Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 42

Baqeer complete - Chapter 42

Baqeer complete Chapter 42: Baqeer complete Chapter 42. Yau tun safe ta tashi da aikin taliya da aka kawo mata daga nan maƙwabtansu za'a yi musu ta gara,…

3,382 words

Yau tun safe ta tashi da aikin taliya da aka kawo mata daga nan maƙwabtansu za'a yi musu ta gara, da yake tun bayan data sayawa Hadiza injin markaɗe da kuɗin kujerunta data sayar sauran ƙudin daya rafe sai ta sake sayen injin taliya ta koma kan sana'arta tunda dama ana ta zuwa nema. Yanzu ta ɗauke hankalinta daga kan mutanen gidan data lura babu abinda suke so da gani irin kasawarta ita da ƴaƴanta. Tana kallon Jamila dake girkin ranar sai kaiwa da kawowa take yi kamar me neman wani abu ita dai ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba, da fai ta lura ba kulata Umma zata yi ba sai ta matso kusa da ita cikin murya ƙasa-ƙasa kamar wacce bata so aji me zata ce tace mata "kin san nan Mallam yazo yana faɗa akan ana yi mishi sata ko?" Bata jira Umma ta amsa ba ta cigaba da cewa "to ashe dai Kamalu ne yake zuwa yana kwashe mishi kayan shago yana kawowa uwar ta ɓoye wai kayan lefe yake tarawa aure zai yi, ko wane sakarkarun iyayen ne zasu ɗauki ƴa su bashi bayan sun san ba nutsuwa gareshi ba, ai dai zamu sha kallo duk ranar da Mallam yasan su suke ɗaukar mishi kaya." Kallonta kawai Umma tayi ta mayar da kai akan aikin taliyarta don ita dama ba shiga irin waɗannan gulmace-gulmacen nasu take yi ba shi yasa suke jin haushinta don duk yadda ka kai da iya tsegumi bata taɓa tofa nata a ciki sai dai ta bisu da Allah ya kyauta kawai. Wucewa Jamila tayi tana cewa "Ai ke matsalarki kenan, babu dama a kawo miki ƴar magana ana so a ɗan tattauna dake sai kiyi wani girim kamar ba kya magana." Murmushi kawai tayi ta cigaba da aikinta, Jamila kenan. Ita yanzu har ta manta da yadda suke haɗe mata kai ita da Abu kowaccen su sai ta ɗauko gulmar ƴar uwarta ta rasa da wanda zata yi sannan suke sanin da zamanta, ko ance musu mahaukaciya ce ita da zata biye musu bayan tasan irin zaman da suke yi da ita. Tana gama aikinta ta tattare wurin ta gyara sannan tayi shigewarta ɗaki ta bar Jamila a wurin ta bita da harara, tana jin takaicin yadda Fatima ke yi musu sam bata shiga sabgar su duk abinda zasu yi mata bata magana sai in sun ƙureta sannan take maida martani ɗaya-biyu tayi shigewarta ɗaki ta barsu ta ciwon zuciya.

***** Tunda Bello ya tafi Germany ta saka ƴan kuɗaɗen daya bar mata a gaba tana sayi banza sayj wofi ko abincin da Habi take girka musu bata ci sai dai tayi order a kawo mata Habi ta fita ta karɓo, babu abinda take yi daga kwanciya sai kwanciya sai dai tayi wanka taci gayu ta naɗe akan kujera tana yawo akan social media, ita ce ig ita ce tiktok don whatsapp ma ba sosai take hawa ba sai idan zasu yi video call da Bello. Duk wani aikin gidan Habi ce ke yi dama can Asiya malalaciya ce bata son moruwa sam shi yasa ta sakarwa Habi aikin gidan nata gaba ɗaya duk da ba wani aikin kuzo mu gani bane tunda ba yaran da zasu ɓata wuri gareta ba. Idan Habi taga yadda take kashe kuɗi tayi magana sai ta rufeta da faɗa tace tana yi mata baƙin ciki don daga Allah ya ɗagata ta samu rayuwar hutu shine sai ta nuna ƙyashi da hassadarta to ta dai kusa tafiya ma ta bar mata ƙasar idan ta daina ganinta sai kuma taga da wanda zata yi, don haka Habi ta daina yi mata magana duk abinda tayi sai ta kawo idanu ta zuba mata.

***** A yanzu Baqeer ya samu nutsuwa ya samu kwanciyar hankali, har wata ƴar ƙiba yayi sanoda kwanciyar hankalin daya samu. Baya da matsalar komai saboda dai Alhamdulillah yana samun kuɗi da contract ɗin da yayi signing gashi kuma kamar kada yayi signing contract ɗin sai mutane suke ta nemanshi da son yayi musu designing ɗinkuna, ga mahaifiyarshi da yake yiwa aiken kuɗi akai-akai haka ƴan uwanshi ya cigaba da taimakonsu kamar da tun ma ba Hadiza ba da dama shine yake ɗauke da nauyin gidanta. Anan ɗin ma ya wadata Dada da dukkanin abun buƙata don baya jira sai ƴaƴanta sun kawo mata duk abinda yasa zata buƙata yana ƙoƙarin ganin ya ajiye mata, tun daga kan kayan abinci, kayan masarufi, fruits ne da duk dai wasu abubuwa da ya kamata, gashi lokaci zuwa lokaci yake turawa Umma kuɗi tayi mata miya ta bawa Salim ya kawo mata duk don ya rage mata ɗawainiyar da take yi dasu. Sosai yake tausaya mata ganin girma ya kamata gashi kuma komai na hidimar gidanta ita take yi ba mataimaki gareta ba sai yaran maƙwabta idan sun shigo waɗanda baka raba gidanta dasu. Har ɗan ƙaramin gas ya saya mata duk don ya sauƙaƙa mata ya rabata da hura wuta da itace. Kullum kuwa ta buɗi baki albarka take saka mishi tana addu'ar Allah ya yalwata arziƙinshi yasa albarka a cikin nemanshi ganin yayi mata abinda ƴaƴan data haifa basu yi mata ba. Yau yini yayi yana sketches daya gaji ne ya fito waje don yasha iska. Leƙawa yayi ɗakin Dada zai ce mata ya fita don kada tazo tana nemanshi bata ganshi ba sai ya ganta a zaune akan sallaya ta jingina da bango tana gyangyaɗi. "Dada" ya kira sunanta bata s bs da ya ɗan ɗaga murya ya ƙara kiranta sannan ta buɗe ido tace "na'am Baqeeru, wani abu kake so?" tana gyara zamanta. "Fita dama zan yi nace kada kizo kina nemana sai na tarar kina bacci, ai gara ki kwanta kada jikinki yayi ciwo kina bacci daga zaune". Girgiza kai tayi tace "ai yanzu na zan tashi na ɗora girki da yake ma ba wani aiki bane mai wahala tunda ka sayo wancan abun shi yasa ma har ka iskeni ina bacci, sai dai ka tsaya ka kunna mini murhun kafin ka fita kasan har yanzu ba sanin yadda zan kunna nayi ba". Ƴar dariya yayi yace "Ke dai kawai kice tsoro kike ji kada ki ƙone shi yasa ba kya iya kunnawa da kanki bayan na nuna miki yadda ake yi ba wani wahala ne da kunnawar ba." Tashi tayi ta bishi a baya tana cewa "naji ɗin ni dai kada ka fita baka kunna mini ba." Sai da ya kunna mata gas ɗin ya nuna mata yadda zata yi ta kashe idan ta gama koda zai daɗe bai dawo ba kafin lokacin sannan yayi mata sallama ya fita. A ƙofar gida ya haɗu da Tanimu zai shiga gidan hannunshi riƙe da babbar leda. Yana ganinshi yace "kai kuma daga ina? Duk yau ban ganka ba saboda babu zuwa makaranta ko." Dariya Tanimun yayi yana sosa kai alamun jin kunya don duk yau bai leƙo Baqeer ɗin ba yace "Wallahi yau a shagon su Nuhu na yini ina tayasu aiki shine ma na karɓo wasu kaya nake so ka yanka mini sai naje na haɗa." Juya keken yayi suka koma cikin gidan yana cewa "ya kamata dai ka dage ka koyi yankan nan da kanka gashi kana son hawa keke amma ka kasa mayar da hankali ka tsaya ka koyi yanka sosai." Dada na ganin shigowarshi tace "Har ka dawo ko fasa fitar kayi?" Tsayawa yayi ya mata bayanin abinda ya shigo dashi sannan suka shiga ɗakinshi. Karɓar kayan yayi Tanimu yayi mishi bayanin abinda yake so yayi, da taimakon shi Tanimu ya yanka kayan don yace ba zai yanka mishi ba sai dai ya nuna mishi yadda zai yi tunda dukkansu koyo suke yi idan bai tsaya ya iya tun yanzu ba sai yaushe zai iya. Yana kallon yadda Tanimu yake yankan yana tunanin ya kamata ya sayi kekuna ko guda biyu ne ɗaya manual ɗaya na wuta su gyara shagon ƙofar gida su zuba su fara aikin anan kafin ya samu ya buɗe babban shago yadda yake da buri, don wuri babba yake so ya buɗe inda zasu dinga ɗinki har da ready made ba wai sai mutum ya kawo kayanshi ba to amma yasan irin wannan wurin sai a hankali zai buɗu ba wai lokaci ɗaya zai cimma wannan manufar ba shi yasa yake so su fara da ƙaramin shagon a gefe guda kuma yana cigaba da sayar da sketches ɗin shi ga kuma contract ɗin da yayi signing ana biyanshi albashi duk wata banda kuɗin da suke biyanshi duk lokacin da yayi musu designing kaya, yasan a hankali da abinda yake samu cikin lokaci ƙanƙani zai buɗe babban shagon kamar yadda yake buri amma yafi so ya fara da ƙaramin wurin hannunshi ya goge a ɗinkin kafin ya buɗe wancan ɗin.

***** "Abu, Jamila." Ya shigo yana ƙwala musu kira tun daga soron ƙofar gida har ya shigo tsakar gidan bai daina ƙwala musu kira ba. Kowaccen su ta fito daga ɗaki, Abu tace "haba Mallam wannan wane irin kira ne haka tun daga ƙofar gida mutane na ji, ai ko miye ma sai ka bari har ka shigo gida." Wata uwar harara ya jefa mata kafin yace "anƙi a bari a shigo gidan, wallahi Abu ki kiyayeni kada fa kiga ina sakar miki fuska kice zaki kawo mini raini sai naci mutuncin ki wallahi. Ina ƴaƴan naku suke? Wallahi yau sai an fitar mini da ɓarawon da yake zuwa yana yi mini sata a shago don ba yarda zan yi ba, haka kurum kuna nema ku karyani bayan baku san da yadda nayi na samu kuɗi na kafa jarina ba sai yanzu da kuka haifi lalatattun ƴaƴa zaku dinga turasu kasuwa suna yi mini ɗauki ɗai ɗaya tun ana yi da kaɗan-kaɗan ina shiru gashi yanzu har an fara ɗibar masu yawa." Gyara tsayuwarta Jamila tayi tace "sai kaje can ka nemi masu yi maka sata amma dai ba ƴaƴana ba tunda kai kanka kasan karatu suke yi basu da lokacin kansu bare har suje kasuwa suna yi maka sata, ahto. Sata kam ai sai zauna gari banza marasa aikin yi waɗanda basu ajiye komai ba sai yawo daga wannan inuwar zuwa waccan inuwar amma ba ƴan makaranta ba masu abun yi." Abu da bata saka baki tayi tsalan jin abinda Jamila tace don tasan Kamalu take yiwa gugar zana tace "to wa kike nufin yana yi mishi satar? Ba dai Kamalu kike so kice ba ko? Don wallahi ɗana yafi ƙarfin yayi sata sai dai kaje can ku nemi ɓarawon kayanka amma ba a ɗakina ba. Sannan ai ba mu kaɗai bane masu ƴaƴa ita Fatima me yasa baka kirata ba sai mu kaɗai saboda mu ka rainawa wayo." Gaba ɗaya sai suka kalli ƙofar ɗakin Umma da duk abinda suke yi tana jin su bata saka musu baki ba ganin ba'a saka da ita ba, ko yansu ma da Abu ta ambaci sunanta bata nuna taji su ba bare ta fito tace wani abu sai ma ta gyara kwanciyar ta tana cigaba da jan carbinta kamar bata ji meke faruwa a tsakar gidan ba.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA SHIDA*

{56}

Ana cikin haka sai ga Kamalu ya shigo ai kuwa Badaru na ganin shi ya damƙi hannunshi yaja shi har ɗakinsu yana cewa "Wallahi bazan yarda ba sai ka fito min da kayana da kake zuwa kana sacewa a kasuwa, nasan babu mai yi min wannan aikin sai kai tunda duk cikin ƴaƴana kai ne gagararre, haihuwa asara." Abu da tun lokacin da ya fara jan Kamalu ta biyo bayansu tayi caraf tace "A'a wallahi Mallam kada ka ƙara kiran ɗana da haihuwar asara haka kuma ban haifi ɗan iska ba, haba ace yanzu duk cikin yaran gidan nan Kamalu kaɗai zaka tsame kace shi yayi maka sata saboda shi an tsane shi ba'a son shi. Idan da gaskiya ai sai kayi bincike idan ka kamashi da laifi sannan ka iya cewa komai ba yanzu da kake lalube cikin duhu ba." Duk da hararar da yake jifanta dashi bai sa tayi shiru ba sai da ta dasa aya tukuna, shi kuwa Kamalu fito ma yake yi da baki yana kallon su ɗai-ɗaya kamar bai fahimci akan me suke hatsaniyar ba. A fusace Badaru yana nunata da yatsa ya fara faɗin "Duk wa ya lalatashi idan ba ke ba shine har zaki zo kina cewa an tsane shi za'a yi mishi ƙazafi, to ba lalataccen bane haihuwar asara wanda bai iya tsinananwa kanshi da komai ba sai dai ayi mishi. Wallahi tun muna shaida juna ka fito min da kayana idan ba haka ba kotu ce zata rabani da kai," ya ƙarashe maganar yana kallon Kamalu da sam hankalinshi baya wajenshi, kaya ne dai yaci kuma ba zai bayar ba sai dai ya ɗauki duk matakin da yake ganin ya dace, dolene ya saci kaya ya hada lefe ehe! Kallon Badaru yayi a wani shagiɗe cikin magana irin tasu ta gagararrun ƴaƴa yace "Don baka so na ba shine zai sa ka ƙala mini sharri ba, haka kurum kowacce shara ka ɗebo sai ka watsa ta a kaina, to idan baka so na ka kai ni bolar ƴaƴa ka jefar mana." Baki buɗe Badaru yaje kallonshi, da ƙyar ya iya cewa "Ni kake faɗawa maganar banza irin wannan Kamalu? To wallahi zaka fita ka bar min gida kaima tunda ba da uwarka muka haɗa kuɗi muka yi ginin ba ah to, na kori Baqeer ma babu abinda ya dameni bare kai gayyar tsiya haihuwar asara." "Kafa daina aibata mini ɗa Mallam bana so, kaje can ka nemi ɓarawon kayanka amma ba Kamalu ba. Taho mu tafi kaji," ta cewa Kamalu, suka fice suka bar Badaru a ɗakin yana cigaba da bambamin masifa don fa ba yarda zai yi ba sai an fito mishi da kayanshi, haka kurum yana ji yana gani ba za'a yita saka shi asara ba.

***** Tun daga waccan ranar Kabir ya ƙara janyewa daga Nabila tunda ya fahimci babu alkhairi a tattare da taraiyar su, gaba ɗaya ya ƙauracewa zaman gidan idan ya fita tun safe baya dawowa sai dare ya tsala sannan kuma ya daina barin ƙofar ɗakin shi a buɗe ko shiga kawai zai ya fita kuwa. Duk wata hanya da Nabila zata ganshi ta ƙara cusa kanta a wajenshi yayi ƙoƙari ya tosheta to itama ta ɗan ja baya dashi tunda wancan al'amarin ya ratsa tsakaninsu. Yanzu ba kasafai ta fiye nemanshi ba saɓanin da da ko bata ganshi ba ta dinga damunshi da waya kenan tana tambayar yaushe zai dawo gida yau tunda ta tashi bata sanya shi a idonta ba, irin waɗannan abubuwan dai da take amfani dasu tana manipulating ɗin shi don shi sam babu sonta a cikin zuciyarshi, to ta yaya ma hakan zai kasance bayan ga matsayinta a wurinshi, gashi yanzu duk yadda ya kai da kauce mata sai da ta janyo suka aikata abinda tun farko yayi ta guje musu afkuwarshi.

***** Tunda Badaru ya shige ɗaki abun duniya ya taru yayi mishi yawa, ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi yaji daɗi. Yana ji yana gani duk wani buri nashi na rayuwa ya wargaje, dama akan Baqeer yake da hope to gashi shima abinda yayi mishi yayi watsi da duk wasu sadaukarwa nashi yayi fatali da burinshi ya watsa mishi ƙasa a ido yana ji yana gani yayi bankwana da tsohon burin daya gina rayuwarahi akai. Tashi yayi yana zagayen ɗakin ya kai gwauro ya kai mari ya rasa abinda ke yi mishi daɗi, yadda al'amuranshi suke ta cakalkalewa shi yafi damunshi gashi yanzu kasuwar ma sai asara kawai yake tafkawa, ya rasa ta inda kuɗaɗenshi suke ƙarewa sai kaɗar da dukiyarshi yake yi yana ƙara jari amma da ƙyar yake iya haɗa uwar kuɗin bare a fitar da riba. To ko dai filin Baqeer zai saka a kasuwa ya ƙara jarin tunda ma ai shi yayi ta wahala da Baqeer ɗin har ya zama abinda ya zama da yayi mishi sanadin mallakar filin, wani murmushi ya saki da yin wannan tunanin don yasan idan har aka sayi filin da daraja ba ƙaramin alkhairi zai samu a ciki ba in yaso sai ya ƙara jarin ya tashi kasuwancin shi abinda yayi ragowa kuma sai ya buɗe shago a ƙofar gida ya zuba kayan masarufi. Tashi yayi ya janyo jakar da yake ajiye duk wasu muhimman abubuwa nashi, zama yayi dirshan a ƙasan ɗakin ya buɗe jakar yana yi mata filla-filla yana neman takardar filin da yasan ba nashi bane. Hankalinshi ne ya fara tashi da yaga har ya kusa gama fitar da kayan cikin jakar bai ga takardar ba. Jiki na rawa ya cigaba da dubawa amma har ya gama bai ganta ba, zazzage jakar yayi a ƙasa ya fitar da komai amma bai ganta ba. Ai tuni hankalinshi ya tashi ya dinga bin takardun nan ɗaya bayan ɗaya yana ƙara dubasu amma bai ga takarda mai kama da wacce yake nema ba. A sukwane ya tashi ya fita daga ɗakin har yana tuntuɓe da dokin ƙofa ya fita yana ƙwalawa Kamalu kira. Ai ba Kamalu da ake yiwa kiran mafarauta ba kowa a gidan sai da ya fito idan ka cire Umma da bata shiga sabgarsu idan har ba an saka da ita ba. Gaba ɗaya suka tsaya cirko-cirko suna kallonshi, yana ganin Kamalu yaje ya cakumi wuyan rigarshi yana cewa "Wallahi ƙaryarka tasha ƙarya, duk inda ka kai mini takardar filin nan sai ka fito da ita don wallahi bazan ɗauki asara ba." Kici-kicin ƙwace wuyan rigarshi yake yi amma ya kasa don ba ƙaramin ruƙo Badaru yayi mishi ba, sai da Abu taga yana neman halakar mata da yaro ta taso ta ɓamɓare hannunshi da ƙyar tana cewa "Haba Mallam kashe shi zaka yi ne?" "Ki rabu dani na kashe ɗan iskan yaron nan wanda babu abunda ya sani sai shaye-shayen banza da wofi, wallahi Kamalu ka fito min da takardun filina idan ba haka ba kotu zan maka ka don bazan kamunta ba ka kasheni tun kwanana bai ƙare ba," Da ƙarfi Kamalu ya ture Badaru jin shakar dayamai yasa numfashinsa ya fara sarƙewa, Badaru baya yai sai kuwa ya bugi bango, ihu ya kwalla jin wani uban zafi ya ziyarce shi a kugunshi, Kamalu a tsorace ya kalleshi yana sauke numfashi, su Abu da Jamila kuwa sunyi kanshi, Jamila ce ta saki salati cike da ƙara tace "Wannan ɗa lalai anyi haihuwaf asara, kashe shi kake sanyi? Inalilahi yau naga abinda yafi ƙarfina Malam, sannu." Badaru da kyar ta taimaka mai ya miƙe yana rike da kwankwaso, Kamalu da sauri yai waje dan Abu ce tamai alama da yai maza ya fita daga gidan, gaba ɗaya Badaru dakyar yake tafiya ji yake kamar ya gurɗe kugunshi, magana kuwa ya kasa yinta saboda uban azabar dake ratsashi, ɗaki Jamila ta kaishi ya kwanta tana mai tausa, wai yau kamar shi danshi zai hankaɗe? Lalai gobe in ya warke dole ya sallami Abu ta koma kauye, matsala ɗaya ƴar uwarsa ce yanzu tana tafiya mutanen kauye zasu isheshi da zirga zirga sai dai dole ta tafi daga ita har ɗanta, Fatima kam tunda ta fito taga abinda ya faru ta koma ciki, ita yanzu zaman gidan kawai yinshi take dan ba yanda zatai dan babu wani abu dake burgeta a ciki. Ranar duk yanda yai bai samu bacci ya daukeshi ba, filinshi kawai yake tunani, ga azabar ciwo da yake ji, wajen asuba ma da gyangyadi ya daukeshi yai mafarkin wai Kamalu ya saida filin ya cinye kuɗin firgigit yai ya farka, hankali a tashe ya yai dafa kirjinshi dake mai nauyi, lalai Kamalu dole ya bar mai gida dan ya tabbatar wannan tsaf zai nakasa shi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull