Baqeer complete - Chapter 43
Baqeer complete Chapter 43: Baqeer complete Chapter 43. ****** Baqeer kam komai Alhamdulila dan ya turawa mutanen nan zane nan kai tsaye sukace komai yayi…
3,242 words
****** Baqeer kam komai Alhamdulila dan ya turawa mutanen nan zane nan kai tsaye sukace komai yayi akan zasu turo mai kuɗi, sunyi mamakin kwarewarshi dan shi kanshi yanzu yasan kwarewarshi tafi ta da saboda karatun da yake yi yanzu, yanka kuwa inya maka shi lalai sai ka dauka wanda ya shekara biyar yana ɗinki ne, haryanzu dai matsalarshi ɗaya itace ta taka keken ɗinki wanda Tanimu ke taimaka mai suma makarantar basu damu ba saboda su kansu mamakin kwarewarshi a yanka da fitar da styles suke, yau suna tasowa yai tunanin wucewa asibitin Junaid dan yanada appointment da physio ɗin dake taimaka mai, da yamma wajen hudu suka isa anan unguwar sukai sallah sannan suka ƙarasa shi da Tanimu suna tafe ba wanda yakewa wani magana dan Baqeer ba kasafai yake zance ba shi kuma Tanimu bai fiya san damunshi da hira ba, wannan dalilin ne yasa zamansu ya ƙara kwari, a bakin gate ɗin suna shiga ya canza yanayin fuskarsa sakamakon motar Zee daya gani, bayan yau kwana biyu kenan bai sata a idanshi ba amma shine zai ganta gun saurayinta? Fuskarnan tasa ta sake murtukewa da yaso ma yace su juya ya fasa dole ma ya shiga ya nuna ya ganta. Kasan ranshi ne ya tambayeshi to in ka ganta sai akai me? Auranka ne akanta ko kuwa soyayya kuke? Bai gama tunani ba yaji Tanimu na cemai "Ya Baqeer mukaje wancan satin zamu?" Kallanshi yai wani abu na sake tasomai yana bin office din Junaid da kallo, kawai ya fara tura kekenshi zuwa office ɗin Junaid sai daya kusa isa aka budo ƙofar office ɗin da sauri ya fara neman shan kwana, ganin haka yasa Tanimu ya taimaka mai, dariyar Zee ya fara juyowa tana cewa "Kai dai wallahi baka rabuwa da neman magana, nidai Allah na faɗa ma kasan yanda zakai ka dai san halina ba mai tilastamin in banyi niyyar abu ba," ta ƙarasa maganar tana kallan Tanimu, kai taɗan karkatar Junaid ne yace "Hmm ina mamakin yanda bakya tunanin halin da zan shiga kike faɗar abinda ke ranki, ki koma mu gama magana please bansan saurin me kike ba." Ganin yanayinta yasa yasan batama san me yake cewa ba, hakan yasa ya tsaya gurum yana kallanta, Baqeer jin kalaman Junaid yasa ya cigaba da tura kekensa, Tanimu na biye dashi, itama Zeey bayansu tabi tana tafe tana murmushi, Tanimu ne ya kalleta cike da jin daɗi ya gaisheta, tana murmushi ta amsa tace "Kanin Ya Baqeer ashe kuna hanya?" Tai maganar tana kallan bayan Baqeer, tsayawa da tura keken yai yanajin yana san ganinta amma kishi ya hanashi, Junaid kuwa cike da takaici ya biyota dan shi ya tsani yaga tanaba gurgun nan mahimmanci, ganin Baqeer baice komai ba ya cigaba da tafiyarsa itama yasa ta kalli Tanimu tace "Daga makaranta?" Kai ya ɗaga sannan yace "Ko gida bamu koma ba." Ta jinjina kai tana cewa "Shi kuma yayan naka yau bayajin yin magana ne?" Junaid yai saurin cewa "Malam Baqeer ashe kana tafe, muje yau ni zan dubaka ma." Kallanshi Baqeer yai sai a lokacin idanunsa suka haɗu dana Zainab, da sauri ya ɗauke idanshi, mamaki ya ƙara kamata ganin ko jiya sunyi waya menene hakan? Me kuma ya faru? Haka sukabi Junaid nan ya dinga sashi yin exercises kala, kala yana ɗan taimaka mai, suna gamawa ya kalli Zeey yace "Paper towel please kiga harna haɗa gumi." Daukowa tai ta mikamai, idanunta nakan Baqeer da ko kallanta yakiyi, wato shi bataga gumin da yakeyi ba shima? Saurayinta kawai ta sani? Kallan Junaid yai yace "Mungode sosai!" "No karka damu, Allah ya kara sauki it seems like kana abubuwan daya kamata am sure we will get there." Kai ya jinjina kawai ya tura kekensa, Zee ta mike zata bishi yaji Junaid yace "Zeey yauwa tunda kin dawo bari ma na nuna miki abu, da na ɗauka sauri kike ashe baki gaji da ganina ba." Waigowa Baqeer yai idanunsa na kanta, kishi yake? San gwadashi taji tanayi tace "J kaima kasan anything for you, nunamin." Idanun Baqeer ne sukai jaa wani abu yaji ya tokareshi, kallan Tanimu yai yamai alama kawai su fita, da kallo ta bishi suna fita ta kalli Junaid tace "Bye." Hannu yasa ya riko hannunta da sauri yace "Zeey wai meke damunki? Menene tsakaninki da gurguncan? Kedai nasan kinfi ƙarfin gurgu shiyasa nake ta ƙoƙarin ganin na cire shirman tunanin nan a raina but yanda kike be having akanshi yana tsoratani." Hannunta daya rike ta kalla wanda hakan ya sashi sakinta tace "J karka sa alaka ta zumincin dake tsakanina dakai ta kare, sannan kalamanka duka ka jira amsar da zan baka a kansu for now banda lokacin ka." Tana kai nan ta juya ta fita, ranta a ɓace tana jin kalaman daya Baqeer ma sunfi wanda ya mata ɓata mata rai.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BAKWAI*
{57}
A waje ta gansu suna neman tarar adaidaita, gabansu ta tsaya tace "Mu wuce Ya Baqeer?" Kai ya kauda yana dube-duben abin hawa, mamaki ya ƙara kamata gani take ko kishi ne ai bai kamata ya ɗin ga banza da ita haka ba, Zee kamar ke ana binki kina wulakanta mutane yau kece kike bi ana wulakantaki? Ido ta kafamai, haka kawai ya juyo yaji zuciyarsa nasan ganinta, kallan juna sukai nan danan idanuwanta suka ciciko kallanta yai shima sai kuma hankalinshi ya tashi, meya mata? Ya ɗauka barinta da saurayinta shine daidai? Jan motar tai kawai ba tare da tace komai ba tai gaba, jiki a sanyaye yabi motar da kallo, wata iska ya furzar yanajin haushin kansa, to menene laifinta? Ai tun farko yadai san Junaid saurayinta ne to jin haushin na menene? Meya sameshi? Haushin kanshi ne ya isheshi har suka isa gida baice komai ba, Dada tana zaune a waje tana jin radio yau lale na dungurmi irin na tsofafi yarinyar makota tazo ta mata tace ta bari sai dare amma yarinyar ta nace akan sai ta mata yanzu, hakan yasa ta kyaleta, ganinsu Baqeer yasa ta saki fuska ta ɗan rage sautin radio ɗin tana cewa "A'a Malam cunkumi an dawo?" "Sannu da gida Dada, amma cunkumin na menene?" "Yo fuska ce kamar an aiko ma da sakon mutuwa me kake so a kiraka dashi?" "Babu." Abinda yace kenan yai cikin ɗaki, Tanimu ne ya kalleta yana gaisheta ta girgiza kai tace "Hala an taboshi ne?" Ya girgiza kai yana cewa "Wallahi ban sani ba Dada." Baki ta taɓe tace "Bakinku ɗaya ai can ku kuka sani." Ta cigaba da sauraran radio ɗinta tana cewa "Ga abincinka can Tanimu." Ɗaukan na Baqeer yai ya fara kai mai sannan ya ɗau nashi yai godiya ya fita. Takaici duk ya gama isar Baqeer me take nufi da kallan datamai da kuma hawayen dake idanunta? Bayan ita kullum cikin fara'a take? Sam zuciyarshi ta kasa nutsuwa ji yake kamar yaje ya sameta yaji meke faruwa.
