Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 44

Baqeer complete - Chapter 44

Baqeer complete Chapter 44: Baqeer complete Chapter 44. Hankali a tashe Mummy ta bita cikin ɗakin sai ta jiyo kakarin Nabila daga cikin toilet, cikin…

2,974 words

Hankali a tashe Mummy ta bita cikin ɗakin sai ta jiyo kakarin Nabila daga cikin toilet, cikin sassarfa ta faɗa banɗakin a take taji wani mugun rashin hankali da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba ya rufto mata lokaci guda ganin Nabila durƙushe a gaban toilet bowl tana kelaya amai. Muryarta na rawa tace "Ke Nabila baki da lafiya amma baki faɗa mini ba? Me ya same ki?" Ita dai Nabila babu baki don sosai ta galabaita da aman da take yi, kusa da ita Mummy ta matsa ta dafa kanta tana yi mata sannu sai dai a ƙarƙashin zuciyarta tana jin wani irin tsoro, tana tsoron kada tarihi ya maimaita kanshi akan Nabila. Da sauri ta kawar da wannan tunanin ta taimakawa Nabila bayan ta gama aman ta kuskure bakinta, tana riƙe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gado sannan ta ƙara kallonta, sai taga tayi mata wani irin fayau fuskar nan ta ɗashe tayi fari tas duk kuwa da Nabila ba fara bace, kalar fatarta chocolate color ce. Sannu ta ƙara yi mata sannan tace "Me ke damunki kuma tun yaushe ne baki da lafiya baki yi magana an kai ki asibiti ba sai ki zauna da ciwo. Ki tashi ki shirya na kai ki asibiti a dubaki, hankalina ba zai kwanta ba idan ba kai ki nayi aka duba mini lafiyarki ba." Gaba ɗaya jikinta yayi yaushi don haka ko magana bata son yi, da ƙyar ta iya buɗe baki tace wa Mummy "ai na samu sauƙi ba sai mun je asibiti ba, dama cikina ne yake ɗan murɗata amma tunda na samu nayi aman sosai naji relief, kawai dai hutawa nake son yi nasan daga na samu bacci na tashi gaba ɗaya nauyin jikin zai sakeni." Wani irin kallon tsaf Mummy tayi mata sai dai bata ce komai ba ta haɗiye abinda take ji a cikin ranta ta kaɗa kanta ta fita daga ɗakin bayan ta faɗawa Nabila lallai taci abincin da zata bayar a kawo mata kafin ta kwanta don bata son zama da yunwa. Tana barin ɗakin Nabila ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya data ke riƙe da ita tun shigowar Mummy ɗakin, gyara kwanciyarta tayi ta janyo wayarta tana kiran layin Kabir sai dai har ta ƙara i rurinta bai ɗaga ba, sake kiranshi tayi amma har ta katse bai ɗauka ba, ajiye wayar tayi akan bedside drawer, dama tasan zai yi wuya Kabir ya amsa kiranta a yanzu da yake ƙoƙarin yakiceta daga jikinshi ta kowane hali sai dai ita kuma babu niyyar barin shi a tare da ita, bata fara don ta daina ba don haka sai dai yayi kauce-kaucen shi ya gama amma dole ya dawo wajenta don bata shirya haƙura dashi ba.

***** Sai da Badaru yayi kwana biyu yana jinyar jikinshi kafin ya warware, Jamila ce tayi fama da jinyar a gefe guda kuma tana ƙara yi mishi famfo tana nuna kamar duk gidan babu wanda ya damu dashi idan ba ita da ƴaƴanta ba. Yana samun kanshi ya tada tijara ko Kamalu ya fito mishi da takardun filinshi ko su fice su bar mishi gida daga shi har Abu data take ɗaure mishi yana yi mishi sata, sai dai fa daga nesa yake duk wata tijara tashi ko kusa da Abu bai je ba bare Kamalu don yana tairon kada ya taɓa ita kanta Abun Kamalu yayi mishi ƙamshin mutuwa don yaga alamar babu imani a tattare dashi tunda har zai iya saka hannu yana neman lahanta shi in banda Allah ya kiyaye. Yana daga ƙofar ɗakinshi yace "Kinga Abu tun muna shaida juna ki faɗawa ɗanki ya fito mini da takardun fili na idan ba haka ba alƙali ne zai rabani daku don wallahi bazan yarda na ɗauki asara ba, haka kurum don rashin tausayi tun yana yi mini ɗauki ɗaiɗaya a shago har ya fara biyo ƴan kadarorina yana kaɗarwa, to bazan lamunta ba tunda dai bada uban kowa na haɗa na nemi kuɗina ba ah to." "Ba dai ubana kake neman ka zaga ba dai ko Mallam?" Tayi maganar cikin ɗaga murya don Kamaku yana ɗakinshi a kwance tana fatan ya jiyota ko ya fito Mallam ya ganshi tunda ta lura kamar yanzu tsoron Kamalun yake ji. Kamar yasan abinda take shirya mishi ya waiwaya ya kalli hanyar soron gidan inda ɗakin na Kamalu yake, murya ƙasa-ƙasa kamar ba shine yake hayagagar nan ba yace "ke fa da neman magana kike, Kawun nawa zan zaga don baki da hankali to na zagi Kawu nace na zagi wa. Ni dai ki lallaɓa ɗanki don Allah ku fito mini da takardun nan ko na samu na ƙara jari idan ba haka ba wata rana abincin da zamu ci ma sai ya gagare mu don kullum kasuwar tawa ƙara ƙasa take yi." Sai data murguɗa baki gefe sannan tace "Wai har yanzu kana nan akan bakanka na Kamalu ne ya ɗauke maka takardun fili? Haba Mallam to Kamalu ya sace maka takardun fili yayi me dasu? Gaskiya ka nemi ɓarawon filinka a wani wuri amma ba Kamalu ba don ni dai babu ɓarawo a ɗakina." Takaici ne yasa Badaru kasa sake cewa komai amma ba don ya haƙura ba don ya lura kamar da haɗin bakin Abu Kamalu yake yi mishi sata shi yasa bata so ana faɗa amma wallahi akan takardun filin nan tsaf zai ture zumuncinsu a gefe ya shigar da ƙararsu har ita Abun a wajen alƙali har sai sun fito mishi da takardun shi don kuwa dai ba yarda zai yi ba. Duk abinda suke yi Umma na daga ɗakinta tana jin su, da har zata faɗawa Badaru gaskiya ita ta ɗaukarwa Baqeer takardun filinshi ta kai mishi kuma har ya sayar yayi amfanin da zai yi da kuɗin don ya daina ƙalawa mutane sata sai dai ta rabu dashi don ba yanzu take son yasan ita ta ɗauka ta bawa Baqeer ba don a yadda ya manta yana da ɗa mai wannan sunan ba taso ya tuna dashi har sai a gaba zuwa lokacin da zai yi dana sanin da baza tayi mishi amfani ba. Tashi tayi ta karo ƙofar ɗakinta ta rufe don bama taso ta dinga jin tashin muryarsu daga nan inda take, zama tayi ta ɗauki radio ɗinta ta kunna tana sauraren shirye-shiryen da ake gabatarwa a lokacin.

***** Tun ɗazu take dakon dawowarshi har kusan ƙarfe sha ɗay da rabi na dare sannan taji ƙarar buɗe gate, sai taji tsayuwar mitarshi har ma da fitarshi daga cikin motar ya rufe sannan ta tashi cikin sanɗa ta fita ta samu wuri daidai ƙofar ɗakin shi ta inda ba zai ganeta ba saboda duhu gashi fitilun wajen duk a kashe suke. Ta gabanta ya wuce sai dai sam bai lura da ita ba har yasa makulli ya buɗe ƙofar ɗakinshi ya shige da sauri kamar mai gudun kada wani ya ganshi sai dai abinda bai sani ba shine wacce yake gujewa na biye da shi a baya, ya turo ƙofar zai rufe tayi sauri tasa hannu ta tare, gabanshi ne ya faɗi daya ganta a daidai wannan lokacin. Sakar mata ƙofar yayi kawai ya koma cikin ɗakin don har ya gaji da yawan yin jayayya da ita tunda yayi-yayi da ita ta fahimci babu wani alfanu a cikun taraiyarshi da ita ta kasa ganewa. Uffan bai ce mata ba ya ɗebi kayan baccin shi ya shige banɗaki ya rufe ƙofar haɗe da saka mata key don yasan a yadda Nabila ta mayar da kanta ƙadan da aikinta ne yaga ta shigo mishi banɗaki alhalin tasan wanka yake yi. A cikin banɗakin yayi wanka ya shirya sannan ya buɗe ya fito, bai yi mamaki ba da yaga har wannan lokacin Nabila na zaune a cikin ɗakinshi bata da alamun tashi ta fita. Sai da ya gama dukkan wasu al'adun ahi na kwanciya sannan yazo ya zauna a bakin gadon yace "Ya aka yi?" Yana ɗage mata gira da sigar tambaya. Kallinshi tayi taga yadda yake kawar da kai baya so ko ido su haɗa saboda yadda ta takura rayuwarshi tace "tun safe nake jiran dawowarka saboda ina da wata muhimmiyar magana da nake so muyi har kiranka nayi a waya don naji lokacin da zaka dawo amma baka ɗauka ba."

A kaikaice ya kalleta yaga yadda ta mayar da hankalinta gaba ɗaya a kanshi ya kawar da kai sannan yace "wacce irin magana kenan? Wai don Allah Nabila me yasa ba zaki sama mini lafiya bane? Nace miki ba zai yiwu mu gina wata alaƙa a tsakaninmu ba bayan mun san dangantakar dake tsakaninmu saboda Allah me yasa ba zaki fahimta bane?" Wani malalacin murmushi ta saki irin na takaici, sai da tasa hannu ta ɗauke wasu sirararan hawaye da suka biyo kuncinta sannan ta juyo ta kalleshi muryarta na rawa tace "ni na daɗe da sanin baka ɗaukeni a yadda ni na ɗauke ka ba Kb to amma ya zanyi? Bani na ɗaurawa kaina ba Allah ne ya ɗaura mini sai dai ni ba abinda ya kawoni wajenka ba kenan abinda ya kawoni daban da wanda kake tunani." Kallonshi tayi sosai taga hankalinshi ya dawo kanta kafin tace "banga period ɗina ba wannan watan abinda yasa nake zaton ciki ne dani." Wani irin sanyi ne Kabir yaji yana ratsa shi kamar wanda aka yiwa wanka da ruwan ƙanƙara, me Nabila take so ta faɗa mishi? Anya kuwa ba mafarki yake yi ba don shi dai ba zai iya tuna wani abu ya shiga tsakaninsu ba duk da dai ita ta musanta amma ta yaya za'a yi ace yayi abu ba tare da yasan yayi ba, shi ko a cikin bacci bai ji alamar yayi abu makamancin wanda ita tace sun yi ba to ta yaya zata yi ciki bayan shi bai ji wani alamu na wani abu ya faru tsakaninsu ba. Wani kakkauran yawu ya haɗiya da ƙyar ya iya ƙwato muryarshi yace "Kin kuwa san abinda kike faɗa? Wane irin ciki kuma Nabila? Kin ma tabbatar lokacin period ɗin naki yayi? Nifa har yau ban yarda wani abu makamancin wanda kike faɗa ya faru a tsakaninmu ba don har yau ban iya tuna lokacin da hakan ya faru ba to ta yaya zaki ce wai kina da ciki alhalin ni dai nasan babu wani abu daya shiga tsakaninmu." Bata san lokacin da ta saki kukan da take riƙewa ba duk yau, kuka tayi mai yawa tana jin wani irin ƙunci a cikin zuciyarta. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan ta ɗago idanun da suka rike suka yi jawur dasu kamar an ɗiga musu barkono tace "Kana nufin ƙarya zan yi maka kenan ko me?" Murya na rawa don hankalinshi idan yayi dubu ya tashi yace "Nifa ban ce ƙarya kike yi ba kawai dai na kasa tuna lokacin da hakan ya faru a tsakaninmu gashi kuma kina cewa wai ciki ne dake." "Wai ne ma?" Ta tambayeshi idanunta na ƙara tara ruwan hawaye, hannu tasa ta ɗauke hawayen kafin tace "kasan dai ko ina ƙarya bazan yi irin wannan ba wacce zata janyo mini zubewar mutunci da ƙimata ta ɗiya mace, bana jin daɗi Kb yanzu kwata-kwata ko abinci bana iya ci ba tare dana amayar dashi ba gashi yanzu har Mummy ta fara gane halin da nake ciki, yanzu ya zan yi idan aka gane ciki ne dani Kabir?" Ta ƙarashe maganar tana mai fashewa da wani irin kuka da yake fitowa daga ƙarƙashin zuciyarta. Ita dai soyayya bata yi mata adalci domin kuwa gashi ta kaita ta baro, bata tsinci komai a cikinta ba sai dana sani. Shi kanshi Kabir ji yayi gaba ɗaya hankalinshi ya tashi, gajiyar daya kwaso ma tuni ya nemeta ya rasa don wannan tashin hankalin yafi gaban gajiyar da yake ji a jikinshi. Komawa yayi ya zauna akan gadonshi suna facing juna, ya rasa wacce irin shawara ya kamata su yanke, tabbas bai kamata su bari wannan maganar ta fito ba don ba mutuncinsu ne kaɗai zai zube ba har da na iyayensu, yasan yanzu idan maganar nan ta fasu a gari haka za'a yi ta yawo dasu a social media bare idan aka ji dangantakar dake tsakaninsu. Sun jima a zaune shiru kowanne da abinda yake saƙawa a cikin ranshi sun kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi bare su tsara wacce zata fishe su. Agogon ɗakin ne ya buga ƙararraar dake alamta ƙarfe ɗayan dare tayi abinda ya dawo da hankulansu jikinsu. Kallon Nabila Kabir yayi yace "to ko zuwa zamu yi a zubar don kin san dai bai kamata mu bari wannan maganar ta fita ba ko?" Tashi tayi tsaye dafe da ƙirji tace "a zubar kuma? Bayan ance mutuwa ake yi idan anje zubarwa." Shima miƙewar yayi yana jin takaicinta na neman kamashi ganin ita ta janyo musu shiga cikin wannan halin sannan kuma ya samo musu mafitar da yake ganin ita ce daidai tana neman ta kawo mishi tangarɗa. Ɗan ɗaga muryarshi yayi duk kuwa da cewa dare ne baya raina sauti yace "to me kike son ayi yanzu idan ba'a zubar ba?" A sanyaye tace "ka yiwa Daddy maganar aurenmu tun kafin...." "What?" Ya katseta a fusace jin maganar da take yi mai kama da a cikin tatsuniya ake yinta.....

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA TARA*

{59}

Hannunshi ta kamo tace "KB tsoro nake yi wallahi, don Allah kazo muje mu yiwa Daddy magana shi zai fahimci soyayya ce ta saka mu…." Fincike hannunshi yayi ranshi na ƙara ɓaci ya shiga jinjina kai yana cewa "Eh lallai na tabbatar kanki ba ƙalau ba, nama gama lura so kike yi mutane su fara nuna mu, sannan kina nufin Daddy shine zai bi bayanki? Shaye-shaye kike yi? To wallahi ki shirya gobe muje asibiti ki zubar da cikin nan, kin ji na faɗa miki, ni ba mahaukaci bane in ke baki da hankali." Yana kaiwa nan yasa hannu ya jata ya turata waje ya kulle ƙofar shi, hawaye ne suka gangaro kan saman kuncinta a hankali tasa hannu ta share, tana juyawa zata wuce suka yi ido biyu da Zeey wacce ta tashi daga bacci ta nemi charger ɗin wayarta ta rasa, shine tayi tunanin duba ɗakin Nabila, tayi mamaki data shiga taga bata ɗakin don har toilet ɗin ɗakin a buɗe yake bare tayi tunanin ko tana ciki, haka ta fito cike da mamakin inda taje kawai taga Kabir ya buɗe ƙofa kafin tayi wani tunani taga ya turo Nabila, mamaki ne ya ƙara rufeta bayan sun haɗa ido, ta ɗan harɗe hannu tace "Aunty Nabs me kike yi a ɗakin Yaya a daren nan?" Gaban Nabila ne yake wani irin faɗuwa don ko Mummy bata shakkar ta ganta sama da Zeey don tasan bakinta ba shiru yake yi ba. Murmushin yaƙe tayi ta matso inda take da sauri cike da maganar raɗa tace "KB ina ji ya sha wani abu ne a waje ya shigo ciki ba a hayyacinshi ba shine ni kuma na tashi fitsari naji motsi na taimaka na kaishi ɗaki," ta ƙarasa maganar tana ɗan kauda kai, mamaki ne ya kama Zeey tace "Are you serious? Shaye-shaye ya koma?" Bata jira Nabila ta bata amsa ba ta fara neman yin ɗakin Kabir cikin ɓacin rai, da sauri tasa hannu ta riƙo ta tace "Ina zaki? Bafa nufina shan wani abu na shaye-shaye ba wani abu ya sha shine cikinshi ke yi mishi ciwo." Tsaki Zeey tayi tace "Karfa ki maidani wata mara wayau please, in naje na tambayeshi zan ji me ke faruwa." Hankalin Nabila ne ya tashi ganin da gaske Zee ɗakin zata je, kuma tasan tabbas Kabir yaji harda sharri take yi mishi to fa ita dashi tasan sun ƙara yin hannun riga, ƙafarta ta riƙe da sauri tace "Zeey ƙafata," kasancewar dare ne yasa tayi maganar a hankali, da sauri Zeey ta dawo ta ɗagota tana cewa "Bigewa kika yi?" Ta ɗaga kai tana alamun shishitu don kar a jiyo su, tare suka koma ɗaki ta kwanta a kan gado tana cewa "Wasa fa nake miki ɗazu dama so nake naga yanda zaki yi ne, saƙo aka bani shine na bashi." Wata nannauyiyar ajiyar zuciya Zeey ta sauke tace "Allah har hankalina ya tashi, kin san dai na tsani shaye-shaye bare mai yi in har Yayana ya fara hankalina tashi zai yi." Murmushi tayi tace "Kema kin san ba zai fara ba balle Daddy ne zai barshi?" Wani kallo Zeey ta mata sai suka yi murmushi a tare, fitowa Zeey tayi ta koma ɗaki, idanu ta rufe a hankali tana hango fuskar Baqeer, wayarta ta ɗauka ta zubawa sunanshi ido, ya ɓata mata rai shi yasa ba zata je ta ganshi ba duk da sun shirya gwara ta nuna mishi ita ma tana fushi, amma me ASF take nufi? Abinda yazo mata kenan kawai ta shiga goggle ta dinga searching ana bata wasu ma'anoni da duk ta kasa ganewa, haka ta kwanta duk ranta a ɓace na son tasan me Baqeer yake nufi, juyi tayi sai kuma ta ɗauki waya taga karfe 1 na dare, saƙo ta tura mishi "Ya Baqeer menene *ASF*? Nifa ka sanyani a duhu Allah zan yi kuka." Tana kaiwa nan ta kifa wayar bayan ta jonata a charge don tasan bacci yake yi.

******

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull