Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 41

Baqeer complete - Chapter 41

Baqeer complete Chapter 41: Baqeer complete Chapter 41. **** Wace irin shakuwa ce mai ƙarfi ke ƙara shiga tsakanin Baqeer da Zainab, a koda yaushe yana…

2,972 words

**** Wace irin shakuwa ce mai ƙarfi ke ƙara shiga tsakanin Baqeer da Zainab, a koda yaushe yana bata mahimmanci a ranshi saboda yanaji Allah ne ya kawota cikin rayuwarshi dan ta daidai ta mai ita, a yanzu yafi da farinciki duk kuwa da bashi da ƙafa a kalla yasan me yakeso yasan yai abinda zai kwantar mai da hankali, ba kamar da wanda Badaru ke kula da duk wani motsinshi ba, komai nashi sai da izinin Badaru gashi yai ta wulakanta ragowar kanensa saboda shi, wannan abu ya dade yana damunshi. Yau Baqeer ne zaune yana yanka shadar da ya siya zai dinkawa Hassan da Husaini da kuma Areef, yanajin da ɗin yanda a yanzu baya taɓa rasa kuɗi kuma haryanzu kuɗin filinshi bai cinye ba, ya tanada ragowar ne dan siyan keken wuta na electric da kuma shirin buɗe shago da yake san yi, wayarsa ce ta fara ƙara alamar an mai waya, kallanta yai ganin wata number yasashi jinkiri kafin ya ɗaga bayan sun gaisa ne mutumin yake sanar dashi akan shine wanda watanin baya ya nemeshi akan zanen da zai dinga musu. Baqeer ranshi ne ya ɓaci ganin sunzo da rainin wayau, taya tun nemenshi da sukai a baya basu sake nemanshi ba sai yanzu? Yanzun ma yasan daga wayar ba wani abu dazai faru. Katse mai tunani yai da cewa "Kayi hakuri matata tace Allah ya mata rasuwa sai abubuwan duk suka tsaya min komai ya fita daga kaina." Nan danan kuma sai jikin Baqeer yai sanyi yace "Allah ya mata rahama." Ya amsa da ameen sannan yace "Na shigo Kano inaso mu haɗu in ba damuwa gobe." Ya jinjina kai yace "Allah ya kaimu, ka turomin lokacin sai nazo." Nan suka tsara inda zasu hadu sukai sallama, sai dai haryanzu baije farinciki ko doki ba aganinsa sai yaga komai ya tabbata zai kwantar da hankalinsa, sam bai yadda da mutane ba yanzu.

***** Kamalu kam duniya tamai zafi shiyasa yanzu in ba ɗau ki dadai da yake a shagon Baba ba babu abinda ke rage mai zafi, gani yake gwara ya ɗauka ya fara tara lefe a dabarance, ya tabbatar Roshini intaga akwatinan laifi goma sha biyu to fa tabbas yasan zata sara ma kaunar da yake mata, za kuma tasan lalai shi ɗin saurayi ne da a ke yayi ake kuma sha'awar aura.

***** A zabure Kabir ya ture Nabila ganin aika-aikar da sukai, nan da nan kanshi yaji yayi wani irin sarawa, me ya aikata? Abinda ya faru daren jiya ne ya fara dawo mai..........

(😑😑Gaba daya Umm Asghar kasa motsi tai, Kabir da Nabila, Ayusher ce ta kalleta jikinsu gaba daya ya kame .)

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* DA *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA HAMSIN DA HUƊU