**** Zeey kuwa gida ta wuce kai tsaye, tana shiga ta ruga ciki tai falan Mumy, Nabeela na falansu tana ganinta ta girgiza kai sai kuma ta canza yanayin fuskarta sannan ta mike tana cewa "Zeey lafiya? Menene?" Bata ko kulata ba sai ɗakin Mumy datai, a tsaye ta ganta tana ninke sallaya da alama lokacin tai sallar la'asar, rungumeta kawai tai tasa kuka, mamaki ne ya kama Mumy ta kalli Nabeela dake bakin ƙofa ta mata alama data tafi, hakan yasa ta juya tana taɓe baki, kallanta Mumy tai bayan sun zauna a bakin gado ta ɗag fuskarta tace "Menene Baby na? Waye ya taɓamin ke?" Kara kankameta tai wanda hakan yasa Mumy tace "Babu wanda ya isa ya samin ke kuka in kyaleshi, Junaid ɗin da kikace zaki je kija mai kune ne wani abin ya faru?" Cike da shagwaba tace "J har isa ya sani kuka Mumy kema kinsan bai kai ba, sannan kunne fa naje jamai akan ya dakatar da iyayensa dan ni bazan aureshi ba." "To meya faru kuma? Nifa kukan ne bazan ɗauka ba." Kwantawa tai luf tana cewa "Mumy ni kawai haushin kaina nakeji, inyi ta bada kaina amma yana wulakantani, haka zan cigaba da rayuwa?" "To ki rabu dashi mana dole ne? Nifa bamga wanda ya isa ya cigaba da samin ke kuma ina kyaleshi ba." Dagowa tai tace "Shine bazan iya ba Mumy yanzun ma ganin yanda ya kalleni ne yasa naji ina neman yin hawaye, anya Mumy kaina kalau kuwa? Bayan ko kalmar so bai taɓa furtamin ba?" Shafar kanta tai tace "Zeey ya kikeso nai dake? Haka kikeso na cigaba da sa miki ido kina wannan san haukan? To shi bama ki da tabbas yana sanki kenan?" Kallan Mumy tai idanunta yai raurau tace "Inadai ganin alama." "Alama shine ya barmin ke ki taho gida kina kuka? Bani numbershi." Nan danan ta zaro ido tace "A'a Mumy abinfa baikai haka ba, kawai dai haushin yanda bai kulani bane yasa naji zafi amma zamu shirya." "Zeey kinsan dai ko kowa a duniya zai gujeki ina bayanki ko? Banasan ki dinga kaskantar da kanki dan Allah ki cigaba da zama Zainab dana sani wace bata barin abu ya dameta." Kai ta ɗaga ta rungumeta tace "Insha Allahu Mumy na, thank you."
Ya dade a ƙofa yana san shigowa amma baisan Nabila ta ganshi ba dan takardun abokinsa daya manta ba tabbas da bazai dawo ba, sam taki tashi daga falan, ganin Zeey ta shigo da mota yasa ya ɓoye da sauri, yana kallo ta shiga Nabila ta bita yasa yai saurin lalaɓowa ya shigo, ɗakin sa yai ya ɗauko takardun sai dai yana buɗe ƙofa yaga Nabila a tsaye ta rike kugu, turashi tai cikin ɗakin sannan ta shiga tasa key, kallanshi tai tace "Ya Kabir badai gudu na kakeyi ba?" Matsar da ita yai tare da yin hanyar ƙofa yana cewa "In gudun naki nake ma ai ba laifi tunda kina neman zama abin gudu." Yana kai nan yai saurin yin waje sam yana mamakin Nabila, tana daga cikin mutane masu hankali daya sani a mata amma baisan me ya sameta ba tunda ta fara nuna tana sanshi yake ganin wasu halaye nata da ke tsoratashi a kullum ana haɗata da Zeey sai dai ko kaffara bazaiyi ba Zeey ko tanasan mutum bazata bada kanta ba, dan tasha yin samari abokansa sai dai ba wanda ma taba fuskar soyayya bare akai ga yin waya, haka zasu karashi binta su hakura, a haka kuma Inna kullum mitarta Zeey batada tarbiyya Nabila ce mai tarbiyya shima kuma Dady kullum maganar kenan.
******** Badaru da tsamin jiki ya tashi dan ko sallah a gida yai, sai wani nishi yake yana wash-wash, Abu kam tun dare take nazari dan tasan Badaru bazai taɓa kyalesu ba daga ita har Kamalu, gashi kuma tunda ya fita jiya haryanzu bai dawo ba balle ta zaunar dashi suyi magana a samu mafita, ƙofa taji an buɗe wajen karfe shiga na safe da sauri ta leka wajen Kamalu ne ya shigo cikin sanda, lekowa tai tamai alama daya shigo ɗakinta hakan yasa ya shigo suka shige kuryar ɗaki, kallansa tai tace "Kamalu ina kake kai kayayyakin Malam da kake ɗauka kadai san bazai barmu ba balle abinda kamai ɗazu." Kallanta yai yace "Amma kina kallo shekani barzaho yaso yi?" "Na sani amma kai dai kasan halinshi, laifinka kawai zai gani ba nashi ba." Taja numfashi ta cigaba "Ina kayayakin daka ɗauka suke? Wai ma nikam Kamalu me kake da atamfofi da lasuka kamar mai tara lefe?" Kai ya kauda ya zauna a bakin gaso yace "Lefe nake tarawa sannan wai me yake min ma da zaice yamin a matsayinsa na uba?" Baki ta saki tace "Lalai Kamalu, lefe kake tarawa? Lefen uban wa kake tarawa da kudin sata?" Cike da ɓacin rai yace "Kinga Umma karki kuskura ki ƙara zaginta, ta wuce duk yanda kike tunani, Roshini dinace, sannan ba abinda zan dawo dashi wallahi sai dai yai abinda zaiyi." Yana kai nan ya mike ya fita daga ɗakin ya barta da baki a buɗe. Jamila ce tai sallama a ƙofar ɗakin Fatima, ta bata izinin shiga, zama tai tana kallan Fatima nata faman tsinke zogale tace "Fatima kinsan yarancan ya jawo Malam ciwo? Shine na zo in akwai ƴan canji a gunki ki bani na siyo mai magani dan jikinshi yayi tsami." Kallanta Umma tai tace "Dama garin neman faɗa da yara ake jawo raini, mutum sai masifa sam ba hakuri ba yadda da kaddara?" "To yanzu dai mu bar maganar ki bani kuɗi dan Malam yana warkewa sai ya hukunta Kamalu dole kuma musha kallo da guda." Wani kallan takaici Umma ta mata tace "Ke kina tunanin kin tsira kenan? Hmm kema kiyi a hankali daga ke har yaranki ba tsira kukai ba, sannan ni banida kuɗi ɗari biyar ce gata nan ki sai mai magani ita kenan gareni." Amsa Jamila tai ta fito tana cewa "Ko gidan ubanwa take samun kuɗi dan dai baza'ace kuɗin kujeru ne haryanzu take dashi ba." Magani ta siyowa Badaru ta bashi yasha tana cewa "Sai hakuri Malam, mata da yarane baka tara na kwarai ba banda ni na damu dakai da haka nan zasu kyaleka kudin magani wannan ba wanda ya iya taimakon mu dashi, yooo sannu wannan a cikinsu wanene yama?" Shi dai Badaru banda takaici ba abinda ke damunsa gashi ya kasa mikewa, a cike yake fam da kowa jira yake ya samu sauki duk sai yaci zarafinsu.
***** Wannan shine karo na ba adadi da Baqeer ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya ajiye, ganin da gaske ya kasa bacci gashi har karfe sha biyu da rabi yasa kawai ya danna ƙiran Zee, ya gashi da duba sunanta yana rufewa, kallan wayar yai ganin da gaske katsewa zatai ba ta ɗauka ba? Ji yai an ɗauka hakan yasa ya kara wayar a kunensa, ga mamakinsa kin magana tai, shima yai ɗan shiru ganin bazatai magana ba yasa yace "Ɗazu naga yanayinki ya canza wani abin ne?" Cike da mamakin kalamansa tace "Nima dazu naga yanayinka ya canza wani abin ne?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ni ba komai." "Nima!" Da sauri yace "No ke akwai abinda ya sameki." Shiru taɗan yi kaɗan kafin tace "Ya akai ka san abinda ya dameni? Bayan ba damuwa kai da yanayin da zan shiga ba?" Kalamanta ne yaji sun dakeshi, me take nufi bayan shi kanshi tsoron matsayin data samu a zuciyarshi yake? "Nasan kinje gun saurayinki so bansan ko abinda yafaru tsakaninku bane ya saki ɓacin rai." Sam baisan sanda kalmar saurayin ta fito daga bakinsa ba, kamar tace mai ba saurayinta bane kawai sai taji batasan faɗa tunda itama batasan menene matsayinta a gunshi ba hakan yasa tace "Wai J? Ni ko kaɗan ba shi ya ɓatan rai ba, ni bana ji ma ya taɓa min abinda zai sani ɓacin rai kawai bana san naga inama magana kana shareni ne, ɗazu abinda kamin ka kyauta? Kamar wanda mukai faɗa ko bamu san juna ba?" Kenan saboda shi ne? Tambayar datazo mai kenan hakan yasa yace "Kenan akai na ne?" Cike da shagwaba tace "Nifa banasan naga ina magana ana disgani gashi kuma a gaban Tanimu ka dinga wulakantani kallo na ma kin yi kai." Shiru yai saboda jin gaɓobin jikinshi sunyi laushi jin yanda take magana kamar mai shirin kuka. Sannan ta cigaba "Allah a faɗan me nai ko aban hakuri." Shidai bazai iya faɗar kishi yake ba, dan tabbas yanzu kam ya shaida kishi ne, kuma hakurin ma bai san badawa tunda yana gani ai an mai ba daidai bane yai, hakan yasa yace "Me kikeyi yanzu?" Tace "A kwance nake." Yace "Hmm akwai pen kusa dake?" Ɗan mikewa tai ta kulla side bed lamp dake gefen gado ta ɗauko da paper tana cewa "Zane za'a koyamin?" Yace "A'a rubutu." Da mamaki ta maimaita kalmar tana cewa "To na shirya." "Yauwa rubuta A" ta rubuta yace "Rubuta S," nan ma ta rubuta yace "Sai ki rubuta F" ta rubuta tana cewa "Sai me?" Yace "Shikenan" kallan abin tak tace "Asf? Me kenan?" Ka faɗa ya ɗaga yace "Ki bincika, ni zan kwanta." Kallan takardar ta sake yi tace "Hakurin fa Allah ba'a bani ba." "In kin san amsar ki dawo ki sanar dani zan baki." "To naji, amma Ya Baqeer please karka sake disgani cikin mutane kaki kulani." "Kema ki daina......." Sai kuma yai shiru ya kashe wayar da sauri, Baqeer me kake tunani? Badai kana gurgu kake neman jawo soyayyar wace ko a haka ka ganta kasan ƴar wani bace? Zee kuwa ta dade tana kallan takardar kafin ta kwanta, zuciyarta fess kamar ba itace sukai faɗa da Baqeer ba.
***** Kwance take a ɗaki Zeey ta shigo tace "Aunty Nabs tashi ki fadamin menene ma'anar kalmar nan?" Kasa magana tai sai sake lumshe ido take, Zeey tace "Nikam kalau kike?" Nabila ta sauke huci tace "Banajin daɗi Zeey ki duba google mana." Cike da kulawa tace "Me ya sameki?" Kai ya girgiza tare da cewa "Ban sani ba haka nan nake jina ba da ɗi." Da sauri Zeey ta kamo hanunta tace "Kila ma yunwa kike ji, muje Mumy na jiran mu muyi breakfast." Kamar bazata mike ba sai kuma ta tashi ta suka fito, zama tai Mumy ko kallanta batai ba sai Dady dake tsokanarta wai ina ta shige kwana biyu? Murmushi kawai tai suka fara cin abinci, Dady sai yaban Nabila yake Zeey kam baki ta taɓe tace "Bakomai Dady tunda nasan gun Mumy I'm the best." "Oho dai kuyi ta yi nidai na fadawa iyayen Junaid suzo muyi magana." Tunda ga haka bata sake magana ba harya gama ya tashi yai ɗaki, Zeey ta bishi akan zata mai magana. Mumy ce ta kalli Nabila da ta kasa cin abinci sai wani jujuyashi take tace "Wai meke damunki?" Ta buɗe baki zatai magana sai ta fara yunkurin amai, cike da mamaki Mumy tace "Meye hakan?" Nan ma zatai magana ta fara yunkurin amai, da sauri ta miƙe tai ɗaki tana sake yunkurowa, Mumy kasa ko motsawa tai sai kuma ta tashi da sauri har tana harɗewa tai ɗaki hankalinta a mugun tashe.
(Hmmm wai inji me ciwon baki.)
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA TAKWAS*
{58}