Baqeer complete - Chapter 37
Baqeer complete Chapter 37: Baqeer complete Chapter 37. ***** Da Asiya ta kafa naci sai da Bello ya ware wasu kuɗi daga cikin kuɗaɗen daya ajiye a bankin…
2,762 words
***** Da Asiya ta kafa naci sai da Bello ya ware wasu kuɗi daga cikin kuɗaɗen daya ajiye a bankin saboda sayen fili ya fara gini tunda gashi Allah yasa zai fara ajiye iyali dole ne yayi planning yadda rayuwarsu zata kasance. A cikin kuɗin ne ya cire wani abu yayi mata sauran kayan gadon da iyayenta suka kasa yi mata saboda takurar da tayi mishi ta hanashi sakat wayar safe daban ta yamma daban ta dare daban duk dai akan ya daure ya sayi sauran kayan ɗakin don kamarsu bai dace ace an shigo gidansu aga ɗaki ɗaya kawai suka iya shiryawa ba. To da yake shima ɗan ƙaryar ne irinta da tayi mishi bayani sai yaga fa eh lallai haka ne shine ya cire kuɗin aka sayi sauran kayan gadon da za'a saka a ɗakunan biyu da suka rage, haka shi ya sayi gas cooker dasu fridge da freezer har da washing machine aka zuba a gidan. Ai kuwa kan Asiya sai ya ƙara girma ta dinga iyayi tana fi'ili ita a dole ta kerewa sa'a ta shiga sahun manya a yanzu. Haka zata kalli Habi ƙanwarta ta sheƙe da dariya tace "ke kam ina ga ai sai dai kiyi amfani da gawayi don banga alamar wanda kike kulawa zai iya yi miki hidimar arziƙi irin wannan ba." Ita dai Habi ko kulata ma bata yi don tace ɓata lokaci ne tsayawa ta biyewa Asiyar suna rigima akan abinda tasan ba lallai ne ya ɗore ba.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
"
Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA TARA*
{49} Tunda Umma ta tafi yake zaune yana lissafi, wayarshi ya janyo jiki a sanyaye tunda har yanzu babu wanda yayi mishi magana, ga mutumin daya amshi zanen nan ya biyashi har yanzu bai sake yi mishi magana ba shima. Saƙo ya gani ta shigo ta direct message ɗinshi buɗe wa yayi don yana da tabbacin Salim ne. Business account ɗin daya gani ne yasa ya buɗe cike da mamaki don daga yanayin dp ɗin ba masu ɗinki bane, yaso shiga cikin profile ɗin su yaga me suke yi sai dai idanuwanshi ne suka gane mishi saƙo ana tambayarshi akan sketch na ɗinki, iska ya furzar sannan ya danna reply akan guda nawa suke so, waya ce ta shigo ta IG ɗin ganin daga su ne yasa ya ɗauka, namiji ne mai maganar nan ya sanar dashi a Abuja suke amma suna da branch anan Kano, zasu turo representative ɗin su yaga inda yake saboda gudun kada su sayi abinda ya watsa gari dole su tabbatar ba zai cucesu ba sannan ba zai bawa wasu zanen da yayi musu ba, don haka suke son sai yayi signing contract sannan su dinga siya. Kai tsaye yace babu matsala shima baya son yin business da mutanen da bai sani ba, mutumin yace "Sai dai mu muna neman ragi gaskiya akan zamu dinga siyan ko wane ɗaya akan naira dubu talatin, saboda yanzu abubuwan ba sauƙi garesu ba, suna kuma son su dinga fito da styles kala-kala wanda zai ƙara inganta business ɗin su." Baqeer yayi ɗan jim kafin yace "No, gaskiya sketching is not that easy sannan ku idan na sai da muku ya zama naku ya tashi daga nawa." "Mun sani amma muna so kasan mu business ɗin gaske muke son yi da kai, muna da branches a kusan garuruwa goma, sannan mu ba ƙananun mutane bane contract zamu yi duk wata zaka dinga bamu kuma duk wata zamu dinga biyanka, in muka yi requesting sketch 20 a watan nan zamu biya ka naira dubu ɗari shida." "In kuma baku yi ba fa?" Baqeer yayi tambayar jin ana neman dauke mishi hankali da abinda ya kamata ya sani, "Well in har bamu yi ba still zamu baka dubu hamsin sai mu ƙara a cikin contracts, ka duba business account ɗin da nayi maka magana dashi." Nan Baqeer ya buɗe ganin yadda suke da mabiya sosai da yadda abinsu ya bunƙasa. Ya sani sarai babu yadda zai yi tunda bai iya yanka da ɗinki da kanshi ba, zai amince dasu sai dai baya da tabbas akan zai dogara dasu. "Okay, sanda zaku turo wani sai muyi arranging inda zamu haɗu." Nan suka yi sallama ya kashe, shiru Baqeer yayi yana bin account ɗin su da kallo sam zuciyarshi bata gama yarda dasu ba kawai dai babu yadda zai yi shi yasa ya amince da hakan. Har zai kifa wayar sai kuma ya dubo sunan Zainab, so yake yi yaji ya take sai dai bai san me zai ce ba, shiru yayi yana tunani, tunowa yayi da ƙofarin da tayi mishi ne yasa yayi mata text, "All good?" Ya tura tare da kallon wayar yana tunanin zai ga reply sai dai shiru babu komai.
**** Zainab ce ta kalli Nabeela tace "Haka Mummy tace?" Nabeela dake share ƙwalla ta ɗaga kai alamar to, da sauri ta fita daga ɗakin ta nufi falo. Mummy na zaune suna hira da Daddy ta zauna a gefen ta tace "Mummy don Allah ki yiwa Aunty Nabs magana tace ke kika ce ta tafi?" Fuska sosai ta tamke tace "Auta ƙyaleta gwara taje ta zauna kusa da Inna tana buƙatar taimako." Daddy ne ya kalleta yace "In ba don Nabeela ba a gidan nan kina tunanin komai zai tafi daidai? Kika jure wannan sai Nabeela ce kullum ke laifi?" Zeey ce ta turo baki tace "Ni dai kullum nice mai hali mara kyau." "Yanzu amsa min ɗin da kika yi a haka shima daidai ne kenan? Nabeela kuwa ko da wasa baza tayi magana haka ba ko da bare ne ya mata magana kuwa bare." Mummy ce tayi saurin cewa "Don Allah ka bari Senate, ita dai bata isa tayi magana ba sai an ce maganar ma bata yi daidai ba?" Kai ya kawar ya ɗauki jarida bai tanka musu ba, yana murmushi don shi kam yasan lamarinsu sai a hankali sam Mummy bata taɓa ganin laifin Zeey, kafaɗarshi ta dafa tace "Ranka ya daɗe ba dai fushi kayi ba? Kai ya girgiza yana kallon Zeey yace "Sai kuyi tayi, sannan a halayen ta kuma bata tunanin bin umarnina ta auri namijin da nasan zai jure halayyarta." Tana jin haka tayi maza ta tashi tace "Daddy na manta ina da abun yi a ɗaki." Ta fara tafiya da sauri sai data kai ƙofar fita daga falon ta waigo tace "Mummy sorry amma bazan barta ta koma ba gaskiya, Daddy sai da safe." Ta waiga da sauri, Kabir ta gani a tsaye da alama ma tsayawa yayi don yaji me suke cewa, wani banzan kallo yayi mata yace "Akan me bazata koma ba? Ko ke ce kika haifeta?" "Kaga don Allah ka bari, kai wai a duniya ba zamu zauna lafiya ba? Neman faɗa har da wanda bai shafeka ba?" Ranshi ne ya ɓaci ganin shi Nabeela ke takurawa a gidan nan don yanzu saboda ita zaman gidan ma ba sosai yake san yin shi ba yayi ƙwafa sannan ya juya, kallonshi tayi ta harari bayanshi sannan ta bishi a baya tana cewa "Yaya K please kasan masu ɗinki irin professionals ɗin nan na mata?" Cak ya tsaya sannan ya kalleta yace "Ɗinki ina wanda yake yi miki na wurin Mummy?" Ta ɗan yi kif da ido sannan tace "Ba ni zanyi ba sannan bata son na Mummy wani take son gwadawa." Jim ya ɗanyi sannan yace "Akwai amma sai na yiwa Najib…….." ai kafin ma ya ƙarasa tace "No, kada ka damu nama tuna." Ta shiga ɗaki tana cewa "Rabani da abokinka yanzu in Baqeer ya sani am sure.." sai kuma tayi shiru kafin tayi ajiyar zuciya a fili tace "Always getting ahead of yourself, a wani waje Baqeer ya ajiyeki?" Kan gado ta faɗa ta ɗauko wayarta, nan da nan ta zaro ido tana ganin tambayar da yayi mata, bata san sanda ta saki wani irin ƙara ba tana bubbuga ƙafa kai kace wani kyauta aka bata. Ta fito daga ɗakin da gudu ta nufi ɗakin Nabeela wacce ke zaune ta saka akwati a gaba, janye akwatin tayi ta riƙo hannunta tace "Aunty Nabs yau shi ya fara nemana." Da mamaki take kallonta tace "Wa?" Kai ta girgiza tana daidaita nutsuwarta tace "Mu bar wannan maganar, don Allah me yake nufi idan namiji ya miki text yace All good?" Ɗan yatsuna fuska Nabeela tayi tace "All good? Har wani kalma ne mai ma'ana daban?" Saketa tayi tace "Share baza ki gane ba," tayi maganar tana fita, kan gado ta faɗa tayi rub da ciki sannan ta kira Baqeer, a lokacin shi kam har ya gaji da jin haushin kanshi da saƙon daya tura yana ganin gashi nan ya janyowa kanshi rashin reply ai, wanda a ganinshi bada kanshi ya gama yi. Ɗauka yayi ba tare da yace komai ba, ita ma bata ce komai ba har kusan sakan bakwai sannan yayi ɗan gyaran murya ita ma gyaran muryar tayi suka sake ɗan shiru kafin ta sake gyaran murya, "Mura kike yi?" Ya tambaya ganin abun nata ba irin nashi bane." "Matsalar a zauna kusa da masu mura kenan sai su sa maka before you know it." "Wa ke mura?" Ta dan rage murya tace "Kai mana Ya Baqeer ka manta kai ka fara gyaran murya?" "Don nayi gyaran murya sai akace kuma mura nake yi?" Ta ɗan kwantar da kanta akan pillow tace "Kuma fa haka ne to ba mura nake yi ba ciwon GM nake." Yanayinshi ne ya canza zuwa na damuwa yace "GM? Me kenan?" Ta dan yi jim sannan tace "G for gyara, M for murya?" Duk yadda Baqeer yaso ya daure kasawa yayi kawai yaji dariya tazo mishi, wani irin shauƙi ne ya dinga ratsa sassan jikinta babu shakka ƙaunar da take yiwa Baqeer ta riga ta gama bin jini da jijiyarta. Yatsa yasa ya sosa kunnenshi ya daidaita kanshi sannan yace "Umma tazo yau." Tace "Haba? Kai masha Allah kace yau cikin farin ciki kake." Yace "Uhmm!" Ta dan ja bargo wani tunani na shiga ranta tace "In tambayeka?" Yace "Eh!" Ta ɗan sake yin shiru kafin tace "Ka yarda dani?" Da mamakin kalamanta yace "Kamar ya?" Kai ta girgiza tace "Kawai tambaya ce." Shiru yayi bai amsa ba, jin haka yasa tace "Ina Dada ta?" "Ta kwanta," ya faɗa yana kallon wayarshi, so yake ya sanar da ita zancen contracts amma yana tunani gwara ya bari yayi signing tukunna don ya kula tafi kowa farin ciki in taga abun alkairi ya sameshi to gwara ya jinkirta sanar da ita har sai ya tabbatar da contracts ɗin . Sun ɗan yi shiru kafin yace "Yace sai da safe." Har zai kashe tayi saurin cewa "Ya Baqeer?" Tsayawa yayi sai dai yanda ta kira shi yasa yaji dim ta ɗan rage murya sosai, cikin wani yanayi tace "Baka ji amsar tambayar da kayi mini ba." Kasa amsata yayi saboda yanayin daya shiga jin yadda tayi maganar, nan ta cigaba "All good, sannan thank you for asking." Wani abu ne ya ɗan tokareshi da sauri ya kashe wayar yana mamakin abinda ke faruwa dashi, Zeey kuwa iska ta furzar da karfi tana shafa sumar kanta. **** Umma tana dawowa ta tarar da Jamila da Abu a zaune yau yan haɗin kan nasu ya tashi dan suna zaune tare suna hira, tasa key zata buɗe ƙofar ɗakinta sai taji ƙofar a buɗe, da mamaki ta kallesu gani tayi sun kawar da kai, ta ciki aka buɗe ƙofar da ƙarfi wanda ya sata tsorata kaɗan ta ɗan yi baya. Badaru ne ya banƙare kofar ya fito yana kallonta sheƙeƙe yace "Eh dama ni nasan ba mutunci ne dake ba kwanan nan, yanzu ko kunya da imani baki ji ba kika yi miya kika juye tas kika kaiwa tsohuwa ni da yake baki ɗauke ni da daraja ba baki ajiye mini ba? Bayan ke kin san Jamila ba lafiya ne da ita ba bazata iya girki yau ba?" Mamakin kalamanshi ne suka rufeta, ba yau ta saba yin miyar nan ba menene suke neman maida abun wani zance daban? Sannan yaushe Jamila ta fara ciwo? Kafin ta gama tunani sai ji tayi Abu na cewa "Sannu Jamila, Allah dai ya baki lafiya." Mallam kayi hakuri ni wallahi naso yin girki kuɗi ne sam babu a hannuna." Kallonta ya sake yi yace "Allah wadan naka ya lalace wannan mugun halin naki shi yaranki suke kwaikwaya shi yasa rayuwar auransu ba daɗi kuma wallahi ni da siyan kujeru ke da saidawa sannan ke da cinye kuɗin." Rai a ɓace ya wuceta ya shiga ɓangaren Jamila, Fatima ciki kawai tayi don ita ta ɗauka ma zancen fili zai yi to in dai wannan ne ita kam ko a jikinta yaje can su ƙarata, da can da take miyar ai bai taɓa sa ido ba sai yanzu, ita fa duk wani abinshi yanzu ya daina hata haushi.
**** Yau Dada haka kawai ta tashi da ciwon ƙafa da take fama dashi da kuma ciwon hakarkari wanda yawanci ciwonta ne tana fama dasu dama lokaci-lokaci balle in sanyi yazo to fa dama sai tayi su kamar sau biyu ko uku, tun dare ta fara ji tasha magani amma bai tafi ba, kwance tayi a ɗaki sai dai hankalinta ne ya kai kan Baqeer tana ganin ya kamata fa yaci abinci, haka ta miƙe da ƙyar ta fito ta nufi ɗakin shi yana zaune yana zana riga da skirt na mace ɗinkin zuwa mishi yayi bayan yayi sallar asuba to baya son ya gudu daga kanshi ne yasa ya ɗauko don ya zana, shigowa tayi sai dai jiri ta fara ji yana neman kamata, a rikice ya taimaka mata ta zauna yana tambayar meke faruwa, Dada kam ido kawai take lumshewa da alama wannan karon bayan ciwukanta har da wani yanayi take ji a zuciyarta. Baqeer idanunshi ne ya cicciko da yaga ya kasa bata wani gudunmawa daya kamata, asibiti ya kamata ayi da ita amma taya zai iya? Cikin sauri ya kira Salim sai dai wayarshi ma a kashe take, ya sake kira nan ma haka, ganin yadda Dada ke sake bin katifa yasa hankalinshi ƙara tashi yanzu in ya kira Umma ya tabbatar ba lallai ma Baba ya barta tazo ba, number Zeey ya kira sam ba tare da wani dogon nazari ba. Zeey kuwa a lokacin Mummy bata daɗe da barinta a ɗaki tana bacci ba don akwai inda zasu je amma tace bacci take yi, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka cikin bacci tana neman maida ita silent don yanzu ma tsautsayi ne yasa tabar wayarta a ringing. Wayar ta kalla sosai ganin sunan dake jiki, da sauri ta ɗaga ganin zata katse. Baqeer hankali a tashe yace "Please in kina available ki taimaka mu kai Dada asibiti! Am really sorry." Ai bata tsaya nazari ba tace "Ganinan zuwa." Dirowa tayi daga kan gado duk ta rikice hankalinta gaba daya baya jikinta, kayan barcin bata canza ba ta saka dogon hijabin sallarta wanda yake har ƙasa kawai ta fito, ko Mummy bata tambaya ba tayi waje ta shiga mota zuciyarta da tunaninta sam basa jikinta.
Meya samu Dada? Meya faru? Tambayar da take mata yawo kawai akai kenan. Baqeer kuwa kusa da Dada yayi, cikin nishi take ce mishi "Baqeer babu komai kar ka damu zai daidaita."
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN*
{50}