Baqeer complete - Chapter 40
Baqeer complete Chapter 40: Baqeer complete Chapter 40. ***** Yau tun safe suke zuba lissafi suna tusawa, ya rasa inda kuɗaɗen shi suke tafiya kullum a…
3,058 words
***** Yau tun safe suke zuba lissafi suna tusawa, ya rasa inda kuɗaɗen shi suke tafiya kullum a maimakon ya cigaba sai baya yake ci ga wasu ƙananun sata da ya rasa wanda yake yi mishi a cikin yaran kantin nashi, duk wasu matakan tsaro daya sani ya zuba musu amma har yau ya kasa dacen kama ɓarawon da yake yi mishi sata. Akwai ranar ma da har an gama ciniki da wata mata da tazo sayen atampopi sai da aka zo saka mata a leda guda ɗaya tace ɗaukeni. Haka aka yi ta nema ba'a gani ba sai wata aka ɗauko aka bawa matar shi kuma yana ji yana gani ya ɗauki asara don kowa yace bashi bane ya kuma rasa ta yadda zai yi ya fitar da ɓarawon daga cikin yaran shagon nashi. Haka nan dai ya haƙura aka gama lissafin ya ware kuɗin da za'a zuba wasu kayan, sai yaga ɗan abinda ya rage mishi bai taka kara ya karya ba gashi kuma dole ya biya ma'aikatan shi hakkinsu. Haka nan ba don yaso ba ya biyasu albashin su ya tattare ɗan abinda ya rage ya tafi gida yana huci kamar yana fatan wani ya shiga gonarshi ya huce takaicin shi a kanshi. Tun daga ƙofar gida yake surfa ruwan bala'i akan tumakin maƙwabta da suka yi mishi kashi a ƙofar gida, yana shigowa tsakar gidan yaci karo da bokitin ƙarfen Jamila a tsakar gidan, ƙafa yasa yayi ball dashi yana masifa akan don me za'a ajiye bokiti akan hanya salon yayi tuntuɓe ya faɗi idan yaji ciwo basu da asara. Daga Jamila har Abu tsayawa suka yi suna kallonshi babu wacce tasa mishi baki, a yadda suka ga ya shigo ɗinnan sun san idan suka ce zasu yi magana idan ransu yayi dubu sai ya ɓaci don sun daɗe basu ganshi cikin tashin hankali irin na yau ba sun san dole akwai abinda ya ɓata mishi rai a waje sun san cewa idan suka saka mishi naki a kansu zai huce su kuwa babu wacce ta shiryawa tijarar shi ta fama da idan ya fara baya jin yi haƙuri idan aka bashi haƙuri shi kamar ana turashi ya ƙara ruwan tijarar da yake yi. Fatima ce me girkin ranar tana jin shi yana faman tijararshi bata fito ba sai da taji shigarshi ɗaki sannan ta fita ta haɗa kayan abincin shi ta ɗauka ta nufi ɗakin nashi dasu. Da sallama ta shiga ɗakin cikin nutsuwarta data zame mata jiki. "Sannu da dawowa Mallam," tace tana ajiye tiren abincin a gabanshi. Wani irin kallo yayi mata idonshi cike da fitina yasa hannu ya buɗe kwanukan abincin nashi sai yaga tuwon masara ne da miyar kuka. Watsi yayi da kwanukan ƙiris bai sameta ba tayi sauri ta kauce kwanukan suka watse anan tsakar ɗakin. "Mallam lafiya kuwa?" Tace tana kallon ɓarnar da yayi a tsakar ɗakin tana jin takaicin wannan wulaƙanci na Badaru, yanzu abincin da wasu suke can suna nema basu samu ba shine shi ya samu don wulaƙanci ya zubar. Nuna abincin yayi da yatsa yace "Miye wannan?" Yana bin miyar data kwanta a tsakar ɗakin da wani irin mummunan kallo kamar wanda yaga kashi. Kallon miyar itama tayi yadda ta kwanta a ƙasan ɗakin sannan ta ɗago ta kalleshi sai dai bata ce mishi komai ba tsabar takaici. "Ke dai Fatima wallahi kin yi asara, baki ji daɗin rayuwarki ba wallahi sam uwar baƙin ciki da mugun hali, abincin ma don mugun hali kin daina tsayawa ki girka mai kyau sai dai ki kwaɓa mana shi duk yadda ta raya miki." Hannu tasa ta tattare kwanukan ta haɗasu wuri ɗaya kafin tace "abinda ka kawo ai shi zaka gani, da ɗin ma da nake yin irin wanda kake so ai ba da cefanenka nake yi ba ka sani Baqeer ne ya ɗauki nauyin yin cefane yanzu kuwa daka koreshi kaga dole ayi da iya abinda ka kawo kawai tunda mai kawowar baya nan." A fusace yace "Yauwa ga maganata nan ta fito, kawai dama kice kina baƙin ciki don nace nakasashen ɗanki ya fita ya bar mini gidana shine kike nuna mugun halinki a abinci ba kya tsayawa kiyi shi da kyau kamar da, to sai dai mugun halinki ya ƙare a kanki, ɗanki ne dai ya bar gidan nan har abada kuma ban yafe dukiyata da lokacina dana ɓata a kanshi ba wallahi in dai baza ku biyani abinda na kashe ba." A razane ta ɗago kai ta kalleshi tace "Baqeer ɗin kake yiwa Allah ya isa kamar ba ɗanka ba Mallam? Wannan wacce irin rayuwa ce da bawa bai san ya karɓi ƙaddara ba, shi ya ɗorawa kanshi ne ba Allah ne ya ɗora mishi ba." "Oho dai wannan kuma ke kika sani, ni dai a biyani kuɗina idan ana son zaman lafiya dani ato." Tashi tayi kawai ta kwashe kwanukan tace "Allah ya ganar da kai Mallam amma In Sha Allahu sai kayi alfahari da haihuwar Baqeer." Tsaki yayi yace "Wa? Nakasashen ne zan yi alfahari dashi?" Bata ƙara kulashi ba ta fice ta bar ɗakin, ajiye kwanukan tayi a wajen wanke-wanke ta shige ɗakinta tana jinjina rashin tawakkali irin na Badaru da har yau ya kasa yarda da ƙaddarar data samu Baqeer.
***** Tunda satin bikin ya kama Asiya ta kasa zaune ta kasa tsaye don kuwa biki ne suke shiryawa na ƙarya irin wanda za'a daɗe ana labari. Events ma wajen kala biyar suka tsara za'a yi kuma duk Bello ne ya ɗauki nauyi koda yake ina iyayenta suka ga kuɗin da zasu yi mata irin wannan bikin na ƙarya. Duk wani ɗan abinda Bello ya mallaka ya shige a cikin sabgar bikin nan sai dai bai wani damu ba ganin ya kusa barin ƙasar yasan daga inda yaje ya fara aikin paintings ɗin shi shikenan zai mayar da fiye da abinda ya salwantar a wajen harkar bikin. Bayan kayan lefe da yayi mata duk wasu kaya da zata saka na fitar biki shi ya ɗinka mata tsadaddu don tace ai abun kunya ne a ga tayi kwalliyar biki da kayan lefenta sai ma ƙawayenta su raina ajinta a cewarta. Da bridal shower aka fara taron bikin inda Bello ya kama mata wani restaurant anan kusa da unguwarsu, duk wani abinci da aka ci a wurin taron restaurants ɗin ne suka basu. Haka event ɗinnan yayi ta yawo a social media, abinda ke ƙara sawa Asiya taji kamar kanta zai fashe don girma, tana ganin itama yanzu ta faso gari lokacinta ne yayi da zata shana tayi rayuwar ƴanci rayuwa irinta ƴaƴan masu kuɗi kamar yadda take da buri. Haka duk wani event da aka yi a bikin yayi ta yawo a social media har aka yi ɗaurin aure. A irin hotunan ne Baqeer yaci karo da hoton ɗaurin auren inda aka ɗauke su Bello ya rungumo kafaɗarta suna fara'a, duk da yanzu ya ajiyesu a gefe ya daina saka damuwarsu a ranshi sai da yaji wani abu ya mintsine shi a zuciya, a tunanin shi ko kowa zai yi mishi butulci bai kamata ace har da Bello ba bayan irin taimakon da yayi mishi a rayuwa.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* Da *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA HAMSIN DA UKU*
{53} Yau ta fito zasuje wani guri ita da Nabila taga layinsu cike da mutane, baki ta taɓe tace "Bai wuce aure ake." Nabila ce ta kalli gun tace "Kamar fa yarinyar nan ƴar iyayin nan ake aure dan naga pictures ɗinta a IG da farko ma ban gane ta ba sai da naga kanwarta na gane itace ta layin nan." Dayake Zeey batasan sunan Asiya ba sai cewa tai "Ban santa ba, kinsan ni ba rike mutane gareni ba." Nabila ta hau kan titi tana cewa "Ni ma ba magana muke ba, sanda bakya nan dai ina ganinta, itace kamar akace saurayin ta yaci gasar zane kamar ko?" Kamewa a zaune Zeey tai da jin Nabila nan da nan hankalinta ya tafi kan budurwar Baqeer da aka yaura, badai ita bace? In itace ya Baqeer ke cike? Nan danan taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci ta dau wayarta tana cewa "Meye handle ɗinta?" Ba tare da dogon nazari ba tace "Cutie_Siya" da sauri ta duba ganin fuskar Asiya duk da ba wani dogon sani ta mata ba yasa bankalinta kara tashi, sam hankalinta ya tafi har Nabila ta gaji da magana tace "Wai menene?" Kallanta Zeey tai tace "Aunty Nabs bana jin yawon nan, plz saukeni kije ke kaɗai." Mamaki ne ya kamata tace "Zeey inje ni kaɗai kamar ya? Bayan mungama planning dake akan tare zamu?" Saman goshinta ta shafa tace "Banajin zuwa plz samu guri kiyi parking na fita." Takaici ne ya kama Nabila, tai parking ga mamakinta mai makon ma Zeey ta maida hankali kan ɓacin ranta gani tai ta fita kawai ta tari adaidaita sahu ta shiga hankalinta a kwance babu alamun ma ta damu. Hannayenta biyu tasa ta shafi fuskarta tana mamakin hali irin na Zeey da sam in tunanin ta yai wani gun bata bi ta kan komai, itama maimokon ta cigaba da tafiyar kawai gida ta koma, tana parkıng motar ta shiga ciki ranta duk ba da ɗi, tana ƙoƙarin yin hanyar dakinta ta hangoshi ya fito sanye da jeans da light brown ɗin riga da alama fita zaiyi dan yana rike da key a hannunsa yana kadawa, idanunsu na haduwa ya fara neman juyawa tai saurin cewa "Kabir in baka zo ba Allah zan ƙira sunanka da ƙarfi Mumy ta fito." Waigowa yai ya kalleta sannan ya tamke fuska sosai ya cigaba da tafiyarsa, har yazo kusa da ita bata matsa ba, yana yin taku biyu gaba da ita yaji ta sa hannu ta zagayo dashi gefen cikinsa, gabanshi ne yai wani irin faduwa hakan yasashi kasa ko motsawa, ya fara sauke numfashi cikin wani yanayi, kanta ta kwantar a bayanshi ta rikeshi sosai tace "My love dan Allah ka barni naji duminka ko na minti talatin ne." Kasa motsi yai saboda wani abu da yake ratsa mai gangar jiki, yawun bakinsa ya hadiya yace "Nabila abinda muke aikatawa ba daidai bane ke fa kanwar Mumy ce wannan wani kwamacala ne?" "Na sani Kabir shiyasa nake ƙoƙarin jure abinda ke raina, ba zina na nemi mu aikata ba, ban kuma ce sai ka soni dole ba dan Allah nidai ka dinga barina ina rungumarka, duminka na ragemin radadin zuciyata, numfashinka ya ragemin kewa da kaunar ka, a haka inaji a jikina san da nake ma zai ragu." Waigowa yai ya kalleta yace "Taya sona zai ragu a zuciyarki ta haka?" Idanunta ne ya ciciko da kwalla tace "Allah zaiyi dan Allah karka hanani tabaka," ta ƙarasa maganar wani kwalla na gangarowa saman kuncinta, janue jikinshi yai ya fita nan ta bishi da kallo tana share kwallarta, wannan wani irin bala'i ne? Tana san abu amma ace wai bazai yiwu ba? Ita alaka ta dameta ne? Indai za'a barta da Kabir koma menene a faɗa ba damunta zaiyi ba. Waigowar nan da zatai taga Mumy ta nufota, da sauri ta fara share kwalla tana neman daidaita kanta, Mumy kuwa tana ƙara sowa ta sharara mata mari ba tare da ta ce mata komai ba, nan da nan gabanta ya faɗi badai taji abinda tace ba? Da hannu Mumy ta nunata tace "Wallahi ki fita ido na, uban me kike cemai da kika tsare shi kina kwalla? Wai nikam Nabila anya bakida aljanu?" Fuska ta tamke sosai ita ma rai a ɓace tace "Bishiyar kuka ne a kaina, ni ban isa nai abu ba sai kin takuramin? Gaisawa ma kenan bazanyi dashi ba sai a hau zargina?" Baki Mumy ta saki, cike da mamaki da tsoron kalamanta, tana nan a tsaye har ta shiga ɗaki lalai dole tasan abinyi akan Nabila tab!
***** Baqeer yanzu abubuwa sun kankama, dan yankan ɗinki inya maka sai ka riƙe baki, sai dai baya dinkawa sai dai Tanimi ya haɗe mai, shi kuma in da na wuta ne yake yi, kafafunsa Alhamdulila yana jin canji sosai a tattare dasu, duk bayan sati biyu yake zuwa asibitin Junaid, wanda tunda yaga ya daina zuwa da Zainab ya haɗa shi da wani physiotherapist ɗin dan sama shi saboda Zee ya nace da zuwan Baqeer ɗin. Shi kuwa Baqeer ko a jikinshi hakan ma da ɗi yamai ko banza dai yanzu baya ganin Zee. Kamar yanda suka saba yau haka sukaje makaranta sun gama kenan suka shiga adaidaita suka dawo gida, a hanya Baqeer ya tsaya ya saiwa Dada lemo da ayaba, yana tafe yana kallan gari da yanda kowa ke ta hada-hada, har suka isa gida nan Tanimu ya fito da keken shi kuma ya hau yana mai godiya, hannu yakai zai fara turawa sai yaji an fara turashi, da mamaki yace "Tanimu karka...." Sai kuma yaga Tanimu a gabanshi, sai a lokacin yajuyo kamshin turaren da yake sai mata wanda yanzu ta daina ma kamshin turarenta ta koma na wanda yake sai mata, baice komai ba itama batace komai ba ta tura keken suka shiga soron gidan shi kuma Tanimu yai musu sallama ya tafi, a soron ta tsaya ta kalleshi tace "Are you okay?" Sai a lokacin ya kalleta, idanuwansu ne suka haɗu da juna wanda a wannan lokacin sukejin kaunar da sukewa juna ta wuce duk tunanin mutum sai dai ita bazata fara cewa tana sanshi ba alhalin bata san matsayinta a cikin ranshi ba, shi kuma bazai iya cewa yana santa ba saboda ajinta ya wuce ace tayi soyayya ko ya auri gurgu, ya tabbatar tausayi ne kawai take mai shima da kunya ya dubeta yace yanaso. "Da me kenan?" Yai tambayar idanunsa cikin nata, kallan shigarta yai riga ce ta ɗan wuce mazaunanta kaɗan sai pencil jeans sai kuma kanta datai rolling da mayafi, yanayinsa ne ya canza nan danan kishi ya turnikeshi taya zata fita a haka? Zee kuwa sam ta manta da shigar da tazo dan hankalinta sam ya tafi da jin auren Asiya. Katse mai tunani tai da cewa "Your Ex itace tai aure ko?" Kallanta yai yace "Oh I thought wani abin ne, yeah na gani." Ta ɗan mai wani kallo tace "Na ɗauka zan ganka kana zazzabin aureta da akai." "In akwai so da matsayi kenan a zuciyar mutum ko?" Kai ta jinjina tace "Yanzu babu?" Tai tambayar cike da san jin amsarsa, wani shanyayen kallo ya mata wanda yasa taji duk komai na jikinta ya sage yace "A haka kike yawo?" Kallan jikinta tai nan taji shakuwa tazo mata, mai makon ta amsa mai tai saurin shigewa ciki tana ƙiran sunan Dada. Dada kuwa tana jinta ta fito tace "Lale da Abu na ai saura kaɗan na sa cigiyarki gidan radio nidai bana iya jure rashin zuwanki dayawa." Rungume Dada tai tace "Allah sarki Dada ta bana san zuwa ne akai-akai kar wasu su fara tunanin gunsu nake sintiri." Tai maganar tana kallan Baqeer, wanda ke zaune ya harɗe hannu yana kallansu, Dada ta kalleshi itama tace "Tab to ba sai suyi tunaninsu su gama ba ni dai nasan guna kike zuwa dan kuwa bazaki zo gun Baqeeru ba yo wannan ma me zai kawoki gunshi? Yaran da magana ma sai ya dinga shan kamshi kafin yai?" Kallansa tai tana guntse dariya ta tace "Ah to Dada kema kinsani ai," cike da zolaya take maganar, lemon ya ajiye yai hanyar ɗakin shi sai dayazo daf dasu yace "Da ɗinta ma nasan ba guna ake zuwan ba." Dada tai caraf tace "Yadai fi maka, ah to tun kafin ka hanamin ita zuwa gwara da ka sani." Har ya shiga ɗaki tana satar kallanshi shima sai dayaje ƙofa ya waigo, da sauri ta ɗauke kai tace "Dada wallahi aikena akai na gudo ganinki bari naje zan dawo." "Kai nidai bangaji da ganinki ba amma bakomai ki taimaka ki dawo." To tace sannan ta juya, Baqeer kasa shiga ɗaki yai har sai da ta bar gidan, idanu ya lumshe inama ba a kujerar guragu yake ba ya sanar da ita abinda ke ranshi? Ya zaiyi da wannan san dake cika mai zuciya? Zeey kuwa gun aiken da Mumy ta musu ta nufa ga mamakinta Nabila bata nan, waya ta mata sai jitai wai tana gida batajin da ɗi, kai Zeey ta girgiza a fili tace "Itadai Aunty Nabs batasan zuwa gun in ba dani ba, na rasa wace irin kunya gareta." Nan ta nufi gida tana mamakin kunya da kara irinta Nabila sam bata hayaniya ko faɗa bakaji tanayi, itafa sam bazata iya irin wannan abubuwan ba dan ko yanda bata iya faɗar abu in ranta ya ɓaci mamaki take bata. **** Asiya Amarya da Bello an tare an kuma sha roman soyayya, ya kashe kudi dan duk kudin da aka bashi na tafiya ya juyesu a bikin nan, Abuja sukaje ya kama musu hotel sukai kwana biyu sannan ya wuce ƙasar Germany inda anan zasuyi jarabawar shiga, duk wanda suka ɗauka zasu ɗau ki nauyin iyalinshi da karatunshi har na tsawon shekara biyar. Asiya haka suka zo airport babu abinda take sai ɗaukan selfie tana sawa a IG kwanan nan da ɗi takeji, ji take kamar tafi kowace mace gata, shiyasa yanzu ba kowa ma take kulawa ba, Habi ma in tana mata magana kamar wata ƴar aikinta haka take mata, shima Bello duniya tai da ɗi matsalarshi ɗaya mahaifansa da suke neman takura mai, shiyasa yanzu yakejin da ɗi zasu bar kasar ma su huta, sunyi akan in yaje yai wata ɗaya zaizo ya ɗau keta dan itama tay applying visa, haka ya wuce ita kuma ta hau jirgi ta dawo Kano tawa Habi waya akan tazo su zauna saboda batasan zama ita kaɗai, taso kin zuwa sai dai mahaifinsu ya sata taje a ganinshi bai dace a barta ita kaɗai ba.