{54}

Yaye bargon yai ya ganshi daga shi sai gajeran wando, kanshi ne yai wani irin sarawa ya sa hannu ya rike kan yana sake tariyo abinda ya faru, dawowarshi kenan daga yawonshi na abokai ya shiga ɗakin shi, kayan jikinshi ya fara cirewa dan bacci yakeji ko ganin su Mumy ba baisa ranyi ba dan kuwa yasan sun kwanta, ya cire kaya ya rage daga shi sai gajeran wando zai sa kayan bacci ta turo ƙofar, kallanta yai nan danan hankalinshi ya tashi, da sauri yasa hannu ya rufe saman kirjinsa yana cewa "Dan Allah fita, akan me zaki ɗinga shigowa ɗakin mutane ba tare da kin kwankwasa ba?" Mai makon tai abinda ya sakata sai ƙara takowa datai zuwa inda yake, nunata yai da yatsa fuskarsa a ɗaure yace "Wai ba magana nake miki ba? Karki kuskura ki ƙara so," nan ma bata kulashi ba sai ƙara takowa da take, tana isowa inda take ta rungumeshi, yawun bakinsa ya hadiya ya fara ƙoƙarin tureta, sake kankameshi tai tace "KB plz ka bari ba zina zamuyi ba, balle kace zunubi muke ɗauka." Da mamaki ya kalleta yace "Wai Nabila kinsan me muke yi kuwa? Me zai faru in wani ya shigo ya ganmu a haka? Dan Allah......" kiss ɗin data fara mai ne yasashi kasa cewa komai, tun yana neman janyeta tana rikoshi harya kasa, nan ya shiga maida mata martani, kan gado ya jata ya cigaba da sumbatarta, saman wuyanta ya gangara gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, Nabila kuwa gani take hakan shine daidai dan wannan ne kadai abinda zai hana Mumy rabata da Kabir dan indai aka hanata auran Kabir to fa har abada bazatai aure ba sai dai ta karashi rayuwarta haka, ko duniya zasu zageta in dai akanshi ne to fa bata damu ba. Kabir cak taji ya tsaya sanda ya fara zuge zip ɗin bayanta, hakan yasa ya saketa sai kuma ya kwanta rigingine yasa hannu ya shafi fuskarsa yace "bazan iya ba, am sorry." Hawaye ne ya zubo saman kuncinta ta kankameshi tace "Naji amma dan Allah ka soni." Hannunta yaje janyewa ta sake kankameshi wanda hakan yasa ya kyaleta, yana ji tana hawaye amma ya kasa hanata, a haka bacci ya ɗauke su wanda bai farka ba sai yanzu. Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke jin komai ya dawo cikin kanshi, Alhamdulila da bai tafka kuskure ba dole yasan abinyi ya kuma kare kanshi daga aikata zina, haryau yaran da ya buge a mota yana zuwa mai cikin rai ya kuma san hakki na nan na binshi dan haka bazai bari ya sake aikata wani babban aikin dazai ƙara mikashi wuta ba. Yanda taja bargo ne yasa shi tsorata ya kalleta hankali a tashe yace "Menene kuma?" Kuka ta fashe dashi tana cewa "Kabir sai fa dana ce maka kar mu gangara," ta ƙarasa maganar tana kuka, mamaki ne ya rufeshi yace "To ai bamu gangara ba." Ta girgiza kai tana sake shashekar kuka tace "Da alama ba'a hayyacinka kake ba nikam na shiga uku na, wallahi ban ɗauka zakamin karfi ba." Jiyai kanshi ya ɗaure nan ciwon kanshi ya ƙara tsanan ta yace "Me kike san cewa? Bayan na tuna komai kuma ba abinda ya faru?" Ta sake sa kuka tace "Iya abinda ka tuna dai kenan amma bayan na kwanta bacci kawai naji ka yayemin bargo ka hau cire mun kaya kamin ta ƙarfi………." Ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka, hannu yasa ya toshe mata baki da sauri yace "Bangane nasa miki ƙarfi ba bayan ko taɓa ki banba. Yaye zanin kaɗan tai sai gata ba pant, sai jini a matse-matsin kafafunta, idanu ya zaro jikinshi ne ya hau rawa, yama kasa gane meke faruwa dan shi dai a iya saninsa bai ko ta ɓata ba, to menene wannan? Hawaye ta share tace "Shikenan ka cuceni, shiyasa nake ta cema na zina ba, dan kaga ina sanka shiyasa kai min ƙarfi, na shiga uku nikam shikenan rayuwata tazo ƙarshe." Kabir gaba ɗaya ya kasa tunani, jikinshi ne kawai yake rawa dan hanayensa ma sai rikesu yai saboda rawar da sukeyi, da sauri ya mike ya nufi hanyar toilet, cikin sauri tace "Ka ƙira min Mumy tsoro nakeji…." Tai maganar cikin rawar murya, dawowa yai da sauri yace "Na kira miki Mumy kamar ya?" Hannunshi ta kamo tace "Bazan iya tashi ba, nan dina zugi yakeyi." Tai maganar tana nuna gun da hannu, gaba ɗaya zufa ke keto mai wannan masifa da bala'i da me yai kama yaushe ya kusanceta? Shi ba shayeshaye ba taya zaiyi abu baisan yayi ba? Shikenan rayuwarshi ta kare ace kamar shi fyade yakewa mata? Matqn mq kanwar Mumy? Inalilahi, kalaman Nabeela ne suka dakatar da tunaninsa datace "Kabir ka ketan haddi ka maidani budurbazar shikenan gwara na mutu na huta." Kallanta yai yace "Nidai kome zai faru karki sanar da kowa abinda ya faru, bansan sanda nai ba haryanzu na kasa gasgata zuciyata, taya zanyi abu bansani ba?" "Hmmm! Dama ance haka maza suke sai suyi abu su maidashi tsautsayi ko suce basu san me hakan yake nufi ba, bari na ƙira Mumy ta maidani gun Inna," tai maganar tana ɗaukan wayarta, da sauri ya amshe wayar yace "Ki bari mu samo mafita yanzu ki tashi ki wanke jiki ki fita zan fitar da bedsheet ɗin." Man ta fara ƙoƙarin mikewa ya taimaka mata ta shiga banɗaki shi kuma ya fito da bedsheet kamar munafiki yasa a bayan motarshi sannan ya dawo, yai sa'a daya dawo bata ɗakin, kasa bacci yai kawai ya zauna ya dafa saman goshinsa, meke faruwa?

******* Maryam ce ta kalli Baban Areef idanunta sun ciciko tace "Yanzu haka zamu cigaba da rayuwa shikenan mu bamuda sirrin kanmu? Ni kenan komai zakamin sai abinda aka tsara ma?" Fuska ya tamke sosai yace "Kiyi hakuri kyaje nan gaba." Idanuwanta ne suka ciciko da kwalla tace "Wannan wani irin aurene ace sam ban da ikon kaina bare insa ran samun ƴanci na? Ace kullum sai yanda akai dani, komai muka tsara sai ka kwashe ka sanar mai? Bamu isa muyi sirri ba?" Hannu ya ɗaga mata alamar ta dakata sannan yace "Kul wallahi na faɗa miki duk wani abu daya shafi Abbana dole ki darajashi kin kuma san sauran in baki bi ba." Yana kai nan ya mike ya fita, hawayenta ta share ya dade yana cewa zata cigaba da karatu yana ki amma yanzu da ya amince ta sa ran amincewar ta gaske ne saboda har takardunta ya amsa kawai sai gashi an dawo mata dasu wai Baba yace kula da yara zatai ko karatu?

*** Washe gari kamar wasa mutanen nan suka ce yaje Aroma cafe, nan yai shigarshi cikin hadadiyar shadda wanda ta sa kyansa kara fitowa, hula ya saka ya sa agoggo da takalmi, nan fa ya fito Muhammad Baqeer dinsa, Salim cikin atamfa ya shirya kasancewar ba mota a hannunsu yasa Salim yace zai tambayi Zainab, sai dai Baqeer kai tsaye ya hanashi yace gwara su nema ko suyi haya amma ba gunta ba, dariya Salim yai yace "Naga fa alama ƴar kunya kukeyi yanzu fisabillahi da mu samu motar bati gwara a sa mu biya?" Gefe Baqeer ya kalla yace "Kuma ko kunya mu kuma sai mu tabe da aran motarta, to Allah a'a ko kuɗin iya kacinsu kenan gwara mu bada." Baki Salim ya buɗe yace "Hmmm ai sai muyi kallo daga gefe tunda kunfi kusa." Baqeer sam bai maida hankali kan me yace ba sai da wasu dakiku suka wuce sannan ya fahimta da sauri yai gyaran murya yace "Munfi kusa a ina kenan?" Waya Salim ya ɗauka ya fito yana cewa "Wai a duba a gani ko?" Yana kaiwa nan yai waje, Baqeer yai dan tsaki yace "Shidai kullum in baiyi zolaya ba baijin dadi," sai kuma yai jimm da gaske sunfi kusa kamar yanda Salim yace? Baisan sanda ya dan motsa leɓensa ba, Salim bai da de sosai ba ya dawo nan sukawa Dada sallama suka fita dan ita kanta bai faɗa mata inda zasuje ba. Sunje cafe ɗin suka tarar bai zo ba, minti biyar sukai Baqeer jiki a sanyaye yace "Salim mu tafi dan Allah." Kallanshi yai yace "Ko mu ɗan jira?" Kai ya girgiza yace "Ba amfani dama can ban yarda zasuzo ba ko ka manta me ya faru?" Salim jiki a sanyaye ya kalleshi zaiyi magana sai ji sukai ance "Muhammad?" Kallansu yai dan haka yake amfani a IG saboda baisan a ganeshi, matashin saurayin ya ƙara so ya mika mai hannu suka gaisa yace "Sunana Nasir, wanda mukai magana." Zama yai suka ƙara gaisawa sannan Salim ya gabatar da kanshi akan shine manager na Baqeer, haka suka zauna akai reviewing contracts ɗin, Baqeer yace a canza wasu abubuwan nan shima Nasir ya ƙara gyara abinda suke so, a ƙarshe Baqeer yace sai sunsa contracts din na shekara ɗaya sannan in za'a sake renewing dole sai dai in su duka bangarorin biyu sun yadda za'ai, nan suka amince aka sa hannu, Nasir sosai ya ƙara gamsuwa da Baqeer dan yanda yake magana kaɗai zakasan yanada talent sosai, anan ya fito da wayarshi ya sake nuna musu wasu zanuka da yai aka ɗin ka, sannan yace dan yana basu zane bazai hana wasu ba, suka amince akan sai dai kar ya bawa wasu irin nasu, cike da jin daɗin handa komai ke tafiya daidai Salim ke kallansu sai hamdallah yake a cikin ranshi, a kuma nan suka biya Baqeer 50k ɗinshi na duk wata sannan suna jiran zane guda goma, zasu bashi rabi in yai zana 5 sannan su bashi ragowar kudin in ya zana ragowar, nan sukai order na drinks suka sha sannan sukai sallama kowa hankalinshi a kwance. Salim yana ajiyeshi ya juya dan yabar shago a kule, Baqeer ne ya kalli Dada sannan ya sanar da ita abinda ke faruwa, guda ta shiga yi ji take kamar ba wanda yakaisu farinciki tace "Baqeer lalai idan Allah ya tsara bawa zaiyi arziki ko mutane zasu haɗu su hanashi sai Allah ya tada shi." Murmushi yai yace "Dada ba komai kaddara ce sai dai a yanzu na gane kaddarar nan itace tasa na gane kaina, na gane mutanen dake tare da ni sannan na tashi na nemi abu da kaina bawai da taimakon Baba ba, ada na ɗauka yafi sona akan kowa na duniyar nan, wanda har nake shakkar san da yake min yayi yawa yana rufemai ido da bai ganin laifina sai dai yanzu na gane." Tausayin Baqeer ne ya kamata tana gani ya wuce ɗaki, laptop ɗin daya siya ya buɗe irin ta zane mai pencil a jiki, bai ma da de da siyanta ba, har zai fara sai kuma ya ciro wayarsa, number Zee ya kurawa ido haka kawai yakeji yana san sanar da ita abinda ya faru, shiru yai yana tunanin ta yanda zai fara sai ya mata text 'A dawon da abuna da aka ɗauka." A lokacin Zeey na kwance kan cinyar Mumy suna kallo ita kuma tana daddana waya, Nabeela na zaune daga gefe tayi shiru tana tunani. Ganin sakon Baqeer yasa ta mike zaune da sauri ta karanta, murmushi tai ta rubuta "Nace sai an ban hakuri." "To ai laifin hakurin ne ban san nayi ba." Ɗaki ta shige ta faɗa kan gado tace "Ka ƙira na faɗa ma mai kai." Kallan wayar yai ta turo "Allah ka ƙira!" Yanzun ma kallan wayar yai kai ya girgiza sannan yace "Reason?" Smiley's ta turo na rike baki tace "Haka kace? Shikenan." Kiranshi tai ya girgiza kai yana murmushin da shi kanshi bai sani ba ya ɗaga "Inalilahi!" Kawai abinda tace kenan ta kashe, hankalin Baqeer ne ya tashi cikin sauri ya ƙirata, tana ɗagawa yace "Lafiya? Meya faru?murmushi tai tace "Hmm haka ake so." Sai a lokacin ya gane me yake nufi kamar zai yi magana sai ya fasa "Me ya sani a kanta? Shi komai nashi ta sani shifa? Ko cikaken sunanta bai sani ba, kawai jiyai bai kamata ya faɗa mata ba, cikin wata murya yace "Ke kaɗai ce a gida?" Hankali a kwance tace "A'a yayana baya nan, to ni da Mumy na ne sai sister ɗinta, Dady ma bai nan." Kai ya jinjina yace "Ku biyu ne kenan?" Nan ma tace eh daga ni sai shi, Mumy tace mun isa. Shiru suka ɗan yi tana mamakin tambayar datazo kai tsaye, zatai magana taji yace "Maryam fa? A makaranta kuka haɗu?" Gabanta ne yai wani irin faduwa me Ya Baqeer yake tambaya? Me yake san tace? Kalamansa ne suka sake katse ta dayace "Secondary ko FCE?" Muryarta ce ta ɗan sarke………

Umm Asgar Ce Da Ayusher Muhd

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BIYAR*

{55} Ta buɗe baki ta rufe ta sake buɗewa ta rufe ta rasa ma amsar daya dace ta bashi, to ita a yanzu tace mishi a ina tasan Maryam bayan har yau bai gane wacece ita ba. Kasa bashi amsa tayi sai cewa tayi "kun yi waya da Umma?" Tana lafiya dai ko?" Ɗan murmushi yayi yana jin wata irin nutsuwa tana ratsa zuciyarshi, yadda Zeey ta damu da Umma abun yana yi mishi daɗi. A shagwaɓe tace "Ya Baqeer," sai da yaji ƙiran sunan nan har tsakar kanshi. Gyaran murya yayi yace "tana nan lafiya, baki je kin ganta ba?" "Na kwana biyu ban je ba amma In Sha Allah zan samu time naje na dubata, kasan fa yanzu mune idanunka dole mu dinga kai ƙafa akai-akai tunda mun san yadda Umma take a wurinka," ta ƙarashe maganar cikin kwantar da murya kamar tana gabanshi. Haka nan take jin wani farin ciki yana ratsa zuciyarta, ta rasa lokacin da hakan ya faru amma a yanzu ta tabbata ba zata iya rayuwar da babu Baqeer a cikinta ba. Sun daɗe suna hira wacce fiye da rabinta tsokana ce suke yiwa junansu. Bayan sun gama wayar Zainab ta kwanta rigingine tana kallon ceiling tana sakin wani ƙayataccen murmushi, so kawai take yi ta ganta a gaban Baqeer sai dai bata cika so tana yawan zuwa wurinshi ba a yanzu kada ya zamanto kullum ita take kai ƙafa ya kamata ace ko yaya ne shima yana kawo mata ziyara idan fa har suna son taking relationship din su to another level. Kaji Zainab dai wai relay, dama kuna relationship ne? Tayi wa kanta tambayar data kasa bawa kanta amsa tunda dai tasan Baqeer bai taɓa furta yana sonta ba yanayinshi ne yasa take ganin kamar shima yana sonta kamar yadda take son shi.

*****

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull