Baqeer complete - Chapter 39
Baqeer complete Chapter 39: Baqeer complete Chapter 39. ***** Yau Baqeer cikin farin ciki suka tashi don an samu mai siyan fili, an turo rabin kuɗin suka…
2,799 words
***** Yau Baqeer cikin farin ciki suka tashi don an samu mai siyan fili, an turo rabin kuɗin suka je shida Salim ya cike form akan zai fara zuwa, sun yi mamakin ganin gurgu da zuwa koyon ɗinki amma jin yace da keken electric zai yi yasa suka amince, sun yaba sosai da yanda duk da rashin ƙafarshi bai hanashi neman abinda zai taimaki kanshi dashi ba, Baqeer nada kyau sannan yana da cikar zati hakan yasa ko a baya mata ke sonshi, a yanzun ma in ba ganinshi aka yi akan wheelchair ba ba'a kawowa yana da nakasa, sun fito bayan sun yi registeration, ajiyar zuciya yayi ya kalli Salim wanda shima kallonshi yake yi kafin a hankali suka yi murmushi yace "Yanzu gobe zaka fara zuwa?" Kai ya ɗaga alamar eh yace "Zamu dinga zuwa da Tanimu kai dai ka cigaba da zuwa kasuwarka kafin na gama In Sha Allahu." Cike da gamsuwa ya jinjina kai yace "Hakan yayi amma ragowar kudin filin fa? Zan turoma yanzu." Kai Baqeer ya girgiza alamar a'a yace " In har da hali yanzu muje bank mu buɗe wani account na saka a ciki ya zama na sana'a ne, bana son mu saka kuɗin a gaba kuma in na gama koyan muzo babu halin buɗe shagon." Kallonshi yayi yace "Hakan yayi, mu je?" Nan suka hau adaidaita sukaje bank na GT suka buɗe account aka tura ragowar kuɗin ciki sannan suka koma, a hanya ya turawa Umma, Hadiza da Maryam kuɗi daga cikin na fili, sannan ya turawa Salim, suka ɗan ƙaro abubuwan gida sannan suka dawo a gajiye gashi gobe zai fara zuwa school. Sun shiga gida yana shiga tsakar gidan idonshi ya sauka kan Zee dake tsaye rike da ludayi, kallon mamaki yayi mata sannan ya kalli ludayin hannunta yayi mata sign da gira akan me take yi? Cike da sakalci tace "Oho, nima Dada tace na tuka mata wai tuwo." Ya kalli ludayin miyar dake hannunta sannan yace "Da wannan?" Ludayin tayi saurin ajiyewa tace "Ahh na manta bari na amsa waya tuntuni ake kirana, tayi maganar tana guduwa daga wurin, Dada ce daga ciki take cewa "Zainabu? Kin tuka?" Ta ƙarasa maganar tana fitowa daga ɗan store ɗin da suke ajiyar kayayyakin su na buƙata, ganin Baqeer tayi a zaune yana kallonta shima ta ɗan waiga tace "Tana ina?" Alama yayi mata da ciki yace "Yaushe tazo?" Ta ɗauki muciya tana cewa "Dazu, kun cike fam ɗin?" Ya ɗaga kai yana shiga ciki, Zeey kuwa data samu ta gudu tana zama a kujera ta sauke ajiyar zuciya lallai tasha da ƙyar wai, me yafi wannan abun kunya in Baqeer yasan bata iya komai ba? Shigowa yayi ya ɗan tsaya gefen ɗakin shi yana kallonta, ita ma kallonshi tayi zuciyarshi na sake jin wani daɗin ganinta da yayi, kwantar da kanta tayi saman kujera tace "Shine ka tafi babu ni?" Wani kallo ya mata tayi saurin cewa "Bafa da wani abu ba amma da mun je tare, ko nima na shiga makarantar mu dinga zu……" kallon da yayi mata ne yasa ta turo baki ta sake maida kanta tace "Na haƙura to," tayi maganar tana kallonshi. Ɗan murmushi yayi kaɗan wanda ya sata zuba mishi ido ita kam ya zata yi da son Baqeer? Ya dago yace "Sai kuma kice zaki shiga makarantar koyon ɗinki saboda me?" Har yanzu kanta na kan bayan hannunta akan hannun kujerar tace "Kawai!" Ya maimaita kalmar tare da cewa "Ban saki ba, kema ki duba abinda kike so kiyi." Ji tayi cikin ranta tace "Kai ne ai." Kallonta yayi jin kamar yaji alamun maganar ta amma bai ji komai ba yace "Me kika ce?" Da sauri ta zauna tace "Ban ce komai ba." Kai ya jinjina zai yi magana sai ga Dada ta shigo tana cewa "Abu ashe kina ciki?" Tace "Waya aka yi mini daga nan kuma na zauna, au bari na tuƙa miki tuwon." Tayi maganar cikin ɗan dauriya, nan tace "A'a yi zamanki ma don ni kam na riga na tuƙa ai, kada ki damu." Ta kalli Baqeer tace "Kayan da Salim yasa a shigo dasu duk namu ne?" Kai ya ɗaga yana cewa "Eh." Ta koma ta shigo da leda tana cewa "Wannan naga kayan shafe-shafe ne? Anya nawa ne ba na Zainabu ba?" Ɗagowar da zai yi sai yaga idon Zeey a kanshi da sauri yace "Naki ne mana Dada." Ta kalleshi tana cewa "A'a fa ban yarda ba ina ni ina shafa irin wannan man? Zainabu ba irin shi bane wanda kika taɓa shafa mini wani mai kalar manshanu?" Dariya suka yi, Zeey tana kallonta tace "Mugani." Miƙa mata tayi Zeey tana buɗewa taga brand na man da take shafawa, hand lotion ɗin irinshi ne sak wanda take sawa a jakarta, da mamaki ta kalli Baqeer wanda yayi saurin shafar bayan kanshi kawai ya gurgura kekenshi yayi ɗaki, sam ya manta lokacin da suka siyo bai ɗauke shi ba daga cikin kayan, yanzu gashinan Dada ta gama bashi kunya don shi kam bai isa magana ba. Zeey kuwa murmushi tayi don ta tabbatar nata ne, sai ga Dada ta sake shigowa da wata ledar tace "Ahaf ni nasan wannan naki ne, kinga mai gurguwa gashinan nawa." Murmushi tayi tana cewa "Kila dai wannan ɗin ma ke ya sayawa." Baki ta taɓe tace "Ni dai kam na bar miki in ma ni ɗin ce don ban isa ba." Har Zeey ta fito daga gidan Baqeer bai leƙo ba.
****** Badaru ne ya dawo daga kasuwa duk yana jinshi a gajiye, ganin abokanshi yayi a zaune suna hira da alama wani abun ne ke shirin faruwa, wajen yaje yana cewa "Ahh Malam Iro kune?" Ga mamakinshi ɗif suka yi kamar ba sune ke hirar nan ana dariya ba, nan fa ranshi yayi mugun ɓaci ganin sun fara watsewa ɗaya bayan ɗaya, nan fa ya sake kaiwa bango ya kalli Malam Iro yace "Wai har da kai? Wani irin cin zarafi kuke neman yi mini ne?" Malam Iro yayi gyaran murya yace "Kai matsalarka kenan faɗa da kuma zargi, zancen Bello muke yi da zai tafi ƙasar waje bayan auransu da kwana biyu to mun san halinka shi yasa muka yi shiru." Ai kuwa kamar an taɓoshi ya fara cewa "Ya tafi sararin samaniya ma ba ƙasar waje ba, yo dama munafiki har ya isa a daraja shi? To sai me? Sai me in yaje? Ko banza dai da ba don ɗana ba bai isa ya zama wani ba, banzaye kawai munafukai." Ya juya yana cigaba da zazzaga masifarshi, yana shiga gida kai tsaye ɗakin Fatima ya shiga, a lokacin tana waya da Baqeer tana yi mishi faɗa akan don me zai turo musu kuɗi bayan yana da abubuwan yi masu muhimmanci a gabanshi, ai tana jin muryar Badaru ta kashe wayar da sauri, sai kuwa gashi ya shigo rai a ɓace yace "Allah ya isa cutata da kuka yi, kun munafurceni yaron nan don baƙin hali ya hanani jin daɗin rayuwa wallahi sai kun san kun yi dani." Umma cike da takaicin kalamanshi tace "Mallam yanzu ya dace ka riƙa yin magana akan ɗanka haka?" Yatsa ya nuna mata yace "Kafin na zabga miki mari kiyi mini shiru, kece ai baƙar munafukar." Ya juya rai a ɓace ya bar ɗakin, wayarta taje ɗauka me zata gani? Ashe bata kashe wayar ba, hankali a tashe tasa wayar a kunne tace "Baqeer?" Kasa magana yayi kawai ya kashe wayar yana jin wani abu ya tokare mishi maƙoshi yana neman hanashi numfashi. A hankali ya shiga neman jawo numfashinshi yana sauke ajiyar zuciya, wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka Umma ce sai yaga Zeey ce, saƙo ta turo mai 'In nawa ne thanks in ma ba nawa bane thanks'. Kallon sunan ta yayi yana tunanin yanda ta shigo rayuwarshi daidai lokacin da yake neman wanda zai fahimci halin da yake ciki, ta shigo rayuwarshi daidai sanda yake neman wanda zai nuna mishi hanya. Saƙo ta sake turowa 'Me kace?' Maimakon ya amsa mata sai ya kira Umma saboda ƙaramar nutsuwar da tazo mishi din yasan tana cikin wani hali yace "Umma karki damu, bansa abinshi a raina ba ina fata kema bazaki saka ba." Bayan sun yi sallama ne taji hankalinta ya ƙara kwanciya Allah dai ya raya mata Baqeer ya kare mata shi. ***** Zeey kuwa fitowa tayi daga ɗaki ganin Baqeer bai mata reply ba, kitchen ta shiga ta kalli masu aikinsu tace "Babba ni kam ya kuke tuƙa tuwo?" Da mamaki Mummy dake tsaye tace "Ke kuma me ya haɗaki da tuƙa tuwo?" Kallon Mummy tayi sai kuma ta ƙarasa wurinta ta rungume ta tace "Haka kawai naji curiosity na son in sani nasan naga suna yi amma ban taɓa gwadawa ba." Shafar kanta tayi tace "Kada ki wani damu da harkar kitchen ke ƴar gata ce duk mai aurenki ma sai ya amince da mai aiki sannan ni da kaina zan nemo mai aikin ke dai ki zauna cikin farin ciki kici kisha." Nabeela ce ta girgiza kai cike da takaici tace "In kuma mijinta yace sai tayi mishi girki fa?" Wani kallo Mummy tayi mata tace "Wannan kuma ba damuwarki bane, sannan in tayi auren in baya son me aiki sai na dinga aika mata abinci daga gidan nan, Nabeela wai ni kam menene matsalarki?" Kai kawai ta sake girgizawa ta juya, Zeey tabi bayanta da kallo. Hanyar ƙofar ɗakin Kabir tayi bata san Mummy ta biyota ba sai ji tayi tace "Uban me zaki yi anan?" Waigowa tayi da sauri ta ɗan kalleta a tsorace kafin tace "Babu komai kawai airpod ɗinshi zan ara." Wani kallo ta sake yi mata tace "Wuce kafin ranki yayi mugun ɓaci, wallahi kin sani nace a'a bana son hauka bana son rashin hankali da tunani." A fusace tayi ɗakinta tana tunani ai zata tafi ta kwanta don haka dole ne taga Kabir babu mai hanata. Zeey kuwa ɗaki ta shiga ta duba wayarta saƙon Baqeer ta gani yace 'Me kika ce?' Murmushi tayi tace "Inyi godiya?" Shima reply yayi mata "An yafe miki shi." Bargo ta shige ta sauke ajiyar zuciya tana jin ƙaunar Baqeer na sake ratsata, gaskiya tana buƙatar hoton Baqeer a wayarta, especially in tayi missing ɗinshi. A hankali ya shigo gidan don ya tabbatar sun yi bacci, tun sanda Nabeela tayi mishi kiss yake jin wata irin sha'awa na taso mishi, gudun ɓarna yasa yaƙi zaman gidan, hannunshi yaji an riƙo, dayake duk fitilun gidan a kashe suke yasa yace "Waye?" Jan hannunshi tayi zuwa ɗakinta, yana shiga dim light ɗin dakin yasa ya ganeta, ajiyar zuciya yayi yace "Nabee……" Sumbatar da ta kai mishi ne yasa ya kasa ƙarasawa….
😒Umm Asghar ne da Ayusher suka kalli juna suka ce "to meke faruwa ne"❓
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BIYU*
{52}
Bai san lokacin da ya fara mayar mata da martani ba domin kuwa ta tayar mishi da wani tsumi ne da bai san dashi ba, tun da ta mamaye shi tayi mishi kiss ɗinnan shikenan ya shiga cikin wani hali, dauriya kawai yake yi amma sai yaji babu abinda yake da buƙata face son kasancewa tare da ita hakan yasa ya kasa tanƙwara zuciyarshi har yaga rashin dacewar abinda suke yi sai kawai ya biye mata suka cigaba da aikawa da juna zafafan saƙonnin da suka sake fitar dasu daga hayyacinsu, kafin wani lokaci har sun dire akan gadonta sai da tafiya tayi tafiya tukunna Kabir ya dawo cikin hayyacinshi ya tuna wacece Nabila a wurinshi da abinda suke shirin aikatawa. Hankaɗeta yayi daga jikinshi ya tashi ya mayar da suturar shi da tuni suka yi watsi dasu suka yi nasu wuri, ko kallonta baya son yi don baya son ganinta a yanayin da take ciki, shi ya rasa wace irin jaraba ce wannan duk yadda yake kakkauce mata sai da tayi nasarar ribatarshi, in banda Allah ya kiyaye yasan da ƙyar idan basu aikata ɓarna ba. Yana gama saka kayanshi ya fice daga ɗakin yana sauke ajiyar zuciya ranshi fal takaicin Nabila. Yana fita tabi ƙofar ɗakin da kallo tana jin takaicin haƙanta da bai cimma ruwa ba don ita a tunaninta idan har ta ribace shi wani abu ya shiga tsakaninsu dole Mummy ta haƙura ta ƙyalesu suyi aure don a ganinta Mummyn ce babbar matsalarta ba wai Kabir ɗin ba. Tashi tayi ta faɗa banɗaki ta kimtsa jikinta sannan ta fito tayi shirin kwanciya bacci ta haye gadonta tana tariyo abinda ya faru a tsakaninsu bada jimawa ba tana jin wani irin daɗi da shauƙi yana ɗibarta. Shi kuwa Kabir yana shiga ɗakin shi ya dannawa ƙofar key don baya so Nabila ta ƙara mamayar shi ta shigo mishi ɗaki bai sani ba, yanzu in banda Allah ya kiyaye da bai san a wane hali zata saka shi ba gashi nan yanzu ta tayar mishi da abinda daa can kwata-kwata bai san dashi ba. Haka ya kasance cikin wani hali har ya dinga ji ko dai ya tashi ya buɗe ƙofar ɗakin ne watakila ta biyoshi sai dai kuma yana kwaɓar zuciyarshi akan wai me yake tunanin aikatawa, shin yana da tabbacin idan ta shigo ɗakin nashi zai iya controlling kanshi kamar yadda yayi a baya? Bai san lokacin da bacci ya ɗaukeshi ba ya dai saka a ranshi cewa dole ne ma ya taka mata burki idan ba haka ba taja shi ga aikata dana sani, shi kuma abinda baya fata kenan a rayuwa.
***** Baqeer ya samu ya fara zuwa tailoring school ɗin, kullum da safe Tanimu yake zuwa ya turashi zuwa bakin titi inda zai tarar musu adaidaita su tafi Makarantar, daga baya ma sai ya nemi wani mai adaidaitan ɗan nan unguwar suka yi ciniki kullum shi yake zuwa ya ɗauke su ya kai su can makarantar idan lokacin tashi yayi yaje ya ɗaukosu ya dawo dasu gida. Sosai Baqeer ya mayar da hankali akan koyon ɗinkin, matsala ɗaya da yaci karo da ita shine da aka ce dole sai sun koyi ɗinki akan normal keke kafin su fara akan mai aiki da wutar kasancewar shi me matsalar ƙafa duk da a yanzu ya fara iya motsata kaɗan-kaɗan saboda physiotherapy session da suke yi da Junaid ga kuma exercises ɗin da koyaushe yake yi a gida, a hankali a hankali ya fara iya motsa ƙafar saɓanin da da baya jin alamun ta ma a jikinshi, a yanzu ya fara jin feelings a wurin sai dai ba zai iya sarrafata yayi kowane irin amfani da ita ba. Duk da wannan matsalar daya samu ta rashin iya taka keke da kanshi duk da buƙatar hakan da ake yi wajen koyon ɗinkin ya mayar da hankalinshi ƙwarai wajen iya sarrafa almakashi don sosai ya ƙware a iya yanka ya kuma iya fitar da designs masu kyau, ɗinkin ma yana gwadawa akan electric machine ɗin tunda ba zai yiwu yayi akan manual keken ba. Wani abun burgewa da yayi shine daya saka Tanimu a makarantar koyon ɗinkin tunda ya nuna sha'awarshi ga ɗinkin sai ya biya mishi duk kuwa da tsadar kuɗin makarantar tunda dama tare suke zuwa yana taimaka mishi da ƴan ƙananun abubuwa irin su taimaka mishi ya hau kan kujerar wheelchair ɗin shi da turashi zuwa duk wani wuri da zai je haka a cikin makarantar ko zuwa mishi aiken sayen wani abu na daga kayan ɗinki haka. Duk da har yanzu mutanen can basu ƙara waiwayarshi da batun contract ba da ɗan abinda yake samu daga zanen da yake yiwa Sani tela ya ɗauke nauyin duk wasu buƙatun shi dana mahaifiyarshi da ƴan uwanshi, da yake yanzu akai-akai Sanin yake zuwa yana sayen zane a wurinshi. Har yanzu dai Sanin ne kawai wanda yake yiwa zane yana biyanshi amma dai Alhamdulillah yana samu bakin gwargwado tunda bai nemi komai ya rasa ba, duk wani abu da yasan zasu buƙata yana ƙoƙarin ganin ya ajiye musu shi, haka nan Umma kullum cikin yi mata aiken kuɗi yake ita da ƴan uwanshi Hadiza da Maryam. To itama Hadizar ga yadda yake ji tana samun rufin asiri da injin markaɗenta don haka ya ƙara samun kwanciyar hankali tunda yasan a yanzu basu da wata gagarumar matsala a rayuwarsu.