan hatsaniyar dake faruwa tsakanin Mummy da Nabila, ace ƙanwarka amma kullum cikin faɗa? Waya ta ɗauka ta kira Nabila akan taji ya take ciki sai dai me? Nabila na dauka ta cigaba da kuka tana cewa "Zeey na shiga uku ina ji ciki ne dani kuma cikin….."ɗif kuma sai komai ya tsaya kamar an ƙwace wayar, gaban Zeey ne yayi wani irin faduwa da sauri taja gefen titi ta tsaya tare da dafa saman goshinta, ciki? Ciki? Ciki kamar ya? Jikinta ne kawai yake rawa sam ta kasa samun nutsuwa, wayarta ce ta fara ƙara ganin sunan Baqeer yasa ta ɗauka da sauri tana sauƙe ajiyar zuciya "Dama Dada ke cigiyarki tana son jin ko zaki zo?" Numfashi kawai yaji tana saukewa wanda nan da nan hankalinshi yayi mugun tashi yace "Zainab! Menene?" Kawai ji tayi ta kasa magana, nan fa hankalinshi yayi mugun tashi yace "Kina ina?" Hawayenta ta share tana son yin magana ta kasa, "Yi mini text ɗin inda kike." Yana kaiwa nan ya kashe wayar, ajiye takardun da yake zane yayi ya fara tura kekenshi cikin sauri, Dada na zaune tana cin abincin da su Hadiza suka dafa musu tuwo miyar zogale tana ci tana jin radio gefenta yarinyar maƙota ce da ta shigo tayata wanke-wanke itama an zuba mata tuwon tana ci, da mamaki take kallonshi tana cewa "Kai kuma sai ina?" Yanda taga yana tura keken da sauri ne ya bata mamaki yana tafiya yana cewa "Ina zuwa Dada." Da kallo ta bishi tana fatan Allah dai yasa lafiya…. Baqeer adaidaita ya tara yana jin gaba ɗaya hankalinshi ya tashi, meya sameta? Bayan yarinya ce da kullum fuskarta ke ɗauke da farin ciki da walwala? Ba dai Junaid bane? Haka ya isa inda ta kwatanta mishi ta text duk zuciyarshi babu daɗi, gaban motarta yace a ajiyeshi, kallon juna suka yi shi da ita dake cikin adaidaita ita tana mota, hawaye ne taji sun gangaro mata, da sauri ta fito ba tare da tace komai ba ta fito da wheelchair ɗin haka ya fito ya shiga ta turashi jikin mota sannan ya shiga ta sake nade wheelchair ɗin tasa a bayan mota sannan ta dawo ta zauna seat ɗin driver, kallon juna su kayi ga mamakinta kawai ta rasa abin cewa sai rauni da zuciyarta ke yi, anya bata da matsayi a zuciyar Baqeer kuwa, in ba haka ba taya zaizo daga sanar dashi? Kallonta yake yi kafin yace "Me ya sameki?" Hawaye ne suka zubo mata wanda tana ganin damuwa ƙiri-ƙiri cikin zuciyarshi yace "Menene? Junaid ne?" Wani kallo tayi mishi ta girgiza kai, yace "To wanene?" Kanta ta kwantar jikin kujera tana kallonshi tace "Ya Baqeer ban san ya zan yi ba, bana so naga Mummy na samun matsala da ƙanwarta sai na dinga ji kamar komai dalili na ne, don Inna tasha faɗa mini cewa nice na rabasu." Bai san kan zancen da take yi ba sai dai ya fahimci abin daga gida ne ya kuma gane inda matsalar take, yace "In ƙanwarta ce ko sun yi faɗa zasu shirya, Umma ma tana samun saɓani da ƴan uwanta amma suna shiryawa." Hawaye ta goge tace "Matsalar ina ga ta yanzu ba mai shiryuwa bace, sannan in Daddy yasan abinda ƙanwarta tayi Mummy ban san yadda zata yi ba….." ta ƙarasa maganar tana hawaye, idanunta tasa cikin nashi wanda suka cika taf da ƙwalla kana kallonshi kaga damuwarta tsantsa a ranshi, yace "Meya haɗa laifin ƙanwarta da nata? Sannan in har laifin babba ne ku samu kakanni ko magabata suyi magana kafin abun ya girma Wani abu ta haɗiya tana kallonshi yaji tace "Ba ita ta haifemu ba ni da yayana, shi yasa danginta basa sonmu."

Daga Umm Asghar har Ayusher kallonta suka yi ,yau me muke ji? Mai karatu kai fa? Ka taɓa kawo haka?

Ku biyo mu wasa farin girki🙌🏻

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Muhd Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN*

{60}

Cike da mamaki Baqeer yake kallonta ga kuma wani tausayi da take ƙara bashi ganin yau ce rana ta farko da yake ganin hawaye a fuskarta haka, zuciyarshi ce ke ingizashi akan yasa hannu ya share mata amma inaa ba zai iya ba, tissue ɗin dake ajiye tsakanin inda take da inda yake yasa hannu ya ɗauka, miƙa mata yayi ta ɗauki biyu ta goge fuskarta tana murmushin yaƙe tana cewa "Ya Baqeer am sorry....." Katseta yayi da cewa "Ki koma gida kiji me ke faruwa tukunna and then make a decision." Cike da rauni ta kalleshi sannan ta ɗaga mishi kai alamar to, shiru suka ɗan yi sai dai shi zuciyarshi cike take da tambayoyi amma baya son ya juye mata su yanzu saboda abinda ke damunta, cikin sanyin jiki yace "Birth mother ɗin ku fa?" Kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace "Tana raye sai dai ta sake wani auren a garinsu, ta sake haihuwar yara mata biyu." Ta ɗago tana kallonshi idanunta taf da ƙwalla tace "Amma na daɗe ban ganta ba kuma itama ba wai ta damu da mu bane." Shima idanuwanshi na cikin nata yace "Ita ta faɗa miki bata damu daku ba?" Yanayin kallonta ne ya canza ta maida idanunta ƙasa tana goge fuskarta tana cewa "Akwai abinda ba sai an faɗa ba kake ganewa, sannan ina da Mummy na har cikin raina a matsayin wacce ta haifeni nake ɗaukan ta don ƙaunar da take yi mana ta dabance a kanmu ta haƙura da neman haihuwa tace mu kaɗai mun isheta rayuwa ba sai ta nemi wasu ba." Ta ƙara kallonshi sannan tasa kanta a jikin stearing motar wani shauƙin ƙaunarshi na ƙara ratsata tace "Kana ganin duk da haka sai na dinga bibiyar wacce bata damu dani ba?" Ga mamakinta gani tayi ya ɗaga mata kai alamar eh, mamaki ne ya kamata tace "Why?" "Saboda ita ta haifeki, baki san uzurin ta ba baki san me yasa bata zuwa ba, sannan don tayi aure ta haihu ba shi zai sa ta daina sonku ba." Baki ta ɗan taɓe tace "Hmm baka san ta bane shi yasa, matar da ko waya bata yi mana taji ya muke? Ya Baqeer mu bar maganarta please, ni yanzu tsorona kada Mummy ta shiga wani hali a dalilin Nabila." Kallonta yake kawai bai ce komai ba, sai ma gani tayi ya maida hankalishi waje, baki ta turo tana neman sake zubo da ƙwalla, daidai nan ya waigo da sauri yace "Please kukan nan ya isa haka nan, bari na sauka kamar yadda nace ki koma gida kiji menene ya faru tukun." Baki ta turo tace "Bari na kai ka gida sai naje." "No kar ki damu zan hau adaidaita." Ido ta zuba mishi wanda har ya kalli waje ya sake kallonta yace "Me?" Kallo take mishi na sakalci da harara tace "Allah a'a ba saboda ni ka fito ba? Ni naga saurin zuwanka ma Ya Baqeer faɗa mini gaskiya a ruɗe ka iso ko?" Gyaran murya yayi yana ɗan gyara kwalar rigarshi cikin son ya waske yace "Dama ina waje sannan ni bana son harkar kuka." "Waje a ina kenan?" Kallonta yayi yace "Ba sai kinji ba uzuri na ne." A shagwaɓe tace "Ya Baqeer please ka bari na saukeka Allah it's not easy shiga adaidaita da wheelchair," ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya alamar lallashi, kai ya ɗaga alamar to, murmushi ta saki shima bai san sanda ya saki murmushi ba yana ɓoyewa don kar ta gani, motar ta kunna sannan suka fara tafiya, shiru suka ɗan yi kaɗan, baya son damunta da tambaya amma yana son yasan me yake faruwa a rayuwarta, ashe itama tana da nata matsalolin kawai dai bata nunawa ne, katse mishi tunani tayi da cewa "Baka fada minu me *ASF* ɗin yake nufi ba." "Dama an taɓa bada assignment a faɗi amsa ba tare da an gwada ba?" Ɗan kallonshi tayi tana dariya kaɗan tace "To ai haka ake yi in aka bada assignment a school ko baka san answer ba za'a sanar da kai sannan ba kace zaka fada mini ba?" "Yaushe kenan?" "Kai lallai ma Ya Baqeer Allah wayau zaka yi mini." Hannunshi yasa a aljihu bai ce komai ba, wata nutsuwa yake ji na ganin ta saki ranta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull