Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 38

Baqeer complete - Chapter 38

Baqeer complete Chapter 38: Baqeer complete Chapter 38. Hankali a tashe Zainab ta ƙaraso gidan, ita ta taimakawa Dada ta sakata a mota Baqeer na biye dasu…

2,604 words

Hankali a tashe Zainab ta ƙaraso gidan, ita ta taimakawa Dada ta sakata a mota Baqeer na biye dasu akan wheelchair ɗin shi sai sannu take zubawa Dada. Wani private clinic ta kai su don tasan idan suka tafi asibitin gwamnati sai sun bi dogon layi, zasu daɗe sosai kafin su samu ganin likita ita kuma a yadda take ganin yanayin jikin na Dada sai take jin ba zata iya kaita inda zata kusa yini bata samu ganin likita ba. Duk wani kai kawon buɗe folder da kama Dada su shiga ɗakin ganin likita duk Zainab ce tayi shi Baqeer nashi kawai ya bayar da kuɗin da aka nema shima don yaƙi yarda Zainab ta kashe musu ko sisinta yace ɗauko su da tayi ma ya wadatar. Sai sintiri take yi ta kasa zama wuri ɗaya don ganin an bawa Dada kulawar data dace. Bayan fitowarsu daga wajen likita ma ita ta tafi da takardar da aka rubutawa Dada magani taje ta sayo a pharmacy, duk inda tayi yana binta da kallo yana tunanin matsayin data taka a zuciyarshi, yana mamakin irin muhimmancin da ya bata don bayan Umma da ƴan uwanshi itace mace ta farko da zai iya neman wata alfarma a wurinta idan buƙatar hakan ta taso don yasan kome take yi zata ajiye tazo inda yake. Anan ya ƙara tabbatar da lallai ta samu babban matsayi a cikin zuciyarshi da bai san lokacin da hakan ya faru ba, babu wani abu da zai yi ya biyata ɗawainiyar da take yi dashi. Tana ta wannan kai kawon a cikin asibitin ashe Mummy nata kiranta a waya ta saka wayar a silent bata sani ba. Sai da aka gama komai har magunguna sun karɓa sannan suka bar asibitin lokacin wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a hanyarsu ta komawa sun zo daidai kan traffic ɗin kwanar sabo ta kalli masu sayar da fruits daga gefe sai ta juya ta kalleshi tace "Am Ya Baqeer." Juyowa yayi ya kalleta sai yaga ita ma shi take kallo wani irin kallo mai ƙoƙarin fallasa asirin dake binne a cikin zuciya, idanunshi ya zuba a cikin nata yana yi mata kallo kwatankwacin wanda take yi mishi, zuciyarshi har bugawa take yi fat-fat kamar zata faso ƙirjinshi ta fito. Wani ƙayataccen murmushin daya saka Zeey jinta tana yawo tamkar akan gajimare don daɗi ya sakar mata kafin ya janye idanunshi daga kanta yana ƙoƙarin danne abinda yake ji yana taso mishi a kanta. Sai da yayi gyaran murya don daidaita muryarshi kada ta gane halin da zuciyarshi take a ciki yace "Wani abu kike so?" A daidai lokacin kuma motar dake bayansu ta danna wani uban horn da yasa Zeey ta firgita, sai lokacin ta lura ashe har an basu hannu motocin gabanta duk sun wuce bata sani ba. Jan motar tayi suka bar wurin sannan tace "Na'am." Ita ma tace tana basarwa kamar bata fahimci tambayar da yake yi ba, girgiza kanshi kawai yayi ya basar don yasan da gangan ta amsa shi a hakan. Lokaci bayan lokaci suke satar kallon juna suna jifan junansu da murmushi mai ratsa zuciya. Ita dai Zeey ta gama haƙiƙancewa ranta son shi take yi da gaske ba da wasa ba shine dai har yanzu take tantamar anya kuwa ta samu zuciyarshi kamar yadda yayi kaka gida a tata. Ita dai Dada tana kwance a bayan mota bata san wainar da suke toyawa ba har suka ƙaraso gida. Da taimakon Zainab Dada ta shiga cikin gida, bata zauna ba tayi mata sallama ta tafi sai data fita sai taga har lokacin yana cikin motar ashe. Fitowa tayi da wheelchair ɗin daga boot ta buɗe ta ajiye a gabanshi daidai yadda zai iya hawa. Da kulawa take kallonshi tace "Zaka iya kuwa, ko na samo wanda zai taimaka maka ka hau?" Girgiza kanshi kawai yayi sannan ya daddafa da ƙyar ya koma kan wheelchair ɗin, ita kuwa sai faman jera mishi sannu take yi kamar mai ciwo, sai taji gaba ɗaya ya bata tausayi kamar ta ɗauke larurar ta mayar jikinta haka take ji. Kasa tafiya tayi har sai da taga shigar shi cikin gida sannan taja motarta ta bar wurin tana jinjina yadda ta ɗauki al'amuranshi da girma haka, sam bata iya sukuni idan har ya buƙaci wani abu bata yi mishi ba.

***** A hankali Nabeela ta tura ƙofar ɗakin ta shiga cikin sanɗa kamar mai gudun kada wani ya ganta. Bata ganshi akan gado ba don haka ta hau jujjuyawa tana ƙarewa ɗakin kallo, motsin da taji daga banɗaki ne ya bata tabbacin yana ciki sai ta shige can cikin ƙuryar ɗakin inda kayan gadonshi suke ta kishingiɗe akan gadon tana danne-danne a wayarta. Bata daɗe da kwanciya ba sai gashi ya fito da towel ɗaure a ƙugunshi sai wani ɗan ƙarami a hannunshi da yake goge ruwan jikinshi dashi. Tana kallon duk abinda yake yi daga nan inda take sai dai ko motsi bata yi ba bare yasan da wanzuwarta a cikin ɗakin har ya gama shiryawa cikin wandon faded jeans baƙi da polo shirt kalar maroon. Sai sannan ta taso cikin rangwaɗa ta nufi gaban madubi inda yake duba tarin turarukanshi yana zaɓar wanda zai fesa. Yana ganinta ya haɗe rai tamkar bai taɓa dariya ba sai dai ko a jikinta ɓacin ranshi bai hanata nufarshi ba kamar yadda tayi niyya sai ma ɗaukar ɗaya daga cikin turarukan tayi ba tare data duba ko wanne bane ta rangwaɗar da kai gefe guda cikin wani irin salo na jan hankali tace "May I?" Bata jira jin ta bakinshi ba kawai sai ta hau fesa mishi turaren a dukkanin jikinshi, takaici ne ma yasa ya tsaya ƙiƙam kawai yana kallonta yana mamakin ƙarfin hali irin nata da bata jin duk jan kunnen da yake yi mata akan shigo mishi ɗaki. Kwalabar ta ajiye ta ɗora hannunta akan kirjinta tana yi mishi wata irin shafa da tasa ya kusa rasa nutsuwarshi, bai yi aune ba kawai sai jin saukar leɓunanta yayi akan nashi cikin wani tattausan kiss, duk rashin jin Kabir baya kule-kulen mata, barshi dai da son harkar chilling da clubbing amma sam babu ruwanshi da shiga sabgar mata shi yasa abun yazo mishi a bazata. Bai san lokacin da ya fara mayar mata da martanin kiss ɗin ba sai can kamar wanda aka yiwa raɗa cikin kanshi ya tuna wacece ita da matsayinta a wurinshi, da sauri ya hankaɗeta yayi baya ya bayar da tazara mai yawa a tsakaninsu ranshi a matuƙar ɓace da wannan rashin hankalin da tayi mishi. A fusace yana nunata da yatsa yace "Bana son iskanci fa Nabila wallahi idan baki fita sabgata ba zan yi miki rashin mutunci irin wanda baki taɓa tsammani ba, haba wannan wacce irin jaraba ce? Ana so dole ne ko an gaya miki kowa ma jaki ne dabba wanda baya aiki da tunani da zaki yi tunanin wani abu makamancin wannan zai taɓa shiga tsakaninmu, ko kin manta ke wacece a wurina da zaki dinga damuna da abin da kika san ba zai taɓa yiwuwa ba, to wallahi ki fita a hanyata kada ki ƙara shigo mini ɗaki idan ba haka ba duk wulaƙancin da nayi miki ke kika saya da kuɗin ki." Yayi tsaki kawai ya fice ya bar mata ɗakin don bama zai iya tsayawa ya jirata ta fita ba. Haka kawai shi da ɗakinshi da gidansu amma tana nema ta takura mishi, yanzu gaba ɗaya baya iya sakewa a cikin gidan don yana tsoron yadda take yawan shigar mishi ɗaki ba tare daya sani ba.

***** Tana komawa gida ɗakinta ta wuce tayi sauri ta shiga wanka ta shirya a gurguje don sai bayan dawowarta sannan ta tuna ashe fa akwai inda zasu je ita da Mummy shaf ta manta saboda hankalinta daya bar jikinta tunda ta amsa ƙiran Baqeer tunaninta gaba ɗaya ya koma wajenshi, bata tashi tunawa ba sai data ɗaga wayarta don ta duba lokaci taci karo da tarin missed calls ɗin Mummy. Sassauƙar shiga tayi cikin pencil trouser da kaftan top data kai mata har wajen gwiwa, medium veil tayi rolling a kanta ta ɗauki turaren wurin Baqeer tayi amfani dashi da tunda ya bata ta daina amfani da kowane turare idan bashi ba har gashi ma ya kusa ƙarewa. Sai data gama shirinta tsaf sannan ta fita zuwa ɗakin Mummy. Tana shiga Mummy tace mata "Ina kika shiga yau tun safe bayan kin san zamu fita kuma shine nayi ta kiranki a waya baki ɗauka ba?" Langaɓar da kanta tayi gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Ayya, i'm sorry Mum wallahi wani ɗan uzuri ne ya fitar dani kuma wayar tawa a silent take ban tashi ganin missed calls ɗinki ba sai da na kusa ƙarasowa gida, i'm sorry please bazan ƙara ba," ta ƙarashe maganar tana kama kunnuwanta duk cikin ban haƙurin. Girgiza kai kawai Mummyn tayi tace "Idan ban haƙura ba ya zanyi dake Zeey, most a times nafi ganin laifin kaina don ni na sakar miki da yawa har haka shi yasa kike abubuwan ki babu shakkar abinda zai je yazo amma in banda haka bayan kin san Daddynku yana gari shine kika saka ƙafa kika fita tun safe ba tare da sanin kowa ba salon idan ya tambayi ina kike na rasa amsar bashi ko."

"Please mana Mum tunda nace kiyi haƙuri ba sai ki haƙura ba abar maganar, yanzu dai gani na shirya ko mun fasa fitar ne na tafi naje na kwanta?" Ta ƙarashe da tambayarta. "Hmm" kawai Mummy tace tana jin rashin daɗin yadda Zainab tayi mata magana sai dai kuma baza ta iya tsawatar mata ba don tana ganin ai har yanzu Zeey ɗin yarinya ce shi yasa bata tauna magana kafin ta faɗeta tasan data ƙara girma zata daina duk irin waɗannan abubuwan da bata so ɗin.

*****

Tun da ya samu aikin contract ɗinnan sai yake ganin bama lallai ne sai ya sayar da filinshi ba yana ganin a cikin abinda zasu bashi ya isa yayi amfani da kuɗin ya biya tailoring school ɗin da yake son shiga sai dai kuma har wasu kwanaki mutanen basu ƙara tuntuɓarshi ba don haka ma yake ganin kamar dama dai wasa da hankalinshi kawai suke son yi, gashi ƴan kuɗaɗen da suka rage mishi a account ma har sun ƙare shima Sani telan bai ƙara nemanshi ba duk da tabbacin daya samu daga wurin Zeey na yayi styles ɗin ɗinkunan daya karɓa a wurinshi har ma yayi wa wasu da yawa irinsu kenan dai yayi ciniki sosai da styles ɗin, yayi mamaki da har yanzu bai dawo ba don shi kanshi sai da ya leƙa shafin shi na IG ɗin yaga yadda yayi ɗinkunan sosai da yawan likes da comments ɗin daya samu na masu son yayi musu irin wannan ɗinkin. Har tsawon sati biyu mutanen nan basu ƙara nemanshi ba don haka yaga baya fa da wata dabara baya ga ya saka filinshi a kasuwa duk kuwa da a farko burinshi ya gina wurin ne, daya samu contract ɗinnan har ya fara murna don yana ganin ba lallai ne sai ya sayar da filin ba amma yanzu idan har yana son shiga tailoring school ɗinnan tofa lallai ne sai ya haƙura da filin nan duk kuwa da yadda yake son gina wurin saboda yadda tsarin wurin yayi mishi, unguwa ce da babu hayaniya tsarin wurin yafi kama da tsari irin na GRA shi yasa ma ya zaɓi sayen fili a wurin saboda irin waɗannan unguwannin na burgeshi yadda basu da cinkoso da hayaniya rayuwar babu ruwan wani da wani bare aje ana saka maka ido a al'amuran rayuwarka.

Waya ya ɗauka ya kira Salim ya faɗa mishi abinda ke faruwa da abinda yake so yazo suyi saboda a yanzu shine kamar manager ɗin shi baya komai sai da shawarar shi, da shi kaɗai ya yarda a halin yanzu don shine mutum ɗaya tilo da bai juya mishi baya ba bayan Ummanshi da ƙannenshi guda biyu Maryam da Hadiza sai ko Zainab da duk abinda ya zama a yanzu yake ganin ita ce sila, he will forever be indebted to her don tayi mishi abinda wani makusancin bai yi mishi ba a rayuwa...

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA ƊAYA*

{51}

Sun saka filin a kasuwa dan haryau dai mutanen basu ce komai game da contract ɗin Baqeer ba shima kuma yana tunanin in ya nemesu zasu ga kamar a matse yake, haka Salim yazo aka sa fili a kasuwa, Umma har sadaka tayi akan Allah yasa komai ya tafi daidai ya bawa Baqeer sa'a don ita kam kwanan nan rayuwa kawai take yi amma babu abinda ke faranta mata rai, a koda yaushe tunaninta yadda zata taimakawa Baqeer har yau tana mamakin yadda ko da wasa Badaru bai taɓa tambayarta Baqeer ba illa harkarshi kawai da yake yi, wannan abu na daure mata kai, wai mahaifi? Yau tana zaune tana fanken sadaka, Abu ta fito da ƙatuwar leda ta ajiye a waje tana kiran Jamila, Umma ko kallonsu bata yi ba balle ta so sanin menene a ciki, Jamila ta fito tana kallonta tace "Saƙon Nusaiban ne?" Abu ta ɗan kalli Umma ta gefen ido tace "Wallahi shine ai dai babu abinda yafi komai daɗi irin Allah ya baka ɗan da zai fitar da kai kunya, yanzu ke kiga abinda ta aiko mun, da ana yi mata kallon wacce bata dashi sai gashi yanzu tafi wacce tayi auran daɗi taimakon iyayenta." Dafata Jamila tayi tace "Yoo wai ba ita ce naji ana zargin uban miji na sintiri ba? Yayi shima ɗa yayi?" Tsabar tashin hankalin da Umma ta shiga taje jefa fanke cikin mai sai ji tayi man ya ƙonata ashe hannunta ta kai kai, cike da tsoro ta kalli Jamila tace "Jamila ni kam kin san harshe yana daga cikin babban abinda ke kai bawa wuta ko?" Kallon Umma tayi tace "To ni dai ba dake nake ba balle kiyi mini wannan mumunan zaton, zance ne nake yi akan labarin da naji a radio, bana son sharri ban kuma san ayi mini ƙazafi." Abu tayi saurin fito da kaya tana cewa "Meye abun tsarguwa in har kun san kuna da gaskiya?" Umma komawa tayi ta zauna tasa ruwan sanyi ta cigaba da suyar ta idanunta sunyi jaa, tabbas sai Allah ya yiwa Maryam sakayya, dama ya za'ayi uban miji ya zauna a cikin gida? Tasan ko ba daɗe ko ba jima wani sai ya faɗa musu baƙar magana akan hakan, da ƙyar ta gama suyar ta zuba musu ta ajiye sannan ta bada aka fita dashi. Tana shiga ɗaki Jamila tayi tsaki tace "Wai kuɗin kujerun ne har yanzu bata cinye ba?" Abu ta ɗauke kai tana duba atamfar da aka kawo mata, sai yanzu ma data kula taga mai arhace haushi duk ya isheta ta maida ita leda tana cewa "Inba su ba ina taga kuɗin kashewa? Bayan yanzu ficika Mallam baya bata?" Nan dai suka cigaba da gulmace gulmacensu na hassada suna yi suna cin fanken.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull