Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 36

Baqeer complete - Chapter 36

Baqeer complete Chapter 36: Baqeer complete Chapter 36. Kallon rose ɗin dake hannunta Zee tayi ta saki murmushi tace "Muje muga Dad ɗinki?" Tayi maganar…

3,460 words

Kallon rose ɗin dake hannunta Zee tayi ta saki murmushi tace "Muje muga Dad ɗinki?" Tayi maganar tana rufe fuska sai kuma ta saki huci tace "Me kike tunani?" Cikin ranta tace "Yanzu kamar ni one sided love nake yi?" Tasa mayafi a kanta tasa rose ɗin a cikin jakarta, kan gadonta ta kalla yau Nabeela bata shigo ba, ta fito tana kiran mai aiki akan ta gyara mata, Mummy ce ta fito daga ɗaki ita ma da alama fita zata yi don ta shirya cikin lace tsadadde, rungumeta Zee tayi Mummy ta shafi bayanta tace "Baby ni kam kwanan nan lafiya kike? Kullum sai dai na ganki da kayan mu na gida?" Murmushi tayi tace "Ya zanyi Mummy? Ni kaina ban san ya aka yi na koma haka ba." Kuncinta taja tace "Yafi son kayan gida ne?" Cike da kunya ta shige jikin Mummy tace "Hmm duk da ban san yanzu ko ya canza ba." Kallon mamaki tayi mata tace "Kin san shine da?" Laɓɓanta ta haɗe tace "Labari ya banu." Tayi maganar tana juya kai, Mummy tace "Nima zan fita ne akwai abinda zan siyo Daddynki matar abokinshi ta haihu zan je barka." Kai ta ɗaga alamar to sannan tace "Aunty Nabs fa?" "Wallahi ban sani ba, bari naje kafin nayi yamma." Nan ta fito ita kuma ta leƙa Nabeela, tana kwance cikin bargo tana daddanna waya, Zeey ta buɗe tana kallonta tace "Aunty Nabs? Meke faruwa?" Kai ta girgiza alamar babu komai kafin tace "Kawai bana jin tashi ne yanzu." Maimakon tace wani abu kawai ta maida ƙofar ta rufe ta fito ta shiga mota, a hanyar fita mai gadi ke bata labarin yaron nan ya sake dawowa ya bashi kayan amma yace ba zai amsa ba. Shiru tayi tana tunanin me zata yi mishi, don duk ranar da Daddy yasan ana biyota har gida lallai ranta ne zai ɓaci. "Yaushe yazo?" "Mai gadi ya ɗan kalli waje yace ai bai ma dade ba don in na fita a guje ma zan ganshi." "Zaka tuna kayan da yasa?" Ya ɗan yi dariya yace "Shadda ce taji jiki daga ruwan sararin samaniya ta koma wata kalar daban." Ta kula neman magana mai gadin yake ji dashi hakan yasa tace "Bani kayan." Da sauri ya miƙa mata tasa a gefe sannan ta fita, da ɗan sauri take tafiya, a gefen wani saurayi tayi parking, kallon motar yaiy garin mamaki saura ƙiris ya faɗi ƙasa, da sauri ya riƙe gefen motar yana haɗiyar yawu yace "Roshni?" "Kana da sana'a ne?" Sumar kanshi ya fara shafawa yana ɗan gyara tsayuwa yace "Eh mai gidan mu nada shago." "Hmm da alama, hope ba satowa kayi ba?" Tayi tambayar tana nuna mishi ledar, yayi ɗan yi yaƙe yace "Roshni ya kike haka?" Fuska ta tamke sosai sannan ta miƙa mishi. Kamalu kamar zai yi kuka yasa hannu ya amsa, sannan ta kalleshi tace "Sata dai sata ce sai a canza hali." Tana kaiwa nan ta mayar da glass na motar tayi gaba, da kallo yabi bayan motar sam kasa motsi yayi, da ƙyar ya iya jan ƙafarshi zuwa gida, sam ya manta ledar dake hannunshi ya shiga. Abu ta leƙo waje don ta zubar da shara ta ganshi, sam bai ji maganar da take yi mishi ba yana tafe kamar ba shi ba, mamaki ne ya rufe shi tasa hannu ta riƙo ledar tana cewa "Kamalu lafiya kake ina magana ba ka ji?" Tayi maganar tana riƙe da ledar, jan jikin da zai yi sai ledar ta yage, atamfa ce ta faɗo, ido ta zaro da sauri tace "Kamalu ina ka samo ta? Ba dai a shagon Babanka ka ɗauko ba?" Sai a lokacin ya kalleta ya kalli atamfar, Abu da sauri ta ɗauka ta ɓoye tayi ɗaki da ita ta samu wuri ta ɓoye a ƙasan gado, tabbas tun kafin ta janyo wa kanta da yaranta magana gwara ta ɓoye a inda ba za'a gani ba.

******* Yana zaune a ɗaki ya zuba wa wayarshi ido anya kuwa za'a dace? Kai ya girgiza da sauri ai komai haƙuri ake yi dashi ba zai yiwu abu kwana biyu ba jikinshi ya karaya, idanun ya ɗan runtse, Zee ya gano tana yi mishi smiling, shima murmushin yayi a bayyane nan ya ɗauko takarda ya fara zanen ɗinki, yana cikin yi yaji Dada tana lale lale da yar albarka. Kofar ya ɗan kalla yace "Da kullum sai tazo yanzu kuwa sai bayan kwana bibbiyu." Bai motsa daga inda yake ba sai dai hankalinshi gaba ɗaya yana waje, mamaki ne ya kamashi ganin tafi minti goma da zuwa amma har yanzu ko Dada bata ƙwanƙwasa mishi ƙofa ba, gani yayi haƙurinshi ya ƙare yasa ya wawwaiga ɗakin, kwanon da yaci abinci ya ɗauko ya gunguro kekenshi ya fito "Dada kina ina?" Abinda ya fara cewa kenan. Ido suka haɗa da Zee dake zaune akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta zuba mishi ido, gyaran murya yayi yace "Dada fa?" "Kawai?" Turo keken yayi zuwa cikin falon yana kallonta yace "Yaushe kika zo?" "Yaushe jikinka ya baka?" Kai ya kauda tasan tunda yayi haka ba zai amsa ba, tana murmushi tace "Faɗa mini Ya Baqeer in banzo ba kana damuwa?" Kallonta yayi nan da nan idanuwansu suka ɗan sarke da juna yana mamakin yadda mace bata kunyar magana haka. Kai ta karkatar tace "Baka yi?" Nan ma bai ce komai ba sai dai yanzu ya ɗan canza yanayin kallon da yake yi mata, neman juyawa yayi da sauri ta rike handle ɗin keken, hakan yasa ya tsaya, juyo da keken tayi inda zai ganta sosai tace "Baka bani labari ba kaje wurin J ɗin?" Kallon da yayi mata ne yasa ta gane me yake nufi tace "Ya plan ɗin school din?" Waya ya ɗauko ya buɗe mata page ɗinshi na IG mai ɗauke da sunan 'MOHBAQ' da yanda ya tallata abun, daɗi ne ya kamata da sauri tayi following ɗin shi, tace "Ko nasa kayan da aka ɗinka mini sai nayi pic daga wuya ne kasa sample?" Wani mugun kallo yayi mata, ita ma dama tayi ne don ta gwadashi, tace "Inyi?" Yanda yake mata kallo ne yasa ta shagwaɓe tace "Me kuma nayi? Ni sarkin laifi?" Kai ya kauda ranshi ya ƙara ɓaci wai tama san me take cewa kuwa? Langaɓar da kai tayi tace "In baka so ba gwara kace a'a ba da kayi shiru, menene a ciki?" Waigowa yayi yace "Na saki?" "Wai so nake yi ka sakani." Jan keken ya fara ƙoƙarin yi tayi sauri ta ƙara riƙewa tace "Naji na haƙura, shikenan? Amma fushin na menene daga tambaya?" Shima tambayar kanshi yayi fushin na menene? Anya Baqeer? Yayi soyayya da Asiya amma bai taɓa jin abinda yake ji akan Zeey ba bayan ya daɗe da ita ya kuma so ta kowa ya sani. Dada ce ta shigo falon hakan yasa ya juya, Zeey da kallo ta bishi tana murmushi.

******

Umma ce a ɗaki ta kalli takardun filin, zata kira Maryam ko Hadiza ta basu takardun su kaiwa Baqeer a samu a saidashi ya fara harkar sana'ar, ai hakkinshi ne tunda aiki yayi a masarautar garin Gombe aka basu kuɗi masu kauri wanda Badaru ya sayi mota dashi, ya ƙara faɗaɗa shagonshi shine da tayi mishi magana ya saya mishi fili 50 by 50, ta tabbatar filin darajarshi ta ƙaru, tasan zai isheshi yayi wani abun dashi, tunani ne yazo mata ai ko itace tace zata je wurin Dada ba zai kawo komai ba tunda bai san a inda Baqeer ɗin yake ba balle ya kawo tana can. Da wannan shawarar taji hankalinta ya kwanta, turaren wuta ta fito ta hura ta koma ɗaki tana tunanin Allah yasa har sai ta kaiwa Baqeer an saida filin sannan hankalinshi zai kai wurin.

***** Nabeela ganin babu kowa a gidan sai ita yasa ta fito ta wuce ɗakin Kabir, shima baya nan kwanciya tayi akan gadon ta jaa bargonshi tana shinshinar ƙamshin shi har bacci ya ɗauketa, sanye take daga ita sai rigar bacci shara-shara. Kabir ne ya shigo ɗaukan abu da mamaki ya hango mutum akan gadonshi, ƙarasawa yayi ya ɗan ɗaga blanket ɗin. A tsorace yake kallonta, me take yi anan? Nan da nan hankalinshi ya tashi, juyawa yaje zai yi ta riƙo hannunshi tace "KB na!" Zare hanunshi yayi yace "Meye hakan kike yi? A ɗakina? Baki da hankali ne?" Tashi tayi hakan yasa jikinta ya bayyana cikin kayan baccin, ta dawo gabanshi a tsorace yace "Me kike yi hakan?" "Kabir plz ka maidani halalinka, I really need you." Fita yayi daga ɗakin ranshi a matukar ɓace, fitowa tayi idanuwanta sunyi jaa suna neman zubar da kwalla.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

" *Ayusher Ce* *Da* * *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS*

{48}

Fitowa tayi daga ɗakin tana share hawaye suka kusan yin karo ita da Mummy sai sannan ta dawo cikin nutsuwarta sam bata san Mumy ta dawo ba. Ganin Mummy tsaye tana yi mata wani irin kallo yasa gabanta faɗuwa sai dai ta dake ta ƙaƙaro murmushi tace "Mummy har kin dawo?" Wata uwar harara Mummy ta doka mata tace "Uban me kika je yi ɗakin Kabir a haka da wannan shigar? Wallahi Nabila ki kiyayeni, zaki tattara ki bar min gidana ki koma wajen Inna don ba zaki ɗaukar min magana ina zaman lafiya ba, ai dai kin san nace miki a'a amma da yake ba jin maganata kike yi ba shine kullum sai kin kai ƙafa ɗakinshi ko?" Cikin jin haushin Mummyn tace "To ni me nayi? Komai nayi sai kin yi min faɗa kamar ba ƴar uwarki ba?" Da mamaki Mummy take kallonta tace "Ni kike yiwa magana a haka Nabila sai kace wata sa'arki, to wallahi tafiya zaki yi bazan iya ba, haka kurum ba zaki janyo min magana ba tunda ke baki san abinda ya kamata ba." Fuuu Nabila ta wuceta a tsaye a wurin tana faɗa ta shige ɗakinta, da kallo Mummy ta bita tana mamakin wai ita yau Nabila ke yiwa rashin kunya haka kamar wata sa'arta akan ta faɗa mata gaskiya. Ƙwafa tayi ta wuce ɗakinta tana jaddada dole ne ma Nabila tazo ta bar mata gidanta idan ba haka ba zata ɓallo musu ruwa tayi musu sanadin abun kunyar da basu isa su warware ba.

*****

Da sassafe ta shirya yau gidan Dada zata je ta yini, da ƙyar Mallam Badaru ya barta ma taje don da cewa yayi me zata je tayi? Sai da tace mishi "Dada ce fa nace maka zan je na gani mahifiyata ba wata can daban ba" sannan ya amince. A cikin kuɗin da Baqeer ya aiko mata ne tayi cefane tayi musu soyayyiyar miya da zata jima bata lalace ba, sauran abinda ya rage kuma ta saya musu kayan shayi dasu sabulun wanka dana wanki sai omon wanke-wanke, dama ta saba yiwa Dada irin wannan sayayyar miyar ta kai mata duk lokacin da zata je ta duba ta don ma ba kasafai Badaru ya cika barinta taje ba sai kuma ya sameta ba mai yawan son tashin hankali bace don haka take haƙuri duk da ba daɗin hakan take ji ba ace suna gari ɗaya da mahaifiyarta amma sai ta ɗauki wani tsawon lokaci kafin taje ta gaisheta. Sai data duba jakarta ta tabbatar takardar filin na nan a inda ta ajiyeta kafin ta ɗauki ledar kayanta ta fice. Sallama tayi wa su Abu da Jamila wanda ke ta gulma ganin gana soyayyar miya, da sun san Baqeer ke bata kuɗi yanzu kuwa sun tabbatar kuɗin kujerunta tasa a gaba take miya, ita dai ta fita tana jin ɗokin son sake saka tilon ɗanta a idanunta bayan wani lokaci da suka ɗauka ba suga juna ba sai dai suyi magana ta waya abinda bai taɓa faruwa ba kenan a tarihin rayuwarsu tun daga haihuwarshi har zuwa girmanshi sai fa yanzu da tijarar Mallam Badaru ta raba su. Ƴar tafiya kaɗan tayi ta samu adaidata sahun daya ɗauketa har ƙofar gidan Dada. Da sallama ta shiga gidan fuskarta ƙunshe da fara'a ta tsantsar farin cikin daya kasa ɓoyuwa. Daga cikin ɗaki Dada tace "Muryar wa nake ji kamar ta Fatima?" "Nice Dada" ta amsa tana nufar ƙofar ɗakin. Cikin barci yaji kamar muryar Ummanshi suna gaisawa da Dada, ai kuwa zumbur yayi ya miƙe zaune yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi. Wheelchair ɗin shi ya janyo ya daddafa ya hau kai ya zauna yana garata, wai kuma sai da yaje baƙin ƙofar ɗakinshi sai yaji ba zai iya fita ba, haka nan yaji tausayin kansu shi da Umman ya kamashi, yasan wannan tsawon lokacin da suka ɗauka a mabanbanta wuri ba ƙaramin dauriya da haƙuri tayi ba. Kasa fita yayi ya tsaya daga nan yana jin sautin muryar Umman da yayi kewa iya kewa. Ita kuwa Umma suna gaisawa da Dada hankalinta na wajen ɗanta kara da kawaici ne kawai yasa ta kasa tambayar inda yake sai kallon ƙofa take yi a kaikaice tana zuba idon ganin ta inda zai ɓullo. "Yana ɗaki watakila bacci yake yi tunda kika ga bai fito ba" Dada tace mata don tana lura da yadda take satar kallon hanya tasan Baqeer idanunta ke kwaɗayin gani. Kunya ce ta kama Umma ta sunkuyar da kanta ƙasa ganin Dada har ta fahimci ɗokin son ganin Baqeer da take yi. Sai ta kasa cewa komai sai da Dada tace "Ki shiga ki ganshi mana ai ya samu sauƙi fiye da lokacin da ya dawo nan, ko daga walwalar da ya samu ma bare da yarinyar nan Zainabu ta haɗashi da likitan ƙashi yana zuwa can asibitinsu yana dubashi." Kallon Dada Umma tayi tace "Zainab ɗin na yawan zuwa nan ne?" Tace "Ai bata kwana biyu bata zo ba yarinyar kirki mai yawan barkwanci da sanin darajar mutane, da badan ita ba Baqeer da har yanzu banajin zai dawo daidai." Jinjina kai Umma tayi har yanzu ta kasa daina mamakin jin wai Zainab ce take yawan kawo musu ziyara har ma da taimakon da ta yiwa Baqeer bayan tasan ƴar tsamar dake tsakaninsu wanda abu har iyaye ya haɗa, wanda tashin hankalin da akai a shekarun baya, sai dai ganin yanzu sun girma kila shi yasa suka zubar da duk wasu abubuwa na yarinta. Tashi tayi ta shiga ɗakin nashi sai ta ganshi daga bakin ƙofa, haka nan taji wani irin rauni ya saukar mata kawai sai ta fara hawaye, tana son Baqeer a cikin ƴaƴanta tana kuma tausaya mishi saboda dattijon yaro ne da bai ɗauki rayuwa da girma ba, mai mayar da damuwar wasu tashi shi yasa ya zame musu bango abun jinginarsu daga ita har ƴan uwanshi, ya ɗauki dukkanin wasu damuwoyin su ya mayar dasu nashi, bai taɓa bari sun yi kukan rashin wani abu ba bakin gwargwado yana kyautata musu. Tsugunnawa tayi a gabanshi ta riƙo hannayenshi a cikin nata tace "Ya jikin naka?" Ɗaga mata kanshi yayi alamun amsawa don haka nan yaji bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa furta ko kalma ɗaya. Cikin rawar murya tace "Ina can ina ta fama da kewarka kai kana nan kana cigaba da rayuwarka cikin kwanciyar hankali." Hannu yasa ya share mata hawayen dake ta faman zuba daga idanunta sun kasa tsayawa tunda ta ganshi. "Nima ina cikin kewarki Umma nayi kukan rashinki a kusa dani sau babu adadi, sai dai nasan in na cigaba da zama cikin damuwa sai kin fini damuwa." Tausayinshi ne ya ƙara kamata ta ɗan yi murmushi na ban tausayi. Zama tayi suna hirar sai tambayarta lafiyarta yake yi tana ce mishi tana nan ƙalau sai dai ya kasa yarda don sai yaga gaba ɗaya ta canja mishi, sai yaga kamar walwalarta ta ragu shi idan ba idon shi nema ke faɗa mishi ƙarya ba da sai yace har ramewa yaga tayi. Sun jima a ɗakin kafin ta turashi su koma wajen Dada da bata katse musu hira ba ta ƙyalesu su ga na sosai don tasan sun yi kewar juna. Yau yini suka yi cikin farin ciki da annashuwa bare da Umma ta dafa musu shinkafa suka ci da miyar data kawo musu sai Baqeer yaji kamar lokutan baya da suke tare a gidansu da sam baya iya cin girkin kowa idan ba na Ummanshi ba shi yasa ko ba ita bace da girki kullum ne sai ta girka mishi nashi abincin daban don a cewarshi su Abu basu iya girki ba baya iya sakewa yaci abinci ya ƙoshi idan su suka dafa. Takan daɗe bata je taga Dada ba amma duk ranar da taje bata barin gidan sai tayi mata kwalema ta share kowane lungu da saƙo na gidan ta goge na gogewa ta wanke na wankewa, kyakkyawan gyara take yi mata irin wanda za'a kwana biyu gidan bai haɗa datti ba. Sai data gama duka waɗannan aikace-aikacen don har wankin kayan sakawar Dada sai da tayi sannan ta fito da takardar filin ta miƙawa Baqeer. Karɓa yayi yace "Takardar miye wannan ɗin Umma?" "Kai dai ka buɗe ka gani mana" tace mishi. Sai da ya buɗe sai yaga takardar filinshi ce dake wajen Baba. Ɗan yamutsa fuska yayi yana kallonta yace "Ki mayar mishi da ita Umma don bana buƙata." Kallonshi take yi itama ta kuwa ɓata rai tace "Bazan mayar mishi ba domin kuwa fili dai naka ne sunanka ne a rubuce a jikin takardar ba nashi ba, sannan da kuɗin ka aka saya bashi ya saya maka ba to na miye kana da buƙatar kuɗin don ka gina rayuwarka sai kace baza kayi amfani da kadararka ba bayan amfanin ajiye kadarar kenan."Juyawa tayi ta kalli Dada sai tace "Takardar filin shi ce daya saya na kawo mishi a saka a kasuwa idan Allah yasa aka dace da samun masu saye ba sai yayi amfani da kuɗin ya biya kuɗin makarantar koyon ɗinkin da yake son shiga ba ga sayen keken ɗinkin tunda yace dole sai dai yayi amfani da mai aiki da wuta wanda baya buƙatar sai ya takura ƙafafunshi wajen taka keken da dai sauran ƴan matsaltsalun daka suka mishi." Dada tace "Haka ne," tana jijjiga kai "Ai daɗin sayen kadarar a ajiye kenan dama." Yana jin su sai dai ya kasa yin musu dasu duk kuwa da yadda baya son karɓar filin, shi duk wani abu daya danganci Baba ma ba son shi yake yi ba shi yasa bai yi wani farin ciki da ganin takardar filin nashi ba dashi a mance ma ya manta yana da wani fili don tun lokacin da aka saya takardun na wurin Baba ba kuma su ƙara yin maganar fiin dashi ba. Dada ya miƙawa takardar filin yace ta ajiye a wurinta don shi ko ganinta ma baya son yi, haka Umma ta ƙara gyara gidan tasa turaren wuta. Sai can da yamma sannan tayi musu sallama zata tafi, sai yaji sam baya son rabuwa da ita da da hali da ya bita sai dai yasan a yanzu zaman gidan baba yafi ƙarfinshi tunda dai shi da kanshi ya kore shi yace ya bar mishi gidanshi saboda ƙaddarar rayuwa ta afko mishi, abinda yafi yi mishi ciwo kenan a duk abinda ya sameshi yadda Baba ya juya mishi baya tamkar bai taɓa sanin shi ba kawai saboda ya gama yi mishi amfani, har da wannan yasa ya ƙuduri aniyar in har ya cigaba da rayuwa da izinin Allah sai Baba yaga yadda Allah zai yi dashi, akanshi zai san cewa nakasa ba kasawa bace, sai yayi alfahari da abinda zai zama don ba zai taɓa zama komai sai anyi mishi ba alhalin Allah ya barshi da ranshi da lafiyar da zai iya tashi ya nemi na kanshi. Har bakin titi ya rakata sai da ya tare mata adaidata sahu ta shiga har ma ya biya kuɗin a cikin sauran kuɗaɗen zanen shi da suka yi ragowa sannan suka yi sallama, bai bar wurin ba sai da adaidaitan tayi mishi nisa ya daina ganinta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya koma gida yana jin kewar Umman ta sake kamashi, fatanshi dai Allah yayi mishi arziƙin da zai ɗauke Umma ya mayar da ita kusa dashi don yana da burin rabata da zaman gidansu wanda bata tsintar komai a ciki sai kayan ɓacin rai.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull